Showing 9001 words to 12000 words out of 65015 words

Chapter 4 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

6

ta sama ta yi fuffuke ta fice oho.

Su Nanah Ahmad na jiyo su na ta s

allama amma ba zan iya amsawa ba. Su ka yi sallama a falo har suka gaji suka shigo dakina.

Muryata suka ji kasa-kasa akan gado sai suka kunna fitilar dakin suka ganni na yi sharkab da hawaye da gumi.

Da gudu su ka karaso su ka daga ni zaune su na ta

mbaya ko lafiya .

Zazzabi mai zafi suka a ji a jikina ya rufe ni. Sannan ba na iya ko daga hannuna balle sauran sassan jikina. Su ka fara shafa min ruwan sanyi su na goge min hawayen da ya kasa tsayuwa.

Su ka ce ina wayata su kira mijina a kai ni as

ibiti ko Mamana. Na ce musu Sharifah ta fasa min waya. Su ka yi carko-carko su na kallon-kallo.

"ina Sharifah?" Su ka tambaya.

Na ce "yanzu ta fita."

Tabbas sun gasgata bana cikin hayyacina. Kuma sun kasa gane menene hadina da damuwa da Sharifah

haka. Matar da ta manta da qawayenta na Nigeria, ta dade da yin hijira ta yi sababbin kawayenta a turai. Tambaya su ke me yasa na damu da ita haka? Kwadayi ne ko kuma kalan dangi?

Haushi ya hana in ba su wannan amsar. Su dai ya kamata a ce sun san ko ni

wacece kuma yaya halina yake. Ba ni da wannan halin ko kadan na shigewa masu kudi ko 'yan gayun da basu damu da ni ba.

Ashe Nanah ta yi saving lambar Mama a ranar da na ari wayarta na kira ta. Dan haka sai da ta kira duk da ina hana ta.

Mamana ta g

igice ance jikina ya tashi, bata jima ba ta karaso a cikin adaidaita sahu da alama ma ba zata bari wani daga cikin yaran gidan su kawo ta ba.

Na tabbatar yau na lahira sai ya fi ni jin dadi zan sha fada. Ta shigo a gigice tana salati. Saboda itama na d

aure na so in zauna amma na gagara zama sai an dafe ni saboda jikin babu kwari.

Mama ta ce "gamo ta yi da wata aljanna mai suna Sharifah a high court daga zuwa wajen wani Alqali aka dawo min da ita a rude."

Nanah ta ce "A a Mama ba aljana ba ce, Sh

arifah Nasir ce fa kawarmu wacce ta yi Samha babbar qawa a bikinta. Mama kin manta Sharifah kawarta wacce kullum su na tare daga sakandire har jami'a?"

Mama ta yi salati ta salance ta ce " au Sharifah Nasir yayar Shariqa yaran da mahaifansu suka rasu ha

r mu ka je gaisuwa da dadewa a unguwar Ahmadu bello way? Toh yaya aka yi so ya koma cutarwa?"

Su Nana suka ce " mun kasa ganewa wallahi Mama, Samha ta kwashe muka je har gidan ta ce mana Sharifah ta rasu ta ji sanarwa a radio. Amma da muka je gidan babu

kowa, gida ya koma kwango."

Maryam ta ce" Sharifah a turai take ta dade bata qasar. Kanwarta ce ma Shariqa ke aure anan garin."

Mama ta daka min wata uwar tsawa mai razanarwa ta ce da ni " ke ki fada min gaskiyar abinda yake faruwa da dalinta na

firgita ki. Fatalwa take yi miki ko kuma sihiri? Yau zaa yi ta a kare dan na san gidan ban manta ba, yanzu zan tashi in tafi."

Na zabura na kama hannun Mama inankuka ina cewa "Mama dan Allah kada ki je ba za ki iya ganin abinda nake gani ba. Sharifah ta

rasu ita da MATATTU ne kadai a gidan."

Mamata ta harare ni gami da fusge hannun ta ta fice tana fada ta ce wallahi gidan zata je ta ci uban fatalwar. Yau ko a ita ko a ita.

Na zabura na ce da su Nanah su riko min Mamana su hana ta zuwa.

Abin hau

shi sai suka ce gara ta je wannan abu ai yayi yawa. Gara a kamo bakin zaren da wuri.

Amma da na ce wata daga cikinsu ta raka ta kada ta tafi ita kadai tunda sun zo da motocinsu sai kowacce ta yi kwana. Sun san abinda muka gani ai ko da kudi aka hada su

ba za su je ba.

