Showing 18001 words to 21000 words out of 111738 words
d'akin da baba ke kwance, har yanzu an hana kowa ganinsu.
"Doctor yaya?".
Numfashi doctor Joshua ya sauke, tareda fad'in lamarin babu sauk'i Alhaji, zafin wut
ar hayak'inta yayi mugun ilata lafiyar Alhaji Isma'il gaskiya, amma muna kan aikinmu, zakuma muyi iya k'ok'arinmu akansa".
Uncle M.A ya jin jina kansa, muryarsa na rawa yace, ''matarfa?".
Shiru doctor Joshua yayi, saikuma yad'anyi murmushi, da
sauri yace, " itama dai hakan". bai jira cewar Uncle ba yay saurin barin gurin.
Cikin sauri Uncle M.A yabi bayansa yana kiran "doctor!".
Harya kama handle d'in k'ofar office d'insa zai shiga ya dakata, saurin maida kwallan sa yayi, haka kawai yaj
i yana tausayin Amatallah da wannan mutumin dabaisan dangan takarsa da iyayen Amatallah d'inba.
Uncle M.A daya k'araso yace, ''please doctor inason muyi magana inhar bazan shiga aikinkaba".
"Babu damuwa Alhaji, zaka iya shigowa". 'Yay maganar
yana shiga office'.
Bayansa Uncle M.A yabi.
Bayan sun zauna Uncle M.A yace, " doctor inason tafiya dasu Kano gaba d'aya, kaga garinnan kuma harmutsewa yakeyi, dukda bamuna fatan damuwar da'ake ciki tawuce hakanba, amma sunada buk'atar kulawar ga
ggawa suda Amatallah, please doctor ka taimakeni".
Cikin tausayawa doctor Joshua yake kallonsa, ya gyara zamansa yana jinjina kai, "nabaka goyon baya d'ari bisa d'ari Alhaji, nima ina ganin hakan shine mafita. yanzuna nan zan shirya muku tafiya kawai
".
Sosai Uncle M.A yaji dad'i, sai godiya yakema doctor.
Babu 6ata lokaci komai yagama kammala, aka kai su Ammi cikin Ambulance, dukda itad'in ta rasu, amma doctor Joshua yakasa fad'ama Uncle M.A d'in.
Amatallah kan a motar Uncle M.A ak
a sakata, haka sukatafi zuciyar uncle cikeda rauni, lokaci-lokaci yakan juya ya kalli Amatallah dake kwance a baya tamkar gawa....
*************
Tafiyar Awa 3Β½ ce ta kaisu garin Kano, kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce.
A cikin gaggawa kuwa
aka kar6esu, saboda ansan da zuwansu, tunkan subaro jos Uncle M.A yakira doctor Shu'aibu ya sanar masa zuwansu. Wannan yasaka suka Tatar da komai a ready, su kad'ai ake jira.
Amatallah ma anbata gado, Dan har zuwa yanzun batasan ina kanta yakeba.
Sai da Uncle M.A yaga komai ya dai-daita sannan yatafi gidansu danya sanarma iyayensa.
Yana shirin shiga mota doctor shu'aibu yafito da sauri yana nemansa. hangosa dayayi yana shirin shiga mota yasashi fara kwala masa kira.
"Alhaji Muhammad! Alhaj
i Muhammad!!".
Harya saka k'afarsa d'aya ya fito, ganin doctor shu'aibu Na tunkaroshi da sauri sai gabansa yashiga fad'uwa.
Doctor shu'aibu yak'araso, "sorry Alhaji Muhammad Labbo! na tsaidaka, so dama.......
Sai kuma yay shiru.
"Ina jinka d
octor, mike faruwane?".
Tsayuwa doctor ya gyara, sannan cikin damuwa yace, " sorry Alhaji Muhammad, ko kasan macen tarasu?, kamarma tun kusan a wanni 22 dasuka wuce".
A sanyaye Uncle M.A ke kallon doctor shu'aibu, ya dafe kansa dayaji yafara sa
ra masa.
Hak'uri doctor yafara bashi, tareda lallashi da masa Nasiha.
