Showing 54001 words to 57000 words out of 111738 words
salon alkunya tunda bai fito kaitsaye ya nuna mata manufarba.......
Katseta yayi da fad'in "kinyi shiru Khadija".
" Uncle nidai dukda bansan miyasa kake son hakanba Na amince ta kwana wlhy". Tayi magan
ar a kunyace.
Murmushi yayi tareda sumbatar bayan hannunta, yace, "ALLAH yay mini albarka Khadija".
Shi duk zatonsa Amatallah da gaske bata gane Inda ya dosaba, Dan kallonsa k'aramar yarinya shataf yake mata.
Nidai nace, " hummm Uncle kenan, sh
ekarar Amatallah 20 yanzu ace batasan miye aureba?, bayan yanzun yaramu sai dai addu'a, 'Yar shekara 15 saita baka labarin mi ake a gidan aure tsaf, in kayi wasa takuma fad'a maka komai dalla-dalla, ai waya
π±
babu masifar dabata kawo manaba a wannan zaman
in, sai dai kawai wad'anda ALLAH ya tsare, amma jeka Facebook kawai kaga ta6ar6arewar tarbiyyar yaranmu.
π
Kama godema ALLA daya baka Amatallah d'in mai kunya, yanda idanun 'yan matanmu ya bushe yanzu suka d'au kunya k'auyanci ai abin ba'a magana, A
LLAH dai ka shiryamana zuri'a kawai.
ππ»
Mik'ewa yayi yana fad'in "tom tashi ki kwanta namiki addu'ar barci".
Kanta a k'asa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta tace, " Uncle ai bansa Sleeping dress".
"Okay, to tashi kisa ka".
Shiru ta
yi kamar bazata tashiba sai kuma ta mik'e ta koma wajen Waldrop d'inta ta ida zaro kayan data fara d'auka d'azun. duk Uncle yana tsaye yana kallonta. toilet d'inta tashiga dan ta Sanka.
Murmushi yayi yana shafa gemunsa, a ransa yanajin k'aunar Amatall
ah da yanda take komanta a nutse, wani lokacin idan tayi Abu yakanga tamkar brother d'insa (to jini ba k'arya baneba aii Uncle).
Yana nan tsaye harta fito, kallonta yayi, dukda tasaka Riga da wando na barcin, hakan bai hanata sanyo hijjabin ba a sama.
Tsaye tayi a bakin k'ofar kanta a k'asa.
Yace, " zoki kwanta mana, ko zakiyi wani abunne kuma?".
Kanta ta jinjina masa alamar a'a.
"Ta kowa yayi a hankali har inda take, ya kama hannunta batareda yace komaiba, har gaban gadon sukaje
sannan ya saki hannunta yana nuna mata gadon da yatsa.
Bata yarda ta kalleshiba ta hau gadon ta kwanta bayan ya gyara mata filon.
bargo yaja ya lullu6a mata zuwa k'irjinta sannan ya rankwafo saitin kanta daf. ita dai Amatallah kallon ikon rabbani
takeyi, da girmanta an maidata baby.
Hannu yasa cikin bargon kad'an yafara tattara hijjabin jikinta, a hankali ya furta "d'aga my best a cire wannan hijjab d'in, babu k'yau kwanciya da hijjab, zai iya kawo matsala ga mai barci, kamar shak'e mutum
da makamancin hakan".
Kanta ta jinjina masa a hankali, Dan yanda ya rank'wafo kanta saitaji kamar zai fad'o mata, har saukar numfashinsa tanaji, taimaka masa tayi yacire hijjabin, kafin ya ida cirewa tayi saurin Jan bargon ta rufe k'irjinta.
Y
ana kallonta, dan haka yay dariya a zuciyarsa kawai. yana gama cire mata hijjabin ya ajiye gefe ya zauna kusada ita a bakin gadon. addu'oi yamata kamar yanda yakema sauran matansa, ya tofa mata a hannu ta shafa itama da wanda tayi, mik'ewa yayi yasake rank
wafowa ya gyara mata bargon, sannan yamatso da fuskarsa daf da tata, hakanne yasaka Amatallah saurin rintse ido dad'an k'ank'ame jikinta zuciyarta tana kuma bugawa da k'arfi saboda kusantowarsa garesa sosai.
