Showing 21001 words to 24000 words out of 111738 words

Chapter 8 - Siyasa-ko-kabilanci-complete

08 Sep 2026

31

kulum cikin yawo daga Kano zuwa jos, har results d'insu ya fito, suduka sunsami abinda suke buk'ata, wannane yasakasu farinciki.

Babu 6ata lokaci kuma aka shiga nema musu makaranta, cikin amincin ALLAH kawu mahaifin Isma'il

yay nasarar sama musu a University ta jos.

Wannan ne dalilin dawowar Muhammad jos da zama, sai lokaci-lokaci yakanje Kano.

Sun fara University babu dad'ewa ALLAH yayma Amina yayar Isma'il rasuwa, sosai rasuwar ta girgiza Isma'il da kawu, hakama M

uhammad danya santa sosai.

Rayuwar samartakar Isma'il da Muhammad abin sha'awace, dan zaratan samarine masu kulada addini da kare Kansu wajen rud'in zamani da samarinmu ke jefa Kansu. Sun maida hankali sosai akan karatunsu, kuma suna samun nasara sosai

.

Suna a level two ALLAH yahad'asu da Khadija, yarinya nutsatstsiya itama, tunda Isma'il yaga Khadija yafara k'aunarta, sai dai ya 6oye abin a zuciyarsa da burin saisun kammala karatunsu ya furta mata.

Sai dai kash Ashe shima Muhammad ya kamu batare

da sanin Isma'il ba, shikam yakasa rik'e hakan a ransa ya furtama amininsa Isma'il.

Hankalin Isma'il yatashi sosai, saboda k'aunar Khadija yakeyi sosai, amma haka yayta jarumtar dannewa, yabama brother d'insa kwarin gwiwwa da goyon baya 100%, shinema da

kansa ya sanarma Khadija soyayyar da brother d'insa kemata. batawani basu wahalaba ta amince, dandanan soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Muhammad da Khadija. Isma'il kuma yanata yak'in cireta a ransa, dan har k'asan zuciyarsa yagama aminta yabarma d'an

uwansa Muhammad ita.

Kullum Muhammad kan takura Isma'il akan yakamata shima yayi budurwa, yanda dasun kammala karatu sai ayi bikinsu tare.

Dariya kawai Isma'il keyi yace katayani nema brother, nifa har yanzu ban k'yalloba.



Suna gab da ka

mmala karatunsu saiga Saliha shima ALLAH yabashi.

Muhammad yayi murna sosai, yakuma k'arfafa d'an uwansa.

Alk'awalin ALLAH ya cika, su Muhammad sun kammala karatunsu, nanma ansha tata 6urza akan komawar Muhammad kano.

Koda Muhammad yakoma gida s

ai mahaifinsa yajawosa suka cigaba da zuwa kasuwa, ahankali Muhammad ya dilmiya a harkar, ya kware sosai tareda kawo canje-canje masu yawan gaske a kasuwancin mahaifin nasa, kasancewar shi d'an zamanine kuma mai ilimi.

Shikam Isma'il yana jos babu abin

da yakeyi, lokaci-lokaci dai yakanzo kano, yayi kwanaki ya koma abinsa.

A wannan tsakanin auren Isma'il yatashi, ALLAH bai cika musu burinsu nayin aure rana d'ayaba, dan Isma'il ne yafara angwancewa. batun yanda shagali ya kasance 6ata lokacine ma

aii.

πŸ˜„

Bayan auren Isma'il Muhammad yakawo musu shawarar sukoma suyi masters nasu, (degree na biyu), 100% Isma'il ya aminta da batun. dan haka suka fara nema a University of Lagos (Lagoon), nanma sunyi nasarar samu kuwa, dan haka suka fara karatun

su cikin nasara. A lokacin Saliha matar Isma'il nada ciki.

Rashin auren Muhammad yafara damun Isma'il, dan haka yafara takura masa akan maganar Khadija.

Amsar daya saba bashice yakuma maimaita masa, akan yana jiran Khadija ne kamar yanda iyayenta s

ukace saita kammala karatu ta.

