Showing 51001 words to 54000 words out of 111738 words

Chapter 18 - Siyasa-ko-kabilanci-complete

08 Sep 2026

5

hankalin Uncle ba, gaba d'aya hankalinsa nakan son ganin Amatallah, soyake kawai yaga halin datake ciki.



Suna cikin cin abinci Fateema ta kalli Nazeefa tana fad'in "Nazeefa wai Amatallah fa?".

Da hannu Nazeefa ta nuna 6angaren Amatallah d'in.

Uncle datun da suka fara maganar ya d'ago ido yana kallonsu yace, " lafiya dai ko bata fitoba?".

Na

zeefa tace, "Yaya ban saniba nima, tundai d'azun tana ciki"..

Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya mik'e yana fad'in "bara Na dubata to".

duk binsa da kallo sukayi, wani haushi yakama Aneesa. Fateema kuma tayi murmushin mugunta, dama danta rama a

binda Aneesa tamata ta tambayi Amatallah d'in, Dan tasan dole mijinsu yayi wani Abu akai.

Anty Maijidda kam da Nazeefa sai dariya sukeyi a zukatansu.

Amatallah da har suka shigo cikin falon tana jiyosu, tana kwance a doguwar kujerar falonta tan

a game a waya, dukda zuciyarta sai harbawa take da fargaba. game d'in kawai takeyi, amma bawai yana mata dad'i baneba, Rabin hankalinta nakan su Uncle d'in.

A hankali yaturo k'ofar falon ya shigo.

Ko kad'an Amatallah bataji shigowar saba, sai

k'amshin turarensa saboda ta juyama k'ofa baya, kuma a la66ansa yayi sallama yanda bazai yuwu tajiba.

Shiru tayi tana hasashe, a zatonta ko tun daga waje k'amshin ke shigo mata.

Uncle kam al'ajabine ya kamashi, shiyyasa yakasa motsawa, tunda yake

bai ta6a ganin Amatallah da kwalliyaba sai yau.

Jin kamar mutum tsaye akanta yasata juyowa cikeda fargaba. da Sauri ta mik'e tana fad'in "Uncle sannu da zuwa, ALLAH banasan ka shi..go..ba ne".

Murmushi yayi, ganin yanda jikinta har rawa yake,

kai kace taga wani ojuju ne, takawa yayi a hankali har inda take batareda yace komaiba, daga zaune Amatallah tad'an matsa baya kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, a kujerar ya zauna shima kusada ita, ai saitaji kamar tatashi ta tsilla a guje.



Hannunsa ya d'ora kan yatsun hannunta datake wasa dasu, yanda Jan lallen yay rad'am ne ya burgesa, murza yatsun yayi, hakanne yasaka Amatallah d'agowa tad'an kallesa.

Komi ya tuna kuma saiya saki hannun, cikin sassanyar muryarsa yace, " haba my best!

Babu fad'a miya kawo gabane? Laifin mi mukayi aka k'i fitowa tarbarmune, ko ba'a murna da dawowarmu mu koma Inda muka fito?".

Hannu tasa ta rufe fuskarta dantaji kunya sosai tace, "Sorry Uncle, ALLAH ba haka bane fa, kawai dai".

Murmushi ya

yi mai k'ayatarwa, yasa yatsun hannunsa biyu ya d'ago ha6arta tareda saka d'ayan hannun ya janye hannayenta data rufe fuska, saita rumtse idanunta.

"bud'e idon to, kifad'amin kawai dai me? kokuma nayi wani Abu".

Tace, "ALLAH uncle inajin kun

ya".

" my best! to miye najin kunyar?, nifa Uncle d'inkine, ko yanzun an daina Uncle d'in dani sai mij......"

Bai kai k'arsheba ta waro manyan idanunta a kansa.

Shima saiya waro nasa kamar yanda tayi yana murmushi har hakwaransa Na bayya

na a fili.

Yunk'urawa tayi zata tashi danta gudu ya rik'e hannunta yana fad'in kinga wasa nakeyi, muje kici abinci, kowa ya hallara babu ke, har Fateema Na tambayarki taga bakizo mata sannu da zuwaba".

"Uncle azumi nakeyi ai".

" azumin m

e my best? Yaufa Saturday?".

Rasa mizata cemasa tayi, dankuwa k'arya ta mullik'a babu wani azumi, tana dai jin kunyar fitane saboda kwalliyarta.

Hakanne yasa yagane k'arya take.

Mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita tsaye.

Ta marairaice mas

a fuska kamar zatayi kuka, "wayyo Uncle da gaskefa nakeyi".

Baima San tanayiba, dan kallonta yake daga sama har k'asa, bak'aramin zama kayan sukayi a jikintaba.....

Ganin hankalinsa bama kanta yakeba ta girgiza hannunsa dake rik'eda nasa.

