Showing 72001 words to 75000 words out of 111738 words
"Oooh to miye?".
" humm, mubar maganar kawai".
"Shikenan an barta, kiduba Na tura miki wani Abu, amma Dan ALLAH inamai rok'onki ko'a fuska karki bari mijinki da abokan zamanki suga fushi a fuskarki, sannan kinutsu sosai wajen shiry
a masa abincin shan ruwa, kikuma tanadi kalaman kare kanki a wajensa idan ya tambayeki dalilinki Na tahowa Baku nemesaba". Kitt Fa'iza ta yanke wayar batareda tajira mi Amatallah zata fad'aba.
Ajiyar zuya Amatallah ta sauke, ga wata k'aunar Fa'iza n
ashiga harcan k'asan ranta, tabbas k'awa tagari rahamace ga kowanne bawa, shigowar Fa'iza rayuwarta ALLAH ne kad'ai yasan nasarorin data kawo mata, takanji tamkar ciki d'aya suka fito da Fa'iza. Addu'a taitayi a zuciyarta hartaji abinda ya rik'e mata mak'o
shinan ya koma, har sukaje k'ofar gida tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, shidai mai napep yanata aikin tuk'insa da saurarenta, ALLAH ma ya taimaketa ba irin masu shegen surutunnan baneba da shiga abinda ba huruminsuba.
Kud'insa ta basa kafin ta shige
ciki. Babu kowa a falon, sai dai yanata k'amshi mai dad'i. Harga ALLAH bazata 6oyeba tsaftar matan gidan Na birgeta, koyayane bazaka tadda falon a cikin dattiba, shirun gidan ya tabbatar mata yara sun tafi Islamiyya.
Bata shiga d'akiba, saita lek'a k
itchen, dan tanata tunanin komi yara zasuci idan sun dawo? batayi zaton wani acikinsu zaimata girkin daya zama wajibi akantaba. Sai dai tashiga mamaki yayinda taci karo da kular abinci dakuma fleets alamun anci abinci, tabud'e kular (jallop d'in shinkafa C
e) maidawa tayi ta rufe tana mamakin waye yayi girkin to acikinsu? Koda wasa tamasan ba Aneesa bace.
Kasa hak'uri tayi dai, tashiga 6angarenta a gaggauce tayi wanka tai sallar la'asar data risketa a hanya, bak'ar doguwar riga jallabiya tasaka, hula ta
sa a maimakon d'ankwalin tanufi 6angaren Fateema dannan tafi zaton an taimaketa.
A falo ta isketa tanashan fanka, a girmame ta gaisheta, itakuma ta amsa cikin fara'a da k'ok'arin danne kishinta.
"Anty Fatee ngd sosai, nabarki da wahalar girki"
.
Fateema ta kalleta tana d'an murmushi, " ayya Amatallah momyn yarace tayi banibama wlhy, taga har yara sunkusa dawowa baki dawo bane".
Mamaki ya kama Amatallah, shiyyasa akeson ka k'yautata zato wa d'an uwanka, duk mugun halin mutun tawani 6
angaren sai kaga mutumin kirkine, tabbas ita kanta tasani, inhar tacire maganar kishin tsiya Na Aneesa batada wata hujjar zaginta akan mugun hali. fita tayi tanamai jin nauyin zargin datama Aneesa.
6angarenta tashiga a sanyaye, a falon sai Siddiqa
fake wasa kawai, tana ganinta tataho da gudu tana gwarancin su Na yara, Dan maganar tata babu dad'i sosai har yanzun, sama Amatallah ta d'agata tana cafewa suna dariya.
Ahaka Aneesa tafito daga bedroom ta samesu, (duk mai son d'anka dolene duk zafinsa
dakakeji kaji sassauci), Dan haka Aneesa ta kallesu da murmushi a saman fuskarta, zama tayi abinta batareda ta tankaba. Amatallah ta sauke Siddiqa a cinyarta bayan ta zauna, gaisheda Aneesa tayi a girmame kafin tace, "Anty ngd fa da girki, nabarki da waha
la ALLAH ya raya su Siddiqa".
