Showing 69001 words to 72000 words out of 111738 words
tashiga wanka. babu 6ata lokaci tafito tayi shirinta cikin zani da Riga Na ata
nfa green da ratsin Orange, kayan sunmata k'yau sosai, dansun haska bak'ar fatarta datasha gyara tanata walk'iya da shek'i, bawata kwalliya tayiba kamar kullum, tana cikin d'aura d'ankwali yaturo k'ofar yashigo da sallama.
Ta amsa kanta ak'asa batareda
ta kalleshiba, har k'asa ta tsugunna ta gaisheshi, idonsa akanta ko k'yaftawa bayayi ya amsa yana guntun murmushi, gabanta yak'araso yasa hannu biyu ya kamo kafad'unta ya mik'ar da ita, "my best! Kin iya gayu fa, koda yake agayama 'yan jos gayu, dama anan
6angaren Ku kwararrrune (sai dai k'arya inji ni......lol
π€π
) jasawa amin afuwa tsokana ce.
Ita duk kunyarsa ta isheta, kanta ak'asa tana murmushi dan jin furicinsa.
Ya matso da ita jikinsa ya rungumeta, a kunnenta yace, "miyasa bakizo kin sh
iryani ba? Ko bakiga haka matana su keyi ba?".
Kunya takuma kamata, takuma lafewa sosai ajikinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, kusan mimtuna 2 ya d'agota yana fad'in " my best karki karyamun azumifa".
Yanzun kam sosai ta kallesa danjin furic
insa, sanye yake cikin farar d'anyar shadda wadda tad'au aikin wuta mai masifar k'yau, yaukam babu malum-malum, rigar kuma kad'an ta wuce gwiwarsa, hularsa Brown color tamkar surfanin gaban rigar, (duk a abunda baifi 3Seconds tayi wannan kallonba.....lol
π
), ta marairaice fuska a shagwa6e tace, "Uncle azumi kuma?".
Gira ya d'aga mata yana murmushi kafin yace, " kin manta yau alhamis ne".
Kad'an ta turo bakinta gaba Dan tuna wahalar datasha wajen had'a break fast, wlhy datasan yana azumi baza tayi
mai dad'in haka ba.
Hannu yasa ya d'ago ha6arta "ya dai? sarkin shagwa6a".
Dariya yabata dayace sarkin shagwa6a, ta murmusa har hakwaranta Na bayyana, " Uncle banfa san kana azumiba, natashi naita wahalar had'a break fast ".
" ooh my bes
t! Sorry, kaina bisa wuya kinji, amma kiyimin irinsa a bud'a baki zanci kinji. kar6a wannan ki sakamin". ya kamo hannunta ya zuba link d'in hannu yana mik'a mata hannunsa na dama.
Dukda tanajin nauyi haka takama hannun tafara k'ok'arin saka masa, danta
iya, wani lokacin takan sakama babanta idan Ammi tana busy zai fita. tsaf ta saka masa har yayi mamaki. "My best dama kin iya?".
Kallonsa tayi tana murmushi, " Uncle ai ina sakama baba".
Shima murmushi yayi tareda kai hannu ya shafa fuskarta
yana fad'in ''oo dadys girl ".
Dariya duk sukayi.
Yace, " k'arasa shirin muje kiyi break nima school d'inku zanje yau".
"To Uncle".
Fita yayi, itakuma ta k'arasa shirin nata, ta saka hijjab da takalmi tafito, duk suna falo, yara nayin bre
ak fast, gaishe da kowannensu tayi cikin girmamawa, kowacce ta amsa cikin danne kishinta, Dan tunda ta fito sukebinta da kallo kozasuga canji a tafiyarta, saidai kuma normal take tafiya babu wani alamun tangard'a. tsaf Uncle duk ya fahimcesu saboda duk ya
nda suke kallon Amatallah d'in akan idonsane, 6oyayyan murmushi kawai yayi, aransa yace " mikukeci nabaka Na zuba guy's ".