"Haba brother, kaikuma saika zauna saita kammala d'in?".

Dariya Muhammad yayi, yadafa kafad'ar Isma'il yana fad'in " cool dawn mana my brother, duka kwana nawane yarage? Insha ALLAH baifi watanni 7 bafa kaima kasani

".

"Haka kullum kake fad'a, amma har yau ni banga wata bakwai d'in zata k'areba, kuma mizai hana kaima baba magana a tsaida rana tun yanzu, bayan ta kammala sai musha biki kawai".

Shiru Muhammad yayi yana nazarin maganarsa, zuwa can kuma yace,

" gaskiyarka fa brother, kaima kazo da shawara".

Babu 6ata lokaci sukayi amfani da shawarar Isma'il aka kai kud'i aka tsaida rana, sai ta kammala karatunta.

Watanni bakwai na cika kuwa akasha biki, lokacin Saliha ta haihu d'an baizo da raiba

.

Wattani shida tsakani saliha yakuma samun wani cikin, amma Khadija dai babu labari.

Watanni tara cif Saliha ta haifi d'iyarta mace k'yak'yk'yawa.

Muhammad yayi matuk'ar farin ciki, tamkar shi aka haifamawa, komai kuwa Na hidimar sunan baby

Muhammad ne yayishi, hatta da suna ma shine yarad'a mata Khadija, sunan mahaifiyar Isma'il, kuma matarsa.

Tun daga wannan lokacin Muhammad yad'auki son duniya ya azama Khadija dasuke kirada (Amatallah), komai yagani Na yara saiya siya matashi, kullun f

irarsa akan best daughter d'in sace.

A haka suka kammala degree d'insu Na biyu daga lagos suka dawo gida, Isma'il jos, Muhammad kano.

Muhammad yacigaba da kulada kasuwancin baba, kuma har zuwa lokacin ko 6atan wata Khadija batayiba, duk k'arshen wa

ta Isma'il kan d'akko iyalansa suzo kano, kokuma shi Muhammad yaje danasa iyalan.................✍

🏻

Kubini bashi a page 11 please

πŸ™πŸ»πŸ˜„

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu

πŸ˜­πŸ™πŸ»

_*

[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍

🏻

_*

*_HASKE WRITER'S ASSO...

_*

πŸ’‘

_{home of expert and perfect writer's}_

*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉

_(Hattara matasa)_

*_Bilyn Abdull ce

πŸ€™πŸ»

_*

*_Ku gargad'i mai gina ramin mugunta!!

πŸ“»

_*

πŸ˜₯πŸ‘ˆπŸ»

Wannan gaskiyane

*Doctor Alh

aji mamman (shata)*

ALLAH ya gafarta maka

πŸ™πŸ»



____________________

*_Number 9_*

____________________



A k'ofar gida yay parking motar sa, sannan ya kama k'ofar zai bud'e, a rufe take.

Shiru yayi yana kallon k'ofar, yasan tunda ba

ya nan bazasu ringa barin k'ofar a bud'eba. Mota ya koma ya d'akko wayarsa. Aneesa yakira.

A yangance tamasa sallama.

Shikuma ya amsa murya na rawa.

Gabantane yafad'i, tacire wayar daga kunnenta ta kuma kallon screen d'in domin tabbatarwar s

hine kokuwa?. ganin shid'inne yasata maidawa a kunnen.

"My dear! Lafiya kuwa?".

Ajiyar zuciya ya sauke, a raunane yace, " kizo ina k'ofar gida......

Bata jira yakai k'arsheba tafito da sauri. K'aramar k'ofar gate d'in ta bud'e ta lek'a.

A

tsaye ta gansa ya jingina da jikin gate, gabanta yakuma fad'uwa, hakan ya kuma tabbatar mata babu lafiya.

Takowa yayi ahankali yashiga gidan, ta kalleshi tana fad'in "dear motarfa".

Kansa ya girgiza mata yace, " fita zan kumayi". yana maganar y

ana tafiya.