Amma me yasa su ka bar Mamata ta tafi basu riko ta ba? Da suka ga da gaske kuka nake rusawa wurjanjan ina cewa idan wani abu ya same ta ba zan yafe musu ba.

Shine suka tashi a guje suka bi ta bakin titi, magiyar duniyar nan sun yi ma

ta akan ta dawo amma ta qi, ta tare adaidaita sahu ta kara gaba. A fusace take kuwa da alama duk duniya babu mai hana ta wannan tafiyar.

Na tabbatar artabu da fatalwa ba zai yiwa Mama kyau ba, gata da hawan jini.

Na koma jabar na kwanta akan gado, b

ayan sun kawo min mummuna labarin cewa Mama fa ta tafi ta qi yarda dawo.

Jama'a a saka Maman Samha a cikin addu'a sai yadda Allah Ya yi ....

😭😭

Madalla da ALQALAMIN JUT

To be continue......

HIRA DA MATATTU ...... 7 (true life story)



NA

JAMILA UMAR TANKO

( JUT)

YouTube:https://youtube.com/@jamilaumartankochannel1167

Jamila umar tanko channel

Facebook:

Jamila umar tanko

Watpad:

Jamila umar tanko

Da na ga kuka da magana ma ba zasu amfane ni da komai ba, M

amana addu'a kawai take bukata dan haka na yi karfin hali na tashi na shiga wanka, sannan na dauro alwallah na yi sallolin da na kasa tashi na yi akan lokaci, na kalli gabas ina nemawa tsohuwata sauqi da sassauci daga sharrin abinda ta tunkara.

Su Nanah

na falo su na ta ciye-ciye da hira da shewa. A jima sai daya ta leqo ni ta ba ni baki ta ce " Samha ki kwantar da hankalinki fa, Mama za ta dawo lafiya ita din Jaruma ce ba irinki ba ce matsoraciya. Yau dai Zaa tantance ko Sharifa ce, ko fatalwarta ce, ko

aljanna ce ma. Mama zata kawo karshen matsalar nan insha Allah."

Haushinsu kawai nake ji saboda ai dan ba uwarsu ba ce kowacce ta kammale tata tsohuwar a gida dole su fadi haka.

Na yi doguwar sujjada ina neman tsari daga mugun ji da mugun gani. Ina

neman tsari daga sharrin Sharifah da maqarrabenta.

Gabana ne yake ta faduwa wannan karon wata mummunar faduwar gaba na ji wacce ta fi ta ko yaushe, na san daidai wannan lokacin Mama ta yi arangama da su kenan.

Sai na daka tsalle na fito falo ina haki

, mu ka yi carko -carko muna kallon juna ni da qawayena.

Su ka zabura suka tambaya ko lafiya? Nanah ta bani wayarta in kira Mama. Nanah ta danno lambar da sauri ta miqa min. Wayar na ringing baa amsawa.

Na sulale na yi zaman dabaro akan kafet ina sa

lati, yayin da kuka ya barke min. Na ci gaba da gwadawa, kira nake ta yi babu qaqqautawa amma baa amsa ba.

Kalaman qawayena ya fi bani haushi wai in daina damuwa ko ta je ma gidan fa babu kowa sai wannan qanin na ta Bello, haka zata dawo.

Na fusata

na ce da su " me ku ka sani game da abinda na sani? Bellon ma ba mutum ba ne, Sharifah da bakinta ta fada min ta ce Bello ya rasu kwana kadan bayan rasuwar Shariqah. Amma gashi nan ina ganin sa duk lungun da na shiga.

Kun ce Sharifah na raye bata ma qa

sar, na rantse da Allah karya ne ni ina ganinta ko minti daya bata da fita ba ku ka shigo, in mutum ce yaya baku hadu a bakin get ko a qofar gida ba?

Yaya aka yi Sharifah ta san za ku zo gidan nan a daidai wannan lokacin? Ita ce ta bani labarin zuwanku

.

Sharifah ta tabbatar min ta fi ni sanin Kudira da irada ta Ubangiji dan ta je inda ban je ba. Sharifa ta tabbatar min ni kadai ta yarda in ganta ba ku ba, kada in sake zuwa da ku. Ranar da mu ka je tana kallonku ku ne ba kwa ganinta nima kuma na gant

a. Maryam Alqali ai kin ganta a ranar amma kika ce sun yi kama ba ita ba ce. Sharifah ta kira ni a waya tana cewa in rufa mata asiri sanadin faduwar wayata kenan ta fashe. Yaya kuke so ku zamar da ni zautacciya ne alhali ina kallon komai a zahiri?"

Nan

fa aka hau muzurai amma da alama sun yarda da cewa Na tabu basu yarda da saitina ba.

