Showing 84001 words to 87000 words out of 96103 words

Chapter 29 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

75

ko gidan radio zamu shiga mu nemi wanda zai biya mana. In bai yu ba akwai kadara, ita za a buge a zo a nemi lafiya."

Mama ta ce, "Allah ya yi maka albarka Sadik. Nima zan tattaro wani abu daga kuWina na bayar a haWa, dan kwana biyu ma babu masu aiko da kuWin."

Islaha ta mi?e tsaye ta ce, "ina zuwa" tana barin wajan kiran Safeera ya shigo wayarta, ta Wauka ta shiga masallaci dan ta Wauka.

Tana shiga suka haWa ido da Daaada ta idar da sallar walha, kallo Waya ta gane Islaha, itama ta gane ta.

Daaada ta washe baki ta ce, "Ishlaya ke ce?."

Islaha duk da halin da take ciki sai da ta yi dariya, dan yadda take faWar sunan yana bata dariya sosai ta ce, "ni ce Daada. Barka da safiya."

"Ba wani nan, ke da kika raka ni gida ki ka gudu."

"Ba guduwa na yi ba, sauri nake yi a lokacin shiyasa."

"Tafi can, ba wani sauri kawai kin gudu saboda na ce zana aura miki jikana. Kuma ni ba wasa nake yi ba, dan har iyayensa na faWawa, yanzu haka shine babu lafiya, mu je tare ki duba sa."

Islaha ta Wan buWe ido ta ce, "Daada kirana ake yi, kira mai mahimmaci, ina zuwa."

Daada ta ce, "kafin ki tafi, a wacce unguwa ki ke?."

Islaha ta faWa mata tana fita dan Safeera ta dame ta da waya sosai.

Daada ta bita da kallo ta gyara zama tana jiranta, dan duk bala'i sai t haWa auren Islaha da Rehaan, ko da zai sha fiya fiya ya she?a saboda ba?in ciki, yarinyar ta yi mata dan haka shima dole ta yi masa. Har wani gyaWa kai take yi a zahiri irin na tabbatarwar nan, ta bi ?ofa da kallo tana jiran dawowar Ishlaya.

Allah ya sa Ishlaya bata jirga ki ba Hajiya Daada>?#?>?#?

1k on telegram

Nana Haleema
'
*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 023.*

Daada tun tana jiran dawowar Islaha har ta gaji, mai kula da ita ta ?araso suka tafi Wakin da Rehaan yake.

Yana zaune shi da Mamy da Riyya Daada ta shiga da sallama, suka amsa ta ?arasa tana ?are masa kallo ganinsa dagashi sai three quater da ?aramar riga, gabaWaya guiwarsa zuwa ?asa a bayyane yake, sai riga mai gajeren hannu, sai hular sanyi a kansa, ya harWe hannu a ?irji yana kaWa ?afa a hankali.

Ya buWe baki zai gaishe ta Daada ta ce, "kai kuma meye haka? Ya zaka yi tsirara a gaban al'ummar annabi?."

Ya kalli kansa jin wai ya yi tsirara, ya Wan yi murmushi bai ce komai ba ta zauna ta ce, "yanzu da na taho da wacce zaka aura haka zata ganka? Kai ko kunya baka ji, kalle ka fa."

Maimakon ya bata amsa sai ya ce, "sannu da zuwa, ina kwana."

Daada ta ce, "lafiya lau. Yanzu mu ka haWu da yarinyar a masallaci, har ta faWa min sunan unguwarsu. Na ce ta zo mu je ta ganka amma ta gudu." Shi dai bai ce komai ba, suka gaisa da Mamy da Riyya.

Riyya ta ce, "Daada ya sunanta?."

"Sunan nata ne wahalar faWa yake yi min, amma sunanta ishlaya."

Riyya ta yi dariya ta ce, "Ishlaya kuma? Wanne irin sunan ne wannan?."

Daada ta taSe baki ta ce, "ke ni ban iya faWa ba, zan zo na san abinda za a yi a kai. Tunda na san sunan babanta da unguwarsu magana ta ?are."

Shi dai kanzil bai ce mata ba yana zaune ya lumshe ido ya jinginar da kai yana tunani kala-kala a zuciyarsa.

