Showing 57001 words to 60000 words out of 111738 words

Chapter 20 - Siyasa-ko-kabilanci-complete

08 Sep 2026

26

dama ai bawai batasan kanta bane, kawai kunyar Uncle da kallon uba datake masane yasata komawa gefe, amma yanzu shawarwarin Fa'iza sun maidota hanya d'od'ar, kuma zatayi amfani dasu.

" hummm, su Amatallah anji jiki Anfara dawowa hanya

🀣

, haka masoyanki sukeson ganinki, musamman ma Tawan (miss Xoxo)

πŸ˜‚πŸ‘πŸ»

___________________________

Sanda Amatallah ta dawo gidan ta tarar Uncle bayanan yafita, Fateema kawai ta tarar a falo za

une, yarama suna Islamiyya.

Sannu da zuwa Fateema tamata, ta amsa cikin fara'a tana mata barka da gida.

Jin maganganinsu ne yasaka Aneesa dake kitchen lek'owa a zatonta Uncle ne ya dawo, dukda cike take da haushin abinda yamata da safe, dan tana ci

ki har yayi break fast yay wanka yafice bai nemetaba, har yanzu kuma bai dawoba, amma dukda hakan tafitone yanzun tarbarsa danta bama Fateema haushi, sai kuma taga Ashe Amatallah ce.

Daga Fateema har Amatallah kallonta sukayi, Amatallah ta d'auke ido

nta tareda mik'ewa ta kwashi takardunta, saida taje k'ofar 6angarenta sanan tace Anty Aneesa sannu da girki fa". bata jira amsartaba tashige abinta.

Ba Aneesa ba kawai harta da Fateema saida ta kalli Amatallah d'in, dan awani salo daban tayi maganar, k

uma cikin sanyinta kamar yanda ta saba, inma Baka saniba bazaka ta6a cewa itace tayi maganar ba.

Fateema tayi dariya a zuciyarta tana fad'in yanzun za'a fara wasan kenan.

Aneesa kam wani k'ududun bak'in cikine ya tokare mata mak'oshi, tama rasa

yanda zata fasaara rainin hankalin Amatallah d'in.

Koda Amatallah ta shiga d'akinta alwala tafarayi tai salla, danta risketa tana hanya ne.

Ko da ta idar bata nemi abinciba, chin-chin d'in dasuka saya a makaranta taci tasha ruwa, sannan tashiga w

anka, tadad'e a toilet d'in kafin ta fito, data fito batayi kwalliyaba, d'akinta tasama key dan bata buk'atar ko Uncle ya dawo ya shigo mata yanzun.

Game taita bugawa a waya abinta har saida aka kira sallar Magrib, tana jiyo hayaniyar dawowar yara tu

n 6pm, amma dai bataji alamar Uncle ya dawoba, hakan yamata dad'i kuwa.

Alwalar magrib tayo tazo tayi salla, tsakanin magrib da isha'i tayi karatun alkur'ani da azkar d'in yamma, daga nan gaban mirror takoma ta zauna, tanutsu wajen yin simple makeup,

takuwayi k'yau d'as. Wasu Pakistan ta saka, rigar sky blue ce, wandon kuma na jins dark blue tayi k'yau sosai, ta taje kamta takuma gyarawa, dama batayi kitsoba, dukda gashinma bawani na kirki baneba, tamkar na (Fatee d'ayyabu Tyw

😜

) d'an siririn gyalenta

shima sky blue tasaka, inba kallon Tsaf kamataba bazaka ta6a d'auka kwalliya tayiba, komai Simple tayishi, sai masifaffen k'amshi datake ta zubawa, wanda sirrin Anty maijiddane da k'awarta mai gyaran jiki

πŸ˜‰

.

Uncle kam yanacan wajen Alhaji Sabi'

u m Ali suna tsare-tsarenasu, saida sukayi sallar isha'i sannan yabaro gidansa, daga nan gidansu yaje, bai wani zaunaba suka gaisa a tsaitsaye saboda yaje da safe daya fita kafin yaje gidan Alhaji Sabi'u, daga nan gidansa ya zarto.

