Showing 54001 words to 57000 words out of 96103 words

Chapter 19 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

64

rage ba?."

Ya kalli mahaifin nasa ya ce, "Abba ai ba laifi bane dan na bari."

"Na san babu laifi Rehaan, sunnah ce ta annabin mu. Amma ita baza ta gani ba."

Ya Wan lumshe ido ya buWe bai ce komai ba, yana mamakin wannan ?arfa-?arfar da Daada take yi masa.

Abba ya ce, "ka yi sallar i'sha?."

Ya Waga kai alamun eh. Abba ya ce, "mu je wajan Daada, ta ce na tattaro kowa, kuma ka san saboda kai zata haWa taron."

Ya kalle sa a sanyaye ya ce, "bani da lafiya Abba."

"Yi ha?uri mu je Win."

A hankali ya mi?e suka fita shiga mahaifinsa zuwa wajan Daada kamar yadda ta ce.

Kusan kowa na gidan yana falon, kasancewar falo ne mai girma sosai, ya Wauke kowa da kowa harda space.

Abba ya shiga Rehaan yana bayansa ya nemi waje can nesa ya zauna, inda ya saba zama inda za a yi meeting yana ?asar, a nan ya zauna ya kawar da kai baya kallon kowa. Kowa ya san haka yake yi, zai yi shiru bazai yi magana ba, sai wani lokacin in abin maganar ya tashi zai ce.

Daada ta bi sa da harara ta ce, "Ka fi ?arfin ka ce min ina yini ko Muhammad?."

Rehaan yana ji ya san dashi take, dan itace mai ce masa Muhammad. A faWar ta baza ta ce Rehaan ba, sunan indiyawa ne. Amma wani lokacin tana faWa, tunda yau da gobe sai Allah.

Ya Wago jajayen idanunsa saboda azabar ciwo, cikin muryarsa mai sanyi da daWin saurare ya ce, "na zo bakya nan. Ina yini?."

"Ka ri?e gaisuwar ka bana bu?ata, tunda ba ta ?asar india bace dole ka ?i gaishe ni."

Ta kalli Abb ta ce, "An samo yarinyar?."

Abba ya ce, "wallahi ba a gansu ba Daada."

"Yarinya ta yi min wannan alkhairin kuma na bari ta fita ba tare da na saka mata ba. Gaskiya ban kyauta ba, amma duk inda take zan nemo ta, zan yi mata tukwici mai girma."

Babu wanda ya amsa mata, ta bi Rehaan da kallo ta ce, "kalli wani gashi a kanka kamar wani kafiri, baza ka taSa ganin muslimi ya ajjige dogon gashi haka ba sai kafurai. Kuma iyayenka suna gani suka zuba maka ido, kai ga Wan gayu mai kuWi, kuma Wan ?asar waje."

Shi dai bai ce mata komai ba ya yi mata shiru yana jinyar kansa.

Ta buga ?wafa ta ce, "Yauwa, bazan lamunci yawan barin ?asar nan da ka ke yi ba Muhammad, ?ananun jikokin gidan nan wasu basu san ka ba saboda baka zama. Kai likita ne, kuma kana da babban asibiti a nan, ka dawo ka cigaba da harkokinka a nan, kasuwancin ma duk k tattaro ka dawo nan, dan baza ka sake komawa ba. Aure zan yi maka, ka tare na ga jikoki."

Sai a lokacin ya Wago ya kalle ta, suka haWa ido jin tana batun aure.

Daada ta buWe idanunta ganin yana kallon ta ta ce, "Eh aure! Ko ban isa bane?."

Ya Wan Wauke kansa daga kanta ya kalli Mamy da kanta yake ?asa, ya kalli Abba da yake kallonsa sai ya sake kallon ta ya ce, "Daada na ce miki ina son aure ne?."


"Sai ka faWa min kana so? Yadda ka ke cuWanya da fararen fata ko ba a faWa ba kowa ya san kana son aure. Za a yi maka aure kafin ka jawo mana abin kunya. Dan haka za a haWa aurenku dasu Juwairiyya, kowa ya huta."

Ya girgiza kai ya ce, "bani da bu?ata, in lokacin yin ya yi zanyi."

"Wallahi sai ka yi, indai har na isa da ubanka to na isa da kai, dole ka auri wacce na zaSa maka."

Ya Wan sauke numfashi? ya ce, "Okay zan yi, a jira in kawo wacce nake so in aura."

Ta harare sa ta ce, "baka isa ba, wannan yarinyar da nake magana a kanta ita zaka aura, tukwicin taimakona da ta yi aurenka zan bata. Ta yi min Wari bisa Wari, jinin fulani ce gaba da baya, mai tarbiyya da kyau, ga za?in murya ta ?arasa faWa tana murmushi tunawa da muryar Islaha.