Kall

onta yayi da sauri, yace, " mikikace my best!?".

A shagwa6e tace, "kai Uncle kana nufin baka jiniba ma?".

Kasa amsata yayi, yaja hannunta dan yakula inhar suka kai wani lokacin a falonnan zai iya kauce hanya ya aikata abin kunya....



''Uncle please zanje da kaina, ALLAH zanma ci abinci". Amatallah tayi maganar da sauri dan ganin da gaske soyake ya kaita har falon yana rik'eda hannunta.

Baice mata komaiba ya saki hannunta, fitowa sukayi yana gaba tana bayansa, dan haka ta 6oye s

osai a bayansa.

Fitowarsa yasaka Fateema da Aneesa d'agowa suna kallonsa, kowa da dalilinta na kallonsa da son suga Amatallah d'in.

Anty Maijidda tace, " a'a Yaya lafiya dai ko? ina Amatallah d'in to?".

Juyawa yay a zatonsa bata biyoshiba,

sai ya ganta a bayansa, tana famar 6uya, matsawa yayi gefe yanda zasu ganta yana fad'in ''k'alau take, kunyarku takeji saboda tayi.....". Sai kuma yay shiru ya k'are maganar da 'Yar dariya yana zama a kujerar daya tashi wadda Aneesa da Fateema suka sakashi

tsakkiya.

Amatallah jitai tamkar ta nurse k'asa dan kunya, Fateema da Aneesa duk sukad'an waro idanu kanta cikin mamaki da ganin k'yan datayi.

Aneesa Na mamakin yaushe Amatallah ta koma haka?, Fateema kuma Na mamakin canjawar Amatallah d'in

a watanni hud'u.

Nazeefa kam cikin nuna kamar batasan da kwalliyar Amatallah d'in ba tace Woow!! Amatallah, wannan wanka yayi, kinfito a amaryarki".

Jabeer da Shehu da Anty Maijidda da Uncle duk dariya sukayi, yayinda wani kishi ya tokare mak'oshi

n Aneesa da Fateema.

Amatallah komawa tayi baya da sauri tashige bangarenta.

Nanfa duk aka saka mata dariya, harda yaran.

Nazeefa tashiga kwala mata kira, amma sai Uncle yace "barta Nazeefa, haka Khadija take da kunyar tsiya".

" Yaya a

i bataci abincin bafa".

" 'Diba ki kai mata kawai, kowama yakamata yay saurin kammalawa yanzu zakuji magrib".

Duk da to suka amsa.

Nazeefa ta d'iba komai dai-dai misali Dan tasan Amatallah batada cin abinci sosai ta kaimata. Har Nazeefa tash

iga ta fito Amatallah bata yarda sun had'a idoba, dariya Nazeefa tayi kawai tafito abinta.



Suna mammala cin abinci mazan suka wuce masallaci, Matan kuma sukayi agida.

Su Uncle basu dawoba sai da sukayi sallar isha'i.

Koda suka dawo basu

zaunaba, shidasu shehu da Anty Maijidda suka tafi gidan iyayensu danya gaishesu, harda Nazeefa Dan tace bazata kuma kwanaba kuma, ba lallashin da Uncle bai mataba tace, a'a.

Anty Maijidda tace yabarta, gara ta tafi. Saboda yanayin zaman gidan nashi ba

mace d'aya bace, idan ta nuna kusancinta da d'aya sai yazama abin magana, sukuma zaman lafiya mai d'orewa sukema gidansa fata.

Badan ya soba suka tafi gaba d'aya. Daga innani har baba sunyi farincikin ganinsa sosai, sai dai innani ta danne abinta a zu

ciya kamar yanda ta saba masa.

Sunsha hira, Dan saida baba yace yaje gida ya huta, gobe idan ALLAH ya kaimu yadawo suyi hiran. haka ya tafi badan hira da iyayensa da 'yan uwansa ta isheshiba.

Tunda suka fita Aneesa tashige 6angarenta, aka Shiga k

'imtsa jiki.

😜

Fateema ma 'ya'yanta taja suka shige Nata 6angaren, Dan k'anwarta zaliha tazo Tamata gyara tun jiya da safe.

Lokacin daya shigo gidan tsit kamar babu kowa, a tsakkiyar falon ya tsaya yana Mazarin INA yakamata yafara Shiga?, waje

n Fateema, ko Aneesa, ko Amatallah?.