Na sharce hawaye na sake kiran lambar Mama wannan karon ta amsa. Ina rawar murya na ce "Mama Samha ce kina ina?"

Ta yi tsaki ta ce " gani daram a gidana yanzu na shi

go."

Na yi ajiyar jin dadi dai na ce " Alhamdulullah! Yaya ku ka yi, kin ga Sharifah?"

Qawayena da gudu suka zo suka zagaye ni suka ce in saka speaker kowacce cike da fargaba.

Mamanta fusata ta ce "zauna nan lusara za ki kashe kanki akan gaibu, na

je gidan na sami saurayin yaron nan, da na buga get shi ya bude min na tambaya ina Sharifah da Shariqah? Ya tsaya yana kallona. Na bangaje shi na shige cikin gidan, babu kowa na yi zage-zagena son raina. Na ja mata kunne na ce ta rabu da ke ko mutum ce ko

aljanna ce ko ma fatalwa ce kada ta qara zuwa inda kike. Na hau har saman benen gidan babu kowa amma na

fadi albarkacin bakina kakaf. Har da qatuwar sanda na dauka na nuna na ce idan ta isa ta fito in ban fasa mata kai ba.

Ko ita fatalwa ce ma dai ta j

i tsoro tunda ta kasa fitowa. Da na fito shima saurayin ban ganshi ba ya ji tsoro ya gudu. Na yi tafiya na bar gidan a bude daman da alama babu masu rayuwa a ciki daga kura sai yana. Dan haka kada in sake ji kin yi maganar Sharifar nan."

Qawayena su ka

zabura su ka ce " Mama haka muka fada mata wallahi. Ta saka Sharifah a ranta ne shiyasa take ganin kamar ita take gani."

Na fada a lokacin da na dora hannu akai nace "wayyo Allahna na ga ta kaina Mama ta dauko mana ruwan dafa kanmu. Bello fa matacce n

e ba guduwa yayi ba ya bace ne, su na kallonki Mama ke ce ba kya ganinsu."

Mama ta surfo min zagi da ni da Bellon sannan ta kashe wayarta.

Su ka dinga jinjina Jarumta irin ta Mama, amma ni tausaya mata kawai nake yi. Ni dai ta bar ni da kaddarar da

Allah Ya dora min Ya san zan iya dauka dan Rabbi ba Ya dorawa bawa abinda ba zai iya ba. Ita zuciyarta bata da kwarin jurewa, saboda girma.

Tashin hankali ya tabbata a cikin zuciyata amma bana gushewa ga neman agaji daga Allah sarkin da Ya halicci Shari

fah da Samha.

Magrib ta qarato dan haka suka fara shirin tafiya gidajensu. Har leda suka samo suka zuba snacks da naman da na tanadar musu su na ta santin dadin girkin Samira a zatonsu ma ni na dafa abincin basu san ko dandane ban yi ba saboda tashin ha

nkali.

Na sake karbar wayar Nanah na kira Samira kanwata na ce ta tambayi Mama ta zo ta taya ni kwana. Dan gara Samira ta kwana tare da ni mu yi artabu da fatalwar cikin dare akan Aliyu ya gane komai. Dan har yanzu bai gama ganewa na zautu ba.

Mama

ta karbi wayar ta ce Samira ba zata zo ba, tsoron nan dole in cire shi a raina idan na sake ganin Sharifah ko da a mafarki ne in fada mata ta koma gidan ta sake zage ta.

Hmmmm kawai na ce dan Mama ba zata gane ba ne, amma tabbas babu riba fada da Fatal

wa. Amma dai ina yi mata addu'a a wanye lafiya.

Kawayena suka tafi suka bar ni na ji kamar in bi su gidajensu. A bakin baranda na yi sallar magrib dan bana so in shige lungu gara kusa da get, na ce kuma su bar get din a bude wayam ina hango masu wucewa

dan ba mu da masu gadi amma na fara tunanin gara a nemo min mai gadi.

Aliyu ya dawo ya iske get a bude wanwar sai ya cika da mamaki musamman da ya ganni a zaune a kan baranda bayan da wuta a gari. Na ce iska nake sha.

Mu ka shiga ciki ya nemi ya kai

ni asibiti saboda zazzabin, na ce a bari ya sauka. Ya min surprise da sabuwar waya mai tsada amma fa ni fadar min da gaba yayi dan na fi kaunar zamana babu waya akan da waya saboda Sharifah ta san lambar wayata sake kira zata yi.

Nan dai na daure na y

i murnar dole aka saka ta a caji ta cika taf sannan ya saka min layina a ciki. Yana kunnawa wata bakuwar lamba ce ta shigo.