Horn yayi kusan s

au 3 sanan su Abulkhairi suka jiyoshi, da gudu suka fito suka bud'e masa ya shigo.

Hayaniyarsu Ce ta fiddo Aneesa, cikin kwalliya take kuwa kamar ka saceta ka gudu, tanata k'amshi abinta. fitowarta tayi dai-dai ta fitowar Uncle daga mota.

Yaransa duk

suka rungumeshi, tarbarsu yayi cikin jin dad'i, yabisu d'ai-d'ai yana sumbatar kumatunsu, suma duk suka sumbaci nashi.

Aneesa dake tsaye gefe yayi kamar bai gantaba saita kuma cika fam, amma dukda haka ta danne fushinta tamasa sannu da zuwa.

Kal

lonta yayi ya sakar mata murmushin dake kasheta.

Babu shiri itama tayi murmushin, Siddiqa dake hannunta ya kar6a, tafara masa gwarancinta yana dariya shida sauran yaran, ahaka suka k'araso babban falon.

kujera ya nuna musu yace su zauna nan su ji

rasa yadawo, ya zaunar da Siddiqa itama, Aneesa na tsaye yawuceta ya shiga 6angaren Fateema.

A falo ya isketa zaune tayi rashe-rashe da k'afafu ta bud'ema kanta fanka, fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso gareta.

"O my tee... Irin wanan bajew

a haka? halan babynane yasaki jin zafi?".

"Kabari kawai wlhy Nurri zufa nakeji sosai kamar nayi wanka a ruwa".

Kusada ita ya zauna, yad'an rungumeta jikinsa yana manna mata kisses a wuya da la66anta, " my tee hakan ya nunamin babyna yakusa zu

wa duniya, ai da kin fara zufarnan nasan haihuwarki ta gabato, ALLAH ya saukeminke lafiya Uwargidana".

"Amin Nurrina". Itama ta sumbaci kuncinsa".

" thanks my tee".

Murmushi tayi batace komaiba.

''Yauwa my tee bara naga Amatallah itam

a naje nayi wanka, yau ina son zama daku Ku duka".

" okey boss sai munji kira".

Rankwashi yad'an kaimata, tunkan hannunsa ya sauka a kanta ta tare tana fad'in "wayyo Nurrina sorry please".

Dariya yayi batareda ya rankwashe tanba, yace, " mats

oraciya kawai, ga tsoro gajan fad'a".

Dariya tayi, shima yafita yana dariyar dajin k'arin k'aunarta har k'asan ransa.

Tunkan ya fito Aneesa tajiyo dariyarsa, da sauri tashige 6angarenta zuciyarta na suya.

Koda tafito saiya Nufi 6angaren Amatall

ah............✍

🏻

πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»

One luv my sweet Fan's

πŸ₯°

*_Ya Rabbi ka kai rahama da gafara kabarin iyayenmu_*

πŸ˜­πŸ™πŸ»

[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍

🏻

_*

*_HASKE WRITER'S ASSO..._*

πŸ’‘

_{home of expert and perfect writer's}_

*_

SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉

_(Hattara matasa)_

*_Bilyn Abdull ce

πŸ€™πŸ»

_*

Comments naku na k'yatar dani ainun.

*_Ummu Ameer, Nana yakaku, maman khalifa, Ummu Ramlat, Layla, Xeecul, mom yasna, m@imun@tu, Maman iman, Jamila fika

_*

_

😨

ALLAH ya albarkaceku da yawafa, aradu kozan cika page d'inan bani gama zanoku, ko 'yan group d'ina kad'ai sa cikashi.

πŸ₯°

inayinku irin Trillion's d'innan wlhy, ALLAH yabar k'auna.