Yaran duk suka gaidata, ta amsa cikeda kulawa kamar yanda ta saba. Itama zama tayi taci abincin kad'an, data d'ago saita kama Unc
le na kallonta, daga k'arshe dai ta d'auke kanta gaba d'aya data kula duk idon matansa a kansune. Shiko gogan ko a jikinsa.
Suna kammalawa suka mik'e, mai napep d'in dake kai yara school yazo, atare suka fito, yaran suka shiga napep sukuma motarsa, Am
atallah ta bud'e musu gate d'in dansu Aneesa babu Wanda yamasa rakkiya (kishi ya hana ...lol
ππ
).
Sunama ficewa Fateema da Aneesa duk sukaja tsaki, saikuma suka kalli juna danjin tsakin nasu yafita lokaci d'aya, basarwa Fateema tayi tad'iba break fas
t tafara ci, Dan yanzun batada jimirin yunwa.
Murmushi mugunta Aneesa tayi, a ranta tace, " muguwa kawai, a fuska tamkar ta kwarai, amma zuciyarki saidai ALLAH. a fili kam tashi tayi tashige 6angarenta.
Fateema tarakata da harara
π
.
Uncle kam
tunda suka tafi Amatallah tayi tsit, cikin raba hankalinsa biyu yafara janta da hira, yana kallon jama'ar gari da yara 'yan makaranta, saikuma tuk'i.
Amatallah dai nata murmushine, wani lokacin kuma tace, ''eh ko a'a". Bai damuba dan yasan muskilanc
in ta, ahakanma washi anajin kunyarsa da kimarsane, amma da Jabeer yana bashi labarin yanda suke kasancewa idan zai kaita school kozai d'akkota yaci dariya.
Maimakon yawuce makaranta kai tsaye saiya wuce gidansu, batayi maganaba saima dad'i taji, shi
kansa yaga farin cikin a fuskarta, murmushi kawai yayi baice komaiba.
Cikin zumud'i tawuceshi ta fara shiga gidan.
Da shehu tafara cin karo yana alwala a tsakar gida, da alama sai yanzu zaiyi sallar asuba.
Cikin tsokana tace, "su Ya Shehu d
ai baza'a canjaba, k'ara'i dai kullum".
Dariya yayi yana mik'ewa, " kece da farar safiya haka Antynmu?....."
Bai k'arasaba Uncle shigo, hakan kuma yayi dai-dai da fitowar Nazeefa itama daga kitchen saboda muryar Amatallah data jiyo, rungume juna s
ukayi suna murna, yayinda shikuma Uncle kema Shehu fad'an k'inyin salla da wuri, harma 8 ta wuce yau.
Tare suka shiga d'akin baba, innani ma nacan, sun taddashi zaune innani na bashi kunu, aladabce suka gaidasu da tambayar jikin baba.
Baba Yaj
i dad'in ganinsu a tare kuwa, hakama Innani dukda bata nuna a fuskaba.
Baba yace, "Muhammadu idan kadawo aiki inason ganinka". a hankali yake maganar.
''To baba, insha ALLAH dana taso zanzo".
Basu dad'eba sosai suka musu sallama suka fito.
bayan sun gaisa da Jabeer shima, Dan sanda suka zo yana wankane.
Sun tafi da alk'awarin Nazeefa na zuwa weekend d'inan.
Yauma ta iske su Rita na jiranta, Dan harma F'aiza tarigata zuwa, ta k'arasa tana tsokanar Fa'iza da wak'ar mai ciki eye ganina
n tafe.
Duk dariya sukayi, Fa'iza tace, " haba yarinya kema kwana nawane".
Hararta Amatallah tayi, tace, "fatan tsiya".
Goodness tace, " na arzik'i dai".
Dariya duk suka kumayi.
Kusan 12 Lecturer d'insu na English bai shigob
a, dukma sun fidda rai da zuwansa, wasuma suna k'ok'arin barin hall d'in sai suka hango wani malami na tahowa. Gabatowarsa ta saka wani d'alibi fad'in "kuttt wlhy kowa ya nutsu boss ne da kansa zai mana lecture yau......"
