Showing 48001 words to 51000 words out of 111738 words

Chapter 17 - Siyasa-ko-kabilanci-complete

08 Sep 2026

36

sake kira bayan kin kammala naji kinbar kuka ko an karya alk'awarin Uncle bawan ALLAH".

hannun tasaka tarufe fuskarta kamar tana gabansa, ta saki wayar a kan gadon, dariya yayi ya kashe wayar, dan yanajiyo mutsu-mutsunta kasancewar sabuwar katifa k

o ledar ba'a cireba aka shinfid'a bedsheets d'in.

Nazeefa ma dake tsaye a bakin toilet dariyar tayi, aranta tana jin sha'awar wannan soyayya ta uncle da d'iyarsa, a ranta tace ALLAH ya daidaita komai cikin sauk'i Amatallah. K'arasowa tayi ta d'auki w

ayarta, saitaga yakashe, ta kalli Amatallah dake shirin sauka a gadon tayi murmushi. Batace mata komaiba tafice d'akinta.

Duk yanda Uncle yace haka Amatallah tayi, ai kam Alhmdllhi tasamu nutsuwa, saigata suna 'Yar hira da Asiya data farka har barci

ya kwashesu.

Washe gari akayi walima 'yan jos suka koma da yamma, bayan sunje gidansu Uncle sun gaida baba da jiki.

Shatara ta arzik'i Uncle yasa Jabeer ya had'a musu, sun tafi sunbar Amatallah Na kuka tamkar ranta zai fita Anty Maijidda da Naze

efa sai lallashinta sukeyi, daga k'arshe dai saida aka kira Uncle yay lallashi da tuna mata alk'awarin datayi Na ta daina kuka sannan tayi shiru, amma sai zazza6i mai zafi ya rufeta, dole jabeer ya nemo mata Magani tasha.

____________________________



Tunda Aneesa ta fuskanci Amatallah Ce ta tare saita hau zum6u-zum6ure wa Alhaji Muhammad.

Shareta yayi, yay tamkar baisan mitakema fushinba, saima ya maida hankalinsa wajen yima Siddiqa wasa, da daddare kuma yakira Fateema tabama yaran sukasha hirars

u. yakira Nazeefa tabama Amatallah tace tayi barci, saboda maganin datasha da yamma, da k'yarma tayi salloli takoma ta kwanta. sallama yamata ya yanke wayar.



_____________________________

Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da jarabawa, ya

u kwanakin Amatallah hud'u agidan Uncle d'inta.

Kullum da safe takanje har d'aki ta gaida Fateema, ta taya Nazeefa aikin gidan tana k'ara nuna mata komai yanda zatayi, Dan Fateema bata iya aikin saboda laulayin datake fama dashi, dama ita haka take fam

a a farkon kowanne ciki.

Ita Nazeefa ma hakan dad'i yamata, Dan koba komai Amatallah zata kuma koyon abubuwan dasuka dace sosai takuma kware da wahalaryi kafin mijin nasu ya dawo.

Yaran kuwa sun maida 6angaren Amatallah nanne wajen zamansu, itakam

jansu takeyi ajikinta sosai, Dan tana kallonsu tamkar k'annenta, kuma hakan Na sakata Nishad'i sosai, saboda ta tashi ita kad'ai kwallin kwal a gidansu, babu Yaya babu k'ani, su Ammine komai nata, shiyyasa shak'uwa tashiga tsakaninsu sosai wadda taketa wah

al da ita har yanzun.

Uncle kam yana kira a wayar Nazeefa yace abata, wani lokacin dataga Nazeefa da wayar saita shige toilet d'in k'arya, har sai yagaji ya kashe, sai idan Nazeefa ta rutsatane sanan take amsar wayar.

Ganin kamar yana takura mata sa

iya rage kiran, koya kira Nazeefa baya cewa abata.

