Showing 1 words to 3000 words out of 67570 words
[10/8, 18:10] Mrs Zaki:
📚
WAYASAN ASALINA
📚
SAUDAT IDRIS NOVEL
📕
PAGE 1
2:00pm
Jirgin yasauka a
Nnamdi Azikiwe International Airport
Tun daga matattakalar jirgin nake i
ya hango wata kyakkyawar yar matashiyar budurwa a kalla zata iya kaiwa shekara ashirin da biyar a duniya
doguwa ce sosai sannan tana da Dan matsakaicin jiki sai manya manyan idanuwanta da dogoyen eyebrows dinta masu matukar baki
Sai Dan madaida
icin lips dinta dayasha red lipstick .
English wears ne ajikinta masu matukar daukar ido Dan wainsu stones ne ajikin rigar da wandon da sukayi matukar matseta sannan sai Dan karamin gyalen data rufe gashin kanta dashi saidai hakan bai hanani ganin
tsayin gashin ba .
Fuskanta a daure yake tunda tasauko daga jirgin sai rarraba idanuwa takeyi ko zata ga Wanda yazo daukanta
Dogon tsaki tasaki sannan naga tasanya Zara zaran hannunta acikin yar madaidaiciyar handbag dinta na kamfanin Gucci
Wayarta tacuro iPhone 7+ pink color sannan tafara kokarin danna Kira da alama tagaji da raba ido saidai kafin takai wayar kunnanta ta hangi wacce taketa jiran dogon tsaki takara tsaki akaro nabiyu sannan tawurga wayar acikin handbag takuma hade rai .
Matashiyar budurwar ce takaraso tace I'm so sorry pinky harara ta wurga mata sannan tace haba leema tun yaushe kikasan naketa raba idanu kozan ganki mutane sai bazamun idanuwa sukeyi mtsw takuma Jan tsaki wacce aka kira da leema tace yi hakuri Dan Alla
h yanzu dai muje Dan karamin akwatun hannun pinky ta amsa tana kuma bata hakuri atare suka jera suka karasa inda leema tayi packing motar ta wajen me zaman banza pinky tabude tashiga leema kuma dasauri tasa akwatun a booth tazagaya tashiga driver side ta
tada motan suka bar haraban wajen.
Juyawa leema tayi tadan kalli pinky sannan tace pinky Dan Allah ki tsaki ranki kinsan fa babbar harka zaayi kuma dole ki dage wajen kara mallake zuciyar minister harfa kyautar mota yamun Dan dai kawai in hada
mai connection dake
Tsakin murmushi naga pinky tayi sannan tace da alama zan kwasa naira wajen tsohon ala kwankwan din daria leema tayi tace sosaima kuwa Dan inaga har Dubai sai kunje Dan da alama baicika son harka anan kasar ba
Murmushi pinky t
akuma yi dan har saida Dan dimple dinta ya losa sannan tace kafin dai inhadu dawani minister sai munje hotel nayi wanka nayi sallah sai mutafi OK leema tace !