Bai gama rufe bakiba Uncle yas
higo, mamaki sosai Yakama Amatallah, dama Uncle yanada alak'a da school d'innan har haka? Tasan dai kamar yana aiki anan, amma bata d'auka yana Lectures ba. Mamakinsa yakuma kamata, yayi masifar tsare gida alamun babu wasa kenan, ta tuna Uncle mai yawan fa
ra'a ashe haka yake a waje. Sai dai yanda 'yan class d'in suka nutsu abin yaso bata dariya, musamman idan tayi dubi da yanda aka raina wasu lecturers d'in, bakamar wasu group na samari da 'yammata da ake kira *Gayun zamani* kallonta takai mazauninsu tagans
u a nutse kamar basuba.
Kallonta ta maida ga Uncle d'in dake magana cikin nutsuwa dakuma kwararren Turanci. Yana bayanine akan zai d'aukesu lecture d'in saboda lecturer mai d'aukarsu yasamu Accident a daren jiya.
Nan suka shiga mishi addu'a.
Tunda yashigo yaga Amatallah, amma yashare tamkarma baisan da ita a hall d'in ba, saidai tuni Fa'iza dasu Rita suka ga kallon dayake satarta dashi, hakanne yasasu shan jinin jikinsu kodai shine Uncle? dukda Amatallah bata sanar dasu Uncle na aiki ananba.
Harya gama lecture d'in yafita sannan suka samu damar tanbayarta, dariya kawai tayi batace komaiba, yayinda Rabin hankalinta ke kan 'yan class d'in dake gulmar Uncle, wani d'alibi harda mik'ewa yaje inda lecturers kan tsaya idan zasuyi lecture ya kwaik
wayi salon Uncle d'in, nanfa aka kwashe da dariya, d'alibin yace, "please guys bai burge kuba?".
Nanma suka amsa da sosaima ana dariya, wata ma a 'yan matan ta mik'e tana fad'in " aini babu abinda yafi d'aukar hankalina gareshi sai salon maganarsa ma
i sanyi da takunsa, kai jama'a malamin nan yayi over, inama zan dace da na tsinci tsuntsu daga sama".
Nanma dariyar aka Sanya da sakin ihu.
Ta kuma kwaikwayon muryarsa yanda yafad'i sunansa, my Name is Muhammad Ahmad labbo, nine zan cigaba da
jagirantarku kafin mai d'aukarku yasamu sauk'i.......
Salon nata yasakasu kwashewa da dariyar ihu suna kiran saikinyi zee-zee.
Ta shafi inda ya d'ora hannunsa ta sumbaci hannunta da fad'in "I love you so much Muhammad mai babban suna".
Na
nma dai bata sake zaninba ihu sukayi.
Dukda wannan Abu dake faruwa Amatallah tayi kicin-kicin da fuska ko sau d'aya batayi dariyaba tunda budurwarnan tafara kwaikwayon Uncle.......
Maganar zee takuma katse mata tunaninta, " kai my guys, ammafa baw
an ALLAH nan akwai tsare gida, ya matarsa keyi?".
Wani yay caraf yace "zee-zee dakin Shiga daga ciki zaki canja manashi".
Dariya ta tuntsure dashi, sannan ta rungume hannunta ak'irji tana lumshe ido, " wayyo! ALLAH Da nikam nasamu duniya, sai
dai kumin addu'ar samun lahira kuma, wlhy da gaske yasace zuciyata sonsa nak.........
Amatallah bataji k'arshen zancenba tatashi tafice saboda wani masifar tsanar zee daya turnik'eta, harma da sauran 'yan ajin dake tayata da ihu.
Rita dasu F
a'iza suka take mata baya da sauri suna kiran sunanta.
Baki zee ta ta6e tana rakasu da harara, kafin ta kalli 'yan ajin tace "tofa kunga wani Sabon salo, ko wata ke sonsa a cikinsu? Tab wlhy Ashe da anyi yak'i a bayaro".
Sosai yanzu ihunsu y
afi na d'azun, wasu dasuma abinda zee take bai birgesuba suka fara ficewa, wasu kam suma abinda kedamun zee shike damunsu wato son Uncle d'in (basusan tsoho bane......lol
ππ
).
