Showing 33001 words to 36000 words out of 65015 words

Chapter 12 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

9

an tabbatar Sharifah mutum ce amma basu gama yar

da ba.

Sharifah ta dube su sai ta yi murmushi ta ce " Su Nana manyan mata."

Ta wuce ta bar su anan a jikin mota su na makerketa. Nana ta fusata ta figo Maryam daga bayanta inda ta labe.

Ta ce " munafukar Allah sai ki labe a bayana sab

oda ke 'yar karama ce, ni kadai ake kullata gashi nan ta ga baqina har da wani habaici take yi min. Muddin ka ga Fatalwa tana habaici akwai magana kenan nan gaba. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Shikenan na ga ta kaina."

Maryam ta yi dariya ta ce "

ance ba fatalwa ba ce ba fa mutum ce an tabbatar da hakan."

Haushi ya sake rufe Nana ta ce " ai kin tabbatar da mutum din ce amma kika gudu kika buya a bayana. Ni da yake barkekiya ce babu in da zan labe ni ake gani ga shi nan ta kullace ni."



Su ka hau kan bene ofishin lauyoyi, Nana ta zo wajen babban yayanta Bar. Inuwa Ahmad ta rako Maryam zasu tattauna akan wani case da Maryam Alqali take so ta shigar.

Anan aka sake yin arangama da Sharifah tana zaune a reception itama tana jiran lay

i ya zo kanta za ta ga lauyanta Bar.Inuwa Ahmad yayan Nana Ahmad ba tare da kowannensu ya sani ba. Ashe waje daya su ka zo an sake cakuduwa.

Nan ma suka yi turus suka ji kamar su koma amma ba hali saboda Sharifah ta tsare su da idanuwan nan na ta m

asha Allah manya-manya. Ga kujerun da za su iya zama dole sai a kusa da Sharifah ne. Da alama yana ganawa da wasu mutane a cikin ofishin, dan haka dole su jira.

Kallon da Sharifah take yi mu su ya wuce na mutane dan ba ta ko qiftawa. Sun kasa gane

dalilin wannan tsare su da idanuwan da ta ke yi.

Maryam ta sake daka tsalle ta koma ta maqale a bayan Nana, dan tafi ta tsawo da qiba da fadi, Idan ta labe a bayanta baa hango ta ko kadan, takaici ya kara kama Nana. Ta shiga zulumin shin ta je su gai

sa da Sharifah ko itama ta share ta su kalli juma kawai.

Su na tsaye basu zauna ba duk da tayin da sakataren yake ta yi musu akan su zo su zauna amma suka ki zama. Su sun san dalilin da ya hana su zama, tsoron Sharifah ne.

Ana cikin wannan hal

i ne sai mutanen cikin ofishin suka fito, Sharifah ta tashi ta shiga sannan su Nana suka samu damar zama. Nana da Maryam sai fada ake yi saboda labewar da take yi a bayanta, Nana ta ce ta daina yi ma ta haka. Maryam ta sha aradu muddin ta ga abin buya wall

ahi sai ta buya a bayanta kuwa.

Sharifah ta dade a cikin ofishin Barista, su na ta tattaunawa da shi da alama case dinta babba ne. Ta fi awa guda sannan ta fito, har Nana ta shiga fargabar ko dai Sharifah ta bace tare da yayanta, ta ji kamar ta je

ta leqa ta gani.

[3/1, 12:30 PM] Jamila Umar Tanko: 3

Sharifah ta fito daga ofis bayan ta gama, ta same su a zaune, ta kalle su suka kalle ta sannan ta fita. Su Nana ba su ji dadin wannan abinda ya faru ba, ya kamata ace sun yi ma ta magana duk da i

tama ba ta yi mu su magana ba ai amma tana da dalili tunda sun dauke ta fatalwa zata ji tsoron ta yi mu su magana don kada su baje da gudu. Sai dai sun rasa abinda za su zaba shin ita ce ko fatalwa ce?

Su ka shiga ofishin Barista da sauri bayan sun yi

ma sa sallama, ko gaisawa basu yi ba Nana ta shiga jero masa tambayoyi.

