Showing 57001 words to 60000 words out of 96103 words

Chapter 20 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

67

so ne?. Ko kuma ?iyayyar da take yiwa Mamy ce ta shafe ni?."

Abba ya kalli Mamy da bata ce komai ba, ya sake kallonsa ganin yadda idanunsa suka yi ja, gashi sun ?an?ance hakan ya tabbatar masa da ba ?aramin ciwo yake ji ba.

Ya tausasa murya ya ce, "ba haka bane Rehaan, ka daina cewa tana nunawa babarka ?iyayya ko kai, duk ba haka bane. Rikicin tsufa ne kawai Rehaan, kuma kai rashin zaman da baka yi a ?asar nan shine yake jawo hakan. Tana ganin ka girma ya kamata ka yi aure, kuma ka ga ta baka dama ka je gidan Abiy, ko gidan Jamila ka zaSi yarinya ka nuna baka so. Shiyasa ta yi haka."

Ya buWe baki zai yi magana sai kuma ya fasa dan maganar bata da amfani ko kaWan, ko ya yi Abba bazai taSa fahimtarsa ba.

Abba ya ce, "Matso Rehaan."

Bai musa ba ya matsa kusa dashi, Abba ya dafa sa ya ce, "duk wani mai Wauke da nasara sai da ya yi faWa da ?alubale a rayuwarsa, duk wanda ka gansa a sama ka duba inda ya taka kafin ta je wannan waje. Allah kai ya nuna a kaf ahlinmu, kai ya zaSa ya yiwa arzu?in da bai yiwa manyan da suke ciki ba. Sai ka yi ha?uri da abubuwan da zaka dinga fuskanta, akwai masu sonka tsakani da Allah, akwai masu fuska biyu Rehaan. Ka karSi duk abinda ya zo maka ka yi ha?uri dashi."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "Abba..." sai kuma ya yi shiru bai ce komai ba.

Abba ya ce, "faWi abinda yake bakin ka Rehaan, ina jinka."

"Zan iya amincewa da komai, amma ban da auren nan. Bazan iya ba, bazan iya ba Abba."

Abba ya sauke numfashi ya kalli Mamy da bata ce komai ba, ya dawo da kallonsa ga Rehaan ya ce, "nima maganar nan ban Wauke ta gaske ba, magana take akan yarinyar da bata santa ba, ta ya zata ce ita za a aura maka?."

Ya sunkuyar da kai ?asa bai ce komai ba, amma a zuciyarsa yana ayyana duk abinda zai faru shi bazai auri zaSin Daada ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma bazai taSa amincewa ba.

Abba ya kalli Mamy ya ce, "Nadira ki yi magana mana, ki kwantar masa da hankali."

Mamy ta kalle sa ta ce, "bani da abinda zan ce."

Abba ya yi shiru dan ya san ba a kyauta mata ita da ?a?anta, ba a yi mata abinda take so, a ko yaushe ita da yaranta ake tauyewa kamar bare. Sau Waya aka taSa amincewa da zaSi daga Sangarenta. Auren Juwairiyya da Jafar shine kaWai aka amince dashi, shima dan shida ?an uwansa sun tsaya kai da fata ne a kai, kuma sun yi addu'a, amma bayan sa babu wani abu daga Sangaren Mamy da zai fito ta amince dashi.

Abba ya ce, "Rehaan jikinka ya Wan yi zafi, ka je ka huta."

Ya kalli Abban ya ce, "Abba ka yi ha?uri, bazan amince da auren nan ba. Aikina ba a ?asar nan yake ba, batun dawowata ?asar nan gabaWaya bai tashi ba Abba."

Abba ya bisa da kallo, dan kafin ka ji abinda Rehan zai buWe baki ya musa masa tabbas abun ba ?arami bane, abin ya kai ma?ura a wajan ?insa a zuciyarsa.

Shi ina ya ga lokacin baka amsa ma balle ya yi maka musu? Ko yaushe cikin busy yake, kana magana dashi sauri yake yi ya bar wajan, ko kuma a kira shi a waya. A ko yaushe in ka ambaci sunansa amsar murmushi ce kawai, kafin ya bada amsa ya shiga wata hidimar.

Abba ya ce, "jeka ka huta, daga baya zamu tattauna akan wannan." Ya mi?e ya fita ba tare da ya ce komai ba.

Bayan ya fita Mamy ta ce, "Me zai hana baza ka barni na koma ?asata dani da ?a?ana ba? Tsananin ?iyayyar da ake yi min ce ta shafe su. Ana tauyewa Rehaan ha??insa sosai, ana yi masa abubuwa wanda baya so. Bai taSa dawowa nigeria ya rayu lafiya ba, ko yaushe cikin ciwo yake har sai ya bar ?asar nan. Kana gani dai, yana saka ?afa a gidan nan ya fara ciwon, ka san ciwon kan nan nasa da naci, in anjima ban san me za a ce ba."