Wannan yasata binsa da sauri itama. babu kowa a falon k'asa, dan haka ya haye samansa, Aneesa na binsa abaya.

A kan gadonsa ya zube yana sauke numfashi, Aneesa ta zauna kusadashi tana tambayarsa miyafaru cikin damuwa.

Bai bata ams

aba, sai dai cewa yayi ''had'amin ruwan wanka".

Jiki a sanyaye tamik'e zuwa bathroom d'insa, ruwa mai d'an zafi ta had'a masa, tana niyyar fitowa shikuma yashigo, matsawa tayi yashiga sannan ta fita.

Yana wanka yana hawaye, lallai duniya abar

tsoroce, jiya iyanzu yana tareda amininsa, amma yanzu gashi awani hali mai rikitarwa, ALLAH sarki Saliha, ALLAH ya gafarta miki

😭

.

Aneesa kam da sauri ta sauka k'asa zuwa 6angaren uwargidanta.

A falo ta iskesu itada yara suna homeworks d'in makar

anta.

Yanda tashigo a rikice yasaka Umman abulkhair saurin kallonta, "lafiya kuwa momyn yara?".

" inafa lafiya ummansu.........nanda ta sanar mata abinda ta Sani gameda canjawar mai gidan nasu, da dawowar babu zato babu tsammani da yay musu, alhal

in gobene yakamata yadawo.

Atare suka fito zuwa d'akinsa.

Bai fitoba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Babu dad'ewa yafito, sannu da zuwa Fateema tamasa.

Batareda ya kallesuba ya amsa yana k'ok'arin shinfid'a abin sallah. Sallar magriba

ya gabatar, sannan yay isha'i, duk suna zaune suna kallonsa.

Yay addu'a yana share kwallar dake bin kumatunsa.

Sosai jikin matan nasa yakuma yin sanyi k'alau, sun k'agara ya idar suji mike damunsa.

Ganin yanda suka damu matuk'a yaga bai

dace yabarsu a duhuba, cikin dauriyar danne hawayensa yaymusu bayani.

Daga Aneesa har Fateema kuka suke sosai.

Mukullin mota da wayarsa kawai ya d'auka yafita zuwa asibitin, yabarsu Aneesa nacigaba da kukansu.

A motama yana driven yana hawa

ya, yakasa jarumtar danna kukansa, tausayin Amatallah da abokinsa kawai ke nuk'urk'usar ruhinsa. a haka ya Isa asibitin.

Jabeer da kawunsu Malam Yakubu ya tarar suna jiran isowarsa.

Gaida kawu Yakubu yayi, ya amsa tareda masa ta'aziyya sannan

suka k'arasa ciki.

Inda aka kwantar da baba sukaje, suduka kallo d'aya suka masa suka fara hawaye. Ba k'aramar k'una baba yasamuba gaskiya, abin ko dad'in kallo babu. barci yakeyi saboda sunmasa allurar barci kozai samu sauk'in rad'ad'in dayakeji.



Jiki a sanyaye sukabar d'akin, inda Amatallah take sukaje, tana kwance kamar yanda ya barta. matuk'ar tausayinta ya mamaye zukatansu, Uncle M.A ya kauda kansa daga kallonta saboda hawayen dasuka cika idonsa, d'an yatsa d'aya yasa ya goge sannan yanemi gefe

ya zauna.

______________________________

Uncle M.A da Jabeer a asibitin suka kwana.

Wajen k'arfe 7:am suna shirin tafiya da gawar Ammi gida dan amata sutura Amatallah ta farfad'o.

Da sunan iyayenta ta farka a baki, tana kuka tana kiran

Ammi da baba ta. da sauri wata Nurse taje ta sanarma doctor shu'aibu Amatallah ta farka.

Dagashi har Uncle M.A a hanzarce suka k'araso.

Tana ganin Uncle M.A tamik'e da sauri tana fad'in Uncle ina Ammina da babana!, suna ina dan ALLAH Uncle? ".