" Yaya ka san wannan matar ashe, wacce ta fita yanzu?"

Ya ce "kwarai kuwa mun dade tare nine lauyanta duk da sai daga baya ta dawo wajena bayan ta gama shan wahala da was

u lauyoyin."

Nana da Maryam su ka hada ido sannan suka sami waje suka zauna. Nanah ta sake cewa "Yaya ka ce kun dade tare ko?"

Ya harare ta ya ce " ina ruwanki da mutanen da su ke aiki tare da ni ne? Menene matsalarki? Kin santa ne?"

Na

nah ta gyara zama ta ce "akan me ake yin shari'a da ita? Ita ta kai kara ko ita aka kai kara?"

Wannan karon sai ya qi ba ta amsa, ransa ya baci har sai da fuskarsa ta nuna.

Ya ce "ku fadi abinda yake tafe da ku kawai,babu ruwanki da case din wa

su."

Maryam ta gaishe shi sannan ta fara bayani. Shi kuma ya na sauraronta.

Su na fitowa Samha suka kira a waya, su ka shaida ma ta sun hadu da Sharifah a ofishin lauya amma sun kasa yi ma ta magana kuma har ta gane su na jin tsorona har yanzu.

Samha ta nuna bata ji dadi ba, basu kyauta ba. Sharifah a halin yanzu soyayya take bukata da kulawa, saboda ta rasa kusan kowa na ta, ta rasa komai.

Duk da ba ta kammala ba ta labarinta ba amma alamu sun nuna haka, kowa ya guje ta saboda

an ganta da wahalar yara. Game da shari'ar ce ma baa san ko da wa suke yi ba. Shin Shariqah take nemowa hakkinta ne bayan ta rasu ko wani zalumci aka yi ma ta daban?

Nanah ta na dorawa Maryam laifi, Maryam na dorawa Nanah laifin cewa ita ce ta f

ara razana. Su ka yiwa Samha alqawari zasu sami lokaci su zo gidanta sai ta jagorance su zuwa gidan Sharifah su ba ta hakuri.



*** ***. ***

Samha na zaune sai ta ga kiran wayar Mamarta ya shigo wayarta, bayan ta amsa sun gaisa kam

ar yadda su ka saba.

Kwatsam sai Mama ta ce " Samha! Yanzu na ji wa'azi a radio yadda kika san da mu ake, game da Sharifah. Malam ya ce babu fatalwa a duniya, babu wanda ya mutu ya taba dawowa duniya. Mun yiwa yarinyar nan mummunan zato."

Samh

a ta ji dadi da jin kalaman da suka fito daga bakin Mama. Alhamdulullah.

Mama ta dora da cewa "idan kin sami lokaci ko ki je gidanta ko ta zo gidanki ki saurare ta ki ji meye matsalarta in sha Allah za mu taimaka ma ta idan bai fi karfinmu ba. Mahai

fiyarsu mutuniyar kirki ce bana manta alkhairan da su ka yi mana a lokacin aurenki. Lokacin da komai ya cabe min, ba mu da kudi su ne masu kudi babu abinda ba su dafa sun kawo gidan nan ba kowa ya ci ya sha ya koshi a taron biki. Bayan haka kuma kayan daki

nkin ma su suka siya mana abubuwa da yawa."

Samha ta gyada kai ta ce "kwarai kuwa Mama ban taba manta alkhairan bayin Allah nan ba. Mamarsu da su kansu, wallahi Mama ban taba mantawa da yiwa iyayen Sharifa addu'a ba har lokacin da ba ma tare, mun y

i zumunci a baya sosai dan ba zan manta lokacin da Babansu yake zuwa mata visiting a sakandire ba, dukka kawayenta sai ya raba mana kudi da littattafai. In sha Allah zan sami lokaci in je gidanta, dan na san a yanzu dai ba zata zo gidana ba, dan tana da z

uciya mun yi mata laifi akan abubuwan da mu ka yi zatonta da su. Ba ta ji dadi ba sam."