Ya Wan sake kallon ta, kallon ?asan ido ya yi mata ya ce, "ke ce ni?."

Ta nuna Abba ta ce, "ni ce ubanka, mara kunyar yaro fitsararre. Kana so ka nuna min ban isa da kai ba kenan ko?."

Ya Wan dafe kansa ya yi shiru kawai bai ce komai ba, sai da ta gama faWanta sannan ya ce, "ban ga dalilin da zai saka ace za a yi min aure yanzu ba, kuma auren ma da wacce ban santa ba."

Daada ta fusata ta ce, "Ni ka ke mayarwa da magana, Ina faWa kana faWa?..."

Ta girgiza kai cikin takaici ta kalli ta ce, "AbdulAziz ka ga abinda ka Wauko mana ko? Ka ga abinda ka kawo mana har cikin gida ko?. In ban da shi waye a gidan nan faWa yana faWa? da yake shi ruwa biyu ne, ba cikakken batulatani ba, ina faWa yana cewa bazai yi b.

Abba bai yi magana ba, dan bai san ya zai yi da rigimarta ba, shi kansa ya san ba daidai take yi ba. Haka kawai ta ce zata yi masa aure, kaf samarin da suka yi aure babu wanda ta zaSawa mata, kowa da kansa yake nemo mata ya kawo kuma a amince. Haka kawai shi ta ce ita zata zaSar masa, ai hakan ba adalci bane.

"Ko da yake ta ya za ka yi kunya? Ta ya ya zaka san kunya bayan ba nonon bafulatana ka sha ba?. Sauran yaran da suka sha nonon fulani ai ba zasu aikata abinda ka yi ba, duk abinda nace shi suke yi saboda jinin fulani ne."

"Kalle ni Muhammad, na rantse da Allah in ka ga ba a yi auren nan ba, to yarinyar ce bata amince ba."

Ya buWe baki zai yi magana suka haWa ido da Abba ya yi masa alama da ya yi shiru, ya sauke ido ?asa, amma yana so ya faWa mata shima indai har anyi auren to tabbas sai dai wani bashi ba, dan zai iya amincewa da komai amma ban da auren wacce bai santa ba, kuma baya so. Mamy ce kaWai zata yi masa haka ya amince, in Mamy ce zai yarda ayi auren kuma a zauna lafiya. Amma Daada kam bata isa ba.

Daada ta ce, "gwara ka ji da kyau, zan saka a nemo min ita a Waura auren ko baka so, sai dai in aka aura maka ita ka sake ta."

?asa-?asa ya ce, "ashe akwai mafita."

Bai san Daada ta ji ba, sai da ya ji ta rafka salati taba tafa hannaye, sai kuma ta fashe da kukan da ya saka Abba ?arasa kusa da ita.

Daada ta ce, "Kaga abinda ka jawo mana ko? Ka ga irin da ka je ka auro mana daga wata ?asar ko?. Kamar ni ina magana yaron nan yana magana, Ina cewa a yi yana cewa baza a yi ba?. Kaf gidan nan babu wanda na taSa saka abu ya tsallake ko ya musa min, amma shi ina faWa yana faWa, da yake idonsa ya buWe ko?."

Abba ya ?arasa ya ce, "ki yi ha?uri Daada, ki daina kuka."

Bata daina kukan ba ta ce, "babu wanda na taSa cewa ya yi yace bazai yi ba, amma shi na saka shi ya ce bazai yi ba."

"Shima zai yi duk abinda ki ke so, bazai sake yi miki musu ba. Tunda auren ki ke so ya yi dole zai yi, duk wacce ki ka zaSa masa ita zai aura ya zauna da ita a matsayin matarsa."

Abba ya kalli Rehaan da ya sunkuyar da kansa ya ce, "Rehaan faWa mata zaka yi abinda ta ke so, ka faWa mata zaka auri duk wacce ka ke so."

Ya Wan Wago idonsa ya kalli Abban, kansa yana juyawa sosai, ya Wan sauke numfashi kaWan ya ce, "Amma Abba...." Abb ya dakatar dashi ya ce, "Yi min shiru, ka amsa abinda nace kawai Rehaan."

Ya Wan cize bakinsa cike da takaici, ta ya zai yi abinda bazai iya ba? Ta ya zai amince da auren da ba ya so? Ta ya ake tunanin zai amince da wannan auren da ba Mamy ce ta zaSa masa ba?.

Abba ya bi sa da kallo ganin ya yi shiru bai ce komai ba.

Daada ta sake fashewa da kuka ta ce, "ya raina ni ya raina ubansa, babansa yana yi masa magana ya share shi kamar bai ji ba. Daman an ce matasan masu kuWi basa jin maganar iyayensu, ga yaro ?arami Wan mitsisi ya raina babansa."