πŸ₯°πŸ₯°

❀

πŸ’ƒπŸ»πŸ‘πŸ»

._

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

Aneesa ma fa akwai farin blood

*_Ma

imuna ado, and xaujatu_*

basa barin a ta6a musu ita

πŸ˜„πŸ’ƒπŸ»πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°

❀

ina yinku kuma

πŸ‘πŸ»

.

____________________

*_Number 22_*

____________________



Kamar yanda yasaba da asubahi yabisu duk ya tada kowacce dantayi salla, yatasa yaransa gaba

suka tafi masallaci.

Koda suka dawo saiya haye samansa yay kwanciyarsa.

Aneesa ma da barcin ta koma abinta, komi tagani kuma saita tashi tafita kitchen had'a break fast. tafara babu dad'ewa Amatallah ta shigo kitchen d'in itama, kallon juna su

kayi, Amatallah tace, "ina kwana Anty".

Cikeda yanga Aneesa ta amsa mata.

Amatallah bataji komai a rantaba, dan har zuwa yanzun bata gama Sanin ma'anar kishinba, tarayu gidansu Amminta ita kad'aice, shiyyasa bata ta6ajin zafi ko haushin wani Abu

da Aneesar keyiba, tanama d'aukar hakan kawai a tunanin halin Aneesar ne.

Kauda tunaninta tayi gefe, tai murmushi da matsawa kusada Aneesa tana fad'in " Anty mizan tayaki dashine?".

Yanzunma a d'age Aneesa tad'an kalli Amatallah, saikuma ta

cigaba da abinda takeyi, "no kije abinki, sonake yau na had'ama my Dear special breakfast da kaina, kodan na nuna masa godiyata na dad'in daya jiyar dani jiya, ai ba ayi mai miji da banba mai girki daban kingani ".

Dukda Amatallah taji duk maganar

Aneesa tsaf, sai dai bata iya fassara magana ko d'aya ba a ciki, amma ta fahimci maganace cikin magana tamata. d'an murmushi kawai tamata tace, " OK bara naje to nayi shirin school, dama inada lectures d'in safe". bata jira amsar Aneesa ba tafice abinta.



Aneesa taraka bayan Amatallah da harara tana ta6e baki.

Nidai nace, " hummmm".

*********

A 6angaren Fateema tunda maigidan ya tadasu da asuba taga Saifuddin a d'akinta saitaji wani haushi, wato ita Dan an raina mata hankali shine aka d'ak

ko yaro aka kawo mata dansu su samu su warwasa yanda sukeso. To aii idanma gaskiyane yau d'akin Amatallah yakamata ya kwana ko, kenan Aneesa tayi wani makircin?, ai ko sai tayi mata abinda zata bak'anta ranta yau d'innan basai gobeba.

Tayi wata 'Yar da

riyar mugunta.

Tofa Uwargida ran gida, mikike k'ullama Aneesar kuma?.

πŸ˜†

**********

Tunda Amatallah tabar kitchen d'in takasa manta maganganun Aneesa, datayi k'ok'arin mantawa sai maganar tadawo mata a rai, sai takejin wani gefen zuciyarta yanajin kama

r d'acin maganar, haka tagama shiryawa sukuku.

Tayi k'yau cikin zani da riga Na shadda oxblood color, zani Rafa sket, saiya fita tamkar sket d'in, hakama rigar Tamata d'as, batawani yi kwalliyaba, fauda kawai ta shafa da kwalli sai lipstick data sa

ka, d'an kwalinma normal d'auri tayi, tana tsaka da kimtsa abinda zata buk'ata a handbag yay sallama.

Amsawa tayi a sanyaye, sannan ta rissina ta gaidashi.

Tsura mata idanu yayi ganin yanda takeyi komai a sanyaye, tamkar mai tunanin wani abu.

"Khadeeja!".

Yakira sunanta yana zama kan stool d'in madubinta datayi shafa.

Kanta a k'asa tace, "Na'am Uncle".