Murmushi Aneesa tayi, " karki damu da wannan, taimakon juna tilasne agaremu komin kishin damukeji akan juna, kishi daban k'yautatawa daban".
"Gaskiyane Anty ngd". daga haka tataso tafito rik'eda Siddiqa.
Zaman
ta tayi a falonta bayan tazubo abinci, tanaci tanabama Siddiqa harsuka gama, daga nan taita biyema yarinyar suna shirme..
A wannan lokacinne kuma Uncle yashigo gidan, bai wani yimusu horn ba yafito dakansa yabud'e gate yashigo, wannan yasa babu wa
dda tajishi dukda kuma bama wutace ke akwaiba bare ace k'arar TV ta hana. hankalin sune kawai bai jeba, Aneesa ma waya takeyi da mutanen Ghana tun fitar Amatallah.
Fateema kuwa tanashan fankarta da ta samu isashshen charge tana karatun addu'in 40rabban
a.
Itakuma Amatallah shirmensu da Siddiqa ya d'auke hankalinta gaba d'aya, tanason yara kodan tasowa datayi ita d'aya kwallin kwal agidansu, koda suna jos haka zatayita jajubo 'ya'yan jama'a Na makwafta, wani lokacin Ammi taita fad'a tamkar ta ari ba
ki, sai dai Amatallah tabata hak'uri, ammafa gobe babu fashi saikin ganta dad'an wani ta yayibo.
Harya shigo falon babu wadda ta fito, shi mamakinema ya kamashi, wai duk matannan biyu babu wacce tasan da shigowarsa, (zatonsa Amatallah bata dawo schoo
l ba, shi saima yanzu yatuna ko tanacanma tana nemansa gashi yataho), Ramsa a 6ace yake shiyyasa yay shigewarsa samansa batareda yanemi kowacceba barema Amatallah daya bari a makaranta.
Ruwa kawai ya watsa ya saka k'ananun kaya wando dogo da k'aramar
Riga, falonsa yadawo yad'an kwanta adoguwar kujera ya lumshe idanu badan barciba saidan son dai yasamu damar yin tunanin halayen mutanenmu masu ban haushi darashin Sanin darajar Kansu da mutuncin yankinsu. Ya jima a kwance yana tunani batareda yasan lokaci
yajaba, hardai yafara jiyo hayaniyar yara sun dawo islamiyya.
A 6angaren su Amatallah da gaske babu wacce ALLAH yabata ikon sanin shigowar mai gidan, kusan 5:00pm Amatallah tashiga kitchen, lokacin Siddiaq tayi barci ta goyata. Da abincin gida ta f
ara, tuwon semo.... Miyar Ogbono tayi, Dan komai Na kalolin miya daba'a amfani dasu anan Kano saida Anty furera ta tanadar matashi, musamman miyoyin k'abilunnan da Amatallah duk ta iya mafi yawa aciki, Dan Ammi batayi wasa wajen tsayawa koyama Amatallah ka
lolin abinciba da aikin gida, wannan yasa batada Matsala akan kowanne fanni Na girki dakuma kulada muhalli (kamar Ammi tasan k'addarar d'iyar tata zama cikin kishiyoyi).
Batawani jimaba ta mammala had'a miyarta, sannan ta d'ora tuwo dakuma wani 6anga
re Na kayan shan ruwan Uncle. Dan danan k'amshi yafara baje gida (had INA had'iyar yawu Nima mai rahoto....lol
ππ
) tsaf tagama komai ta kimtsa kitchen d'in, tana mopping yara suka dawo daga islamiyya.
Jin suna Neman Abbunsu yasata fitowa daga kitch
en d'in, Dan duk iyayensu Na d'akunansu. hayaniyar yarance ma ta fiddo Aneesa.
Kusan tare suka fito da Amatallah.
Tuni yaran sun arta sama aguje, sunsan Abbunsu yana gida tunda ga motarsa a waje.
Aneesa da Amatallah suka kalli juna, Ane
esa tace, "dama ya dawo?".