Abba ya ce, "Rehaan!."

Slowly Rehaan ya ce, "zan yi."

Abba ya ce, "kin ji abinda ya ce, zai yi duk abinda ki ke so."

Ta share hawayenta, daman na rigima ne ba na wani abu ba, daman so take kawai ya amsa ta ce, "ina so a haWa aurensa da na Juwairiyya."

"An gama."

"Ina so ka nemo min gidansu Ishlaya a ko ina take, ko da an yi mata miji ka bi duk yadda zaka yi a warware auren a aura mata shi. Ta shiga raina sosai, kyakykyawa ce jinin fulani, mai kirki da tarbiyya. Ita nake so ya aura, ko dan saboda ta koya masa kaWan daga cikin tarbiyyar fulani, wacce ba a koya masa da yana yaro ba. An bar shi cikin turawa, ana koya masa yaren matsafa."

Abba da ya ke ya san rigimar kayyasa sai ya ce, "shikenan, in sha Allah za a yi duk abinda ki ka ce."

Daada ta ce, "hakan shine kwanciyar hankalina, akasin hakan kuma an nuna min ban isa ba, an nuna min ni Win ba kowa ba ce a gare ku."

Abba ya ce, "za a yi in Allah ya yarda, ki kwantar da hankalin ki Daada."

Daada ta kalli Mama ta ce, "Batun nemo masa mata da nace ki yi na soke, na samo yarinya daidai dashi."

Mama cike da ba?in ciki da takaici ta ce, "Shikenan Hajiya" ta faWa tana kawar da kai gefe, domin wallahi bazata bar auren nan ya yu ba, yadda ta ce mai tarbiyya da hankali ita akasin hakan take so ya aura, sai ta san yadda ta yi ta kifar da batun auren ko ta wanne hali.

Daada ta ce, "kowa ya tashi ya bani waje, saura na ji wata magana ta sake Sullowa."

Rehaan ne ya fara mi?ewa yana yamutsa fuska saboda ciwon kai.

Yana jinta tana magana akan gashin kansa ko kallonta bai yi ba ya yi ficewarsa, yana aiyyana ko ta wanne hali bazai auri yarinyar ba, sai dai duk abinda za a yi ayi. Ya ga ji da jure abubuwan da baya so a gidan, a wannan lokacin sai dai ran kowa ya Saci, amma bazai yi aure ba. In kuwa ya yi auren, sai dai in Mamy ta zaSa masa ita.


Topa, ya abin yake ne? Saheer ne ko Rehaan?.


Nana Haleema
'

*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ? ? ?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 015.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

       -

Daada ta bisa shi da harara ta ce, "Wan laSuSu mai zubin mata kawai."

A lokacin Mamy ta mi?e zata fita daga falon bata kalli Daada ba.

Daada ta ce, "ko waye zai zuga Muhammadu auren nan dai sai ya yi, kuma yarinyar da na gani ita zai aura."

Mamy bata juya ba ta fita tana girgiza kanta kawai, dan ta san da ita Daada take.

Daada ta kalli Abba ta ce, "kai ko bani da rai abinda za a yi kenan, ko yau na faWi na mutu ka tabbatar da wannan yarinyar da na gani ta zama matarsa."

Abba ya bita da kallo kawai, mamakin kalamanta kawai yake yi. Haka kawai daga haWuwa da yarinya ba tare da ta santa ba ta dinga zancen ita zata aurawa Rehaan? Ba gwara a aura masa Waya daga cikin ?an uwansa na gida ba, amma batu akan auren wacce ba a sani ba ai bai tashi ba. Yana biye mata ne saboda babu yadda zai yi mata, amma shima bazai yarda da auren ba.

Abba ya ce, "shikenan Daada, ki kwantar da hankalinki, za a san duk abinda za a yi."

Ta kalle shi cike da harara ta ce, "kai a hankalina nake fa, ka daina yi min kallon mahaukaciya ka gane?. Duk abinda nake faWa na sani, duk abinda zance na san me nake faWa, ba mahaukaciya bace ba ni."

Abba zai magana aka yi sallama aka shigo. Babban Wanta wanda suke kira da Abiy ne ya ?araso ya zauna a gefen da Abba.

Abiy ya gaisa da Daada, ta amsa ba tare da ta kalle sa ba, kasancewarsa Wan fari ko sunansa zata iya kira, kallonsa ma sai an yi da gaske take yi saboda kunya

Abba ya gaisa da shi ya amsa sannan Abiy ya ce, "Wazu aka ce min Daada ta fita, ba a san inda ta tafi ba."

Abba ya ce, "wallahi keke ta hau, babu inda ban je nemanta ba amma ban ganta ba. Sai daga baya ta dawo a keke."

Daada ta ce, "Rabon zan haWu da yarinyar da Muhammad zai aura ne."