Uncle M.A baice komaiba yashiga motar, kansa ya kifa a sitiyarin motar yafara hawaye. Kusan mintuna 7 sannan yad'ago, motar ya tada yabar asibitin.
_________________________
_____
Tunda yashigo gidan Innani dake tsakar gida tana alwalar magriba kebinsa da kallo.
Jingina yayi da bango, batareda ya saniba hawaye suka fara bin kumatunsa.
Da sauri Innani ta k'arasa alwalar, "kai lafiyarka kuwa? Da girmanka ka
ke kuka? Miya faru, yaushe kadawo ma?".
Yanda Ammi ta jero masa tambayoyin saiya samu kansa dakuma fashewa da kukan.
Shiru Ammi tayi tana kallonsa, jikinta sai rawa yakeyi.
Cikin d'an daka tsawa tace, " wai baka jinane?".
Share hawensa
yayi, sannan yashiga bata labari.
Innalillahi ...... Kawai Innani ke iya ambata.
Baba na daga d'aki duk yanajinsu, saidai baya iya fitowa sai an fiddoshi, maganar Uncle M.A bak'aramin girgizashi tayiba kuwa.
Ana cikin haka saiga Jabeer yashig
o shima, nan suka had'u sunata jimamin abin, jabeer ma harda kukansa rurus.
Bayan Uncle M.A yashiga sun gaisa da baba, shima yak'ara masa bayani sannan yatafi gidansa danya d'an kimtsa sannan yakoma kar Amatallah ta farfad'o babu kowa a kusa.......
.....β
π»
_Dan ALLAH ina rok'onku Ku ringa turama masu cigiya, saboda ALLAH banida time d'in turama kowa ta PC, amin afuwa saboda uzurina, hakanne zaisa nasan kuna k'aunata
ππ₯°π₯°π₯°
._
One luv my fans
ππ»
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu
πππ»
_*
[
1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
*_Duk naga comments
naku, kuma sun k'ayatar dani gaskiga.
π₯°π₯°
sai dai wani Abu yasakani dariya matuk'a, kunsan minene?. Masu cewa Uncle M.A yama Amatallah tsufa
π
._*
*_Wai miyasa abinda zai iya kasancewa gaske Reader's ba kuson ganinshi a Novel's? Abinda na sani kuka s
anine, ko a zahiri mai shekarun uncle M.A ba tsoho baneba, kisamu wani a anguwarku mai d'iyar dazata iya kaiwa 18years, tazam kuma itace d'iyarsa ta Fari ki k'iyasta dashi, ko Wanda yakai shekara 60 yana auren budurwa ai, balle 47years, kuma ko a cikinmu a
kwai wad'anda mazajensu suka kai wad'an nan shekarun, my Abdull ma shekarunsa kenan
π€£π
._*
_mu rubuta abinda azahiri zai iya zama gaske kuce bai daceba, muyi Wanda mu da Ku kunsan bazai yiwuba Ku zagemu kuce muncika k'arya ko
π€£
._
_koma Yaya dai A
LLAH yabar zuminci, Dan mu daku duk munacin amfanin junane, inba mai karatu babu abinda zaisa Marubuci 6ata lokacinsa, hakama inba Marubuci mai karatu bazai samuba littafinba, mun gode sosai, irin Trillion's d'innan
π€π»π₯°π₯°π
._
____________________
*_N
umber 10_*
____________________
An gudanar da zana'idar iyayen Amatallah a gidan mahaifan Uncle M.A, Innani tasha kuka lokacinda taga gawar Isma'il da matarsa a shinfid'e, lallai duniya batada tabbas ko kad'an.
π
Wandama ya d'aura d'ammara da
ita saiya kwance.
Babama yashiga rud'ani sosai, dan sai da ciwonsa yayi tamkar zai motsa, sai allurar barci akai masa.
Har aka binne su Uncle M.A na kuka, koda suka dawo daga mak'abarta d'akin Jabeer yashige ya kwanta, kuka yake tamkar ransa z
ai fita.
Dolene ka gansa kaji tausayinsa. shima dai daga k'arshe dole allurar barcin Jabeer yasaka akai masa.