Su na kashe waya sai Samha ta ji hawaye yana ta sirnano ma ta na tausayin Sharifah.

Aliyu ya shigo ya iske ta na kuka, ya razana a tunaninsa ko mutuwa ma

aka yi. Dakyar dai ta iya bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Mama, da labarin da su Nana suka ba ta cewa sun ga Sharifah a wajen lauya. Tabbas Sharifa tana buqatar kulawa, tana bukatar wani da zai tsaya a gefenta ya na karfafa ma ta guiwa ko da baa

taimake ta da kudi ba.

Tambayar da Aliyu ya yi ita ce "ina mijinta yake yanzu ko basa tare?"

Samha ta ce "tare da kai fa ta ba mu labari, ba mu ji karshen labarin ba amma kamar da alama basa tare dan tana ta ambaton rashin kirkinsa. Ba ta taba

jin dadin zama da shi ba."

Aliyu ya tambaye ta "menene abin yi yanzu?"

Ta ce su Nana sun ce zasu sami dama su zo ta jagorance su zuwa gida Sharifah dan su ba ta hakuri. Ba su saka rana ba dai amma zasu zo.

Ya ce duk ranar da suka zo

ya bata izini ta je koda ba ya gari. Samha ta ji dadi ta yi godiya sosai.

Ta shiga tunano irin abincin da Sharifah ta fi so idan zasu je sai ta dafa ma ta ta kai ma ta. Dan ta san ita da yaran za su ji dadi a kalla zasu ga an kula su.



***

*** ***

Bayan wasu kwanaki ne qawayen Samha su ka hadu su dukka suka zo gidan Samha.

Anan aka tayar da magana aka dinga hayani, maryam da Nana dai an basu laifi an ce ba su kyauta ba akan tsoronta da suke ji bayan sun tabbatar ba fatalwa ba

ce yanzu.

Samha ta na daga kicin ta na tsomo baki. Ta yi musu girke-girke kala-kala daman ita cikakkiyar chef ce har ma tana da makarantar da take koyar da girki. Ta na son girki kuma ta iya girki, tabbas ta sha karbar kambun yabo idan aka yi gasa i

ta ke cinyewa. Sunanta ya yadu ya bazu a fadin birnin Kano da ma arewa baki daya.

Ashe da walakin goro a miya shiyasa dangin Aliyu su ka kasa yin nasara wajen tursasa shi akan ya rabu da ita ya auro wata. Ya qi fur ya ce shi sai Samha ita kadai. All

ah sarki ya ce haihuwa ta Allah ce, tunda likita ya tabbatar mu su shi da ita dukka lafiyarsu kalau lokaci kawai suke jira. Ga shi kuwa lokaci ya zo, bai yi garaje ba, ya yarda da cewa baa yiwa Allah shishshigi, baa yi maSa tilas. Allahu akbar! Mai yadda Y

a so a lokacin da Ya so.

Su Nanah su ka ci su ka yi haniqan har da ma su daukarwa miji da yara a 'yar roba, saboda dadin abincin ba zasu taba iya dafa irinsu ba.

Samha ta saba ganin hakan dan haka baya bata mamaki, dan duk wanda ya ci abin

cinta sai ya yi santi kuma sai ya so ya kaiwa masoyansa su ma su dandana.

Amma fa ba dukka abincin ta kawo musu ba, ta ware na Sharifah daban ta adana a kicin. Abincin me yawa kuwa kasancewar ta ga su na da yawa, ga yara, ga Bello.

Samha b

a ta karbi lambar wayar Sharifah ba duk da ma alamu sun nuna ba ta riqe waya, sai wata karamar waya ce a hannu Hamidah. Amma dai za su yi shahada su je sun san ko ba ta gida yara na gida tunda akwai makaranta islamiyya da boko, ba za ta fita da su ba.



A mota daya su ka dunguma suka tafi wato motar Nana ita ce babba. Su ka isa gidan Sharifah suka iske Bello ya fito zai shiga motar nan da su Nana su ka ga Sharifah a ciki a wajen barista, ashe motar Bello ce.