kai tsaye Western Dreams Hotel suka nufa dayake daman leema tayi musu booking
Leema daidai inda zatayi parking tabige wata mota dake niyan fita daga hotel din ai dasauri tafaka motar tafita pinky ma haka ganin me motar sukayi yana duba inda aka bugar mai a hankali yadago yakallesu daga sama har kasa sannan yaja tsaki leema kam das
auri tace Dan Allah Kayi hakuri matsifa yafarayi yace inbanda rashin hankali da kamun kai mezaisa abugar mun mota pinky dogon tsaki tasaki sannan takalli leema tace muje Dan Allah idan kaso kada ka hakura Dan rainin hankali Ana bashi hakuri yana wani tada
ma mutane jijiyoyin wuya kallonta kawai yakeyi zuciyarshi namai wani zafi dakatar da ita yayi sannan yace ke wacece juyowa tayi takalle shi tana wani karkada idanuwa tace sunana pinky sannan taja hannun leema sukabar wajen
[10/8, 18:10] Mrs Zaki:
📚
WAYAS
AN ASALINA
📚
SAUDAT IDRIS NOVEL
📕
PAGE 2
Buga motar yayi dakarfi da hannunshi yace damn it takosan koni wanene lallai saina koyama yarinyan nan hankal
i
Kara kallon inda suka buge mai yayi yaji wani bakin ciki
Abunma dayafi bata mai rai favourite car dinshi ce and even the Color black tsaki yaja yashiga motar yabar haraban hotel din
Room 105
Aka basu suna shiga pinky tace wash nagaji wlhi
ita dai shuru leema tayi Dan taga lambar motar guy dinnan da alama Dan gidan mr president ne kallonta pinky tayi sannan tace hey what's wrong wit yhu kada dai kice mun a tsorace kike
Uhmm leema tace sannan tace yaron mr president nefa I think so tsaki
pinky tayi tace so what ni kinga Bari inshiga in wasa ruwa tunkan kibata mun rai uwar tsoro .
Leema tace bazaki gane bane idan har shine Dan president wallahi zaman abuja sai yagagare mu ko tankata pinky batayi ba tashige bathroom tasakar ma kanta s
hower !
Dan ita Sam batasan tsoro ba Dan daidai take da uban kowa ma
Bata jima ba tafito daure da tawul a inda tabar leema tasa meta daria tafashe dashi tace kinban kunya wallahi banza leema tamata Dan ita a tsorace take
Tabe ba
ki pinky tayi sannan tashirya cikin wainsu arnakun English wears riga da wando sunyi matukar fito mata da duk wata surar jikinta hijabi tasaka ta tada sallah tana idarwa tazauna zaman kwalliya .
Saida tagama tafeshe jikinta da alia sannan tadau
ki handbag dinta takalli leema data rafka uban tagumi tace baby am done muje danna kosa inji masu mutane biyu a hannuna dakyar leema ta tashi tamikawa pinky key car din murmushi kawai pinky tayi sannan suka fice.
[10/8, 18:10] Mrs Zaki:
📚
WAYASAN ASALINA
📚
SAUDAT IDRIS NOVEL
📕
PAGE 3
Parking space suka karasa pinky tashiga driver side leema kuma tashiga wajen me zaman banza .
Sannan pinky ta tada motar sukabar haraban cikin hotel
din
Saida sukayi nisa da hotel din sannan pinky tace uwar tsoro ina mukayi
Leema tace maitama OK kawai pinky tace sannan tayi hanyan zuwa maitama wakar Chris brown tasaka tadan kure volume a hankali take bin wakar har suka karasa maitama sannan l
eema tafara nuna mata hanyan daza tabi har zuwa guesthouse din minister
Daidai wani katafaran gida suka tsaya pinky tayi horn saida gate man din yaleko tukunna ya wangale musu gate din suka shiga cikin haraban gidan
A hankali pinky tace wow
leema tace hmm ai saima kinshiga ciki tukunna pinky tace inaga karshen ta gidan nan zansa yabani daria leema tayi hade dacewa nasan Zaki iya
Murmushi pinky tayi ta karkada idanuwan ta
Saida sukayi parking sannan suka bude murfin motan ata
re suka fito ko wacce rike da handbag dinta pinky tawurga key car din acikin handbag din sannan takalli leema tace muje kinsan yanzu kuma kece yar jagora murmushi leema tasaki sannan tace wannan haka yake
Akusan tare suka jera suka doshi cikin kaya
taccen parlour din
Parlourn bakaramin haduwa yayi ba saidai ko kadan pinky bata tsaya bin parlorn da kallo ba waje suka samu a daya daga cikin kujerun parlorn suka zauna sannan leema tadauki wayarta dake cikin jaka tayi dialing din number din mini
ster bugu daya yadauka daman kaman jira yakeyi
cemai kawai tayi gamu a parlour daga cen yace OK OK Ku hauro upstairs katse wayan tayi sannan takalli pinky tace yana upstairs muje bin bayanta pinky tayi har suka karasa cikin kayataccen parlorun da mi
nister yake zaune yana ganin pinky yawani wangale baki yamike yaware mata hannayenshi yayi Mata alaman
tazo wani mayataccen murmushi tasakar mai sannan takarasa tashige cikin jikinshi welcome yace mata sannan ta amsa cikin tsiririyar muryarta tace thanks d
ear .