Da mamaki Abiy ya ce, "Rehaan zai yi aure ne?."

"Daada dai ta nemo masa mata. Yarinyar da ta taimake ta, ta dawo da ita gidan nan, ta ce ita zai aura. Kuma babu wanda ya santa, ko sunanta ba a sani ba balle inda take. Amma Hajiya Daada? ta ce itace matar Rehaan."

Abiy ya yi murmushi dan ya san rigimar babarsu,? ga tsufa ga rigima ya kalle ta ya ce, "Daada a ina take?."

Daada ba tare da ta kalle sa bata ce, "ko a ina take ita za a nemo ya aura, in dai na isa daku."

Abiy ya ce, "To Daada. Da har ina cewa yaje gida wajan ?an uwansa ya Wauki Waya, gida bata ?oshi ba ai ba a kaiwa dawa ba."

Daada ta ce, "sau nawa ana cewa ya yi hakan, ya aikata ne?. Yana can fararen fata sun Wauke masa hankali baya girmama yarensa da asalinsa. Dan haka babu batun auren ta gida, tunda ana nuna masa ya?i ya buWe idonsa, zan aura masa wannan ko da ba ya so."

Abiy ya ce, "Shikenan Daada, duk yadda ki ka yi daidai ne. Allah ya sa ta gari ce." Ta amsa ba tare da ta kalle sa ba tana Wauke kanta gefe.

A lokacin aka sake yin sallama aka shigo, mahaifin Jafar Alhaji Ahmad ya shiga da sallama, duk suka amsa suna yi masa barka da zuwa.

Ya amsa yana gaishe da Daada, ta amsa da?yar tana Wauke kai kamar bata so. Su kuwa suka gaisa dashi da fara'a da girmamawa sannan ya yi mata sallama ya tafi.

Daada ta bisa da kallo bayan ya fita ta ce, "Wan kishiya har wani Wa ne? Ba dan yarinyar nan Jurwaiyya ta nace ba, ta ya zan haWa zuri'a da ahlin kishiyata?. Shi kuma Jafar ya ma?alawa Muhammad, komai tare suke yi kamar tare aka haife su."

Su dai basu ce komai ba, amma suna mamakin wannan kishi na Daada da har yanzu ta kasa mantawa dashi. Duk waWanda take magana akai sun rasu, ita kaWai ce ta rage a cikinsu amma har yanzu kishi take da ?a?ansu.

Kuma gashi mahaifin Jafar yana da kirki da son ?an uwasa, ya Wauki Daada kamar babarsa, tunda mahaifiyarsa ta rasu ya mayar da Daada itace uwa a agaresa. Amma ita bata gani ko kaWan, yadda take nuna masa ne ya saka ya janye jikinsa daga zuwa inda take sosai, sai hanya ta biyo dashi zai shigo su gaisa ya tafi.

Sallama suka yi mata suka fito. Abiy ya kalli Abba ya ce, "Amma baza ka zuba ido ayi wannan auren ba ko?."

"To ya zan yi mata?."

"Ka san yadda zaka yi, amma auren wata yarinya da ba a santa ba bai tashi ba. In ta nace sai ya yi auren, akwai ?an uwansa mata. Gidana akwai Nana, gidansu Jafar ga Ikram, gidan Jamila akwai Zainab. Dukkansu sa'anin Juwairiyya ne, me zai saka bazai Wauki Waya ba?."

"Gwara Zainab da Nana zata iya amincewa, amma ka ga Ikram, wallahi baza ta yarda ba. Da ya ta amince da auren Jafar da Riyya da za a sake Wauko wata daga cikin gidan?."

"Gaskiya ka san yadda zaka yi, kar ka bari ayi masa abinda baya so."

"In sha Allah zan yi." Daga nan suka yi sallama ya shiga mota ya tafi.

Abba kai tsayw apartmet Winsa ya wuce, ya kira Rehaan a waya ya ce yazo ya same shi shida Babarsa.

Ba a jima sosai ba Mamy ta fara shiga, kafin ta zauna ya shigo yana tafiya a hankali, ya zauna ya dafe kansa da hannu biyu.

Abba ya ce, "ciwon kan ne?."

Rehaan ya sauke hannunsa daga kansa ya ce, "Abba meyasa komai ni ake yiwa dole a gidan nan? Meyasa kowa za a barsa ya yi rayuwarsa yadda yake so, amma ni ko yaushe sai ace sai na yi abu dan dole?."

"Ka yi ha?uri Rehaan, babu yadda zan yi da Daada ne. Yadda ka ke yiwa mahaifiyarka biyayya, nima haka nake yiwa tawa."

"Amma Abba meyasa Daada bata son farin cikina? Komai da ta Wauko sai ta ce ni, komai ni. Akwai abinda nake yi mata wanda bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login