Aneesa kam bayan tagama fushinta ta sakko Dan kanta batareda ya kula da lamarintaba, danshi tausayi da dariya take bashi..

*_one Week ago_*



Sati d'aya cif da tarewar Amatallah tafara zu

wa school, Jabeer dakansa yakaita a motar Uncle.



Sanye take cikin shigar mutunci, dantasha gargad'i wajen Uncle sosai. Atanface siket da riga porpul mai haske da ratsin pink kad'an da bak'i, saita saka pink d'in hijjabi mai hannu iya gwiwa, ta sa

ka d'an abubuwan dabaza'a rasaba a cikin pink d'in lady's bag, takalman tama flat pink, duk da bawata kwalliya tayiba tayi k'yau sosai, sai k'amshin turarenta marar k'arfi dake fita k'ad'an, inba ma kusada ita kakeba bazakajiba kam.

Gaba ta bud'e zat

a shiga Jabeer yace, "a'a shiga baya abinki Amatallah".

Kunyace ta kamata, ta duk'ar dakai tana murmushi, a hankali tace, " a'a Yaya Jabeer, kabari Na zauna a gaban kawai, kaiba driver d'ina bane".

Murmushi kawai yayi shima, yabud'e mata murfin m

otar tashiga gaban sanan yatada motar suka fice daga gidan.

Motar tayi tsit, babu mai magana acikinsu, Jabeer yamaida hankalinsa ga tuk'i, itakam Amatallah kalle-kalle kawai takeyi tana sauraren redio daya kunna har suka shiga cikin BUK.

Tunda s

uka shigo take addu'oin Neman nasara a rayuwar wannan makaranta dazatayi.

Guri Jabeer yasamu yay parking, har Amatallah zata fita yace, "ki kunna wayarki Ya Muhammad yace zai kiraki".

Kanta ta jinjina masa batareda ta juyoba.

Atare suka fito,

Amatallah nata kallon mutane dake kai kawo, wasu 'yan mata da samari wasu kuma samari zalla, wasu 'yan mata zallah, kowa dai da abinda yakeyi. wasu kuma daga cikinsu duksun zuboma su Amatallah idanu, hakanne yasaka Amatallah duk'ar dakai, Dan ita irin muta

nen nanne da basu cika son taron jama'a ba.

Jabeer ya kalleta yace, " muje".

gaba yay tabishi abaya har zuwa wani Office. sai da yayi Knocking aka bashi izinin shiga sannan yashiga Amatallah Na binsa abaya.

Mutumin dake zaune a office d'in wan

da da alama shine mamallakin office d'in koda ba'a fad'aba, ya fad'ad'a murmushinsa da fad'in "Jabeer kun iso?".

Jabeer ya amsashi da " eh yaya Lawan".

Ta gefen ido Amatallah ta kalleshi, shima dai zai iya kaiwa sa'an Uncle d'inta. sai dai yafi

Uncle k'iba sosai, Dan zaima iya ninkashi biyu.....

Maganarsace ta katse mata tunani, ta kalleshi da Sauri saikuma ta kauda kanta, zama tayi kujerar dayake nuna mata. bayan zamanta ta gaidashi a ladabce. Shikuma ya amsa cikin fara'a.

Sun tattauna d

a Jabeer, aka bata wasu takardu tasaka hannu sannan suka masa sallama suka fito.

Har department d'insu Jabeer ya rakata, ya d'an mata bayani sannan yamata sallama yatafi bayan yabata 1k, yace bayan sun gama takirashi.

Kanta ta jinjina masa tayi god

iya.

Tafiyar Jabeer babu dad'ewa wayarta tafara wringing, Jakarta tabud'e ta lalubo phone d'in, ganin sunan Uncle saida gabanta yafad'i, d'an wawwaigawa tayi Dan Neman inda zata zauna. A dakalin barandar wajen taje ta zauna, dan taga wajen yanada tsaf

ta, ta d'aga wayar tasa a kunne.