Gyaran Murya leema tayi tace da alama honourable yamance dani anan tunda nakawo ma pinky murmushi yayi yace leema aikinki nakyau ki saurari alert zuwa anjima bude baki tayi tace nagode honorable Allah yabar ma pinky .
zama suk
ayi akan kujerun parlourn pinky kam har cikin zuciyanta tsohon ala kwakwan nan da alama zay takura mata dayawa gashi kato dashi kuma baki dashi gashi sai uban muni ita kam ta tsani mummuna a rayuwar ta
Amma yaza tayi tunda tana bukatar kudi wajen cik
ar burinta .
Kallonta minister yayi pinky ta kashe mai ido daya tana tsakar Mai murmushi
Kara jawota yayi zuwa jikinshi yace uhm Allah yayi halitta anan kifada duk abunda kikeso zan baki
Dadine yakamata acikin zuciyanta
Kallon jun
a sukayi da leema suka tsakar wa juna murmushi
Tabe baki pinky tayi sannan takara kashe murya cen kasa tace
Baby inda so samune sabuwar mota nake bukata yanzu da sai kuma tayi shuru irin jan ajin nan minister yace ke tawa ce kisaki ranki kifadi
koma meye
Thank yhu pinky tace sannan tace gidan nan nakeso daria taji yasaki yace indai gidan nanne ayau zan mallaka maki takardun shi
Kasa magana tayi sabida batayi tunanin zay amince haka dasauri ba
Saida ta tattara nutsuwarta sanna
n tace wow baby thank yhu
You are too much sai tadan kaima peck a kumatu
Wani lumshe ido yayi sannan yace wace kalar mota kike so
Sai insa akawo maki Dan tabe baki tayi sannan tace range rovel 2017 black color hade da tic
Minister yace
angama ranki yadade .
tun daga bakin gate nafarko aketa gaidashi hade da daga Mai hannu ko kallonsu bayyi ba duk da wulakanta mutane ba dabiar shi bace
Yau dinne ranshi abace yake
Bama inda ake parking yayi ba Dan ko p
arking space baya jin zay iya karasawa .
Ko kullle motar bayyi ba yayi hanyan katafaren shiga cikin gidan fuskarshi a hade kai tsaye part dinshi yawuce Dan yana bukatar kadaicewa ko zuciyarshi tayi sanyi
Fadawa yayi kan katafaren gadonshi kirar
royal bed saidai wannan yafi Royal bed kyau dakuma girma
Rintsa idonshi yayi pinky kawai yake gani a lokacin da take gaya mai bakaken maganganu buga hannunshi yayi ajikin gadon dakarfi yace waye ubanki a kasar nan ni captain AJ saina koya maki hankal
i
[10/8, 18:10] Mrs Zaki:
📚
WAYASAN ASALINA
📚
SAUDAT IDRIS NOVEL
📕
PAGE 5
Pinky tace magajia itace uwata itace ubana she's my family hawayene suka cika mata ido tace leema nasan rayuwar da mukay
i bame billewa bace amma hakan ne kadai mafita a gare mu bansan iyayena ba magajia Kawai nasani ita kadai tunda natashi .
And sai bayan kinzo nakara ji nasamu wata family
Leema ita kanta magajia batasan asalina ba batasan kowa nawa ba itama tsin
ta ta tayi
Abun dake damuna WAYASAN ASALINA
Leema dafa kafadar pinky tayi tace koma suwaye iyayenki komin Daren dadaiwa Zaki San asalinki please kidaina sa damuwa a ranki
Pinky tace nadaina sabida burina yafara cika ina son inzama fitattaciya
ta hakan ne kadai zan iya gano iyayena .