Rasa mizai fad'a mata yayi, yay tsaye kawai yana kallonta, idonsa taf da hawaye. Doctor shu'aibu ne kawai ke lallashinta. da k'yar yasamu ta tsagaita da kukan.

Doctor yamatso kusada Uncle M.A, ahankali yace, " Alhaji Muhammad yakamata mubarta tag

a gawar mahaifiyarta........

Bai k'arasaba Jabeer yashigo yana hakki, ''yaya! Yaya! Kuzo yaya Isma'il ne, gashi can.......

Suduka basuji k'arshen maganarba suka fice da gudu, harda Amatallah dake binsu cikin layin rashin k'arfin jiki.

'Dak

in da Baban Ama ke kwance suka shiga.



Hannunsa dabai k'oneba sosai yake mik'oma Uncle M.A, yana kiran brother a ahankali. ga numfashin sa Na fita da k'yar.

Uncle M.A ya k'arasa da hanzari gareshi, shima hannun ya mik'a masa yana hawaye da f

ad'in sannu brother.......

Dai-dai nan Amatallah tashigo tana tangad'i, kawu yakubu da wasu mutane hud'u suma suka shigo d'akin.

K'ara Amatallah ta kwala tazube awajen saboda tozali datayi da babanta.

Dukansu kanta sukayi har Uncle M.A daya zar

e hannunsa daga na babanta.

Baisan ya cacumotaba yana kiran Khadija! Ke Khadija!! Please karkimin haka kema dan ALLAH Khadija. Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ya ALLAH gareka nake, a gareka kuma nake neman taimako......yak'arashe maganar yana fashe

wa da matsanancin kuka.

Shima Jabeer kukan yafara ganin yanda yayansa ke kuka sai kace ba babban mutum ba.

Baban Ama ma hawaye yake yana murmushi da kallon abokinsa da d'iyarsa.

Da k'yar doctor shu'aibu yasamu ya janye Amatallah daga jikin Unc

le M.A.



😭

kai jama'a, ALLAH ka gafarta mana.

πŸ™πŸ»

Kusan mintuna 16 aka samu komai ya lafa, amma Amatallah tana a halin doguwar suma.

Uncle M.A ya koma inda Baban Ama yake, saboda kiran sunansa kawai yake.

Yanzuma hannunsa yarik'e, ahank

ali yake iya magana, amma duk suna jinsa sabida shiru da d'akin yayi.

_"d'an uwana kaga yanda k'addara tayi damu, tsakanin jiya kawai zuwa yau, mungodema ALLAH brother, danshine mafi hikimar masu hikima akan hakan, mutuwa tabbatacen abune akan kowann

e bawa, saidai kowa akwai sanadin tafiyarsa brother, wannan mu shine namu sanadin d'an uwana, duk duniya banida kamarka, dukda inada dangi amma kafisu matsayi agareni, sun kashemin Saliha ta hanyar soka mata wuk'a, awannan halin na isketa bayan dawowata sa

llar magriba, nikuma sun kunnamin wuta, tabbas nasan yaran da Khadija taganine sukai wannan aikin, brother! Na d'auki hakan a matsayin K'ADDARARMU, ga Khadija nan nabaka halak malak, ita kad'aice tarage mini, babu kuma mai iya rik'emin ita tamkar ni sai ka

i d'an uwana Muhammad, ba ruk'on Amatallah kawai nakeso kayi nawani d'an lokaciba, sonake ta kasance a gareka har k'arshen rayuwarka. brother inaso yanzunan a d'auramaka aure da Khadija..."_

Wata muguwar zabura Uncle M.A yayi, jikinsa da muryarsa na

rawa yace, ''brother mikake fad'ane haka?, haba brother khadija fa d'iyatace, inajinta tamkar su Saifudden ne a zuciyata, karkayi haka dan ALLAH brother, gara kace na aurama j........



