Showing 27001 words to 30000 words out of 111738 words
Amatallah ta girgiza masa kanta.
Yacigaba da fad'in kowanne irin matsayi ka taka a rayuwarka inhar bakajin tsoron ALLAH ba to kaifa ba komai baneba, duk k'ask'ancin waninka inya kasance mai tsoron ALLAH toya fika agareshi, ubangiji shika
d'ai yasan iya adadin halittun daya halitta masu numfashi a duniya, kuma shine ya tabbatar mana duk sai ya d'and'ana mana mutuwa, wad'anda suka rigamu tafiya ba sauri sukayiba, muda muka rage bamuyi jinkiriba. A wannan ga6ar ina mai baki hak'uri, da rok'o
nki akan kizama cikin bayi masu ambaton Alhamdullahi ala kulli halin aduk yanayin dasuka tsinci Kansu a rayuwa, ki kar6i jabawarki da hannu biyu dankizama cikin salihan bayi muminai..........."
Hawayene masu zafi suka fara zarya a kumatun Amatalla
h, tabbas bayanan uncle namata nuni akan babu babanta a duniya, ahankali tace, "uncle babana yarasu ko? Karka 6oyemin, kafad'amin, insha ALLAH zuciyata zata iya d'auka, domin ubangiji baya jarabtar bawa da a binda bazai iyaba. namaka alk'awarin kasancewa c
ikin bayin ALLAH masu hak'uri da kar6ar jarabawa ko wacce iri".
Da k'yar ya iya had'iye wani kulutu daya tokare masa k'irji, sannan ya d'aga mata kai a hankali shima hawaye nabin nasa kumatun.
Jikinsa kawai tafad'a tasaki kuka mai tsuma rai,
hannu biyu ya kar6eta ya rungume, suka cigaba da rairawa a tare, abin gwanin ban tausayi.
Sun d'auki tsawon lokaci ahaka kafin Amatallah cikin kuka tace, " uncle Ammina fa?".
"Sai hak'uri Khadija, Saliha tama rigayi brother ra..s....u...wa...".
yak'arashe maganar da k'yar, saboda wani d'aci dayakeji a zuciyarsa.
Sunyi kuka mai isarsu shida ita, kafin doctor Shu'aibu yazo yana lallashinsu, dole akama Amatallah allurar barci danta samu nutsuwa.
*_One week later_*
Alhamdllh a sati d'ay
annan daya gabata abubuwa masu yawa sun faru, ciki harda rud'ani mai rikitarwa da Amatallah ta shiga, dole aka d'akkota daga asibiti aka maidota gida wajen innani.
Basu 6ata lokaciba aka dage mata da addu'oin dangana da hak'uri, Alhmdllhi ansamu nasaro
ri kam, Dan addu'a takobin mumini Ce.
Nutsuwa tazo mata sosai, sai dai yawan kuka datakeyi, sannan maganama yanzu kam saita wunima batayiba.
Kullum uncle Na hanyar gidansu innani.
Nazeefa da Innani suna matuk'ar k'ok'ari wajen rage mata kewa
da yawan damuwa, hakama jabeer, Shehu kam sai a hankali, danshi dama bayajin magana, zaman gidamma bayi yakeyiba, danma yana masifar tsoron uncle Muhammad d'inne yake rage wani abun.
Har zuwa yanzun daga Amatallah har matansa babu Wanda yasan da zancen
aurensu, innani da babane kurum sai jabeer da maijiddah suka Sani, ko Nazeefa batasan komaiba.
Bayan sati uku da rasuwarsu Ammi cif baba yace yakamata asanarma Amatallah zancen auren, karya zam saita saki jiki kuma akuma maidata ruwa, gamma taji k
omai yanzun tahak'ura baki d'aya, hakama matan uncle yakamata Susan halin da'ake ciki.
Innani tayi na'am da wannan batu, Dan haka aka kira kawu yakubu da doctor shu'aibu, sai Su jabeer kuma.
Kowa dai ya hallara.