Ya kalle su ya kawar da kansa gef

e, kafin ma su sami waje su gyara tsayuwar motar, ya shige motarsa ya tafi, da alama har yanzu haushinsu yake ji musamman ma Samha.

Su ka fito suka iske get din a rufe, sai su ka cika da fargabar ko babu kowa a gidan. Wadanda har yanzu zuciyoyinsu

basu gama yarda da cewa ba gidan fatalwa ba ne, suka ji fargabar kwankwasawa yayin da wasunsu irin su Samha gaba gadi suka hau bugawa.

Sai can da jimawa suka jiyo motsin tafiya, aka zo aka bude. Hamidah ce ta bayyana wannan karon idanuwanta sun yi j

ajawur, alamar ta sha kuka.

Su Nanah su ka daka tsalle suka yi gefe, Samha ta harare su alamar su daina yin abinda suke yi haka.

Samha ta rungume Hamidah ta na lallashi ta tambaye ta ko lafiya take kuka?

Amsar ita ce "babu komai."

Sa

mha ta ci gaba da lallashinta akan ta fada ma ta abinda yake faruwa. Amma Hamidah ta dage ta ce ita babu komai.

Samha ba ta yi mamakin kukan da Hamidah ke yi ba, saboda ta ji labarin shakuwarta da Shariqa dole har yanzu ta yi kukan rabuwarsu.



Samha ta tambaya "Mamarku na cikin gida?"

Hamidah ta gyada kai ta ce "Eh ta na sama."

Samha ta kama hannun Hamidah su ka yi gaba tana ci gaba da ba ta hakuri da yi ma ta nasiha akan ta yi hakuri, kowanne mai rai mamaci ne. Mu dukka anan wat

aran za mu mutu mu tarar da su acan."

Su Nana su na ta jan kafa su na tafe su na sanda yayin da zuciyoyinsu ke karkarwa. Har yanzu gidan tsoro yake basu duk da dai an gyara, ba irin yadda su ka gan shi rannan ba, ada dai ga duhun bishiya, ga na da

tti da kura amma yanzu fes da shi.

Su ka hau sama cikin wani katafaren falo mai girman gaske kuma ya tsaru kamar a turai. Sai mamaki ya rufe su, ai basu taba zaton har da gyararren waje a gidan nan ba, sun zaci kwango ne kawai.

Kowacce ta

sami kujera ta zauna yayin da suka bawa Hamidah fulasan abincin da suka kawo mu su, ta karba gami da godiya sannan ta dora akan dining table, ta koma gefe ta tsaya.

Sun tambaye ta ya fi a kirga shin ina Mamarta take dan ba su ganta a falo ba, sai H

amidah ta yi shiru ba ta ba su amsa ba.

Ba su ankara ba muryar Sharifah su ka jiyo a daya daga cikin dakunan.

Ta na magana cikin fushi da daga murya ta na cewa "ke 'yar uwata Shariqah ki koma ki kwanta. Na rantse da Ubangijin da Ya busa min num

fashi kuma Ya raya ni nake yawo a doron kasa, kuma Shine Ubangijin da Ya dauke miki numfashi kina kwance a karkashin kasa, ba zan bari 'ya'yanki su wulaqanta ba. Ki koma ki kwanta, ki koma ki kwanta na ce , ki je ki huta abinki. Wannan yaqin na rayayyu ne

ba na Matattu ba ne."

Daga Samha har kawayenta su ka daka tsalle suka miqe tsaye, yayin da su ka bazama neman kofar da za ta sada su zuwa waje. Aka hau damben bude qofar da ta qi buduwa sai da kyar.

Su ka falfala da gudu kai ka ce gudun famfa

laqi suke yi, ba su tsaya a ko ina ba sai da suka gansu a farfajiyar kofar gida a bakin motarsu.

Huci su ke musamman Nanah 'yar lukata. Ta na ta huci ta zaro mukullin motar daga cikin jakarta ta ce sai dai wata ta karba ta tuqa.

Ta ci

gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login