_Da sauri Baban Ama ya katseshi cikin hawaye, "a'a brother kar

kace komai dan ALLAH, inhar nid'in d'an uwankane da gaske, bakuma k'yamar had'a zuri'a kakeyi daniba ka amince da auren Khadija tunda ALLAH bai haramta makaba, karkayi dubi da d'iyatace, kasancewarta a wajen kane kawai zaisaka ruhina nutsuwa a cikin kabari

na, inada tabbacin har Abadan bazaka ta6a barinta tayi kukan rashina ni da mahaifiyarta ba, duk Wanda zaisan muhimmancin Khadija ko kulawa da ita bayankane, dan ALLAH ka amince, danni lokuta k'alilanne suka rage a cikin dak'ik'un rayuwata, brother nima mu

tuwa zanyi, insha ALLAHU tare zaku bunne gawata data matata, bazan rayuba brother, Nika d'ai nasan minakeji, please ka amince dan girman ALLAH da k'aunar dake a tsakaninmu._

Kowa a d'akin kuka yakeyi saboda tausayi.

Uncle M.A yana kuka yace, "

indai hakan zai sakaka farinciki na AMINCE brother, na amince da auren Khadija dukda ina kallonta a matsayin d'iyata, insha ALLAHU zaka tashi brother, cuta ba mutuwa baceba..........

Kasa k'arasawa yayi saboda kuka daya sark'esa.

Baban Ama ya k'a

ra k'ank'ame hannun Uncle M.A yana fad'in "ngd da amincewarka brother, kasani farinciki, zanbar duniya cikin shauk'in farincikin ganin auren Khadija da ALLAH yabani ita d'aya tilo a duniya, ALLAH yasaka farinciki da kwanciyar hankali a rayuwarku, ALLAH ya

hana duk wani azzalumi tasiri akan wannan aure, ina rok'on alfarmar a d'aura yanzunan brother kafin numfashina ya k'are.

Kai kawai Uncle M.A ke d'aga masa yana zubda kwallah

*****

Kawu yakubu da sauran mutane hud'u, sai doctor shu'aibu da a

bokan aikinsa doctors kusan 10+, sai Jabeer dawasu mutane k'alilan masu jiyya suka shaida d'aurin auren *_Alhaji Muhammad Ahmad labbo da Khadija Isma'il uba (Amatallah)_* akan sadaki naira dubu 30 da kawu yakubu yabada, bayan Jabeer yayi saurin zuwa ATM y

a fidda, kawu yakubu ne wakilin ango, yayinda Baban Ama da kansa yay waliccin auren d'iyarsa tilo Khadija (Amatallah).

Ana gudanar da d'aurin aure cikin dariya da tsantsar farinciki, amma nasu Amatallah acikin kuka da tsantsar k'unar rai aka d'auras

hi, babantane kawai keyin kuka da murmushi lokaci d'aya.

Cikin farin ciki ya k'ank'ame hannun Uncle M.A yana masa godiya, tareda k'ara jaddada masa Amanar Amatallah.

Kuka kawai Uncle M.A keyi yana fad'in "brother bazaka mutuba, kabar fad'a domin A

LLAH, cuta ba mutuwa baceba brother....

Murmushi mai ciwo Baban Ama yayi, " brother sai dai hak'uri, mutuwa kam tazama tilas, ka tabbatarma Khadija na yafe mata, ALLAH ya albarkaci rayuwarta, yasaka mata hak'uri da juriyar danganar rashinmu, tayi hak'

uri da k'addarar data shigowa rayuwarta, watarana sai labari, badan ALLAH baya sonta bane ya d'aukemu, watak'il hakan shine mafi alkairi a rayuwarta, ngdma ubangiji dayabamu damar rayuwa da ita na tsawon shekaru 18, har zuwa yau danaga aurenta, ALLAH yayi

mata al ....bar.... ka.......

Baban Ama ya k'arasa maganar a rarrabe, ahankali kuma yafara kalmar shahada.

Lamarin daya rikita Uncle M.A kenan ya rungume Baban Ama yana kuka mai ciwo da k'unar zuciya......

Jin jikin Baban Ama ya saki yasaka

Uncle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login