Aneesa da Fateema sai mamak
in wanna taro sukeyi, su duk zatonsu akan ruk'on Amatallah ne, anason aza6i wadda za'a bamawa acikinsu, tunda sunsan dolene mijinsu zai cigaba da rik'onta.
Fargaba dukta cika Uncle, damuwarsa d'aya akan yanda Amatallah zata kar6i zancen auren ne.
Bayan addu'oi da aka gabatar kawu yakubu yamik'e a nutse yafara jawabi tundaga farko har k'arshen abinda ya wakana aranar da Baban Ama zai rasu.
Tun jikin Amatallah Na rawa a 6oye harya fito fili, tafara karkarwar rawar sanyi sosai, kuka kam tama nem
esa tarasa gaba d'aya.
Anty maijiddah dake kusada itace tajawota jikinta tana lallashinta.
Idon uncle k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi balle yatuna akwai wasu halittu su Aneesa awajen.
Daga Aneesa har Fateema kam mutuwar zaune sukayi, kowacce
takasa motsin kirki, har kawu yakubu yagama jawabi yakoma nasiha agaresu.
Tashin hankali kenan, Wanda ba'a samasa rana.
Wannanfa shine ana wata gawata tazo.
Dad'i sosai yakama Nazeefa, Dan aganinta babu Wanda Amatallah tadace dashi kamar yayan
su Muhammad, lallai wannan shinefa ake kirada *HA'DIN ALLAH*.
har taro yatashi mutum uku basu iya koda tariba, Aneesa, Fateema, garama Amatallah tanata hawaye da rawar sanyi.
Ranar kam haka ta kwana rijif da zazza6i mai zafi ajikinta, sai sambatu
takeyi dakiran sunan Amminta da baba.
Da k'yar innani tasamu tayi barci, dama ita ba had'in auren ba, halinda yarinyar zata tsinci kanta, dakuma yanda zata kalli al'amarinne damuwar.
___________________________
Alhmdllh k'ura ta kwanta, zuwa y
anzu jos da Kaduna abubuwa sunfara dai'daita, sai dai bak'aramar asarar rayuka dana dukiyoyi akayiba, lamarin ko k'yan gani babu, abin tashin hankalin abin yafi shafar matasanmu, kusan duk sune aka kashe da raunika kuma ga wad'anda suka rayu.
A kudanc
in k'asarma Alhmdllh komai ya lafa, sai kuma yad'a 6arnar da akayi a kafafen yad'a labarai Na waje dana gida, hanyar samun kud'i kuma ta bud'ema 'yan jaridu.
Jami'an tsaroma sai fankama suke, hakama 'yan siyasa abin kamfen dayima jam'iyya mai mulki g
ugar zana tasamu, muma kammu talakawan ba'a barmu abayaba, sai zabga kalaman ALLAH wadai muke ga gwamnati batareda dubi da mune muka haddasama kanmuba.
K'asar duk tabi ta rud'e da surutai marasa kan gado, kowa k'abilarsa da addininsane mai gaskiya, babu
mai yarda a jingina masa koda laifi d'ayane, masu tsoro kuwa harsun tattara inasu-inasu sunma k'auyikansu da yankinsu saukar angulu, Na kudanci sunkoma yankinsu hakama arewaci, kowa 'yancin fad'ar albarkacin baki dayake ik'irari dashi tasashi kasa yima k'
asar k'yak'yk'yawan fata, saima k'ara Neman hanyar kare kai Dan aganin wasunmu bata mutuba rufa tayi, akwai sauran yak'i agaba, kowa yakoma gidane yasawo sulken yak'i.
A 6angaren manyan k'asar kam d'if kakejinsu, kaikace babu sarakunan gargajiya a
k'asar, malaman k'asar da pastors sunyi gum da bakunansu basa cewa komai sai sunsami ke6ancewa da mabiyansu a k'uryar lunguna, wasunsu suzama masu tunzura matasan da nuna musu sune masu gaskiya, k'alilan dasuke Na kirki sune masu tsawatarwa da nuna kuskure
da illar abinda yafaru.