Abba ya sauke numfashi, ya Wan yi shiru kafin ya tausasa murya ya ce, "Bana so na ji kina cewa ana nuna miki ?iyayya ke da ?a?anki...."

"To ba haka bane? Waye yake ?aunata a gidan nan?. A Sangaren ?an uwansa mata Janan ce kawai take nuna masa so. Duk yadda ya so da su sake dashi, duk yadda yake yawan maganarsu, duk yadda yake ?o?arin faranta musu, su kuma ba?insa suke gani."

"?angaren mazan kuma gasu nan dai, har gwara Zayyad ya kan Wan sakar masa fuska, sai Salman, shima dan yana da matsalar ?wa?walwa ne da bazai sauraresa ba, bayansu babu kowa kuma. Kawai dan na kasance ?ar wata ?asar ba jinin fulani ba shine duk abinda ya faru."

Abba ya sake tausasa murya ya ce, "ba sa son Rehaan, amma wa Allah ya Waukaka a kansu? Kaf ahlinmu da dangin mu gabaWaya akawai wanda Allah ya yiwa abinda ya yiwa Rehaan?. Tun daga kanmu iyaynensa har ?asa, babu wanda Allah ya bawa dama da baiwa irin wacce ya basa. Dole ya dinga fuskantar ?alubale, dole ya dinga fuskantar abubuwa irin wannan saboda Waukakar da Allah ya basa."

"Hmmm! Nima dai bazan amince da auren nan ba, duk abinda za a yi sai dai ayi, amma bazan taSa bashi goyan bayan ya auri yarinyar da bamu santa ba. Dan kawai bashi da gata, ba a son ya auri yarinyar da yake so kamar kowa?."

"In kuwa auren ya tabbata, jinin nawa da ba a so, jinin nawa da ake ?yama,tabbas sai na haWasa da wacce naga dama nima, zan Wauko mace Waya daga dangina na aura masa. Domin ina da iko da shi, ina da iko da Wana fiye da kowa...."

Sai kuma ta sassauta murya ta ce, "ka yi ha?uri, amma ana yi min abinda bana jin daWi a gidan nan."

Abba ya sauke ajiyar zuciya, ya Wan yi murmushi ya ce, "Nadira in bakya kwantar da hankalinki ta ya hankalin Rehaan zai kwanta? Ki adana damuwar nan, babu wanda ya isa ya yi nasara akaan Rehaan matu?ar Allah bai rubuta ba. Don Allah ki yi ha?uri, kar ki bar komai ya dame ki."

Mamy dai ta yi ajiyar zuciya tana kallon gefe Waya. Ta Wan girgiza kai bata ce komai ba.

? ?? ?angaren Mama tunda ta bar Sangaren Daada hankalinta yake a tashe, babban tashin hankalinta bai wuce wacece wacce Daada ta gano ba. Sai zagaye take yi a Waki, har aka buWe Wakin aka shiga.

Janan ce ta shiga Mama ta bita da kallo ta ce, "yauwa, Wazu kin ga yarinya da ta dawo da Daada ne?."

Ta Wan yi jim sannan ta ce, "gaskiya ban ganta ba, da Banisha suka gaisa. Lafiya Mama?."

Mama ta girgiza kai bata ce komai ba, sai daga baya ya ce, "jeki kawai." Janan ta juya ta fita.

Mama ta ce, "Wacece yarinyar nan? A ina take?."

Sai kuma ta girgiza kai ta ce, "bata isa ta auri Rehaan ba, matu?ar ta cika qualities Win zama mace ta gari wallahi Allah bazai aure ta ba. Bana so ya auri ta gari, bana so."

Sai kuma ta dafe kai ta ce, "wacce yarinya ce wannan, Wacce yarinya zan samu na haWa aurensu? Wacce yarinya zan shiga fita, in biyata ta amince da auren nan?."

Ta furzar da iska ta ce, "sam bazan zaSo daga ahlina ba, bazai yu na aurawa wata a cikin dangina Rehaan ba. Kaf ?a?ana babu mai auren matashin mai kuWi kamar Rehaan, dan haka yarinyar da na sani baza ta taSa zama matarsa ba wallahi!. Babu ?ar ?awa, ko ma?oci, ko ?ar Wan uwa, da suka isa su auri Rehaan wallahi!."

Ta naushi hannunta ta ce, "bazai yu ba wallahi, dole na san abinda zan yi!."

BuWe ?ofar aka yi aka shigo, ta kalli wacce ta shigo ganin Umma ce sai ta bita da kallo.