Mi?ewa tsaye ya yi ya saka takalmi zai fita, Mamy ta bishi da kallo ta ce, "ina zaka je kuma?."

Kafin ya bata amsa Daada ta ce, "to meye naki na tambaya? Yaro bazai je ya Wan motsa jiki ya taka ?afarsa ba, daga ya tashi sai a fara tambayarsa, ke lallai ga mai Wa ko?. Sam baku da kunya, baku san kara ba. ?an farin ki ke yiwa wannan rawar kan, mtswww me ake yi da jinin da ba na fulani ba?."

Daada ta kalli Rehaan ta ce, "jeka inda zaka je. Amma ka je ka saka doguwar riga sai ka fita, haramun ne fita a haka." Ray ya koma ya zauna yana haWe rai, fuska babu walwala ya ce, "na fasa fitar, tunda bata so."

Daada ta saki baki tana kallonsa ta ce, "Saboda uwarka bata so dole ka koma ka zauna, dole ka nuna min itace ta haife ka bani ba. Amma ko ka ?i ko kaso ni na haifi AbdulAziz, ina da iko da kai fiye sa kowa." Shi dai bai kula ta ba, ya rufe ido ya buWe, ya Wauki wayarsa yana dunnawa dan yana bu?atar tafiya Jedda a cikin satin da za a shiga.

Islaha kuwa tuni ta manta da wata Daada, tunda ta fita ta shigo da Saleem da Safeera, suka shiga suka duba Baffa daga nan suka zauna ana tattaunawa akan halin da ake ciki.

Safeera ta ce, "a.c wajan nan bata damun ki? Na san ki bakya son sanyi."

Islaha ta gyara facemask ta ce, "ina manage ne kawai, amma a takura nake wallahi. Jiya ma attack na samu."

Saleem ya ce, "Islaha ni fa ina zargin Asthama ce dake."

Safeera ta ce, "itace ma wallahi, duk wani alamominta ya gama bayyana a tare da ita."

Islaha ta ce, "to ya zan yi? An yi gwaje-gwaje masu yawa an tabbatar da babu."

Safeera ta ce, "kawai ki zo asibitin nan, dan ance indai ka zo asibitin nan kamar ka je asibitin turai ne. Duk wani ciwo da yakr ma?ale a jikinka zai bayyana zasu gansa."

Saleem ya ce, "yanzu ya maganar Baffa?."

Islaha ta ce, "ku faWawa Chairman gobe bazan samu damar zuwa ba gaskiya, zan je bank zan nemi loan in zasu bani. Dashe za a yiwa Baffa, kuma ana zancen miliyan sha biyu."

Safeera da mamakita ce, "miliyan sha biyun za ki ara!?."

"Ta ya zasu bani miliyan sha biyu ni da ba babbar ma'aikataciya ba? Zan dai nemi yadda zasu bani kawai."

Saleem ya ce, "ke da ba ma'aikaciyar gwamnati ba ta ya zasu Wauki loan su ba ki? A wanne kuWi zasu dinga cirewa?."

Islaha ta sauke numfashi tana Wan runtse ido, dan ciwon mara take yi kaWan-kaWan. A sanyaye ta ce, "bana ce ba Hamma Saleem, kawai a jikima nake jin zan warware matsalar nan in sha Allah."

Safeera ta ce, "kar ki yi abinda zaki cutar da kanki, ki yi iya ?o?arinki, kar ki yi abinda zai lalata miki aiki ko sunanki. Ki bi komai a sannu, na sanki da gaggawa. Wani abun sai kin yi ki ke danasani mara amfani."

Ta Wan runtse ido tana sake ?an?ame jikinta, Safeera ta ce, "kema dai kina da matsala, maimakon ki saka hijjab sai ki Wauko wannan mayafin ki yafa? Gashi nan sai ?an?ame jiki ki ke yi saboda sanyi."

Islaha ta ce, "yanzu meye abin yi?."

Safeera ta ce, "Hamman ki ya sani?."

"Sadik ya ce zai faWa masa."

"Gaskiya Sadik aboki ne na gari wallahi, ya tsaya a kan harkokin abokinsa kamar yana wajan."

"Gaskiya yana da ?o?ari wallahi."