Kiss ya manna mata a goshi da kumatu, sai k
uma ya dakata yana kallon fuskarta da yanda take k'ara k'ank'ame ido, yanda tayin saita bashi dariya harya murmusa, yace, " bud'e idon mana my beat ki kalleni".
"Ya salam" tafad'a a zuciyarta tareda mamakin wannan lamari na Uncle, tana masa kallo
n salihi Ashe shima A ne na bugawa a jarida.......
Batakai k'arshe. Tunanin taba taji saukar la66ansa akan nata.
A zuciyarta tace na shiga tara ni Khadija, Uncle zaka kasheni da kunyarka wlhy.
Saida ya sumbaci la66anta sau biyu sannan y
amik'e tsaye sosai yana murmushi idonsa a kanta face d'inta.
"Sai da safe my Heartbeat! ko kawai nashigo bargon mu kwanta abinmu, mu warware sadaukar da kwanan?".
Bargon taja da sauri tarufe har kanta gaba d'aya.
K'aramar dariya yayi ya
matso kamar zai bud'e mata bargon, murya k'asa-k'asa cikin rad'a kamar mai tsoron ajisu yace, " Ina matuk'ar Sonki keda Salonki my best Darling. goodnight, zan kwana da mafarkinki".
Bai jira cewar taba yakama hanyar fita, yamasan bazata ceba d'in, fit
ilar d'akin ya kashe ya fice, bayan ya kunna fitilar wayarsa.
6angaren Aneesa ya komai, tana nan kwance yanda ya barta, tayi kuka harta godema ALLAH, bai mata maganaba ya d'auki Saifudden ya fita, wajen Fateema ya kaisa, dukda barci takeyi abinta han
kali kwance itada yara, haka ya shinfid'eshi kusada 'yan uwansa yamasa addu'a sannan ya koma wajen Aneesa. yanzuma yanda yabarta haka ya isketa, ya d'auke Siddiqa daga gabanta ya gyara mata kwanciya gefe saboda gadon babbane ba laifi.
Duk abinda yakeyi
Aneesa na jinsa, tun shigowarsa ta farko har d'aukar Saifudden ya fita dashi, ko kad'an batayi zaton Amatallah zata yarda ya dawo wajen taba, anya idan itace zata iya kuwa? sai taji Amatallah ta birgeta.....
Ajiyar zuciya ta saki yayinda taji ya rungu
meta.
Hummm, nayi nan, Dan yau Uncle da neesarsa babu sauk'i.
π€
πΆπ»
ββ
Tumda Uncle yafita Amatallah ta sauke ajiyar zuciya a fili tace, ''kai Namijima sai abarsa, duk yanda kake kallonta a nesa ba haka bane, saika zauna dashi kake gane Natural co
lour d'insa, wlhy a baya idan wani yacemin haka Uncle Muhammad yake saina k'aryatashi, humm Ashe ya wuce tsammanina ma".
Hannu takai ta shafa bakinta, saikuma taja bargo da sauri takuma rufe fuskarta tana rintse ido da fad'in ''wayyo Uncle Muhammad ka
kasheni wlhy, yanzu tayaya zan iya kallonka da safe?, shikenan na mutu ni Amatallahin Ammi da baba".
Haka taita sambatunta ita kad'ai, hardai barci yazo mata, takuma 'yan addu'oi ta gyara kwanciya.............β
π»
Ni dai mai d'aukar rahoto nayo w
aje ina dariya wa shirmen Amatallahin ku
πππ»
.
_Nasan saboda yawan page d'in nan yau har saikun kai jibi kuna karantawa
π€
, kusan Read more 7 fa
π€£π
, asha karatu lfylfy._
π
ββ
π€©ππ»
One Luv my sweet fan's
π₯°ππ»
.
