Showing 108001 words to 111000 words out of 111738 words

Chapter 37 - Siyasa-ko-kabilanci-complete

08 Sep 2026

18

wasu mazan

πŸ™πŸ™„

.

ALLAH dai ya shiryesu Uncle.

**************

Ana gab da za6e sukasha binkin Aysha da Dr yazeed, Wanda Uncle ne komai a bikin, duk wata hidima daya kamata iyaye suyi shine yayma Aysha, kuma

baigazaba wajen zuwa takanas ya fad'ama danginta komai, harma da rok'onsu wasu sushiga lamarin auren, koba komai dai d'iyarsuce, kimarsa da halin dattako yasakasu nad'o gari zuwa bikin, tabbas jikinsu yayi sanyi daganin Goodness (Aysha) bata rasa komai Na

rayuwaba, saima d'aukaka da ALLAH yak'ara mata, ga miji ga karatunta mai yankeba, Wanda fatansu tasha wahala sabida rashin tallafinsu, a haukarsu hakan zaisa tadawo addininsu, shiyyasa suka koreta, to Ashe Na kwarai basa k'arewa, saigashi ALLAH yaymata na

sibi da samun wasu dagin masu k'aunarta.

Bata nuna musu komaiba, saima kar6arsu da nuna musu har yanzu sunada muhimmanci a rayuwarta, dan ba'a canjama tuwo suna.

Su Ama.... Sune amarori k'irjin biki.

Ahakadai taro yatashi lafiya, amarya tatare

gidan mijinta, Innani harda hawayenta Na rabuwa da Aysha, dan harga ALLAH tana k'aunar yarinyar har cikin ranta.

To shatu ALLAH yabada zaman lafiya da zuria d'ayyiba.

😻🀝🏻

************

Za6e yagudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yanda su

Uncle sukayi fata, Alhmdllh kuma ansamu biyan buk'ata daga matasan wajen za6en shugabanni Na gari masu kishin k'asar dason cigabanta.

Sannan matsan dayawa sunsami wasu fannoni Na madafun ikon k'asar , kamadaga ministers, Commissioners, da wasu fannon

i daban-daban Na muk'amai

πŸ˜πŸ‘πŸ»

.

Saimuce ALLAH yatayaku rik'o

😻

.

******* ****** *******

Yau takasance Juma'a, tunda Uncle yadawo sallar juma'a shida yara bai sake fitaba, sukayi Lunch gaba d'aya kamar yanda yazama doka yanzu agidan, duk weeke

nd tare sukecin abinci suda yaransu.

Sallar La'asar tasaka taron firar watsewa, Uncle da yara suka tafi masallaci su Aneesa kuma kowa tashige d'akinta.



Da sauri Amatullah tak'arasa gaban gadon ganin Raihana dake barci Na neman sakkowa, tat

ashi tuni, kasancewar yarinyar tanada matuk'ar hak'uri ko kuka batayiba, tagaji da wasa agadon shine tafara k'ok'arin sakkowa, ALLAH ma yakawo Ama... d'in datasha k'asa.

Dungure mata kai Ama... tayi tana fad'in "mamana dakin fad'o Aida kinjamin masifa

wajen Uncle nasan bawai zai ragamin baneba".

Kamar Raihana taji mi Ama... ke fad'a saita ta6e Baki tana niyyar yin kuka, rawa Ama... tafara mata tana rera mata wak'a kamar yanda take musu itada Rayyan idan suna rigima.

Tuni Raihana tayi shiru t

akoma 6alle Baki tana dariya, Ama..... ta sauketa tana dariyar itama, yauwa Ammi Uwa mai dad'i, zauna kiyi wasa nayi salla kafin Rayyan yatashi shima, yau inada Shiga kitchen".



Idar da sallarta babu dad'ewa tajiyo kamar ana magana sama-sama daga

babban falo, kuma tamkar muryar Aneesa.

Cire hijjab tayi ta d'auki Raihana dake wasa a k'asa tafita (dan tuni yaran sunama rarrafe).

" momyn yara lafiy......."

Maganar Ama... takatse lokacinda idonta ya sauka akan zee-zee dake zaune itada Rit

a dawasu 'yammata biyu Wanda duk Amatullah ta sansu amma ta manta sunansu.