Safeera ta ce, "ni kuWin nake ganin sun yi yawa, bayan na aiki ga na ?ananun abubuwa da zasu zo. Abinda zasu karSa a hannunku Allah ne ya sani."


Islaha ta ce, "nan ne maganin damuwarmu Safeera, babu wanda ya faWi wani abu mara kyau akan asibitin nan. Amma ni kaina na san mun kawo kan mu gidan mutuwa, dan iya kuWin da aka cire na file kuWine masu yawa, balle yau ya kwana biyu, kuma ba a karSi komai a hannunmu ba. Haka zamu daure ko kadara ce za a siyar don a ceto lafiyar Baffa."

Saleem ya ce, "gaskiya Baffa ya cancanci ayi masa komai Islaha, amma ya kamata a dinga tunani. Wallahi in ba a biya kuWin asibitin nan ba tsaf zasu kama mutum su kulle. Asibiti ne babba fa, kuma asibitin babban mutum ne."

Islaha ta ce, "asbitin waye wai?."

Saleem ya ce, "Mr Ray, wanda mu ka je nema har hotel. Wannan asibitin mallakinsa ne."

Islaha ta wara ido ta ce, "da gaske?."

Safeera ta ce, "ke da baki sani ba?."

"Wallahi ban sani ba, kuma naga sunan mace ne, ba Ray kamar yadda aka saba gani a abubuwansa ba."

Saleem ya ce, "ance sunan Mamansa ya saka. Wannan asibitin shine asibiti na farko mai tsarin turawa da aka fara yi a kaf Nigera, shiyasa ko yaushe a cike yake da ?an gayu da masu kuWi. Duk iyayin ?an Abuja, nan suke shigowa ana duba su, dan asibitin ba dai kyau da tsari ba. Komai irin na turawa, hatta mai kula da mara lafiya nurses ne, masu jinya akwai Waki na musamman da aka tanada dan su. Abinci da komai a nan ake bayarwa. Gashi kamar hotel, gininsa ya yi kyau da tsari."

Islaha ta girgiza kai cikin mamaki ta ce, "tabWi, lallai wannan Ray Win yana da matu?ar kuWi, ko iya incomes Win da yake samu a iya asibitin nan ai ya ishesa rayuwar duniya."

Saleem ya ce, "kuWi ba kaWan kenan Islaha, yana da kuWi kam sosai."

Ta Wan girgiza kai ta ce, "Allah ya fitar damu lafiya daga nan kawai."

Suka amsa da amin kafin ta ce, "Don Allah ku faWawa Chairamn kwana biyu bazan dinga zuwa ba, duk da zan yi masa massage, amma ku faWa masa dai."

Saleem ya ce, "lallai gobe akwai ?unci, kar ki manta gobe kina da talkshow."

"Ai sai dai yayi ha?uri kam, dan gaskiya bani da nutsuwar da zan iya yin komai" ta faWa tana shafa goshinta dan mararta ta fara damunta da ciwo, duk da ta sha magani amma ciwo take yi mata sosai.

Safeera ta kalli Mama da take gefe ita da yaranta, ta kalli Islaha ta ce, "matar nan bata ?aunarki, amma kina ta faWi tashi akan nemawa mijinta lafiya." Islaha jin ciwon ya matsa mata sai ta mi?e da sauri ta ce, "ina zuwa" ta faWa tana barin wajan da sauri.

Safeera ta tashi ta bi bayanta amma har ta shiga elevator ta bar floor Win.

Tana shiga ta ga ta kalli madannan da suke cikin elevator Win. Numbers ne, sai R, sai G, sai P. Kawai sai ta danna P Win, ba tare da ta san ina zai kai ta ba. Yana buWewa ta ga car park ne, tana fitowa ta ji Wumi da wucin motoci. Ta tako a hankali tana kallon wajen, yana da girma sosai, tana ganin irin wajen a Kdrama da india.

?umin wajen ya ratsa ta sosai, ta ja numfashi da ?arfi ta sauke, ta samu waje ta tsaya yana runtse idanunta.