πŸ˜‚πŸ€

...........✍

🏻

πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»

One luv

πŸ₯°

_Dan ALLAH idan mutum ya tambaya daga farko maishi yaringa tura mishi, ku Na tausayimin mana, kodan k'ok'arin muku typing danake kullum, abubuwan sunmin yawa, banason kuma maso

yina yaga Na wulak'antasa wlhy ko kad'an, Duk masoyina Na gaskiya nasan zai taimakeni._

😊🀝🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*

πŸ™πŸ»πŸ˜­

[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍

🏻

_*

*_HASKE WRITER'S ASSO..._*

πŸ’‘

_{home of expert and perfect write

r's}_

*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉

_(Hattara matasa)_

*_Bilyn Abdull ce

πŸ€™πŸ»

_*

*_Jiya maganar gaskiya naci dariyar Comments naku over, dan naga zanga-zanga kuka shirya yimin akan kwanan Amatallah jiya

πŸ˜‚

, especiall

y 'yan Group d'ina da Group d'in party, sai Kundin Haske da Group na Manshat , sai dai network yamin iya shege, amma ngd sosai walhy, ALLAH yabar zumunci, bilyn Abdull Na yinku irin Trillion's d'innan, I love you wujiga-wujiga._*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ€πŸ»πŸ‘πŸ»

.

_____

_______________

*_Number 21_*

____________________

Yadad'e tsaye yana canki canka, daga k'arshe dai yashiga 6angaren Amatallah, babu kowa a falon sai dai k'amshi mai dad'i dake tashi, tsayawa yay kallon falon, Dan d'azun ta rikitashi bai kalli koma

iba, komai yayi k'yau yanda ya kamata, cikin yabama k'ok'arin k'annensa Na za6o abinda yay dai-dai da ra'yinsa shida Amatallah yashiga bedroom d'in. nanma babu kowa, amma ko ina tsaf yake kuma k'al, gadon yasha gyara, ga ta saka filolin a wani style mai k'

yau, guntun murmushi yayi kafin yamaida kallonsa ga bathroom inda yake jiyo motsin ruwa alamar wanka takeyi.

Juyawa yayi yafita kafin tagama ya dawo.

Saiya shiga 6angaren Aneesa.

Tana zaune abakin gado cikin wata rigar barci jaa datayi masi

far mata k'yau da haska farar fatarta, Siddiqa takema shirin barci, Saifudden Na kwance a gadon haryayi barci.

Tsayawa yay kwai yana kallonta danba k'aramin k'yau tamasa ba a rigar barcin, cikin wani salo ta d'ago idanunta tana kallonsa tareda d'an far

i.

Murmushinsa mai k'ayatarwa yasaki, yataka a hankali zuwa gareta, dai-dai ta shinfid'e Siddiqa a gadon.

Ta baya ya rungumeta cikin kunnenta yace, "zaki kasheni da salonki my Neesa".

Dad'i ya kamata, ta juyo sosai suna fuskantar juna, sai k

awai ta fad'a jikinsa suka rungume juna tsam, tace, " I miss u so much my Dear".

"Me too my Neesa". yafad'a yana d'ago kanta, bakinsu kawai ya had'e waje d'aya, yashiga mata wani salo mai rikitarwa.

Su duka sun haukace, kai kace yau suka fara

ganin juna, sai da Uncle yaga abin zai zarta sannan yacire bakinsa a nata, ya kuma rungumeta da k'yau a jikinsa suna maida numfashi. kusan mintuna biyu sannan yace, " My Neesa kinsanfa yau niba naki baneba, Na Amaryane".

Idontane yacika da kwalla, y

anzu kam ba zafin kishi bane kawai, harda tsananin buk'atuwar da take ciki, wata hud'u ba wasa baneba, takuma k'ank'amesa kamar mai gudun arabasu, (dukda tana buk'atarsa bazata ta6a cemasa karyaje wajen matarsa ba, duk zafin kishinta bata fatan shiga hak'k

'in wata a abokan zamanta).

Jin laimar hawayenta a k'irjinsa saita bashi tausayi, yasan yanayin Aneesa sosai, wata hud'u ba wasa baneba kuma agareta, Dan baita6a nisan kiwo basa kusa dashiba kamar haka.

Jin yana k'ok'arin d'ago kanta saitayi saurin

share hawayenta, koda tad'ago saita masa murmushi, murmushin shima yamata, yasa hannunsa biyu yakamo kumatunta, cikin kuma k'asa da muryarsa yace, "sorry my Neesa, ban fad'a Dan wulak'antaki ba, saidan kawai hak'intane Na sauka a wajenta, kuma namata kwana

ki 7 kamar yanda yake a shari'a, amma karki damu zan nema mana mafita idan kin amince".

A sanyaye tace, " wace mafitace dear?".

Lumshe idanunsa yayi tareda kissing la66anta sannan yace, "zanje Na rok'i Khadija tabamu kwana d'ayannan kawai domin

Na kwaranye miki k'ishinki".