Aneesa ta katseta da fad'in "kokin sansune Auntyn yara?".

Sosaima kuwa, aiduk school mate d'inane, ''amma lafiya kuwa Rita?".

Yatsine fuska Rita tayi tana wani

taunar cingom, a yangance ta nuna zee.

Ama.... Ta maida kallonta ga zee d'in, ''Zainab lafiya?".

Saida Zee tamata wani kallon sama da k'asa sannan tace, "maigidan nazo nema".

Fateema dake fitowa tace, " maigidan kuma? shikam Nurri miya had'

ashi da wad'annan masu kamada kilakin?".

Daga zee har muk'arabanta babu wacce ta tanka, saima taunar Cingom sukeyi, jikake k'ass! k'ass!! k'ak'as!!!.

Saida suka gama shan k'amshinsu sannan d'aya daga cikin 'yanmatan biyu tace, "Amaryarku ce tazo gai

sheku ".

Kallon juna Aneesa da Fateema da Amatullah sukayi, Aneesa sarkin rashin hak'uri tafara lailayo musu zagi.

K'in tankawa sukayi, saima cigaba da iya shegensu sukayi.

Ana haka maigidan yadawo, kallon matan nasa dasuka tsareshi da idanun t

un shigowarsa yayi, " lafiya kuma kukam?".

Aneesa Ce ta nuna masa su zee tana k'ara kumbura baki.

Gabansa yafad'i, azuciyarsa yace yarinyarnanfa ta gundureni, yanzu abin yakai harma gidana..........?

Fateema ta k'atse tunaninsa, "Nurri waisu

waye sune?".

Kallonta Uncle yayi, sannan ya kalli yaransa dake tsaye cirko-cirko suna kallon iyayensu da wad'annan bak'i dabasu san kosu wayeba.

" Abulkhairi ja k'annenka kuje tsakar gida kuyi wasa, kar Wanda yadawo sai an kirasa".

"To Abbu".



Suna fita Uncle ya kalli su Zee.

" miya kawoku gidana Zainab?".

Kanta ta sunkuyar k'asa tana wani murmushi, "nagane kusan 2weeks baka picking calls d'ina shiyyasa nace bara nazo naga lafiya".

Tsayuwarsa yagyara sosai, hannayensa zube

cikin aljihun blue d'in jallabiyarsa, ya fiddo d'aya yashafa gemunsa sannan ya maida, cikin sauke numfashi yace, " k'alau nake, kawai ayyukane sukamin yawa, ngd".

Yana gama fad'a yanufi samansa batareda yakuma kallon kowacce acikinsuba, harsu Amatullah

d'inma.



Wani mayataccen kallo zee tabishi dashi, yanda ma yake taka steps d'in benen kawai abin birgewane, harya kai k'arshe kuma bai juyo ya kallesuba.

Su Aneesa suncika sunyi FAM, shin me mijin nasu yake nufine? Budurwar tasace kenan da gas

ke?.

Ai bak'inciki hana Amatullah maganama yayi, saita juya 6angarenta kawai.

Aneesa ce tafara masifa, "to gayyar tsiya arna a idi sai a tashi abar mana gida ko, tunda bana gado baneba".

Su Rita zasuyi magana Zee ta hanasu, tamik'e tsaye tana f

ad'in " kutashi muje, karku wani damu kanku, kwana nawane nazama matar gidan nima, kowacce shegiya acikinsu saita bar gidan da k'afafunta, dan nikad'ai nakeson kasancewa da abin sona, duk d'unsu basukai matsayin Na had'a kishi da sub.......

Dukan da An

eesa takaima bakinta yasakata yin shirun dole, tadafe baki "kai kai nikika dakarma baki?"....

" andaki bakin naki, Ku kama gabanku ma kafin mu jigataku a falonnan''. Cewar Fateema.

Kwafa su Zee sukayi suka fice.

Fasifa k'awayen nata suka ha

u yi bayan sun fita, akan miyasa bata bari sun koyama matannan hankaliba.

Tace, "kubarsu, lokacinsune, daga sanda nashigo gidan babu mai sake yin tari acikinsu, kudai kusaka ido kusha kallo."