*_Two days later_*
Alhmdllh yau kwanakinsu Baban Ama biyu a k'asa, amma Ammi kwananta uku da rasuwa.
Duk da 'Yar Nutsuwa taz
oma su Uncle M.A hakan bai hanashi warewa gefe yasha kukaba wani lokacin, musamman inyaje asibiti duba Amatallah da Nazeefa ke zaune da ita, dawata k'anwar Innani, gwaggo Rakiya.
Har yanzu Amatallah bata farfad'iba, dan doguwar suma tayi, amma tana sam
un kulawa daga likitoci sosai.
_______________________________
*_Jos_*
A jos kam lamari yayi k'amari, k'ank'anin Abu yajawo mutuwar d'aruruwan al'umma da asarar dukiyoyi, abinda yafaru akan SIYASA dalilin wasu marasa jin magana ya rikid'e yazama
fad'an k'abilanci da addini.
'Yan jaridu da kafafan yad'a labarai na social media sai baza rahotannin k'arya sukeyi, anrasa jin jinar magana akan dalilin wannan rikici na *SIYASA KO K'ABILANCI!?*.
A dalilin hakan kuma wasu gur6atattun matasa mas
u ruguza zaman lafiya suka kuma tada rikici a KADUNA, ik'irari sukeyi wai ankashe 'yan uwansu dake jihar Jos, dolene suma su d'auki fansa.
Ba'awani ja danisaba Kano ta d'auka, babu gaira babu sabar nanma wasu bara gurbin matasan suka haikema wasu k'a
bilu dake killace awata anguwa da ik'irarin d'aukar fansar abinda akaima 'ya uwansu a Kaduna da jos.
Abinda yafaru a kano yabama k'abilun kudancin k'asar suma tada tasu husumar, suka fara kisan 'yan arewacin k'asar a nufin d'aukar fansa
π¨ππ»
ββ.
_h
um wane irin tunanine da matasan k'asarmune? Mike shiga kanmune? Muke za6ama kammu da k'asarmu irin wannan rayuwar? Wace riba mukeci ko nasara idan mun girmama irin wannan rikice-rikicen dabumuma San tushensuba, karfa Ku manta idan ta rikice da kai da ni d
uk bazamu shaba, ahalinka da nawa babu Wanda zai tsira, dukiyar k'asarmu zata ruguje, karatunka danawa Dana 'ya'yanmu duk zai zama labari, watak'ilma kaida kazama jagoran fad'ad'a tashin hankalin kaine zaka fara mutuwa ko ahalinka, Ku kalli gagis, zike, k
show, dasu aka fara, an tarwatsa ahalinsu da basujiba basu ganiba, Amatallah dabatasan tushen rikicinba an rabata da iyayenta, an tarwatsa mata family saboda son zuciya irinna gur6atattun matasanmu, wad'anda mugun tunaninsu bayasa mu d'aukesu a jerin masu
amfani da amfanar da k'asarmu, basuda buri saina haddasa rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI!?* Saboda son zuciyarsu, kullum zuciyarsu na karanta musu AMUTU KO AYI RAI ba damuwarsu baceba, da ance an kad'a tambarin SIYASA saikaga jikkunan matasan k'asarmu na ra
war Mazarin shirye-shiryen duk yanda takama, basuda zuciyar k'yak'yk'awan fata wa k'asarsu ko nagartar ginata ta hanyar zarran mazatankar samartaka na k'uruciya da ALLAH yabasu. miye ribarka idan an siyeka dawasu 'yan kud'ad'e dankayi jagoranci wajen halla
ka ahalinka da k'asarka? Wadda bakada kamarta, bakada Inda yafita, duk Inda zakaje saikazama abin tsangwama da gudu , watak'ilma akiraka d'an ta'adda mai lasisi, bakada damar shan ruwan wata k'asa cikin salama tunda ba k'asarka baceba._
Yanzu haka wad'
anda suka baka kud'in duk 'ya'yensu basa k'asarma, sannan su sunada tsaronda babu wani mahalukin daya Isa ya tunkari gefen anguwanninsu ballema yasamu ganin su, amma kai anbaka kud'in siyen ahalinka batareda kayi dogon tunaninaba, basuda Matsala da watsewa
ko tarwatsewar k'asar, dan sunada isassun kud'ad'e a ciki da wajen k'asar, sunada lasisin zuwa kowacce k'asa su warwasa batareda an tsangwamesu ba kamarkai daza'a kafama tantin d'akunan tamfol ko buhu ko katako a filin ALLAH ana kiranku da suma *'YAN GUDU
N HIJIRA*
π
.