*_ya ALLAH ka gafartama mahai
fina._*
πππ»
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
*_Humm
m, jiyakam ai magana gagarata tayi a kowanne groups, dan jiya kad'an garage nasha Suburbud'a hannunta masoyan Amatallah
ππ
, Aneesa zata jamin jaza'i, nibada laifiba
πππ»
._*
Haba masoyan Ama..., karku damu zaku fanshe ne
π₯°ππ»
.
___________________
_
*_Number 23_*
____________________
Koda Uncle ya koma gida ya taradda Fateema kawai a falo, Aneesa kam tana 6angarenta.
Gaban Fateema ya k'arasa ya sumbaci Goshinta da cikinta, d'agowa yayi yana dariya da fad'in nabiya bashi my tee...
Itam
a dariyar tayi tana fad'in kafita koba sabulu".
zama yayi inda Aneesa ta had'a break fast, batareda ya nemetaba yazauna yaci kad'an kamar yanda ya saba. Fateema kam dad'ine ya kamata, tasan cin abincinnan dayayi bai nemi Aneesa ba saitayi tamkar ta fa
she dan haushi.
Yana hayewa samansa itama ta tashi tashige 6angarenta, dama da biyu ta zauna falon.
π
*********
Amatallah bayan sun fito lecture suka nemi waje can gefe suka zauna suna sauraren ta.
A nutse tabasu labari tana kuka, suma sunayi,
aka rasa mai lallashin wani cikinsu, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru suna bama Amatallah hak'uri, sosai suka tausaya mata.
Itama Rita tace zata basu labarinta gobe.
Duk suka amsa da ALLAH ya kaimu.
Amatallah tanason tambayarsu mag
anar da Aneesa ta mata da safe, amma tana ganin kamar suma bazasu fahimtaba, musammanma su Goodness, dan haka tayi shiru da nufin zata tambayi Fa'iza ita kad'ai.
Suna fitowa lecture ta k'arshe Goodness da Rita suka nufi hostel, yau basu musu rakkiya
ba saboda kowa yagaji.
Da wannan damar Amatallah tayi amfani ta sanarma Fa'iza abinda yafaru tsakaninta da Aneesa, dakuma tambayar da Uncle yamata ta 6oye masa.
Kallon mamaki sosai Fa'iza kema Amatallah, tace, "dama bakida wayo haka Amatallah?. W
ace mace ke sadaukarma kishiya kwananta? Sai dai haihuwa ko lalura wlhy, Lallai bakisan miye kishiba Ashe. Wlhy duk da kike ganina k'aramarnan bana bari kishiya tasamu lagona, bazanyi kishin haukaba kuma bazan raga mata ba".
" ban ganeba Fa'iza, ke
ma kinada kishiyane?".
Dariya Fa'iza ta mata, "lallaima Amatallah, koda yake duk yandafa muke dake d'inan babu Wanda yasan gidan wani, toni rana d'aya aka d'aura aurena da kishiyata, ni da safe ita da rana, kuma yanada wata matar, saidai tana gidansu
, sa6anin dasuka samune yayo auren huce haushi damu mu biyu, yanzu kuma shirin dawowa take an sasantasu".
Ba k'aramin mamaki da al'ajabi bane yakama Amatallah, a ranta tace halin maza sai abarsu. a fili kuma tace "amma Fa'iza kunsan da haka kuma kuka a
ureshi?".
" to yazamuyi Amatallah, auren zumincine, da mamana da babansa uwa d'aya uba d'aya, waccan kuma budurwarsace dama, saboda itanema suka rabu da matarsa akan yace zai Aurota ta tada hankalin kowa a families d'in, harya kai gamata saki d'aya s
aboda sakko iyayensa datayi a haukarta, mamansa kuma tanada zuciya, hakan yasa tace bayan auren dayakeson k'arawa yahad'a dani mu zama biyu, saitaga yanda uwargidansa zatayi d'in, shinefa dalilin dayasa aka d'aura aurenmu rana d'aya, ni da safe ita da azhu
r, kusan shekara biyu kenan, uwargidan bata kuma wani aurenba, bakiga yanzu duk yanda tafita hayyacintaba, kullum cikin bibiyarsa take tana bashi hak'uri da rok'on ya maidata, dan suna matuk'ar son juna, to shine manya dai suka shiga aka sasanta, yanzuma j
ibi zata dawo".