Dariya suka shek'e da ita damata jinjina.

Koda su Zee

suka fita sai Aneesa da Fateema suka nufi saman Uncle, a zaune suka iskeshi hankali kwance yana searching tasha a TV, sallamarsu kawai ya amsa batareda ya kallesuba, dan yasanma miya kawosu.

Fateema tace "wai yanzu nan Nurri wannan kuma wacece?".

Kallonta kawai yayi ya kauda kansa,

Aneesa takuma maimata masa tambaya, " Dear maganafa mukeyi! Wacece wannan kilakin?".

"To mikukeso Na fad'a muku? Nace ba abinda kuke tunanin bane, kumin kallon mayaudari, kokuwa nace sona take ni bana sonta

ku kirani mak'aryaci, inama mai baku shawarar karku tasirantar da abinda bakuda ilimi akansa a zuciyarku.

Babu wacce ta tanka masa acikinsu, sukayima ficewarsu suka barmasa falon.

Kallo kawai yabisu dashi, ya sauke ajiyar zuciya ta 6acin rai, tab

bas lokaci yayi dazai takama yarinyarnan Zainab birki akan haukarta, tunda har tsaurin idonta yakai ta kwaso k'awaye tazo masa gida wajen iyalansa, harma tadunga musu furuci mara k'yau, (dan yana jiyo duk abinda yafaru bayan barinsa wajen), iyalinsa sune m

utuncinsa, martabarsa da dukkan sirrinsa, bazai lamunci wata ko wani ya raina masa suba ko 6ata rayukansu, yayi kwafa yana jingina kansa jikin kujerar da lumshe idanu.

Yakai tsawon lokaci yana tunani awajen kafin ya sakko k'asa, babu kowa a falon, yaram

a suna tsakar gida suna wasa, ya kalli 6angaren Aneesa yaga arufe, Fateema ma a rufe, saiya nufi Na Amatullah.

Tunda Ama... tajiyo k'amshin turarensa ta ajiye Rayyan datake bama nono tashige bathroom, tanajin Rayyan d'in ya fashe da kuka amma bat

a kulaba tarufe bayin.

Da sauri Uncle ya k'araso ya d'aukeshi, jijjigashi yafraayi yana fad'in "oh my brother na, waye yasaka kuka? Ina Antyn tajene?".

Rayyan yayi shiru tareda lafewa jikin babansa, sai ajiyar zuciya, zama yay falon yana jiran f

itowarta, amma bulum, mamaki yakamashi, yatashi yalek'a bedroom d'in babu kowa, sai Raihana a kan gado data koma barci, zama yayi abakin gadon yana jiran fitowarta, nanma shiru kakeji.

Ama.... kuwa zamantama tayi a toilet d'in tana charting hankalinta k

wance, duk kuma bidirin da Uncle keyi tana jiyoshi. tashiyay yafara knocking d'in k'ofar bathroom d'in, amma shiru kakeji. mamaki yakamashi, kodaima bata d'akinne? wannan tunaninne yasakashi ficewa da Rayyan a hannu, tsakar gida yafita inda yaran ke ball,

zama yay yana kallonsu da tunanin lamarin matan nasa fal a kansa, wato dai sun had'e masa kai kenan, yay murmushi da k'arajin k'aunar matan nasa a ransa

😊

.

Kiran Sallar magriba tasakashi tasa yaran maza gaba suka tafi masallaci kamar yanda yasaba

, yabama Ummita Rayyan suka koma falo itada Siddiqa da mah-mah.

Jin sunfita masallaci Ama.... tayi sallah sannan tashiga kitchen nata, tadafa cus-cus. taimaza takai masa nasa ta sakko kafin su dawo.



Koda yadawo bai nemesuba, yaransa yat

asa gaba suka tafi falonsa, acan sukaci abinci sunata masa hirar makaranta, shikuma yabiye musu, dan yau sune abokan hirar tashi.

Saida yaga wasunsu sun fara gyangyad'i sannan yatashesu, yarakosu k'asa, kowa yashiga d'akin mamansa, shikuma yashiga 6ang

aren Ama.... domin kaimata Rayyan da shima yay barci.