Mararta ta Waure matu?a, a duk ranar da zata fara preiod haka take fama, in zata yi kamar zata mutu saboda azaba, duk da sai ta sha magani amma kafin fitar farko tana wahala. Ta je asibiti sau babu adadi amma babu wani amfani, dole ta ha?ura ta rungumi ?addara. Wani lokacin in ciwon ya dame ta, sai ta nemi waje ta fashe da kuka mai ?arfi ko zata ji daWi.


Bayan wata mota ta samu ta zauna, ta haWa kai da guiwa ta fashe da kuka mai sauti, tana jan numfashi da?yar tana juya kanta cikin azaba. Ta jima a haka, tana kuka tana addu'a har ta Wan fara jin daWi.

Ta fara ji tana flowing kaWan, ta dafe kanta da duka hannayenta, tana ji ciwon yana Wan raguwa kaWan. Ido ta lumshe tana jin yadda zazzaSi yake ratsa jikinta.

Wayar ta ce tayi ?ara, ta Wago da?yar ta kalla ta ga hamma ne yake kira ta Whatsapp call, saboda shi bata kashe data.

Ta jawo wayar ta Wauka ta saka a speaker ta ce, "Hamma."

A gigice ya ce, "Matar Hamma lafiya, Me ya same ki?."

"Babu komai, mura ce kawai."

"Kamar ya mura ce? Ga maganar ki tana nuna min baki da lafiya?."

"asibitin da mu ke zuwa ne akwai sanyi sosai, shiyasa nake mura."

Ya Wan ja numfashi ya ce, "meyasa ki ka Soye min batun rashin lafiyar Baffa?."

Bata ce komai ba dan bata cikin yanayin maganar, ya ce, "irin wannan ba a Soyewa kin ji?."

Bata amsa ba ya ce, "Abu ne da ya zama dole na sani. Yanzu na turawa Sadik kuWin da yake hannuna, kuWin kayan lefenki ne da Adda take siyowa, su nake ta so na gama haWawa kafin in dawo, amma Allah bai rubuta hakan ba. In sha Allah komai zai warware, kuma za a samu ?odar da zata yi daidai in sha Allah."

Islaha ta ce, "Hamma in na faWa maka rashin lafiyar Baffa daga zuwan ka, hankalinka bazai kwanta ba, shiyasa ban faWa maka ba."

"Ina kwanciyar hankali mahaifina yana kwance a asibiti? Ai babu kwanciyar hankali Islaha. Haka Allah ya tsara, kuWin da ake ta haWawa dan a gama gini zasu tafi a neman lafiya."

"Neman lafiyar shine gaba da komai Hamma."

"Hmm auren naki ma samun lafiya ne. Sadik ya faWa min likitan da ku ka fara gani a babban asibiti ya same sa wai yana sonki. A wannan asibitin da ku ke ciki ma baza a rasa wanda yake sonki ba. Ko ina aka je sai an ce ana sonki, ba dole na yi gaggawa na aure ki a huta ba."

Ta yi dariya tana sauke numfashi, ciwon yana lafa mata a hankali. Cikin dauriya ta ce, "Amma ai ni ban ce ina sonsu ba."

"in na killace ki a gidana mai faWar ma baza a samu ba, in kuwa aka samu wanda ya yi wannan gangancin, al?ali ne zai raba mu. Shiyasa nake so ayi auren nan a huta. In shekara ta zagayo ki haifa min kyakyawan baby mai irin skin Winki."

Ta yi murmushi bata amsa ba tana jin zazzaSi yana ratsa ?asusuwan jikinta

Islaha ta ce, "ina zuwa Hamma" ta faWa tana kashe wayar tana ji mararta na cigaba da ?ullewa.

Ta gaji da zama a wajen, ta mi?e da?yar tana dafe kanta saboda nauyin da ya yi mata, ta Wan sauke numfashi tana jin fitar abin kaWan a jikinta, dan tasan farkon zuwa baya yi mata flowing sai kaWan shiyasa take shan wahala har sai ya zuba sosai take jin daWi.

A hankali take tafiya tana ji kamar zata kifa, bata ganin gabanta ko kaWan, idanunta a lumshe suke, rana takawa kamar mara jini.

Babu zato ta ji an bangaji mutum, wayar hannunta ta faWi ta yi ?ara mai nuni da ta fashe, dan ta daku a ?asa.