Kowa yazama d'an jari hujja, mutuncinsa kawai yake k'ok'arin karewa da yankinsu, zancen nuna gaskiyar muzama k'asa d'aya al'umma d'aya son zuciya yasa mungina rami duk mun binne furucin bakunanmu, mai k'ok'arin so a gyara
saikaji jama'ar yankinsa sun rad'a masa suna *MARA KISHIN KAI*.
humm kai da shi mai tada husuma komai yanka albashin had'a rikice-rikice wanene mara kishin kai aciki?.
Wlhy idan bamu gyaraba wankin wula tana dab dashirin kaimu tsakiyyar dare mai duh
uwar dazamu kasa koda ganin tafikan hannunmu.
Da ni da kai duk 'yan k'asane, munada zarrar kawo canji koda ta hanyar tsarkake zukatanmu ne da gyara halayyarmu.
Ba gwamnati da shuwagabanni ne kad'ai ke buk'atar gyaraba, hatta damu talakawan masu ik'
irarin Neman gyara da hura haccin sai an gyara d'in muna buk'atar gyara kanmu.
Taya kakeson k'asarka tazama mai tsafta ta hanyar jagorancin shuwagabanni amma kai talakan k'asar kullum kana tebirin 6arna.
Bakasan darajar zuminciba, bakasan muhimman
cin addininka da koyi da k'yawawan aiyyukan daya kawo makaba, bakasan wace k'yautatawa yakamata iyalanka su samu daga garekaba, balle ajega zancen makwafta da abokan zamanka Wanda addini ya banbantaku, baka Neman abincinka ta hanyar hallal balle kaciyar da
iyalanka suzama nagartattu masu tsafata, kullum harshenka yana kan aibanta 'ya'yan jama'a da zund'en matan mutane, sai hassada da ganin k'yashin cigaban d'an uwanka fal ruhinka.
Kina mace kinkasa son abokiyar zamanki balle 'ya'yanta, kullum zuciyarki
cik'in k'yashi da bak'inciki take idan mijinki ya k'yautatama iyayensa da 'yan uwansa, kinkasa nutsuwa wajen bautama ubangijinki amma kece sahun gaba agidan uwar gulma ko gidajen Malam tsubbu da bokaye anufin Neman taimako, burinki kullum ace kece sama dak
owacce mace a6angaren k'yale-k'yale da kayan k'awa Na duniya, buri dason burga yahanki fad'ama mijinki gaskiya yayinda kikaganshi bisa karkatacciyar hanyar dazata iya kaiku wuta ke da shi da 'ya'yan dakuka haifa,
Kana matashi amma kullun burinka akan
kayi kud'i kake, ka auri mace ajin farko a k'yawawa kasaka acikin gidanka Na k'awa danta zame maka fure, babu ruwanka da tarbiyyarta ko addininta balle nasabar data fito, jin kanka kake on top kai yanzu kafara zamaninka mutuwa da sauran tak'i a tsakaninku
da ita, baka ganin kowa da gashin arzik'i saboda kai ka iya kuma karanka yakai tsaiko, kasani sai dai ka sanar babu mai sanar da kai saboda kasha boko ka k'oshi, da ance kayya kaine sahun farko a masu d'akko makami afara y'ar rere tsakaninka da jama'ar ga
ri, aganinka kai dai-daine bakada matsala da duniya, koyanzu kabarta hankalinka a kwance tunda baka haihuba.
Wlhy muji tsoron ALLAH, mufara tuna komu su waye kafin gangar shaid'an tamana tasiri a zukata mu kwashi filin rawa muna tangad'in maye dajin ka
nmu can k'ololuwar sararin samaniya muna yawo cikin giza-gizai.
Kowa yaje inda zashi yadawo akwai rana d'aya tak da za'a baka littafin ayyukanka a hannun haggunka ko damarka, wannan za6in yarage naka.
Duk nau'in shed'ancin dakakeji ka gawurta tarih
i ya nuna anyi wani kafinka, kuma anshafeshi yazama labari tamkarma bai zoba.
To kaikuma asuwa da naka tak'adarancin bazai zama labariba harma ayo Wanda yafika k'warewa.
Abin mamaki dukfa da wannan halayen namu amma mukeson samun shugabanni nagar
i, bayan ALLAH yafad'a mana, dai-dai sugabanninmu dai halayenmu kuma.
