Showing 63001 words to 65015 words out of 65015 words

Chapter 22 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

17

Sharifah ta yarda ta koma ta zauna bayan Aliyu ya fita sai suka hau fada. Sh

arifah ta harari Samha ta ce " kin sami waje ne shine kike yi mana abinda kika ga dama dan kinga ana lallabaki."

Samha ta yi ma ta gwalo ta ce "oho dai mijina ya baki amanata kuma kin karba."

Samha ta bude nama jifgi ne guda ta ce Sha

rifah ta sa hannu su ci. Sharifah ta ce ta koshi amma a daukarwa Bello, ya na gida yana jin yunwa. Gida bi biyu Samha ta raba komai ta ba ta rabi.

Samha ta kalli Sharifah ta ce " lalali ki na da zumunci da son 'yan uwa, Bello fa ba yaro ba ne a

mma kina ta shagwaba shi. Kuma kin ce ko shi bai taba taimakonki da taliya kwaya daya ba a lokacin da baban yara ya qi ciyar da su, amma ke har yanzu kina wahala da shi."

Sharifa ta ce "haka ne amma babu komai. Haka zuciyata take bana iya hanawa.

Bello ya na da kudi amma nawa yake ci kin ga ai hannun da yake sama ya fi wanda yake karba a wajen Allah.".

Samha ta ce "bayan mun dauke ki fatalwa mu na gudunki sai gashi kin koma zama fes 'yar gayu, kin gyara gidanki da jikinki da yaran na

n, da suturu masu kyau.

Sharifah ta yi dariya ta ce "kaina na yiwa fada na cire damuwa da depression, na fara dawo da rayuwata kamar ta da dan na fuskanci kai za ka fara son kanka kafin wani ya so ka.

Na dukufa da gyaran fatata da sh

an supplements da gyaran jiki da kunshi da turaren wuta. Na fitar da tsofaffin kayanmu na kyauta na siyo mana masu kyau.

Na Samo almajirai suka yi sati su na kwashe bola da sharar tsakar gida. Ni da Bello mu ka hada kudi, dan aurensa ya kusa zai

zauna a kasa. Shari'a ta kare kuma hankalina ya kwanta mutane masu guduna da masu surutu na lalace ta kare min sai daina murna, Sharifah ta tafi ta dawo."

Samhabta ce " ina kika sami kudi?"

Sharifah ta yi dariya ta ce "kin manta Ina da Al

lah?."

Samha ta ce " Shine Ya ce mu tashi mu nema Zai taimake mu."

Sharifah ta ce "rannan na ce miki zan yi meeting da matar gwamna, na fara samun kananan kwangiloli, ina samun 'yan kudi, wasu

manyan ma sai nan gaba dan na samu an hada n

i da oga kwata-kwata her excellencymun tattauna ta yi alqawura. Alhamdulullah mu na saka ran samun babban rabo. Har na bawa Bello kudin motata zai kawo min daga America, tunda harkarsa ce. Wannan motar da nake hawa ta sa ce."

Samha ta ce " ina g

aida ke, ga mace mai kamar maza. Allah Ya kara rufa miki asiri kawata, da mu baki daya."

Sharifah ta ce " Amin."

Samha ta ce " ba ki bani labarin yadda ake ganin matacce a yi hira da shi ba fa.Ranar da muka je gidanki ma kina magana da Shari

qah a zahiri. Zuwa ta yi kenan?"

Sharifah ta yi dariya ta ce "an kwashe yara an ki dawowa da su, na je har gidansa na iske basa nan ya boye su. Sai na dawo gida raina a bace na kwanta na yi bacci, shine na ga Shariqah a mafarki cike da damuwa.

Motsin shigiwarku ne na farka shine ku ka ji ina yi ma ta wannan maganar, a mafarki na ganta na ba ta amsa a zahiri."

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce " kenan duka labarin da kika bani kika ce tana ta binki da wanda kika ce ta gyara kwanciya da m

aganar waya da ku ka yi, da kuma ganinki da ita na farko a bakin rijiya da magruba dukka a mafarki ne kenan?"

Sharifah ta gyada kai ta ce " tabbas a mafarki nake ganin Shariqah kuma muke magana, har nake gane danuwarta "

Samha ta d'a

la ma ta duka a cinya ta ce " shine ki ke ta wahalar da ni da kwakwalwata? Na dauka a fili ma kike ganinta."

Sharifah ta yi dariya ta ce " na yi miki haka ne dan na ga kin yarda akwai fatalwa a duniya ni kuma na san baa mutuwa a dawo "



Samira ce ta shigo yayin da Sharifah ta miqe ta dauki babbar ledar, ta yi musu sallama ta tafi. Ba dan Samha ta na so ta tafi ta bar ta ba. Dan hirar ba ta ishe ta ba.