Ajiyar zuciya tasaki sannan tagyara tsayuwarta tana fad'in " a'a dear, itama anshiga hak'inta kenan ai, nida ita duk Abu d'ayene a wajenka, maganar wadda kafiso wannan a zuciyarka yake, tsananin k'aunarka da kishinka dana

keyi bazaisa na jagoranci abinda zaisa katashi ranar kiyama da shanyanyen jiki har Na kaika wuta ba, insha ALLAH zanyi hak'uri har tayi kwanakinta, amma kasani INA matuk'ar Sonka da kishinka, harma nakanji nafi kowacce mace Sonka da kishinka a duniya".



Tausayi tabashi, Dan haka Yakuma d'ora bakinsa kan nata batareda yayi maganaba, yashiga kuma nuna mata tsantsar soyayyarta dake cikin zuciyarshi shima. Sunja adadin wasu lokuta kafin Aneesa ta janye jikinta da k'yar, kan gado kawai ta haye ta kwanta tare

da juya masa baya.

Yasan kuka takeyi, Dan haka baice mata komaiba yajuya yafita jiki a sanyaye. Samansa ya haye, yaje yay wanka da shirin barci. Babu dad'ewa ya sakko.

6angaren Fateema yashiga, takashe komai Na falon, sai fitilar wayarsa ya kunn

a, d'akin yaran yafara Shiga yaga babu kowa, hakan ya nuna masa suna tareda ita kenan, d'akintama fitilar a kashe take, data wayarsa ya haska ya hangosu a kan gado sun jeru suna barci, murmushi yayi ya k'arasa garesu yana ayyana soyayyar uwa da 'Yaya a zuc

iyarsa.

Duk saida yabisu d'ai-d'ai yama kowa kiss a goshi, Fateema kam harda d'an tsotsar la66anta sannan yama cikinta da wuyanta kisses yamusu addu'oi yafita dukda yasan Fateema tamusu suma yaran tasakasu sunyi.



Amatallah tunda tafito w

anka taji kamar k'amshin turaren Uncle, gabantane ya fad'i, cikin sand'a ta lek'a falo azatonta yana can, ganin wayam babu kowa tasaki ajiyar zuciya sannan tadawo. Zani ta d'aura tasaka hijjab tayi shafa'i da wutiri, idarwarta kenan tacire hijjabin ta d'or

a saman gado, tabud'e Waldrop danufin Neman kayan barci yay sallama, ba k'aramin tsorota tayiba da ganinsa, taja hijjab d'in data cire tasaka da Sauri duk da yama Rigada ya shigo d'in, Yakuma ganta a yanda bata son.

Murmushi kawai yayi, ya k'arasa baki

n gadon ya zauna.

Kanta a k'asa tamasa sannu da zuwa.

Idonsa a kanta yace, "yauwa my best! Kin daina kukan tafiyarsu Nazeefa ne?".

Kwallace tacika idonta, ta d'ago kad'an ta kalleshi ta duk'ar da da kanta.

"Kukan dai kuma?".

Gi

rgiza kai tayi da sauri.

Zamansa ya gyara yana nunu mata kusa dashi, " zoki zauna naji to".

Dukda tanajin kunya haka ta zauna amma d'an Nesa dashi. Idonsa akan yatsun hannunta dake d'aukar hankalinsa yace, "to, ya school?".

" Alhmdllh Un

cle".

"Masha ALLAH, babu dai wata Matsala ko?".

Kanta ta girgiza masa da fad'in " eh uncle".

"Alhmdllh ai haka akeso, zuwa da safe Na duba Nagani idan da gaskene, yanzu alfarma nazo nema".

Cikeda mamaki ta kalleahi, " uncle! Alfarma kum

a? a wajena?".

Kansa a jinjina mata fuskarsa d'aukeda guntun murmushi. "Alfarmar kwananki nake nemama Aneesa".

Ko kad'an Amatallah bata fuskanci inda maganarsa ta dosaba tace, Uncle ban ganeba ai".

Shiru yayi yana nazarin tayaya yakamat

a yamata bayani, sai kuma yamatso kusada ita sosai, hakanne yad'an sakata jin tsoro heartbeat d'inta Na k'ara gudu, kamar zatayi magana saikuma tayi shiru.

Duk da ya fuskanceta hakan bai hanashi kamo hannunta ba ya saka a nasa, " uhm INA nufin kibari

yau Aneesa ta kwana d'akina".

"Wayyo Uncle, ni mizai sakani Na hana Anty Aneesa kwana d'a......."

Saikuma takasa k'arasawa saboda maganar Tamata nauyin fad'a.

'Dan murmushi yayi, aransa yace tunda kinsan ma'anar kwana d'akin nawa, a hanka

li abinda nake nufinma zaki gane ai. a fili kuma yace, "Nasani bazaki hanataba, amma hak'inkine ai".

Zuwa yanzun kam Amatallah tagama fuskantar Inda Uncle d'inta ya dosa, amma nauyin maganar bazaisa ta ta6a nuna masa ta ganeba, saima mamakinsa take a z

uciyarta dukda shima azancen NASA akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login