Har Amatallah zatace da bata saniba, saikuma taga ai abin kunyanema ita mai girki bata san miji yadawo ba, kuma alamar yaran ta nuna tabbas Abbunsu yadawo d'in. " eh Anty yadawo babu jimawa sosai, yad'an kwantane ya huta
".
"To, ALLAH yasa lafiya dai, Dan dear baya barcin yamma gaskiya".
Cikin son kare kai Amatallah tace, " kansa ke ciwo".
''Ayya shiyyasa, ALLAH yakawo sauk'i. Wai yanzunan k'atuwarnan kika goya haka? bak'ya gudun ciwon k'irji?".
Murmushi Amatallah tayi, tagyara zaninta data Goya siddiqa dashi daga sama tana fad'in "lah Anty aibatada nauyi".
" lallai kam, sannu da k'ok'ari, aini bama zan iya aiki da yaro a bayaba, Umman yaracema da wannan k'ok'arin".
Murmushi kawai Ama
tallah tayi batace komaiba.
Aneesa ma tajuya d'aki abinta.
Amatallah kam tsaye tayi tana kallon matattakalar benan, kodai Uncle fushi yakeyi da ita danta taho?. Jitai kwalla tacika idonta, jiki a sanyaye tanufi saman, takula gabma ake da shan ruwa
. Baya takoma tad'ibo dabino awani d'an kwano, tad'ora a tire da ruwa da cup, hakan duk yana cikin aikin fa'iza data koyar da ita, da kuma training d'in Ammi dabazata ta6a mantawaba, (kunsanfa duk abinda katashi kaga anayi agidanku mawuyacine kiga kaima Ba
ka aikatashi a gidan mijiba, iyaye saiku kula wlhy saboda 'ya'yanmu masu tasowa).
πππ»
.
A falo ta iskesu shida yaransa, duk suna a jikinsa kowa nabada labarin abinda aka koya musu, sallamarta tasakashi d'ago idanunsa ya kalleta. Koda suka had'
a ido saita sakar masa murmushi, hakanne ya sanyaya zuciyarsa daga haushinsu dayakeji.
"Sannu da zuwa Uncle". tafad'a murya k'asa-k'asa.
Dukda surutun yaran hankalinsa Na kanta, kuma yaji mita fad'a. ya d'auke idonsa akanta yamaida kan Abulkhair
i, "Abulkhairi kuje maza a canja Uniform ayi alwala nima ganinan sakkowa mutafi masallaci kunji".
Atare suka mik'e suna fad'in to Abbbunmu.
Daga shi har Amatallah da kallo suka raka yaran, kowa Na murmushi.
Ya maido kallonsa kanta, " my best
kinyi k'yau da goyon kuwa".
Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "ngd Uncle, kadawo lafiya".
Still murmushi shima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kallonta, " ba godiya zakiminba tunda ba k'yautar Siddiqar nabakiba, kawai kema kidag
e ki haifomin naki".
taji kunyar maganarsa, Dan haka ta kauda kanta gefe tana murmushi.
Yasa hannu yakamo nata, cikin zolaya yace, ''kokuwa yau zamu samune ma kawai nayi shiri?".
Batasan sanda ta dubeshiba tana zaro ido waje, shima yayi yan
da tayi, sai suka tuntsure da dariya kuma.
Tace, "kai Uncle".
Yace, "ALLAH my heartbeat ".
Murmushi kawai tayi, shikuma yashafi kumatunta, "Matsoraciya wasa nakeyi, sorry nataho Na barki a school ban nemekiba, 6atamin rai akayine".
'Dan kall
onsa tayi da mamaki, har zatayi magana saikuma tayi shiru, gwarama kawai tabarsa a yarigata tahowar.
"Fad'i mana".
Yayi maganar idonsa akanta.
" a Uncle babu komai, gashi can ana kiran salla".