" bakida lafiyane?".

Yanzunkam sai da ta kallesa, idonta yad'an Tara kwalla, saboda haka kawai maganar Aneesa har yanzu

cin zuciyarta takeyi, tanason tasan ma'anar maganar, Dan yanayin da Aneesa Tamata maganar kawai ya tabbatar mata bamai dad'i baceba.........

"Khadeeja!". Yakuma kiranta dad'an k'arfi Dan ganin tatafi wani tunanin, hakan kuma ya tabbatar masa akwai a

binda ke damunta d'in.

Da Sauri tace, " na'am Uncle, INA jinka".

"Kina jina ko kina tunani dai my best, kinga please fad'amin damuwarki, karki 6oyemin khadeeja, yanzu nine Brother, nine Ammi, nine Uncle, kuma nine Miji, duk abinda yadameki

nizaki tunkara Na share hawayenki kona kare mutuncinki nakuma kwato miki hak'k'inki kinaji ko".

Kanta ta jinjina masa tana had'iye kukan dayazo mata.

"Yauwa my Best! to fad'amin kinji, ki d'auka yanzu Nid'in Ammice, nasan dai bazaki iya 6oye

mata damuwar kiba ko?".

Muryarta Na rawa tace, " ALLAH babu komai Uncle".

"Khadeeja ban yardaba, Bahaka muka rabuba jiya da daddare". yayi maganar yana tasowa zuwa gareta.

Handout d'in hannunta da bag d'in ya amsa ya ajiye akan gadon,

ya d'ora hannayensa duk biyu a kafad'arta, idonsa Na kallon fuskarta.

Ita kuma ta duk'ar da idonta tana kallon k'afarsa.

Cikin sassanyar muryarsa wadda takuma komawa slowly yace, " waye ya 6ata miki rai a gidanan? Fateema!".

Ta girgiza kan

ta.

Yace, "Aneesa!".

Shiru tayi.

Hakanne yasashi fahimtar Aneesa Ce.

Iskar bakinsa ya furzar sannan yakuma cewa ''Aneesa Ce ko? mita miki?".

Hawayen datake mak'alewa ne suka zubo a kumatunta, murya Na rawa tace "babu abinda fa tamin Uncl

e, kawai naje tayata girkine tace nabarsa zatayi, shine naji babu dad'i, gani nake ko wani Abu namatane, tunda kaga da bakanan kullum tare mukeyi da Anty Nazeefa , wani lokacin kuma da ita Anty Aneesar, shiyyasa yanzu datace Na barsa sainakejin babu dad'i

kamar wani laifi namata".

Iska Yakuma furzowa a bakinsa, kafin yamatso da ita jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar lallashi. Sunkai kusan Minti 3 a haka sannan ya d'agota, hannunsa yasa ya goge mata hawayen kafin yakai bakinsa ya sumbaci go

shinta. " ki daina damun kanji Indai akan hakanne kinji my heartbeat, badan kin mata laifi bane, kawai inaga Dan taga zakije school ne, amma zan mata magana, daga yau karki kuma zubarmin da hawayennan masu tsada akan wata a gidannan, kema matar gidace kama

r kowaccensu, zankuma tabbatar musu da hakan kinji ko?".

Kanta ta d'aga masa alamar to.

Yace, ''yauwa my babyna, yimin murmushi mana konaji sanyi". 'Yay maganar yanajan kumatunta'.

Hakanne yasata sakin murmushi mai k'ayatarwa.

Sumbatar

goshinta da kumatunta yakumayi yana fad'in "yauwa kokefa my best".

Kunya dukta kama Amatallah itadai.

" kinada lectures d'in safene?".

"Eh Uncle".

" Okay, to k'arasa shirin ki sameni a falo mutafi, idan Na ajiye yara a School saina k'arasa

dake".

Kanta ta d'aga masa alamar to. shikuma ya juya yafita.