Ya miqa min da sauri lambar ta yi kama da wacce Sharifah ta kira ni dan haka na qi karba.

Da aka sake kira ya ga na zabura sai

ya dinga mamaki, dan haka shi ya amsa. Aka qi yin magana.

An kira ya fi sau uku idan ya dauka baa magana.

Ya dube ni ya ce "ke fa ake nema dan in an ji muryata baa magana ki karba ki amsa kawai.

Dan kada zargi ya shiga kuma gashi ba zan iya am

sawa ba na fashe da kuka na ce" ba mutane ba ne MATATTU ne."

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Aliyu ya fada cike da mamaki inda ya bude baki ya na kallona. Can kuma sai ya fashe da dariya har da kyakyatawa. Ya ce shi ko a mafarki ma bai taba jin wannan k

almar ma. A wanne fim na gani? Dan ya san ni da son kallon horror fim.

Takaici ya sa na tashi na shige daki na tayar da sallar Isha'i.

Tabbas cikin dare an sha artabu a mafarki, abin ma ba zai musaltu ba. Su Sharifah ne a cikin mafarkan mun tafi wat

a duniya, wannan karon magana suke ta yi 'cacaacaacaa caaaaa' ban san ma me suke cewa ba. Na san dai akan Mama suke magana zagin da ta je ta yi musu.

Allah ka kawo min dauki kawai a cikin wannan sarqaqiya mai wuyar ganewa.

Kwana biyu dai shiru ban ga

Sharifah ba dan na daina fita ko ina kuma bana kunna wayata sai jifa-jifa dan na san Mama tana yawan nemana kullum sai ta kira ta ji lafiyata.

Da daddare ina zaune na ga an kira ni da lambar Mama da na amsa sai na ji muryar Samira a gigice ta ce min "

Mama fa lafiya mun rasa kanta."

Gabana ya yanke ya fadi na zabura na miqe tsaye na dafe kirji na tambaya "kamar yaya kun rasa kanta? Ba dai Sharifah ta gani ba?"



Samira ta ce " Aunty yaya aka yi kika san Sharifah ta gani? Sunan Sharifar take

kira wai ta zo har dakinta da yamma. Ta ce ta jinsu zagin da ta je ta yi mata ai itaman'yarta ce ba ke kadai ba ce 'yarta. Kuma ai da ba sai ta je ba da ta aika an kira ta." Wai daga nan ta bace.

Ban gama jin labarin nan ba na sulale na fadi akan kujera

. Aliyu ne ya fito daga daki ya gan ni zan shide.

"Kai ni wajen Mama." kawai nake cewa Mama babu lafiya itama ta fara ganin MATATTU irin nawa.

Ya fusata da jin wadannan kalamai daga bakina sai ya dauko wayarsa ya kira lambar Mama.

Samira ce ta

amsa ta tabbatar masa ga Mama nan a kwance tana surutai har tana barin wasiyya. Ta ce Samha kawai take so ta gani akwai wasiyyar da zata bar ma ta, ta zo su yi sallama.



Ya jiyo muryar Mama na kuka yaranta ma na kuka sai hankalinsa ya tashi.

Mu

n isa gidan a gigice mun iske Mama a kwance akan doguwar kujerar falo ana yi mata firgita tana numfarfashi. Daman ni na san zaa rina wai an saci zanin mahaukaciya ranar sallah, na hana ta, amma ta qi yarda gashi nan ai.

Mama ta fara bani labari ta ce "

da la'asar ina sallah a cikin dakina sai ga Mace ta shigo da baqar abaya, sai kawai na ji gabana ya fadi tun kafin ta karasa shigowa. Ta yi sallama gami da cewa 'yarki ce Sharifah Nasir Mama, wannan zuwan na ki ne."

Ina sujjada ban san sanda na zame n

ayi ruf da ciki na kwata ba, na kasa tashi ba. Shikenan nima na fara ganinsu."

Mama ta fashe da kuka, ina kuka tana yi.

Mama ta ci gaba da cewa "ta zo daf da kaina ta durqusa a nutse ta gaishe ni cike da ladabi ta ce " Sunana Sharifah Nasir kawar S

amha."

Kirjina yana ta bugawa yayin na ji kamar an zare min laka babu inda yake motsi a jikina sai idona da yake qifqiftawa ya kasa rufuwa, ina kallonta tana kallona.

Ta ce da ni "Mama kin zo gidanmu kina ta fada kina zagina akan in rabu da 'yarki.

Ai ina kallonki ke ce ba kya ganina saboda ko na fito kin ganni ranki a bace ba za ki fahimce ni ba, ni kuma ba zan iya yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login