Sassanyar muryarsace tamata sallama.

Itama a sanyayen tace, "wa'alaikassalam, Uncle ina kwana".

" lafiya lau my best, amma mu munshiga yini nan, ya Ku isa makarantar?".

"Eh Uncle, harma Yaya Jabeer y

atafi".

"okay, to babu wata dai matsala ko?".

" eh Uncle, komai normal".

"To Alhmdllh, saikuma a dage, banda wasa da k'awayen banza please my best! Kinji, banda biyema samari dan ke matar aurece kin sani".

Idontane yacika da kwalla,

itafa kokad'an batason atuna mata wai tanada wani aure, aurenma Na Uncle d'inta.........

" kuka kikeyi ko my best!? ".

Da sauri ta share hawayenta, tace, " a'a Uncle ina jinka".

''Imyiim, bagashi naji muryarki Na rawaba".

"Unc

le murace kawai keson kamani".

" kokuma Uncle akeson yima wayo ba, anyway koma dai Yaya kiringa tuna alk'awarin da kikamin na kin daina kuka".

Kuma share hawayen tayi, sannan tace "to Uncle, insha ALLAH bazaka sake jiba".

" haka kullum k

ike fad'amin ai, amma kin kasa cika alk'awari".

"To kayi hak'uri Uncle, zan kiyaye yanzu. yasu Anty da siddiqa?".

" suna gida lfy lau, ni ina school ne".

"Uncle inka koma ka gaida minsu".

" zasuji insha ALLAHU, yanzu ki samu wata a w

ajen saiki tambayeta inkunada Lecture by this time kinji".

"To Uncle sai anjima".

''Ok bey bey my heartbeat".

Da sauri tace, " Uncle!".

''Yace uyim, yayane? kobaki yarda ke heartbeat d'ina bace?". A wani salo yay maganar.

Da s

auri ta yanke wayar, shikuma ya tuntsure da dariya daga can.

Nima dai Na tayaka Uncle

🀣

, nasan Fans ma zasu tayamu

πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»

.

Amatallah tana yanke wayar ta rik'e ha6a tana fad'in "o ni Khadija, dama haka Uncle yake?".

Amatallah kad'anma kika gani indai

Uncle ne

πŸ˜‚

.

Mik'ewa tayi tana cigaba da juya lamarin Uncle d'inta a zuciya, harta k'arasa wajen wata dake zaune can gefe itama cikin shiga ta kamala, aganinta ita kad'ai ta dace tama tambayar da Uncle yace tayi, dan tun tana waya taga wucewarta ha

r zamanta awajen.................✍

🏻

πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»

One Luv my sweet Fan's

πŸ₯°

*_ALLAH yajik'an iyayenmu._*

πŸ˜­πŸ™πŸ»

[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍

🏻

_*

*_HASKE WRITER'S ASSO..._*

πŸ’‘

_{home of expert and perfect writer's}_

*_SIYASA

KO K'ABILANCI_* ⁉

_(Hattara matasa)_

*_Bilyn Abdull ce

πŸ€™πŸ»

_*

_masoyanmu Amanna afuwa dajin *YAR SARKI CE* shiru, wasu 'yan dalilaine suka kawo hakan, amma insha ALLAH zata cigaba

πŸ₯°πŸ₯°

._

____________________

*_Number 20

_*

____________________

Wani Saloon Ya Jabeer yakai su Amatallah, a can suka iske Anty maijiddah, itadai Amatallah sai mamaki take a k'asan ranta.

Babu 6ata lokaci wata farar mata tajata wata k'ofa, Ashe cikin gidane, koda suka shiga saita

kaita wani d'aki, zani tabata tace tacire kayanta tana zuwa.

Amatallah dai mamaki dukya kasheta, amma duk abinda aka sakata babu musu takeyi, tasan Anty maijidda dai bazata cutar da ita ba.