Sharifah na isa gida ta ana kiran magrib, ta bawa Bello abinda ta kawo masa

ta shiga ta yi sallah.Ta na idarwa, wayarta ta gani tana ta haske da alama sako ya shigo.

Sako Samha ta rubuta ma ta kamar haka:



"kawata ina tare da ke a dukka halinda kike ciki, ki dauke ni a matsayin 'yar uwarki jininki in

a tare da ke duk halin wuya ko dadi. Ga kudi nan naira dubu dari biyu na turo miki ki yiwa yara soyayya ki kula da su. Sannan na yi miki alqawarin duk ribar da na samu a makarantata ta koyar da abinci zan dinga raba ta gida uku, Kashi daya zan dinga baki

dan ki kara kula da yara. Na sami number ki da account number ki a wayarki a lokacin da kika shiga bandaki, dan na san idan na tambaye ki ba za ki bani ba. Ina yi miki addu'a Allah Ya taya ki riqe.

Na gode Amiyarki Samha.Mahmud.



Haway

e mai zafi gami da tausayin kanta da kanta ne ya far ma ta. Ta rantse da Allah a wannan zamanin da wuya ka sami mai sonka saboda Allah haka. Gashi dai kawata har ta fi 'yan uwanta,ta tausaya ma ta, ta yi ma ta kyautar bazata.

Sharifah ta ba ta

amsa da kalamai masu dadi ta nuna godiya da jin dadi. Haka ta tsaya tana kallon alert din dubu dari biyu a dunkule, abinda babu wanda ya taba yi ma ta haka a danginta bayan su na da masu kudin da zasu iya kyautar miliyan biyu ma ba tare da sun san sun yi

ba yin ne ba zasu yi ba.

Haka Sharifah ta ke jin saukar alert daga Samha lokaci-lokaci ba tare da ta saka rai ba, na kudi masu yawa kuma. Tabbas alkhairi baya

faduwa a kasa, ta tuna sanda kudin motar zuwa makaranta da kudin handout yake gagara

r Samha da Aliyu. Sharifah ce mai siya ma ta ko ta bata kudin mota ko ta dauko a motarta ta kai ta makaranta kuma ta biyo ta sauke ta idan sun tashi.

Dan halak baya manta alkhairi ashe Samha ba ta manta ba itama. Allahu akbar!







*** *** ***

Wancan labarin ya rage tsakanin Samha da su Nana Ahmad ne, an hadu an haura an sauko an daidaita. Samha ta sha aradu duk mai daukar Sharifah fatalwa zasu bata idan Sharifah fatakwa ce itama su dauke ta fatalwa, duk daya suke sa

i dai su guje su, su biyu.

Sharifah ba ta ce komai ba bata ma san an yi ba, sai dai ta ga Samha ta kawo su dukka gidanta, bayan sun gaisa ta ci gaba da sauraronsu, su ka gama bayani da bayar da hakuri. Ta ce ya wuce kuma ta gode.



***

*** ***



Kwanci tashi Allah Ya sauki Samha lafiya ta haife 'yan biyu su dukka mata, kyawawa kamar ubansu. An sha murna, abin mamaki aka saka mu su suna Sharifah da Shariqah.

Da farko da aka fadawa Sharifah ba ta yarda ba, ta z

aci wasa ne.Tabbas sun cika ma ta burinta da ta roqe ta a asibiti ta ce a sakawa baby sunan Shariqah, da suka zama tagwaye sai aka saka mu su har da sunanta.

Sai yanzu ta sake yarda tabbas Samha aminiyar kwarai ce, haka da yardar Aliyu da ta mama. D

an Samha ta basu labarin Sharifah tas kuma ta ce dan Allah su dauke ta danginsu. Dan tana bukatar ja a jiki da soyayya da kulawa.

Akwati guda Sharifah ta yiwa yaran cike da kaya har da 'yan kunnayen gwal, da alama kwangila nan mai karfi ta fara sau

ka.

An hadu a sunan Samha da su Nana sai ga Sharifah da Fanna sun iso.

Fanna ta cafke Nana gam ta riqe dan ta ga alamar tana dan jin tsoronta har yanzu. ta ce " ni ma fatalwa ce na zo mu tafi mu yi HIRA DA MATATTU a kabarina."

Zo ka ga

ihu a wajen Nanah, kowa ya kwashe da dariya har da kyakyatawa.



Alhamdulullah!

Karshe!!

Madalla da alqalamin Jut.





Mu hadu a sabon littafina mai suna LOKACIN DA NAKE RAYE.

[3/6, 5:19 PM] Jamila Umar Tanko: Haqqin malla

ka:Jamila Umar tanko

Copyright: Jamila umar tanko





Wannan littafi mai suna HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne.



300 ne kacal Zaa biya

0112240731

Gt bank

Jamila umar tanko



Idan an biya a turo shaida

r biya ta wannan lambar:

08061225337



Na gode

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login