Sannan takai hannu tashare hawayen fuskanta tasaki murmushi tace next week fa zamu koma skool kinsan kuma lectures yawuce mu dayawa leema tace nasani amma kwana nawa zakima minister
Pinky tace ina tunanin f
our days ai yayi Dan bana son naci irin na tsofaffi .
Bata bari leema tace komaiba taja hannunta tace ke muzagaye gidan muga yanda yake dakuma irin rayuwar daza mufara yi aciki daria leema tayi tace irin wannan kosawa haka .
AJ kai tsaye pa
rt din su Mami ya nufa zaune ya tadda kannan shi a parlour suna pictures Mimi tana ganinshi tace yauwa ga ya AJ pls ya kazo miyi snapping pictures ko so dayane tsaki yaja yace matsalar Ku tayi yawa wallahi yaran nan wai yaushe zaku gama hutun ne kutafi su
mayya dake rike da camera din tace maybe next week
Sagir dake tsakiyan su yace pls ya AJ kazo mudauka koso dayane Mami ce tafito daga bedroom tace haba alamin katsaya Ku dauka mana bata rai yayi yace Mami pls alama tamai daya tsaya kawai sudauka tsak
ashi sukayi a tsakiya yawani hade rai Mami murmushi tayi tace Alamin smile mana haba .
Dakyar yayi murmushi suka dauki pics din Mimi ce tace gaskiya duk gidan nan sumayya kinfi kama da ya sagir yace aiko a skool ne da anga Sumy zaace kanwar ya AJ wai s
unfi kyau sumayya tace ehmana munfi kyau nida ya Dan da abba muke kama Mami tace oho wato kina nufin abbanku yafini kyau daria gabaki dayansu sukayi AJ yace haba ai Mami kinfi abba kyau .
Mami tace aina sani bama saika fadi munba daria su sumayya suka
yi yana kallonsu kowa yayi tsit.
sannan yace Mami gobe zanje Dubai Abba yace bazay samu daman zuwaba zayyi baki gobe
Mami tace Allah yakaimu Mimi tace Dan Allah ya kaje damu akwai film din dazaa nuna a cinema ranan Saturday sumayya tace pls ya s
agir ma haka OK yace sannan yace bana son takura kuma saiku shirya dawuri mami tace agida zaku sauka ko hotel AJ yace hotel dai ai gidan zay mana ba dadi tunda keda abba baku nan
Mimi tace ya amma dai kaima zaka cinema dinko galla Mata harara yayi yac
e inada aikin yi saiku tazama kuna cika ma Mami kunne
Daria Mami tayi tace nafi so suringa cikamun kunnan tunda kai bakason yin hira da kannan ka
Baice komai ba yafice yana murmushi yasaba da korafin Mami tuntuni part dinshi yawuce !
6:
00pm
Minister yakira leema a waya yace Mata motar Pinky ta iso tana parking space baijira cewar taba yakatse wayan wani ihu leema tayi tace new babe tazo pinky dake shan ice cream tace bangane ba leema tace yanzu minister yakirani wai motarki tana waje p
inky
Mikewa tsaye tayi tace OMG leema tace new babe pinky tace wannan yafi new babe nayi mamaki fa hannun pinky leema taja suka yi waje suna hango motar suka tsaki ihu suka rumgume juna wani Dan saurayine yakaraso yamika musu key car din yatafi ai da
sauri suka karasa wajen motar suka bude suka shiga suna duddubawa pinky tashiga ta tada motar leema tace Bestie congrat
Komi is OK murmushi pinky tayi tace thanks dear
[10/8, 18:10] Mrs Zaki:
📚
WAYASAN ASALINA
📚
SAUDAT IDRIS NOVEL
📕
PAGE 4
Dunkule hannunshi yayi yana fitar dawani iska me zafi
Daidai lokacin akayi knocking saida yadan dadai sannan yace come