Showing 9001 words to 12000 words out of 111738 words
Dariya sukayi gaba d'aya, harda Amatallah datayi murmushi tana satar kallon uncle M.A d'in.
sun d'an ta6a hira, harya kira Fateema da Aneesa suka gaisa da Amatallah da Amminta, amma kowacce badan ra
nta yasoba, musamman Aneesa dakejin zafin Amatallah sosai, (koda yake halintane, tanada zafin kishi, akan Alhaji Muhammad d'in
π
, saboda auren soyayya sukayi).
Sai wajen tara suka tafi da k'yar, akabar Ammi da Amatallah.
dukda baba Ama Na fa
rgabar barinsu su kad'ai, saboda halin da Amatallah ke kwana aciki, gefe kuma yanajin kunyar barin abokinsa ya kwana shika d'ai, haka dai suka tafi yana addu'ar ALLAH yasa su kwana lfy..........β
π»
*_masoya, INA alfahari daku over wlhy_*
ππ»ππ»
On
e Luv my fan's
π₯°
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
πππ»
_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_(home of expert and perfect writer's)_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
____________________
*_Number 4_*
____________________
........"Haba dan yanzu Ku kun k'yauta kenan? har a kama su zike kusan 2days amma babu Wanda ya sanarmin acikinku?".
"To yanzu da ace shi gagis ya mutu fa? Kenan baza
ku sanarminba? Kunsanfa yarannan sunada maruk'ar amfani a garemu yanzu, dolene komai k'ank'antar Abu mu tsaya musu....".
" sorry sir!, muma bamuji zancenba sai d'azun wani acikinsu Daba'a kamaba yazo yafad'a mana".
"Yaza'ayi ku sani kuwa? tunda b
akwa maida hankali wajen kula da aikinku. yanzu ina gagis yake?".
" sir! Yana asibiti kwance, sukuma su zike suna police station."
"Mtsoww!!, aikin banza kawai, yanzu saiku shirya muje mu kar6o su zike, dan sunada matuk'ar amfani a tafiyarmu. S
hikuma gagis zuwa gobe sai wasu acikinku suje su dubashi a asibiti".
" okey sir!.
_(Nace, "hummm, hattara matasa, kun gadai halin 'yan siyasar k'asar tamu, wannan d'an takarar bata gagis dake kwance a gadon asibiti yakeba, a'a, tasu zike yakeyi, dan
su sunada lafiyar dazaiyi amfani dasu, shiyyasa zaije da kansa ya kar6osu a hannun police, amma gagis, zai tura wasune daga mutanensa su duboshi, tunda shi bashida amfani agareshi a halin yanzu. to wlhy haka kuke a wajensu, sai zaku musu amfanine suke kula
ku, idan kuma rashin lafiya ko wani tsautsayi ya sameku basuda matsala daku
π€·π½
β, bare kuma idan sun d'ane kujerar
πΊ
dasuke nema
π€¦
ββ)._
_____________________________
"Dear amma dakayi hak'uri da tafiyar nan sai da safe idan ALLAH ya kaimu mana".
d'ago idanunsa yayi yana kallonta da murmushi, saboda yanda tayi maganar.
cikin tsokana yace " my Neesa kodai bakison kwananki ya gudune?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana 'Yar dariya, "kai my dear! Nidai ALLAH bance haka ba, ai nasan ma
ganin baba zaka amsone".
"Tom shikenan my Sweet Neesa, amma ba maganin babane kawai yasani tafiyar yammarba gaskiya, dan Alhmdllh jikin baba da sauk'i, bakamar wata d'aya daya shige ba. Amatallah ce batada lafiya, suna asibiti ma an kwantar dasu".
Tuni fara'ar fuskarta ta ragu, babu yabo babu fallasa tace, " ALLAH yabata lafiya".
Daganan tamik'e ta hau had'a masa kayansa.
Binta yayi da kallo kawai, yad'an girgiza kansa yana murmushi, baisan miyasa dukkan matan nasa suke nuna kishi aka
n Amatallah ba?, bayan sunsan jinjinar alak'ar dake tsakaninsa da mahaifin yarinyar, sun kuma san babu yanda za'ayi ya iya auren Amatallah, danshi matsayin d'iyarsa yake kallonta, bai ta6a banbanta matsayin Amatallah dasu Abul-khair ba. Sai dai kuma matans
a sun gaza gane hakan, ayanzu haka suduka insunga Amatallah d'in bazasu iya ganetaba, saboda tadad'e batazo kano ba.