Abincinma dazakaci ko ruwa saiya gagareka, ballantana maganar lafiyarka ko akasinta.
Haba matasanmu, kudawo cikin hankalinkufa, kubar yadda da 'yan jari hujja masu amfani daku wajen amfanuwarsu suna haddasa fad'ace-fad'acen addin
i ko SIYASA da K'ABILANCI ta sanadinku, ni da ku damuke a arewaci da kudanci duk munada ikon canja mummuna zuwa k'yak'yk'yawa, duk Wanda kagani Asama mune muka kaishi, kuma munada ikon ingizoshi k'asa ayayinda muka fuskanci d'an wawasone akan abinda yake m
allakinmu, da wahalhalinmu suke tak'ama da baza riguna da cin zarafinmu suna zare idanu, to muma saimu gyara domun gyaro abinda ke cin dunduniyarmu, mukiyayi saidai RAYUWARMU akan rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da wasu tsiraru ke jagorancin haddasa mana domi
n cimma wani burinsu akanmu, sai matasanmu sunyi gyaran halayensu sannan madafun iko da ragamar k'asarmu zata iya dawowa hannunsu
ππ»
.
Wannan k'alubalen nakune matasanmu
πͺπ»πͺπ»πͺπ»
.
Amma ta sanadin zaman lafiya a k'asarmu da muhimmin sanin daraja
r kawunanku, kuyi fatali da duk wani banbancin addini ko k'abila kuzo mu rungumi juna domin kawo sauyi wajen tankad'e da rairayar duk wasu masu rusamu ta k'ark'ashin k'asa, karike na rike ki rike mu rike hannun juna domin maida matasanmu jagorori akan mada
fun ikonmu
πͺπ»πͺπ»π
. Ta hanyar zaman lafiya da k'aunar junanmu cikin zarrar amsa suna 'yan *NIGERIA* k'asa d'aya, uwa d'aya uba d'aya.
π³π¬
Karmu bari mu ruguje daga ansa sunanmu na 'yan k'asa d'aya dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*
ππ»π’
Ko sh
ed'ancin wasu jagorori masu nemawa Kansu mutunci kawai
ππ»
.
a wannan ga6ar dolene masu karatu susojin dangan takar dake tsakanin Alhaji Isma'il Uba da Alhaji Muhammad.
π€
Kubiyo bilyn Abdul domin jin tushen labarin.
πππ»
__________________________
__
Alhaji Muhammad Ahmad Labbo, shine cikakken sunan Uncle M.A.
'Dane na farko daga Alhaji Ahmad Labbo.
Alhaji Ahmad Labbo cikakken basakwace ne d'an kasuwa, kasuwancine yakawoshi garin Kano, a da yakanzo ya sari atanfofi yakoma sokoto,
sai dai daga lokacin da tafiya tafara nisa saiya dawo garin na Kano baki d'aya, yasamu shago a kasuwar kwari.
A nan Kano ALLAH yahad'ashi da matar aure Zainab (innani).
Shekararsu 1 da aure ALLAH ya albarkacesu da haihuwar d'a namiji, Wanda yaci s
unan Muhammad (Uncle M.A kenan). bayan Muhammad innani tasake Maijiddah, sai Barirah, (amma ALLAH yay mata rasuwa), sai Jabeer,, Shehu, Nazeefa auta.
Gwargwadon iko 'ya'yansu sunsami tarbiyya, sannan sun tsaya tsayin daka domin ganin sun sami ilimin
addini dana zamani.
Muhammad yarone dayataso k'ark'ashin kulawar mahaifi, dan innani tana kawaici sosai alamarinsa irinna 'ya'yan Fari, bata fad'ar sunansa, sannan kuma bakomaine take sakashi acikiba
Amma a k'asan zuciyarta tana matuk'ar
k'aunarsa fiyema da sauran 'ya'yanta.