"Tabb, lallai wasu matan basuda hankali, nifa banga mafitaba ga macen da zata rud'ar da kanta wai dan miji zai sake aure, raini yake kawowa wlhy, kowa yanamaka kallon shashasha, kinga yanzu ta jama kanta daga d'aya anmata biyu, kuma
mijin bazai kalleta da darajaba kamar da can?".
" wlhy kuwa hakane Amatallah, ALLAH dai ya sassauta mana kishinan, wasu Matan sun Gaza gane kishi cikin SIYASA tafi kawo zaman lfy da daraja wajen miji, kamazo kana hauka kan Namiji baisan kanayiba".
"Tokin gani, kuma wlhy kishiyarma indai kina nuna mata komai ba komaiba a fiska koda kina kishinta a rankin saikinga tana shakkarki da tsoron takaki, dan baki bata wata k'ofar dazata rainakiba, kuma mijin bazai ta6a aminta ta raina kiba, kinga ai kin nema
ma kanji daraja har wajen dangin mijin. yanzu wlhy Uwargidanmu inkikaga yanda take kishinta saita burgeki, amma Aneesa ba a magana, harma mamaki take bani".
''Karki damu Amatallah, zan koya miki wasu abubuwan, dukda shi zama da kishiya basai ankoyama m
ace shiba, wahalama na sakata ta koya, kamardai yanda ni wahalarce tasani koyon".
"Kai dan ALLAH?".
dariya Fa'iza tayi, " ALLAH kauwa Amata, ke idan INA Baki labarin gidanmu ALLAH saikice k'arya nake, ai garaku na fahimci kishin masu Ilimi akey
i a gidanku, mu Amaryarmu tafi uban kowa zafin kishi, ga uwargidan itama babu sauk'ice".
"To ALLAH ya k'yauta".
Nandai suka d'an tattauna, Fa'iza ta ankarar da Amatallah abinda Aneesa ke nufi da maganarta.
" kinga daga yanzu kema sauk'i shir
ya aii, amma dan ALLAH inason tambayarki, kumafa ki fad'amin gaskiya inhar kin yarda dani".
"Na yarda dake wlhy Fa'iza, shiyyasama nafad'a miki sirrina ai".
Murmushi Fa'iza tayi, sanan taja hannunta suka zauna kan wata baranda, dan dama basukai
ga fita gate ba.
Kafad'arta ta dafa, " Amatallah shin kinason Uncle d'inki kuwa?".
Dariya Amatallah tayi, sannan tace, "gaskiya kikace na fad'a miki kuma zan fad'a miki Fa'iza. lokacin da akai aurenmu dai bana masa son aure, dan kallon uba nake ma
sa, lokacin ga rud'anin rashinsu Ammi, amma tunda na fahimci yanason cikar burina akan karatu, da k'aunar dayakema mahaifina sainaji nafara masa SO irinna aure, Ahankali kuma yaytamin abubuwan dasukaja ra'ayina ta waya, da kuma taimakon shawarwari da k'anw
arsa Nazeefa taita bani, saina kuma gane babu Wanda yasan muhimmancina da kuma zaiji tausayina kamarsa, nasan kuma wannan babana ya kalla harya k'ulla wanan auren, Wlhy Fa'iza ina son Uncle har cikin raina, saidai ina masifar jin kunyarsa, musamman idan na
tuna alak'arsa da mahaifina".