Umma? ta ce, "Mama wai ya abun yake ne? Wacece yarinyar da ake magana akai ne?."

Mama ta ce, "abinda nake so na gano kenan, na kasa fahimtar wacece wannan. Dah ta bani dama na samo wacce yake so, da ta ce ta bani dama har na fara plan Win nemo wata karuwa in biyata domin ta auresa. Amma an Sata min plan Wina."

"Yanzu ma bai Saci ba, mu cigaba daga inda muka tsaya, in an ganota Win, indai bata yi mana ba kar mu sake mu amince, ko ta wanne hali a lalata auren nan."


"haka za a yi, bazai taSa auren wacce ta dace ya aura ba, shiyasa bazan taSa bari ya auri wata daga dangi ba. Daga can waje za a samo, itama wacce bata dace ba."

"Dakyau, haka nake so naji. Bara in je na bawa Salman magani na dawo mu cigaba da tattaunawa. Dole mu dage a nemo yarinyar nan da wuri" ta faWa tana fita daga Wakin.

Mama ta bita da harara tana jan tsaki ta ce, "Babar mahaukaci!."

? ? ? ? ? ? *******

Islaha kuwa tunda suka bar wajan Daada take ta murmushi ita kaWai, in ta tuna rigimar matar bata sanin lokacin da take dariya ita kaWai.

Musaamma yadda take faWar sunanta da yadda take cewa zata aura mata jikanta. A haka ta ?arasa gida, ta biya mai keke kuWinsa ta shiga cikin gidan.

Tana shiga suka haWa ido da Umman su Safeera, ta Wuka ta ce, "Mama ina yini, Umma ina yini" ta faWa tana niyar wucewa.

Mama ta ce, "tun ?arfe huWu na asuba ki ka bar gidan nan, baki dawo ba sai yanzu bayan sallar i'sha. Ace kin je yawon ta zubar ki ce ke ba haka ba."

Islaha dai bata ce komai ba, tana jin Umma ta ce, "to ke har san tabbatar miki? Ai ko baki faWa ba kowa yana ganin idanun yarinyar nan ya san ta san maza. Kai tsaye take kallon idon ka ta yi magana, in ba mata irinsu ba babu mai kallon idon na gaba dashi ya yi magana."

Islaha ta shiga Waki ta yi alwala ta yi sallah, sai a sannan ta ji tana jin yunwa sosai.

Ta fito fito a sanyaye tana jin Umma da Mama suna tattaunawa akan tafiya aikatau wata ?asar.

Islaha zata gifta Mama ta ce, "ga baiwa kin ajjiye ko? Sai dai ki je yawon ki, ki dawo ki tarar na dafa miki abinci ko? To baki isa ba wallahi, yau ba ki da abinci a gidan nan."

Ta tsaya cak bata ?arasa ba, ga yunwar da take ji tana neman hallakata, dan ji take kamar ana Waure mata cikin ta. Iya tea kaWai ta sha tun safe, bayan shi bata cin komai ba.

Ta koma da baya ta Wauko rabin kuWin da Saheer ya bata jiya, ta fito ta ?arasa gaban Mama ta ajjiye.

Islaha ta Wan kalli Mama sannan ta ce, "ayi ha?uri da wannan, babu yawa."

Mama ta kalli kuWin ta ga basu wuce dubu goma ba, ta harari kuWin ta ce, "iya abinda aka biya ki daga daren jiya zuwa yau kenan?."

Shiru ta yi bata ce komai ba, dan tana gudun buWe bakinta akan Mama, duk ranar da ta mayar mata bazata ji daWi ba, tana ha?ura ne kawai in ta tuna Saheer, shiyasa bata cewa komai.

Mama ta ce, "baki ji me nace ba?."

Islaha ta du?a ta Wauki kuWin ta juya da niyar barin wajan.

Mama ta ce, "ke dakata, dawo da kuWin nan."

Ta Wan yi murmushi kafin ta ce, "kin ce ya yi kaWan ne, shiyasa na Wauka."

"Ajjiye malama, ki je ki zuba abinci." Islaha ta juya tana murmushi, wato ita Mama indai da kuWi an wuce wajan kawai.

Tana barin wajan Umma ta ce, "yanzu yarinyar nan ce tace baza ta je aikin nan da ki ka faWa min ba?."

Mama ta ce, "shiyasa na juyo gurin ki, in Safeera zata je a satin nan za a yi mata komai ta wuce, in kuma baza ta je ba, ke ki girgije yaran nan ki Waga kawai. In kina zaune wallahi zaki ga zaunau."