"Alhmdllh" yafad'a tareda mik'ewa yashiga be
droom d'insa, babu dad'ewa yafito, da alama alwala yayo da brosh. Zama yayi inda ya tashi, yaci dabino uku yasha ruwa kafin yamik'e yana shafar gefen kumatun Amatallah, "bara naje masallaci babyna".
"Adawo lafiya" Amatallah tafad'a a kunyace".
Itama sakkowa tayi danyin sallar, ta sauke Siddiqa agadonta tashiga bayi.
Su Uncle basu dawoba saida akayi isha'i, zuwa sannan tad'an gyara fuskarta da hoda da kwalli da d'an janbaki kamar yanda Anty maijidda da Nazeefa suka gargad'eta akan bakoda y
aushe ake zuwa wajen miji fuska a kod'eba.
Ranar dai Uncle yaci girkin Amatallah yana mata Santi, itako sai dad'i takeji tana dariya, daga Fateema har Aneesa babu Wanda ya tanka, yara kuwa suna taya Abbunsune.
Yauma a d'akinta ya kwana, tasha
kunya kamar jiya, koma nace fiye da jiya, Dan yaukam Uncle kasa barinta yayi harda 'yan wasanni, Wanda ganin ta tsorata yak'yaleta daga baya sukasha barcinsu, dukda yarigata barci ita tsorone ya yanata saida taji yayi.
*_5days ogo_*.
Kwanakin A
matallah 6 kenan da kar6ar miji, a kwana shidannan ba'a maganar shak'uwarsu, dan koyaya dai tasaki jiki dashi, dama kuma hakan shine fatan Uncle d'in. gashi kuma gobe Fateema uwargida zata kar6eshi ko Aneesa, duk kuma sai Amatallah taji babu dad'i, koba ko
mai tasaba da kwanciyar dasukeyi tare a gado d'aya.
Da daddare suna kwance, barci sukeyi hankali kwance, Amatallah Na jikin Uncle ta dabaibayeshi kamar zata shige jikinsa. bugun k'ofane ya farkar da Uncle, ga Amatallah kam hakan bamai sauk'i baneba, s
aboda shegen nauyin barcinta.
Da k'yar yazame Amatallah a jikinsa yatashi gabansa na fad'uwa, tabbas yasan babu lafiya, yakumafi kawo hakan ga Fateema.
Ilai kuwa yana bud'ewa yaci karo da Aneesa wadda take a rikice, sai yarfa hannaye take tana safa
da marwa.
Yana bud'e k'ofar tayo kansa, " dear Umman yarace babu lafiya, ina k'yautata zaton ko nak'uda wlhy......"
Abinda yafaru shine tun farkon dare bayan Uncle yashiga sunyi sallama takejin babu dad'i dajin alamomin ciwo, amma harya fita ba
ta iya fad'a masaba dankarya tashi hankalinta, saima ALLAH yakawo barci ya figeta da wuri, acikin barci ta farka da matsanancin ciwo, cikin azaba ta d'akko wayarta da nufin kiransa, saidai takira har sau biyu bai d'aukaba, hakanne yasata maida akalar kiran
ga Aneesa. Arikice Aneesa tashigo wajenta, ganin nak'udace ta d'auke yaran d'ai-d'ai tamaida 6angarenta, shine taje ta tado Uncle bayan itama takirasa bai d'agaba. Shikuma ya danne wayarne da filo harta shiga silent bai saniba, wannan ne yasa bai d'aga ki
ransuba.
Har rige-rigen shiga 6angaren Fateema sukeyi itadashi, zuwa sannan kuma Fateema nak'uda gadan-gadan.
Aneesa tace dear mutafi asibiti mana".
"Neesa kalli agogofa, 2:41am akwai had'ari gaskiya, mudai bata taimako muga ko ALLAH zai
sa mudace ta haihu lafiya".
Aneesa tayi na'am da hakan, addu'a Uncle yafara tofama Fateema a ruwa, hannunsa rik'eda d'ankwalinta yana share mata gumi. Aneesa kuma Na taimaka mata dawasu dabarun...