Kwance ya taddata tana bama Raihana nono, wadda keta d'aga k'afa d'aya tana wasa dashi saboda dad'in shan nonon datakeji. Kallo d'aya Ama... tayi masa ta kauda kanta, guntun murmushi yayi, ya sa

uke Rayyan dake a kafad'arsa saman gadon, baimata maganaba yabud'e dirowar yaran ya d'akko kayan barcin Rayyan ya fara saka masa, sai lokacin idon Raihana yakai Kansa, sakin nonon tayi da sauri ta rarrafo wajensa tana murnar ganinsa (yanda Uncle yake tatta

lin yaransa da yawan d'aukarsu yasa sukayi mugun sabo dashi, zakiga duk k'iwar da yaronsa zaiyi dawuya shi yayi masa), d'aukarta yayi yafara cillata sama tana dariya shima yanayi, sai Rayyan kuma yasaka kuka shima a d'aukesa. dariya Uncle yayi tareda zama

yajawoshi jikinsa shima yana fad'in "jealous ko my Sweetheart".

Amatullah dai duk tana jinsu amma tayi kamarma batasan sunayiba, shirin barcinta kawai tayi tazo gefen gadon ta kwanta.

Shima shareta yayi, saida yaga ya lalla6a yaransa sunyi barci s

annan yatashi ya fice.

Mintuna k'alilan yadawo bayan ya shishshiga sashen su Aneesa yayima yara addu'a yafito bai kula kowaccensuba. Shi dariyama suke bashi wlhy.

Idon Ama.... biyu, tanajin sanda ya shigo harya kashe fitilar d'akin ya hawo gadon.

6oyayyar Ajiyar zuciya tasaki, shikam yayi tashi a fili yana fad'in " I miss you my heartbest".

Shiru tamasa.

Acikin kunnenta yace, "wai duk kishinne ginbiyata? kinsan ko matan duniya sun k'are babu abinda zanyi da yarinyar can, yakamata Ku she

deni aii, amma keda 'yan Uwanki kun had'e min kai kunata fushi dani".

"Fushinmi zamuyi dakai, namu ALLAH ya sanya alkairine aii, miye namu danzakayi amarya".

Sassanyan Murmushi yayi yana shafa kanta, ganin kalaman baki bazasu mataba yakoma sal

on dazata fahimcesa. (

πŸƒ

‍♀nayi nan).

Bayan wani d'an lokaci Na koma, saina taras Uncle Na lallashin Ama... dake kuka, yabata labarin tundaga farkon had'uwarsa da Zainab (zee) har zuwa yanzun, yak'are damata kalaman kwantar da hankali da lallashi,

ya tabbatar mata itace autar mata a gidansa har Abadan insha ALLAH. cikin dai hikimarsa ya shawo kanta harta yarda dashi da bashi hak'uri.

Yay dariya da kuma rungumeta yana mata daddad'an kalamai.

Hakama Aneesa saida yakoma d'akinta ya lallashi

abinsa, damata bayani dallah-dallah akan zee kamar yanda yayma Ama...., itama Fateema hakan yamata, duk suka gamsu da komawa tattalin mijinsu tamkar da, amma saida suka saci number zee a wayar Uncle suka had'a kai su uku bayan sun kirata sun saka Hans Free

suka mata tatas da gargad'i mai zafi akan mijinsu.

Hakanne yasaka zee kiransa tana kuka dafad'a masa abinda matansa sukai mata, yana k'ayataccen murmushi yana saurararenta, saida takai k'arshe sannan yay k'aramar dariya yana gyara zama a kujera (daya

ke a kasuwa yake).

Cikin sasaanyar muryarsa dake kashe ga6o6in Zee

😜

yace

"To kinga ai saikiji gargad'insu kifita hanyar mijinsu, nidai babu ruwana, tuni na sanar dake banida burin k'ara aure, matana sun isheni, dan haka kisama zuciyarki salama

ki sami miji kiyi aurenki, nabarki lafiya inakuma baki shawarar karkiyi gigin sake zuwa gidana, Dan babu ruwana idan matana suka miki wani Abu, nid'in mijin hajiyoyine

πŸ˜†

, ALLAH yabamu alkairi.