Islaha ta Wago a hankali suka haWa ido dashi, ta sauke facemask Winta dan wajan babu sanyi sai Wumi, hakan ya yi daidai da yanayinta, bazai cutar da ita ba.

Tana kallonsa suka haWa ido, ta Wan yi siririn tsaki tana kallonsa, tana tuna haka ya yi mata a hotel ya zuba mata shayi, yau kuma ya yar mata da waya. Ta ja ta tsaya, tana jira ya bata ha?uri, sannan ya kuma sunkuya ya Wauki wayarta ya bata.

Rehaan tsaf ya gane ta, dan shima ita yake nema dan ya saka ta san shi waye. Sai kuma ta bashi mamaki, yana tunanin ita ko ina tana nan?. Ya ganta a hotel, ya ganta a lokacin ta samu attack, yanzu kuma gata a car Park.

Cikin seconds ya gama kallonta, ya Wauke ido daga kanta, ga raSa ta gefenta zai wuce dan bai yi niyar magana ba.

Islaha ganin haka sai ta ce, "wait mr man."

Ya Wan tsaya kaWan ta, ta dawo gaba ta tsaya tana kallon idanunsa. Idanun da suke yiwa duban jama'a wahalar gani, idanun da ko ka samu damar ganinsu kwarjini baya bari ka kalli cikinsu, idanun da suke da kaifi, in ya juya su a kan mace sai ta zauce.

Amma Islaha ko War bata ji ba, ta ce, "kai wai wanne irin mutum ne, Ka buge mace baza ka iya cewa ta yi ha?uri ba?."

Ta sunkuya ta Wauki wayarta, ta ga screen Win ya zama fari alamun ya samu matsala, ta juya masa fuskar wayar ta ce, "ranar da na ganka a hotel ka zuba min tea a jikina, yau gashi ka fasa min waya. Kai baka san darajar mace bane ko kuma darajar Wan adam ne baka sani ba gabaWaya?."

Cikin faWa take yi masa maganar kamar yaron ta, ko Mamy da ta kawo sa duniya bata taSa yi masa faWa haka ba. Shiyasa ya tsaya yana kallon ikon Allah, yana mamakin ?arfin hali da ?arfin zuciyar yarinyar, dan ko a haka ta yi nasara a kansa a karo na farko.

Islaha ta kuma fusata ta ce, "wula?anta Wan adam ba abu ne mai kyau ba, kuma indai zaka dinga yiwa irinmu wula?anci wata ran ai an samu wata ta zabga maka mari wallahi. Nima kawai dan ina da tarbiyya ne, amma wallahi da sai na mare ka. Ba a yi mana mu ?yale, akan gaskiyarmu sai dai a kaimu a kulle."

Rehaan ya Wan cize bakinsa, bai ce mata komai ba dan bai nuna nata alamun ya ji yarenta ba. Walking slowly ya wuce ta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa akan yarinyar.

Islaha ta Waga murya ta ce, "aikin banza, kuma wayarta da ka fasa min Allah ya isa."

Ya tsaya cak jin kalmar ta daki zuciyarsa, ya Wan rutse ido ya buWe, kamar zai juyo sai ya fasa kawai ya danna key Win motar ya shiga ya ja ya bar wajan da sauri.

A lokacin Safeera ta ?araso wajan, tana dafata, "tun Wazu nake neman ki, me ki ke yi a wajan nan?."

Islaha ta bi motar da kallo, ta kalli ta ce, "wani Wan rainin hankali ne kawai ya buge ni ya fasa min waya, kuma ko yi ha?uri ya kasa faWa min. Wallahi zuciya ce ta hanani, da sai na zabga masa mari. Kin san haka ya yi min a hotel, mu ka haWu ya zuba min tea, kuma ya ?i kallona ya wuce abin sa."

Safeera ta ce, "Haba Islaha! shine ki ka yi masa rashin kunya?."

"To ubana ne, ko haihuwata ya yi da zan ?yalesa? Ki duba asarar da ya yi min fa, kawai dan yana ta?ama da wani abin duniya sai ya dinga wula?anta ni?. Kema kin san bazan ?yale ba wallahi, in na ?yale aka taka ni aka wuce ba sunana Islaha ba. Ke ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login