A wannan time d'inne kuma Amatallah tafarka ar
ikice saboda mafarkin Anty Fateema datayi tana kuka, ta laluba babu Uncle, ai babu shiri ta wantsalo daga gadon, hijjabi kawai ta d'ora a saman kayan barci ta tafito, tundaga falo tafara jiyo nishin Fatima da maganar Aneesa tana fad'in daure Umman yara, in
sha ALLAH kin kusa.
Wani nishi da Fateeman tasaki yasaka Amatallah fashewa da kuka saboda tausayi, saikuma tad'an tsagaita taji kukan jariri ko murnarsu Uncle d'in da haihuwar amma saitaji tsitt, saima gauron numfashi da Uncle yasaki tareda fad'in "Fa
teema!!"...............β
π»
ππ»
mun shiga d'ari, kardai Uwargida.....
π€
ba ruwana
π
.
π€©ππ»
One luv my Sweet fana
π₯°
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
πππ»
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_
{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
____________________
*_Number 29_*
____________________
"A'a dear karka damu tana numfashi, n
akula tagajine kawai......
Aneesa batakai k'arshen zancenba Fateema takuma yin wani nishin mai k'arfi saiga jaririya ak'asa tana watsal-watsal, atare suka furta Alhmdllh.
Amatallah ma ajiyar zuciya ta sauke, tana dariya tana kuka, Uncle yafito d'a
ura ruwa da Aneesa ta buk'ata ya ganta tsaye ta jingina da Bango idonta arufe, ganin tana kuka da dariya saita bashi tausayi, yajawo hannunta ya rungumeta yana fad'in ''to kukan ya Isa haka ALLAH ya sauketa lafiya, yaushema kika tashi?".
Tana share h
awayenta tace, " Uncle tun d'azunne".
"To shiga ki taimakawa Aneesa Ku gyarata bara Na d'ora ruwan zafi".
" to Uncle ".
Tsaf Aneesa da Amatallah sukaita hidimar taimakon Fateema, Aneeaa taima jinjira wanka, Amatallah ta gyara wajen, yayinda Un
cle ya taimakawa matarsa shikuma, kafin Safiya komai yayi tsaf, tasha tea ta kwanta itada sargad'ed'iyar jaririya dansu huta. ALLAH ma ya taimaki Amatallah lecture biyune da ita suma duk Na yammane.
Da safema bayan sunyi sallar Asuba basu hutaba, said
a sukaga yara suntafi makaranta, Uncle kam yana d'akinsa yanata barci tunda suka dawo salla.
Ai yara Na tafiya daga Amatallah har Aneesa kowacce takoma gado, dama yara tea and bread suka basu Dan Neman sauk'i.
Gidan yayi tsit, mai jegoma barci ta
takeyi Na ramuwar kusan kwanaki, Dan tunda suka dawo bazatace ga randa tasamu isashen barciba, kullum rabi da rabine, itadama tafiya nak'udar tsaye, shiyyasa haihuwar takanzo mata da sauk'i kuma randa tatashi.
Sai kusan 9 Uncle yafara tashi, shima yau
dai kasuwa dama kawai zaije.
Yasha mamakin jin gidan tsit, Fateema yafara lek'awa yaga har lokacin barci take daga ita har jinjirar, ya lek'a Aneesa itama, tayi d'ai-d'ai abinta a gado, ta danne Siddiqa da k'afa d'aya alamar k'ila barcin taso hanata sh
iyyasa tamata haka.
Murmushi yayi yafito zuwa d'akin Amatallah, nanma abin yabashi dariya yanda tabaje abinta tana shak'ar barci, kansa ya girgiza kawai. Aransa yace lallai su mata anji jiki yau.
π
Kitchen yashiga abinsa, ya had'a tea da soya kw
ai uku yad'auki bread yafito, shikam da yunwa yatashi yau, kodan jiya dayasha ruwa bai wani ci abin kirkiba saboda zuwan alhaji sabi'u gidan, bayan tafiyarsa kuma barci ya takurashi dole ya kwanta batareda ya nemi abincinba. Dole yatashi da yunwa kuwa, ga
matan