Tana gama cirewa babu dad'ewa matar tadawo da kwa6a66en

Abu a boket k'arami.

Mik'a mata boket d'in tayi, tace, "dan ALLAH karki cutar da kanki, ki tabbatar ko ina Na jikinki yasamu, bayan kin gama murje jikinki saiki shafa wannan shikad'ai a fuskarki wannan kuma bayan kin gama zanzo nasaka miki a gashi. d

aganan kishiga nan cikin, ta nuna mata wani k'aton bambu da aka saka wani Leda.

Kai Amatallah ta jinjina mata.

Duk yanda matar nan tasakata haka tayi, abun sai wani masifar k'amshi yakeyi, haka dai tagama murje ko ina najikinta tashiga banbun kamar

yanda matar tace, kusan mintuna biyar da kammalawarta matar tayi Knocking k'ofa da tambayarta ta kammala.

Amatallah ta amsa mata da eh.

Shigowa tayi, taga Amatallah tayi yanda duk tace, taji dad'i, dan haka tafara shafa mata d'ayan abun a gashinta,

tana gamawa tasaka bak'ar Leda ta d'aure mata kan, tafice ta barta.

Sai da Amatallah tayi kusan awa biyu sannan matar ta shigo tahad'a mata ruwan d'umi da k'amshi, sai wani sabulu tabata tace tayi wanka.

Indai tak'aice muku sosai Amatallah t

asha gyara a d'akinnan, kusan awa 3 sannan suka dawo ainahin wajen saloon d'in, su Anaty maijidda sai yaba k'yan da tayi sukeyi, Nazeefa harda tatta6ata.

Itadai Amatallah murmushi taitayi, ita kanta tanajin canji Na musamman a jikinta.

An kuma

wanke mata kai aka gyara matashi, sanan aka mata kunshin Jan lallale da bak'i.

Dole ka ganta kasan Amaryace, tahad'u sosai abin harma ba'a magana, ga wani sirrin k'amshi Na musamman.

Basubar saloon d'inanba saida aka yima Amatallah simple makeu

p mai burgewa, ba'a cikashi d'inanba yanda zai canja mata kamanni, amma tayi k'yau masha ALLAH.

bayan matar nan ta had'ama Amatallah wasu kayan gyaran jikin dazata ringayi a gida suka tafi.

Anty maijidda gidansu ta wuce, Jabeer kuma ya maida A

matallah da Nazeefa gida.

Kusan k'arfe 3:26pm lokacin, kuma ALLAH yasosu Aneesa bata dawoba.

Dawowarsu babu dad'ewa sukaji dawowar Aneesa, itama gyaran jiki taje, takumayi k'yau sosai wlhy, sai shek'i da walk'iya takeyi kamar amaryar itama.

Ba

tawani 6ata lokaciba tashiga ketchin, dama kafin ta fita ta tanaji komanta, had'awa kawai zatayi.

Nazeefa Ce tafito ta tayata komai, danta hana Amatallah fitowa. Tace baza'a ganta ba a waje sai su Uncle sun shigo gidan.

Rashin ganin Amatallah yas

a Aneesa d'aukar koma bata gidan, bakuma ta tambayi Nazeefa ba.

K'arfe hud'u suka gama komai, suka kuma gyara gidan da bazama kowanne lungu da sak'o k'amshi mai dad'in gaske.

Aneesa ta shigo 6angarenta dan tsara kwalliyar tarbar mai gida.



Amatallah tana idarda sallar la'asar saiga Nazeefa ta shigo, itace ta zaunar da ita ta gyara mata kwalliyarta datayi alwala wasu guraren suka d'an 6aci.