Tab d'i, ashe kam da sauran kallo
😨🤔
.
Kayi nazari, kiyi nazari, nayi nazari, muyi nazari domin gano illolin takubban shed'anarmu komunada rabon gyarawa kafin randa mala'ikan
mutuwa da rundunarsa zasu zagaye sashinmu Dan k'udundunar ruhinmu zuwaga Wanda yayka yayni dama duniyar da abinda ke cikinta.
ALLAH ka ganar damu gaskiya koda bazata mana dad'iba, ka tasirantar da ita agaremu, mu kar6eta mukumayi aiki da ita danmu samu
komawa ga ALLAH cikin salama
😭🙏🏻
.
_____________________________
"Wai kana nufin bazakayi break fast ba agida dear?".
Gyara zaman hular kansa yayi, sannan ya d'auki turare ya fesa, kafin ya juyo sosai yana fuskantarta, cikin sassanyar muryars
a yace, ''sorry my neesa, wlhy ina saurine, dan inada meeting a da lectures k'arfe 12, gashi inason shiga naga jikin baba, nakumaje kasuwa, yau kayanmu zasu iso. Please kimin afuwa mana my sweet".
Ya k'are maganar da matsawa kusada ita ya rungumeta a j
ikinsa.
Bakinta ta d'an turo kad'an, cikin d'aurewar fuska tace, " kai dai kanason ganin Amatallah kawai, babu wani duba baba".
Lumshe idanunsa yayi yana guntun murmushi, ya d'agota daga jikinsa yana mai zuba idanunsa kan k'yak'yk'yawar fuskarta d
atasha kwalliya.
"My neesa! kina ganin nayi laifi kenan koda ganin Khadija zanje? a tunanina koda babu aurena a kanta ta cancanci irin wanman kulawar daga gareni, karfa ki manta jinin brother d'inace ita. a zatona kodan halin da yarinyar ta tsinci ka
nta ta cancanci kubar mata ni gaba d'ayama ai".
Sosai Aneesa ta zaro idanu waje, " mubar matafa kace?".
"Eh mana". 'Yay maganar cikin d'age gira'.
Bakinta ta ta6e, cikin matuk'ar hasala tace, " ai wlhy ba haifi d'iyar dazan banmata kaiba, r
aba dai-dan kama danekiyi tsoron azabar ALLAH ne kawai yasani hak'uri, nifa wlhy harma mamaki nakeyi yanda kayarda da auren d'iyar cikinka, shin baka tunanin kamata tsufane?".
Wani abune ya soke zuciyar Uncle M.A, ya kafe Aneesa da idanu ko k'yaftaw
a bayayi. tabbas maganarta ta mugun shigarsa. bai ce mata komaiba ya d'auki wayarsa da key yafice.
Bayansa Aneesa ta raka da harara, yau ko shiga su gaisa da Fateema bai yiba. Sai tashin motarsa kawai taji.
Da kansa yabud'e gate ya fice, sannan ya
fito daga motar ya yarufe, tafiya yake amma maganar Aneesa nakuma tasiri a zuciyarsa, shikansa tunda aka d'aura aurenan abinda ke damunsa kenan, sai yaga kamar an cutar da Amatallah, duk da shikam garas yake jin kansa da lafiya, bai San miyasa maganar Anee
sa tamasa zafiba da yawa, bayan shima yasan gaskiya tafad'a.
Hannunsa yakai yashafo ma dai-daicin gemunsa, kafin ya furzar da iskar bakinsa yana kuma dafe sitiyari.
Ya d'anja lokaci a hanya kafin ya isa gidansu, saboda 'yan makaranta.
Babu ko
wa a tsakar gidan, sai dai yaji kamar alamar mutum a Ketchin.
Yasan maybe Nazeefa ce, Dan haka saiya wuce d'akin baba. Sai da yayi sallama, aka bashi izinin Shiga sannan ya shiga.
Innani ya tadda gefen baba tana gyara masa rawani bisa kansa data
yafa masa, da alama wanka tamasa, kullum da sassafe take masa wanka ta shiryasa, shiyyasa saika taddashi tsaf.