A baya basu nuna kishin Amatallah d'in, amma tun zuwan dayayi jos sati 4 daya wuce kar6o maganin baba, saiya d'auki pictures d'in Am
atallah a wayar babanta (abokinsa), shikam harga ALLAH bada wata manufa yayi hakanba, shiyyasa daya dawo yanuna musu hoton dansuga yanda tak'ara girma, shima kusan 3years bai gantaba, suna ganin hotunan suka canja fuska. tundaga lokacin ko maganarta yayi s
aisun nuna jin haushinsu, yarasa miyasa suke hakan shikam?.......
Ta6asa datayine yasashi dawowa hayyacinsa, har yanzu bata saki fuskaba tace, ''gasu Na had'a".
Mik'ewa yayi yana fad'in ''to sannu da k'ok'ari, ya d'auki sauran abin dazai buk'a
ta da tsarabar daya yoma Amatallah yasaka a madaidaiciyar bag d'in data had'a masa kayan.
Jakar ya d'auka, yad'ago yana kallonta, tsaye take jikin mirror, tayi kicin-kicin da face, ahankali yatako gabanta, yad'an murmusa kafin ya rungumeta a jikinsa,
acikin kunne yaymata rad'a, sannan ya sumbaci la66anta da goshinta yana fad'in "saina dawo".
Duk da maganarsa tasaka zuciyarta yin sanyi, amma saita gimtse, batace komaiba tabiyo bayansa, jakar takar6a suka sakko k'asa tare.
Babu kowa a falon, yar
a duk suntafi school.
Kallonta yayi yace, ''bara nayi sallama da Fateema".
Kauda kanta tayi daga kallonsa, batace komaiba.
Gaba yay abinsa, zuciyarsa Na mamakin kishi irin na mata. komin k'ank'antar Abu sai sun nuna kishi akansa, musamman
Aneesa tafi fatima kishi.
A Falo ya tadda Uwargidan tashi zaune tana kallo, tamasa sannu da zuwa.
Amsawa yayi yana zama kusada ita, idonsa akan TV yana kallon film d'in datake kallon. sai kuma ya maida kallonsa kanta.
" Fateema zanje Jos ne
".
"Jos kuma Nurri? Da ranarnan? Ko jikin babane ya motsa?".
" a'a, ba jikin baba bane, zan dai kuma amso masa maganin nan ne, daganan naduba jikin Amatallah batada lafiya, sunama Asibiti an kwantar da ita".
Dukda maganarsa ta soki
zuciyarta amma saita danne, tace, "ayya ALLAH yabata lafiya? Mike damunta haka?".
" Uhm to, bandai saniba, d'azu nake waya da Brother shine yake sanarmin."
Azuciyarta tace shine kake sauri katafi tunda ga 'Yar Goal. afili kuma tace, "ALLAH yabata
lafiya to, a gaida mana dasu".
"okey zasuji".
Harya mik'e yakoma ya zauna, yakula da yanda itama yanayinta ya canja, amma dayake tafi Aneesa hankali tayi k'ok'arin danne kishinta, yay murmushi yana fad'in "koma abinda zan tuna baza'a baniba?".
Kamar zatace bagashi zakaje inda za'a makaba. saikuma ta danne tace, ''to mikake so?".
Girarsa d'aya yad'age yace, " komima?".
Kumatunsa ta sumbata.
Shima haka ya sumbaci nata, sannan suka fito.
Aneesa Na falo tsaye, tagama cika fam d
a haushi, koda suka fito bata kallesuba tayi gaba abinta, binta kawai yayi da kallo, itakam Fateema saita ta6e baki tana Harar bayan Aneesa.
Har jikin motarsa suka rakashi, Aneesa tasaka masa bag d'in a gefensa, bayan yatada motar yamik'o musu hannuns
a Na dama, d'aya bayan d'aya sukayi musabaha
π€π»
, sannan yace, "abama yara hak'uri nayi tafiya basu saniba, sannan dan ALLAH karna dawo naji abinda zai 6ata raina, Ku kama kanku, insha ALLAH 2days kawai zanyi nadawo".
Atare sukace insha ALLAH bazakaji
komaiba, ALLAH ya tsare.
Yace, " amin to my Sweet wife's". dan son tsokanar su yace, " Amma bakuce na gaida Amaryaba".
Kowacce kauda kanta tayi gefe basuce komaiba, dan bak'aramin dukan zukatansu maganar tayiba, ashedai hasashensu gaskiyane?.
Da sauri Aneesa tashige ciki tana hawaye.
πΉ
Jiyayi kamar ya kwashe da dariya, amma saiya gimtse, ya kalli Fateema dake tsaye har yanzu yace, "my tee... bud'emin gate to, tunda bazakuce Na gaishetanba, saina dawo".
Kanta kawai ta d'aga masa, tanufi
gate tabud'e masa, harya fice yana d'aga mata hannu, tamaida tarufe sannan takoma cikin gida zuciyarta Na k'una, dajin tsanar Amatallah.