Da k'yar su Fa'iza suka lallashi Amatallah dake kuka, goodness tace, "ai
hankali aka kiya miki, saiki tashi dan kamo mijinki, wazai kallesa yace matansa Uku bare yayi tunanin yakai shekarun dakika fad'a mana, wlhy sisi kardai kiyi sake.....
Sosai suka mata fad'a, bakamarma Fa'iza dakejin tamkar ta mangareta.
Koda aka
tashi lecture d'in k'arshe wajen 2:30 bata nemesaba, dukda kuma yace idan tagama ta kirashi, tafiyarta tayi bayan tasha gargad'i wajen Fa'iza akan kartaje tamasa shirme tunda bashine yace zee tasoshiba, kuma tabata shawara akan abin sharruwa daya kamata t
a had'a masa.
Tadai tafi tana zun6ure-zum6ure. (Ama...kishi lol
π
)
_________
Uncle kam baisan wainar da'ake toyawabama shi, saidai idan yatuno yanda Amatallah ke satar kallonsa a aji yakanyi murmushi.
Yasamu ganawa da dukkan lect
urers d'in, Yakuma kawo musu kudirinsa na kafa k'ungiyar matasa dakuma zawarcin abokan tafiya.
Wasu sun bada had'inkai, wasukam sunata 'yan kame-kame saboda sunji maganar hardata kud'i, duk Uncle ya lura dasu.
Ya tausasa harsher yana fad'in " kar
fa hakan ya dameku, bawai tilasne saika zuba kud'inkaba, inhar zuciyarka atsarkake take da nufin son a gyara tafiyar matasan zaka iya bada gudun mawarka, Dama munsaka maganar kud'inne saboda tallafama Matasan dabasu sami koda karatun secondary d'inba, sai
Mike ganin Sana'a yafi dacewa su a tallafesu da ita, saikuma wad'anda karatun Nasu ya tsaya iya secondary d'in, sunada buk'ar mu taimakesu domin cigaban karatunsu, saboda wasu sun cancanta amma rashin tallafi yasakasu maida takardunsu kasan jakka sukoma ma
ula ko dabar siyasa ko shaye-shaye, akwai kuma Matasan dasun kammala karatun amma babu aikinyi, bazai yuwu kowanne saiyazama ma'aikacin Gwamnati ba, Dan bazata iya d'aukar kowa aikiba, to kunga saimu tallafa musu da sana'oin hannu dazai rik'e rayuwarsu kod
an rage musu rad'ad'i wajen tunzuruwarsu ga aikata ta'addanci, mukuma cire musu ak'idar nayi karatu dolene Nina naga kaina a office. Wad'annan hanyoyin zasu rage ma matasanmu yawan Shiga TARKUNAN 'yan siyasarmu masu gur6ata tunaninsu da kud'i harsuna hadda
sa mana rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI*, kudancinmu sunrigada sunyi nisa a irin wannan taimakon, zakiga mutum d'aya ya d'auki nauyin yara goma karatu, koma fiye dahaka, babu kuma abinda suka had'a, kawai k'auyensu d'ayane. Amma mufa 'yan arewa duk iri-iren
wad'annan abubuwan bamayi, kullum burinmu mu Gina k'aton gida, musa tsala-tsalan mata da ma'aikata masu yimusu hidima, saika samu harabar gidan mutum d'aya da mota goma, har yaran gidan k'anana sunada motarsu da ake kaisu yawo, amma gawasu suna cikin wahal
ar rayuwa bama tausayinsu, idan munga idonsu ko kud'insu sai sun tsaya takarar kansila ko ciyaman ko d'an majalisa ko gwamnan jaha, to sannanne zasuna mana 6arin kud'i kamar basusan ciwonsuba, a wayonsu idan sun hau kujerar mulki sunsan zasu maida fiye da
abinda suka watsa mana".