Tunda yashigo baba da innani suke binsa da kallo, Dan tabbas sun gano alamun damuwa a fuskarsa, duk da sunsan damuwar rashin isma'il har
yanzu bata barshiba, hakan bai hana baba fad'in "Muhammadu lafiya kuwa?."
Duk girman d'a agaban iyayensa yarone
😊
.
Dan haka sai Uncle M.A yakuma jin zuciyarsa tayi rauni, zama yayi ya gaida iyayen nasa, da tambayar ya jikin baba?.
Tambayar
baba yasake mai maita masa. Innani dai batace komaiba, tama kauda kanta daga garesu, tanata ninke kayan baba daya cire, sai dai dukkan hankalinta Na kansu.
Yay k'asa da kansa, cikin sanyin muryarsa yace, "baba akan maganar auren nanne, sai nake g
anin kamar an cutar da yarinyarnan, musamman idan akayi dubi da shekarunta da nawa".
Murmushi baba yayi tareda gyara rawanimsa dayake rufe masa fuska, yace, " miyasa kake wannan tunanin Muhammadu?, ai ba haramun baneba idan mai shekarunka ya
auri kamar Khadija, sai dai malamai sukance yin zai iya zama cutarwa ga ita yarinyar zuwa gaba, Dan sanda zaka kai wasu shekarun tsufa ita kuma sannan take tashen k'uruciyarta, kaga zata iya cutuwa saboda kai k'arfinka ya ragu, amma zakaga wani kuma idan
ALLAH yabashi lafiya babu abinda bazai iyaba alokacin, (anta6a ma sheaik jafar Mahmud Adam tambayar nan, irin wannan amsar naji kuma yabada) amma ALLAH bai haramtaba, saboda masalahar gudun yad'uwar zinace-zinace yasa malamai sharhantawa".
" kai kumam
a ai shekarunka basukai adamun ba har irin haka".
A raunane uncle M.A yace, ''baba shekara 47 fa".
Da sauri Innani ta juyo ta kalleshi, baba kuma yay guntuwar dariya.
"Muhammadu kai yanzu shekarunka 47?".
"eh mana baba, koma nafine?".
'Yaya maganar a raunane'.
Yanzun kam ba baba ka d'aiba, har Innani sai da ta murmusa.
"Lallai Muhammadu, to ai ko auren namu baima kai 45 ba sai a watan jibi, kuma awatan da aka kawo zainabu gidannan a watan tasamu cikinka, wannan lissafin kane d
ai kawai".
" to Amma baba a takardar haihuwata ai hakane".
"Yo Muhammadu takardar haihuwa ba kaine kaima kankaba lokacin dazaka sakandire, koka mantane?. lokacin da aka haifeka zainabu a rogo ta haihu, Dan ana goyon ciki a lokacin, tun cikinka
Na wata bakwai akazo aka tafi da ita can, sanda tadawo min nan kanada wata biyu da kwana 26 a duniya, sannan ana arba'in biyu idan mace ta haihu tana wankan jego.
"Na dai manta taka mai-mai miya faru karon haihuwarka, amma an haifeka da shekara 1 ak
a kifar da gwamnatin gawon, Murtala ya hau mulki, sai dai bana mantawa abinda nake ganin zan iya k'iyastashi da haihuwarka lokacin dai an cireka a mama da kwanaki 6 obasanjo yazama shugaban k'asa a mulkin soja ko zainabu?, da wannan kawai zan iya k'iyastaw
a gaskiya, saika bincika shekarun kagani".
Innani tad'an gyara tsayuwarta a jikin bango, batareda ta kalli Uncle M.A ba tace, " hakane Malam dan bazan mantaba har shi ubasanjo ya sauka ba'a dawomana dashiba, har sai da iya ta rasu, dan munma fid
da rai akan zai dawo wajenmu, nama haifi maijiddah har da cikin Barirah".
"Wannan gaskiyane zainabu, dan haka saika lissafa kaga shekara nawa ya kama, ka had'a da shekaru biyu kafin