Nikam bilynku Nace, "wannan fa shine gudu a duhu masu karatu
π€£π₯΄
".
Yana tuk'i yana dariyar abinda matan nasa sukay
i, a fili yace, " dama kun kwantar da hankalinku my wife's, Muhammad bashida burin k'ara aure, koma zanyi babu yanda za'ayi Na auri 'yar cikina, Amatallah she is my daughter ".
Da wannan tunani yak'araso gidansu mahaifarsa.
A k'ofar wani gida
yay parking motar, gidane irin ginin da, sai dai ko ina mulmule yake da siminti, tundaga k'ofar gidan har zuwa bangon gidan.
Yatura murfin yashiga soron gidan da sallama, karo sukaci da wani saurayi dabai wuce 30years ba.
"A ya Muhammad barka da zu
wa".
" yauwa Jabeer, daga ina haka kuma? bakaje aiki bane?".
"Wlhy naje yaya, mantuwa nayi nadawo d'auka, ina yarana? duk suna lafiya dasu Aunty's?".
" lafiyarsu k'alau, ya jikin baba?".
"A alhmdllhi wlhy, yanzu haka nabaro innani nabas
hi kunu dayasa a dama masa".
" masha ALLAH, jiki yafara sauk'i, bara to nashiga, dan zanje Jos ne".
"Amma yaya Muhammad tafiyar yamma?".
" to yaza'ayi Jabeer, ai ranar dole sai dole, bara nashiga dai".
"To shikenan, ALLAH ya tsare hanya
, a gaida mana su Yaya Ismail da iyalansa".
" insha ALLAH zasuji".
Musabaha sukayi
π€π»
, shi ya shiga, shikuma yafita.
Tsakar gidan babu kowa, sai dai a share yake tas, sai kuma k'amshin girki dake fitowa daga kichin d'in tsakar gidan.
Kai ts
aye d'akin baba ya nufa, tunda jabeer yace innani tanacan.
Sallama yayi a k'ofar d'akin, sai da aka bashi izinin shiga sannan yashiga da sallama.
Mahaifinsu na zaune a saman k'atuwar katifar da yake jiyya, ya jingina da filuluwan da innani ta sak
a masa a jikin bangon, yatsufa sosai gaskiya, duk da hadda alamun rashin lafiya data kuma fiddo tsufan nasa, danma 'ya'yansa tsaye suke Kansa wajen kulawa dashi, musamman ma Alhaji Muhammad d'in. Sai dattijuwa itakuma tana zaune a kujera 'Yar tsugunno kusa
dashi, itama dai babu laifi ta manyanta sosai gaskiya, sai dai jikinta yafi Na baba k'arfi, saboda lafiya da ALLAH yabata, hannunta rik'eda ludayi zata saka a kwanon shan ruwa, da alama tagama bashi kunun.
Tunda yashigo tamasa kallo d'aya saita kauda
kanta gefe. baba kam murmushi yayi, idonsa akan sa..
Ya tartare malun-malun d'insa ya zauna a k'asa kusada babansa shima yana murmushi, "sannu baba, ina yini?".
Ahankali baba yace, " lafiya lau Muhammadu, ya iyalanka?".
"Lafiyarsu lau baba,
ya k'arfin jiki?, duk da dai yauma naga Alhamdulillahi".
Murmushi baban yak'arayi, yace, " gaskiya ne Muhammadu, jiki kam sai dai mucigaba da godema ALLAH".
"to Alhmdllh baba, ai mu haka mukeso, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana masu amfani".
Baba ya amsa da ''amin Muhammadu".
Kallonsa ya maida ga innani data kauda kanta gefe tun d'azun, yace, " Innani ina yini".
Kuma kauda kanta tayi sannan ta amsa masa. ta tambayi iyalansa.
Shima kansa a k'asa yace duk suna lafiya.
Ba
tace komaiba tafara yunk'urin tashi.
Da sauri yace, "innani dama zan koma jos ne wajen maganin baba, dan naga yanajin dad'insa, daganan kuma zan duba d'iyar Isma'il batada lafiya, har an kwantar da ita a asibiti ma".
Yanzu kam sosai ta kalleshi
, tace, " subahanallah, badai Khadija ba?".
"Eh innani ita".
" miya sameta?".
"Wlhy nima ban san dai miyake damuntaba, sai dai naje tukunna".
Daga innani har baba addu'a suka mata, sannan baba ahankali yace, " amma Muhammadu zakayi tafiyar da
re ai".
Kallon agogon hannunsa yayi, "baba insha ALLAH kumin addu'a zan Isa da wuri, yanzu dana fita salla kawai zanyi Na d'auki hanya".