ππ»
Jinjina Fa'iza tama Amatallah, " ammafa kin birgeni, dan kar6ar k'addarar ki dakikayi shine Abu mafi muhimmanci, na tabbata kuma k'addarar alkairice, dawatace saita bijire tace yamata tsufa. Maganar kunyarsa kuma ka
rki damu, daga randa kuka kasance k'ark'ashin inuwa d'aya zaki rage da kanki wlhy, nima nayi wannan kunyar Akan ya Usman, amma yanzun hummm".
Dariya sukayi gaba d'aya harda tafawa.
Fa'iza tacigaba da fad'in ''yanzu Amatallah akan abokan zamanki za
n baki shawara, saifa kin mik'e sosai, inba hakaba su maidaki sakarai har mijinma yacigaba da d'aukarki haka. Ki kama mijinki ram ki rik'e dan yanda kike bani labari nakula mijinku d'anson soyayyane da kulawa da mace, kiyi k'ok'ari kema ki samu rabonki kaf
in su tsufar dashi kinan kunya na tsutarki. inhar yau yabuk'aci ki kar6i kwananki wlhy ki kar6a, kuma ya buk'aceki karki bijire masa, yanda yanzu ake yayin mutuwarnan".
''Kai Fa'iza ALLAH kinban kunyafa".
"A'a ah yarinya zauna kallon ruwa kwad'o
yamiki k'afa, yanzu maza tsada sukeyi shiyyasa kowacce mace ke tattali idan tasamu, karki bari kunya tasaki zama bora a gidan mijinki. kuma kin burgeni dabaki fad'amai ainahin abinda Aneesa tamikiba, dan da kanki yakamata ki rama, karki raga mata, intaga k
eda uwargidan halinku mai k'yaune itama zata fara gyarawa, kinga kun jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan, Ku k'ara daraja da soyayyarku wajen miji, kun kuma gyara halayyar abokiyar zamanku yanda zaku samu zaman lafiya sosai".
" gaskiyane Fa'iza, s
hikenan zanyi amfani da shawarar ki, Aneesa kuma zan nuna mata ainahin Natural colour d'ina, dan nakula kallon shashasha takeminne, batasan Amatallah bata d'aukar rainiba, halin rayuwane kawai ya maidani haka, bana fad'a amma kuma nasan yanda zan zauna dak
owanne irin mutum".
"ALLAH ko kwanan dakike gani na barmata yahad'a da inajin kunyarsane, kuma itama ina son na gwadata, shiyyasama naje tayata girkin da safe, dannaga yanda zata kar6eni, hakan duk yana cikin dabarun da Anty maijidah ta koyaminne".
ππ»
Tafa mata Fa'iza tashigayi tana dariya, " da k'yau Amatallah, Ashe kemad'in A ce ban saniba".
"ALLAH Fa'iza ba wai haka baneba fa, kawai dai bana son rainine ALLAH kuwa, ina son idan na nuna maka girmanka kajashi".
" gaskiyane Amatal
lah, ALLAH yabamu zaman lafiya dai, nima jibi uwargida zata dawo, bansan kuma wane zama zamuyiba da ita".
"To ai yanzu kece Uwargida kenan".
Dariya Fa'iza tayi sosai, takama k'arfe ta mik'e da k'yar tana fad'in "su Uwargida anji jiki".
Ama
tallah ma mik'ewa tayi tana dariya, "babufa wani aniji jiki, karkima yarda akawo miki raini, kece Uwargida".
Haka dai suka tafi suna tsokanar juna, kowa tasamu Napep tashiga.
Shawarwarin Fa'iza sunyi tasiri sosai a zuciyar Amatallah, Hakanne k
uma yasata d'aukar aniyar ramawa ta cikin ruwan sanyi, a ranta tanajin itama zata shiga a dama da ita, dan tana son Uncle d'inta, tunda tasan zama dashi babu cangi har Abadan saidai mutuwa, to mizaisa tacigaba da cutar kanta Aneesa na kallonta a banza, ita
fa ta tsani tana ganin mutuncin mutum yanemi zubda darajarsa a gurinta,