Wani material pink colour da akaima d'inkin sket da Riga Nazeefa tabata,

d'inkin yayi 'yau ov

er, gashi yafitar da ainahin Shep d'inta, sannan colour d'in ya haska bak'ar fatarta. Nazeefa tamata d'auri mai k'yau, itadai Amatallah kallon ta kawai takeyi cikeda mamaki, amma takasa cewa komai, ita damuwartama yanda zata had'u da Uncle d'in nata, dan k

unyarshi takeji sosai, musamman ma idan ta tuna da yanda yake mata a waya yanzun.

Bayan Nazeefa ta gama mata komai hardasu sark'a da abin hannu, ta fesheta da turarurruka masu k'amshin tsiya da shiga zuciyar mai shak'arsu.

Hummm, masu karatu, ya

ufa Amatallah d'inku ba'a magana, ni tsorona ma karta haukatar mana da Uncle fa

πŸ™†πŸ»

.

Aneesa ma tanacan tana tsara nata gayun, itamafa babu sauk'i, dan wanka iya wanka tayi, ta bulbule lungu da sak'o Na jikinta da k'amshi, dama harda Siddiqa aka tafi gid

ansu innani.

A can kuwa 4:30 nayi su Anty maijidda da yara suka tafi tarbo su Uncle a airport.

5:8pm jirgimsu ya sauka.

Uhhm nafad'a lokacinda naga Fateema Na sakkowa jirgi da k'yar, cikinta ya tsufa, tak'ara k'yau da haske ga k'iba, Alhaj

i Muhammad Na bayanta shimafa ba'a magana, ya murje dakuma kwarjini, sajennan da gemunsa sunkuma yin bak'i sid'ik, sai furfura d'ai-d'ai data k'awata gemun nasa, wadda bazamuce ta tsufa bace sai dai baiwarta da ALLAH yamasa.

Da gudu yara sukaje suka t

arosu suna ihun Kiran Abbunsu da Ummansu.

Alhaji Muhammad duk yahad'asu ya rungume harda yaran Anty maijidda guda uku, bayason su Ce zasu rungume Fateema dantayi nauyi.

Tsaye tayima tana kallinsu da murmushi jin dad'in ganinsu.

Anty maijidda ta

k'araso tana mata sannu da zuwa da tsokanarta uwar biyu.

Duk dariya sukayi, aka shiga gaishe-gaishe kafin su k'arasa mota, dole saida suka had'a da taxi dan motar tamusu kad'an.

Duk hayaniyar da akeyi a gidan Amatallah Na jiyowa daga d'aki, gaban

ta sai kuma fad'uwa yake, heartbeat d'inta nak'ara k'arfi, amma takasa fitowa Dan kunya takeji.

Uncle kam tunda Aneesa tafito idonshi akanta, bak'aramin k'yau kwalliyarta tamasaba, gadan-gadan shi ta nufa zata rungume amma saiya doje ya d'auki Siddiqa

da Umminta, Dan bazai iya abin kunyarnan gaban k'annensa da yaransaba.

Lamarin yabama Fateema dariya sosai, danta lura tsaf da nufin Aneesar dakuma abinda mijin Nasu yayi Na gujema manufarta.

Nazeefa ma ta lura, ta juya fuska tana dariya.



Duk da abinda yamata ya 6ata mata rai, amma saita danne, ta k'araso daf dashi tana masa sannu da zuwa, cikeda fara'a ya amsa mata da kanne mata ido d'aya. ta sakar masa da wani sihirtaccen murmushi kuwa da d'age masa gira.

Kallo d'aya tama Fateema tac

e sannunki.

Ran Fateema ya 6aci da rainin wagon Aneesar, ya gida kawai tace itama tayi gaba abinta.

Har suka k'arasa ciki yana baza idon son ganin Amatallah amma babu ko k'urarta. Anty Maijidda Na lura dashi, sai kawai tayi murmushi, a zuciyarta t

ace ya Muhammad Amatallah tawuce arhar ka ganta kai tsaye, saika bita har d'akinta.

Dukda daular abincin da Aneesa ta had'a musu bata d'auke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login