" to shikenan ALLAH ya tsareka, yakaika lafiya kaji".
Amin baba, ALLAH ya k'ara lafiya".
Sukace amin.
ya fiddo kud'i a aljihun babbar rigarsa, saman katifar ya d'ora, "innani ga wannan kowani Abu zai taso bana nan, insha ALLAH jibi zan dawo".
Batareda ta kalleahiba tace, " da kama bar kud'inka, dan Wanda kabada jiyama ko ta6asu ba'ayiba, munada komai
agidannan, d'azuma jabeer yayo cefane mai yawa dazaiyi iya kaimu sati".
"Duk da haka a ajiye innani, ina Nazeefa da Shehu? Banji motsin suba".
"Nazeefa ta tafi gidan maijiddah, zata tayata aiki abokiyar zamantace ta haihu jiya, Shehu kam wai yat
afi makaranta yace"..
"ALLAH sarki, to ALLAH ya raya, shikuma ALLAH yasa gaskiyane, tunda nasan halinsa. bara naje lokaci Na k'ara tafiya".
"Katsaya kaci abinci, naga Ramatu takusa gamawa".
Agogonsa Yakuma kalla, ya d'an kwantar da murya, " k
iyi hak'uri Innani, gara naje karnayi dare, naci abincima babu dad'ewar nan."
"addu'a duk suka masa, yafita yana amsawa, zuciyarsa nak'ara masa dad'i, dajin k'aunar mahaifan nasa. salla kawai yayi ya d'auki hanya.
_______________________________
Koda d'an siyasar nan Mr Pam da jama'arsa sukaje police station sai suka nemi ganin d.p.o
Bayan ankaisu office d'insa, suka gaisa cikin mutunci, sannan ya mik'a buk'atarsa ga d.p.o nason asaki su zike, da farko d.p.o yaso ya tirje.
Amma
tunda Mr Pam ya fiddo 'yan dubu-dubu bugun Abuja sai d.p.o ya waske. Mr Pam yay murmushi ganin yanda d.p.o yayi.
Ya ajiye kud'in agabansa yana fad'in "Yaya za'a banisu yalla6ai?".
" wata 'yar dariya d.p.o ya d'anyi, yasa hannu kan kud'inda Mr Pa
m ya ajiye, sannan yace, "yanzun kuwa".
Daga Mr Pam har yaransa biyu dake tare dashi dariya sukayi.
Duk wani ciku-ciku daya dace Mr Pam yayi, yasamu nasarar fiddo su zike.
Wad'anda tunda aka bada belinsu suka fito da k'udirin d'aukar mataki aka
n Amatallah da ahalinta.
Su duk zatonsu babantane yamusu shunen 'yan sanda suka kamasu.
Shiyyasa suka k'udirci ramawa..........β
π»
_(wannanfa Shine halin mafi yawan jami'an tsaron k'asar tamu. Shin tayaya za'a samu gyara? bayan masu gyaran suma su
na buk'atar a gyarasu, *CIN HANCI DA RASHAWA* yazama abokin kowa a k'asarmu, kuma duk a dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*, zakiga d'an siyasa yayi duk wani shigi da fici wajen samun yanda yakeso, koda bai cancantaba. Zakiga ankama mai laifi awani waje, amma s
aboda bad'an yankin bane, ba d'an k'abilar bane sai a masa mummunan hukunci, amma idan k'abilarsa ne babba awajen, da 'yan uwansa sunzo sun mik'a sai a fiddashi, komai girman laifinsa, shiyyasa zakuga idan mutum k'abilarsa nada wani babban muk'ami awaje ba
yajin tsoron shiga kowanne tarko, saboda alfarmar dayake da ita, shin yaya zamu kira matsalolin k'asarnan?, *SIYASA KO K'ABILANCI!?* ne ke jagorancin lalacewarmu
π€·π½
ββ?.)_
*_ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu
ππ»π
_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typ
ingβ
π»
_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
*_Happy Birthday Abba gana, ALLAH yak'aro shekaru masu a
l'barka da amfani a duniya da lahira
π―π»πͺππΎπΉ
_*
____________________
*_Number 5_*
____________________
Kusan 5pm ya isa garin jos, damma ba gudu yakeba, yakuma tsaya a garin Mr Ali yayi sallar la'asar, dan yana ganin kafin yashigo gari time y
a shige sosai.
Baban Ama... da Ammi duk suna a asibitin, Amatallah na kwance, idonta biyu, amma tarufesu, su Aminta ne kawai ked'an hira duk akan ciwonta.
Wayar baba tayi ringing, cikin fara'a ya d'auka yana fad'in "inaga brother ya iso kam".