Afalo ya iske yara angama shiryasu, zama yayi duk suka zauna kusada shi suna gaidashi, ya amsa yana sumbatarsu d'ai-d'ai a kumatu.

Babu dad'ewa Fateema tafito cikin kwalliya,

(a raina nace Uwargida kina fama da kankinma bazaki hutaba

🀭

).

Tunda ta fito idon Alhaji Muhammad Na a kanta, sai murmushi suke sakarma juna, mik'ewa yayi ya taimaka mata ta zauna, yanason yad'an sumbaceta amma ga yara, Dan haka yamata magana rad'a-ra

d'a, "sorry my tee.. My children's na kallonmu".

Murmushi tamasa, Dan tasan miyake nufi, yanason sumbatarta ga yara, tasan bazai iyaba.

Gaidashi tayi da tsokanarsa ango kasha k'amshi, duk angwancinne yasa aka manta damune?".

Wata 'yar dariya y

ayi, yakuma k'asa da murya Dan kar yara su jisu, " my tee... Nazama abin tsokana kuma? ai na shiga kina wanka, su Abulkhairi basu sanar miki bane?".

Itama dariyar tayi, tace, "wasa nakeni Nurrina, ya gajiyar hanya".

"Alhmdllh my tee.., ammafa

akwai, gashi yau dolene nad'anyi wasu yawo wlhy a cikin gari".

" amma dai daka hak'ura kad'an huta yinin yau a gida, zuwa gobe saikayi duk abinda kakeso".

"Ai fitar tanada muhimmanci my tee..., Alhaji Sabi'u a matse yake dason ganina, ni

ma kuma dai hankalina na kansa, za6e yakuma gabatomu gab, dolene muyi wani motsi da gaggawa kinga".

Kallonsa take cikeda so da k'auna, jin mijinsu take harcan k'asan ranta saboda k'yawawan halayensa...

Ahaka Aneesa tafito daga 6angarenta ci

kin kwalliya ta samesu. ganin yanda suke kallon junansu sai kishi ya kamata, harara ta balla musu.

Sarai Fateema ta ganta, amma shi bai gantaba saboda yabata baya kad'an.

Dariya Fateema tayi a ranta, da fad'in bakiga komaiba 'yan mata, saima anjima

ma kin shiga tarkon dazan d'ana miki.

Fitowar Amatallah yasaka Fateema janye idonta daga kansa, ta maida kan Amatallah tana murmushi, " Amatallah kin tashi?". tafad'a cikeda fara'a.

Itama Amatallah d'in murmushin tayi, kafin tabata amsa yaran

duka sukayo kanta suna fad'in "Antynmu ina kwana!". Kowa na 'Yar rige-rigen fad'a da shigewa jikinta.

Duk had'asu tayi ta rungume, ta amsa musu da tambayar sun tashi lafiya?.

A tare sukace " lafiya lau antynmu".

Daga Uncle har Fateema kallon

su suke suna murmushi, zuciyoyinsu najin dad'in yanda Amatallah keson 'ya'yansu, (masu iya magana kance mai d'a wawa) wannan yasaka Fateema kanji sassaucin kishin Amatallah tunkan ta tafi Dubai,, dan duk wada yaga yanda Amatallah kema yaran yasan har zuci

yartane.

Guntun tsaki Aneesa tayi tashige kitchen. tana jiyo yanda Amatallah ke gaida Fateema cikin girmamawa, itakuma Fateeman tana amsawa tamkar da biyu. jitai duk tak'ara tsanarsu suduka.

Uncle kam dad'ine sosai yakuma kamashi, Dan ganin yanda

Fateema take bama Amatallah kulawa, sai yaji takuma girma da kima a idonsa.

Yarane kawai sukayi break fast d'in, Amatallah ma tea kawai tasha, danji tayi bazata iya cim ko lauma d'aya daga abinda Aneesa ta girkaba, saitaji ma'anar maganganunta

sannan.

Uncle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login