Bayan kammala primary d'in Muhammad yadage akan boarding yakeson zuwa, babu yanda iyayensa suka iya suka shiga cuku-cukun kaishi Government secondary school Bichi.
A canne ALLAH ya had'ashi da Isma'il U
ba Salisu, Wanda rana d'aya aka kaisu makarantar, shi an kawoshine daga Kusada local government dake jihar Katsina. tun daga wannan ranar suka k'ulla alak'ar abota mai k'arfi, suna kiran junansu brothers.
Kowa a makarantar ya d'auka 'yan uwan junane ma
kusanta saboda k'auna da tattali dasuke nunama juna.
Ko kad'an Muhammad baya k'aunar yaga anta6a Isma'il, haka shima Isma'il d'in, idan aka kama d'aya da laifi, akazo hukuntasa sai d'ayan yay tsale yace shine, dan bayaso ata6a lafiyar d'an uwansa. idan
kuwa d'aya bashida lafiya ai saika d'auka dukansune suke jiya. gaskiya akwai k'auna mai k'arfi a tsakaninsu mai kuma ban mamaki.
Kafin kace mi duk families nasu sunsan da wannan k'auna tasu. har yazam Isma'il kanzo Kano Hutu gidansu Muhammad, haka shi
ma Muhammad kanje jos ko kusada hutu........
Isma'il Uba salisu shine cikakken sunan Baban Ama, d'an asalin jihar jos ne, Dan anan yataso yaga iyayensa,
Su biyu iyayensu suka Haifa, Amina itace babba, sai Isma'il. tun suna k'ananu mahaifiyarsu
ta rasu, babansu wanda suke kira da kawu yak'ara auren wata makirar mace mai suna Huzaiyya, takan nuna k'aunarta a garesu agaban mahaifinsu, amma dazarar bayanan tashiga gallaza musu kenan, makircinta yahana kawu fahimtar komai akansu. ana haka ALLAH ya fi
ddoma da Amina miji, amma fatauci yake zuwa jos shi d'an katsina ne a kusada L.G. wannan yasa koda akai aurenta sai aka kaita Kusada.
Tunda Amina tayi aure sai Isma'il yakuma shiga uk'ubar huzayya, wannan yasakashi tada hankalinsa akan shi akaisa wajen
'yar uwarsa Amina. Mahaifinsu bai fahimci komaiba, shi duk tunaninsa Isma'il na kewar Amina ne. Haka ya d'akko Isma'il da kansa yakawoma Amina danufin yayi hutu. Sai dai koda hutun Isma'il ya k'are saiya dage akan bazai komaba, kawu yay lalla6ar duniya Is
ma'il yace bai komawa. haka dole kawu yabar Isma'il awajen Amina.
Mijin Amina ne ya nemawa Isma'il makarantar boarding ta Bichi danya cigaba da karatunsa, tunda yagama primary a jos.
Daga wannan lokacinne kuma suka had'u da Muhammad labbo, Wanda ya
zame masa d'an uwa kuma aboki.
Idan anyi Hutu Isma'il yakan fara zuwa kusada ne yay kwana biyu sannan ya wuce jos. Wani lokacin kuma a kano yakeyi gidansu Muhammad, a wani karon kuma su wuce jos shida muhammad d'in suyi acan bayan sunje kano, kokuma k
owa yatafi gida, sai bayan kwanki kamar uku zuwa hud'u saiya tafi gidansu d'an uwansa hutun. har lokacin kuma Amina bata haihuba.
Ahaka suka kammala karatunsu Na secondary, sun rabu cikin damuwa sosai alokacin, Dan kokad'an basuyi murna da gradu
ate d'in nasuba.
Kwanaki bakwai kacal dayin candy d'insu Muhammad yakasa hak'uri yashirya sai jos, sosai Isma'il yay farin cikin ganinsa, hakama kawu.
Har zuwa yanzu huzayya tananan da makircinta, amma zuwa yanzu Isma'il baya d'aukar raininta.
Haka suka maida Kansu