😝



Tundaga wannan ranar zee tafita harkar Uncle, bata sake

kiransaba balle turo masa messenges.

Haka kuma rayuwar tacigaba da turawa.

3years later

😜🀣

ALLAH mai girma da d'aukaka, yau gasu Ama... ana bikin yayesu amatsayin manyan likitoci kwararru, bakunansu sunkasa rufuwa saboda tsabar fari

n ciki, hakama Na danginsu wad'ada sukayi tururuwa halattar taron.

Ciki hardasu Uncle da matansa duka, Anty maijiddah Nazeefa zaliha Asiya su aunty Firera da mazansu su kawu Hafizu, matansu Alhaji Sabi'u da dangin su Fa'iza, harda dangin Su Aysha (go

odness) wad'anda ayanzu sun sakko suna ziyarar 'Yar uwarsu itama tana ziyaryarsu, harda d'anta Muhammad (Wanda taima Uncle takwara

πŸ˜„

) suna kiransa Yaseer.

Angudanar da taro cikin sha'awa da birgewa, tareda kar6ar k'yaututtuka dasu Ama.... suka samu, Un

cle jiyake tamkar ya had'iyeta saboda dad'i da k'ara sonta, Dan har yanzu Ama.... tana cikin k'uruciyarta, yanzunema take kuma kilewa tana zama hamshak'iyar mace, ga 'yan yaranta su Rayyan abin sha'awa, sunyi girma sosai da wayo, har sun shiga school tuni,

tundagasu kuma bata sakeba, koda yake Fateema ma da Aneesa shiru, tundaga Abubakar Aneesa ma bata sakeba, hakama Fateema tunga mah-mah.

Sunsha hotuna tamkar babu gobe, harda Innani da gwaggo Rakiya wadda su shehu suka matsa tilas sukazo suma, Nazeefa

da Zaliha da Asiya ma duksun sake haihuwa tuni.

Tarodai yatashi lafiya cikin farinciki da annashuwa, kowa yakama gabansa.

Su Uncle suka nufi gida inda acanma Uncle yahad'a liyafar cin abinci saboda farantama Amatullah rai, anci ansha an gyatse kuw

a, lamarin sai sambarka.

*_Kishi kumallon mata

🀣

_*

Tunda su Fateema sukaga Amatullah tafara aiki sukayi tsalle suka dire akan suma aiki zasuyi, kowacce ta kakka6o takardunta daga k'asan jaka.

Uncle yay dariya sosai sannan ya had'e fu

ska.

"Amma lallai bakuda hankali, ai kuda aiki saidai Na gidana, idan kun manta bara Na tuna muku to, alokacin dana aureku babu wacce ta shekara a gidana Na tuntu6eku akan kozakuyi aiki?, ince kowaccenku nunamin tayi batada ra'ayi, Ku kulawa dani kawa

i kukasa agaba, ban gajiyaba nakuma muku hannunka mai sanda akan Sana'a, nannama kukayi kunnen uwar shegu dani, saikuma yanzu dan kunga Khadeeja kuma kuce saikunyi? to idanfa ba 6acin rai kuke nemarwa gidanmu ba kuma ajiye wannan maganar mucigaba da rayuwa

rmu, itama data nuna batason aikin ko karatun bazan bartaba, amma tun farko ta tabbatarmin hakanne burinta, shiyyasa nabata goyon baya wajen cikarsa, Ku kama kanku, mud'in ba yara baneba balle kuce, yanzu inada k'aton saurayin yaro dake shirin kammala Seco

ndary, banason shashanci, dan haka kutashi ku bani waje".

Haka suka tashi kowacce ranta a jagule da Dana Sanin k'in amincewarsu tun farko, dayanzu suma sunzama manyan hajiyoyi da ake damawa dasu, amma sukaima Kansu sakkiyar da babu ruwa, gashinan suna

zaune Ama... tafara karatu harta mammala tazama hamshak'iyar likita abin alfahari ga mata

πŸ˜†πŸ˜œ

.

Bayan kwana biyu suka bashi hak'uri ganin yanata faman fushi dasu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login