"Mun manta damaganar alk'awuran aiki dasukai masa, wannan tunanin namune ya Karya arewacinmu, akowane lamari mune koma baya, yanzu damuna taimakon matasanmu wasu azzalumai sun isa su sami damar haddasa mana tantin ta'addaci
a yankinmu? Bakwajin ciwon yanda ake kashe mana matasa ana kama wasu acikinsu ana jinginasu da ta'addancin? Idan kana ganin babu d'anka aciki ko k'aninka, baka tunanin ta6ar6arewar komai har 'ya'yan naka su taso suma sugaza amfana da komai na k'asarsu? Shi
n bakwa tunanin ba ayanzun matsalar takeba sai zuwa nangaba mun rasa jagororin tallafin arewacinmu, sufa matasannan damuke zuba ido wajen kallon lalacewarsu koma jagorancin lalacewar tasu watarana sune zasu zamto rik'e da k'asar. Shin mikuke tunani akansu
idan k'asar tazama a hannunsu? Kuna ganin 'ya'yanmu k'anana zasu shane? Kokuwa yankinmu damu kanmu zamusha? Kufayi tunani akan wannan lamarin, dan duk d'inmu iyayene, kuma yayyane, musan zafin damukeji yayinda mukaga d'aya acikin zuri'armu kangararre, shin
bakwa tunanin ya sauran iyaye sukeji suma?. Akiraka mai kud'ine abin birgewa kokuwa ALLAH ya aminta da k'yawawan aiyukanka? Wannene za6inku?!!!".
Duk shiru sukayi tamkar ruwa yacisu, saikuma jikkunansu sukayi sanyi da dukkan furicinsa, sunsan ta
bbas gaskiya yake fad'a, nanfa k'ananun maganganu suka fara tashi k'asa-k'asa.
Cikin fusatar 6acin rai Uncle yakwashi takardunsa yafice daga d'akin taron, duk kiran da Alhaji Sabi'u da shugaban makarantar kemasa bai ko waigosuba.
Ajiyar zuciya Alh
aji sabi'u ya sauke, ya kallesu da kulawa "kuyi hak'uri ransa yarigada ya 6aci sosai, Alhaji Muhammad labbo mutumne mai kishin k'asarsa da yankinsa, mai irin tunaninsane kawai zai fahimci zafi ko bak'incikin dayakeji akan ta6ar6arewar Arewacinmu. Ga form n
an duk mai son kasancewa a tafiyar tamu saiya samu shugaban makaranta ya yanka ya cike, naira dubu d'yane kacal, bayan mun mammala samun abokan tafiya kuma saimu fuskanci tsare-tsare nagaba, Dan abin yazo mana a kure, za6e yagabato, somuke kuma mu nunama '
yan siyasar k'asarnan matasanmu sune *KASARMU* dolene kuma a dama dasu tako wane fanni."
Daga haka shima yamusu sallama yafice, yarage dagasu saisu.
Nan dai sukaita tattauna lamarin, wad'anda sukayi na'am atake suka yanki form d'in.
Wasu kuma d
ai basuce komaiba a kan lamarin.............β
π»
_bara nabi Amarku sarkin kishi
πͺπΆπ»
ββ_.
π€©ππ»
One Luv my sweet fans
π₯°
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
πππ»
_*
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_{
home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
_Gundumemiyar gaisuwa gareku da fatan alkairi *Hafsat Rano, Ummu Hanan (mamana) Mzzdaddy, Maryam wasagu
, Aysha Manshat, Maman Shaheed, Ummu Affan (mamana) Bily s fari* na gaisheku nakuma Na gaisheku, inayinku over, ALLAH ya k'ara basira agareku writer's d'inmu
π₯°π₯°π₯°ππ»π
_
____________________
*_Number 28_*
____________________
Tana cikin Na
pep kiran Fa'iza yakuma shigowa, d'agawa tayi batareda tayi maganaba.
Fa'iza tace, "wlhy Amatullah ina mai baki shawarar karkije gida kina kuka ko fushi, ki saki fuskarki, dama wai haka kike da kishi kema?".
" bazaku ganeba Fa'iza, nifa ba ki
shi baneba".