Umma ta ce, "wannan a rubuce yake wallahi, ki Wauka an yi an gama, dan ni zan je ba Safeera ba."

"Ya fi dai, dan wallahi kuWi ake samu lokaci Waya. Kuma tsaf zasu yi miki kyautar mota ko kyautar gida. Ga kwana a c, ga aikin ba wani yawa ne dashi ba, sai kinga dama zaki Wan motsa. Bakya ganin waWanda suka tafi suna yin ?iba?."

"Ina gani woman leader."

"Kaza ce, da ac, da hutu ga albashi mai tsoka. Ni ina mamakin matan da suke dan?arewa a gida su kasa taSuka komai saboda miji. Mtsw! Allah na tuba ba dan ina samu daga inda nake zaune ba, babansu Saheer Win banza? Da yanzu ina can ina haWa hajata wallahi."

"Ai kin lasa min zuma a baki ne yar uwa, wannan tafita dole a yi ta."

Mama ta Wan taSe baki ta ce, "ki dai gama komai da gaggawa, in ke ce Win gobe ki zo a je a san abinda za a yi, in Safeera ce itama ki turo ta gobe a gama komai."

Umma ta ce, "haka za a yi Woman leader, zan san abinda zan yi kuwa yanzu nan. Bara ma ki ga" ta faWa tana mi?ewa ta fita daga falon.

Islaha tana jin su har Umma ta fita, ta san dai ko me za a yi Safera baza ta amince ta bar ?asar nan saboda aiki ba, kuma itama Umman tasan ba zuwa zata yi ba, saboda Baba ba irin Baffa bane. Shiyasa hankalinta bai wani tashi ba. Ta zuba abinci ta zauna a kitchen Win ta ci ta sha ruwa sannan ta fito.

A lokacin Hanan ta shigo tana yatsine fuska kamar mai na?uda. Mama ta bita da kallo ta ce, "sai yanxu?."

Hanan ta ce, "Mama na tsaya na samo kuWi mai tsoka ne fa, kin ga" ta faWa tana nuna nata bandle na rafar ?an dari biyar biyar guda goma, sababbi kar mi?a??u.

Mama ta buWe ido tare da mi?ewa tsaye cikin mamaki da farin ciki, ta karSi kuWun tana kallo, kafin ta rungume Hannan ta ce, "Hanan a ina ki ka samo kuWin nan masu yawa haka?."

Ta Wan yi murmushi ta ce, "Haba Mama, yaushe ki ka fara tambayar a ina na samo kuWi?."

"Ke dallah ba ina nufin ki faWa min ba, wanda ya baki nake so na ji."

"Tunda na samo ai shikenan Mama."

"Farar haihuwa kenan, masu baiwar da maza suke basu kuWi ba tare da sun ba da kansu ba. Ina ji daku ?a?ana."

"ki ri?e duka Mama, ni na gaji bacci zan yi" ta faWa tana wucewa ciki.

Mama ta buWe murya cikin murna ta ce, "Allah ya yi miki albara, Allah ya ?arawa neman ki albarka."

Labiba da take kallonsu kishi ya kamata, ta ji a ranta ta ya Hanan zata kawo dubu Wari biyar ita bata kawo ba? Ta ya zata zuba ido Hanan ta fita kawo kuWi gidan?.

Ta girgiza kai tare da yin ?wafa, ta yi tsaki ta ce, "dubu Wari biyar ce ba fa Mama, ba wata tsiya ba. Sai murna ki ke yi kamar ta bani miliyan biyar.

Mama ta kalle ta ta ce, "wata tsiya ce mana Labiba, ke kin kawo Wari biyar Win ne?."

"Ai na fi ?arfin na kawo ?ananun kuWin wallahi. Nawa ce dubu Wari biyar?."

"Tunda baki taSa kawowa ba ki yi shiru."

"Ai dan na canja waya ne. Amma ki zuba ido, zan kawo wanda ya fi na ta wallahi."

"Mu gani a ?asa."

"Zaki gani Mama" ta faWa tana shiga Waki cike da hassada da ba?in cikin an fita.

Islaha dai bisu da kallo, ganin yadda ake?gasa akan samo kuWin da ba a san daga ina suke zuwa ba, har kishi ake nuna ?arara akan Waya ta kawo Waya bata kawo ba.

Ta girgiza kai, tana koyar darasi mai girma a gidan Mama, tana ganin dramar da take so ta ga ?arshenta, dan ta san ba za a yi happy ending ba. Bata ce komai ba ta shiga Waki jikinta duk a gajiye...


Nana Haleemad'?
'

*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 016.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

___________________

Umma tana fita daga gidansu Saheer gidan ?awarta Atika ta shiga, aminiyarta kuma abokiyar sirri. Tana shiga ta Wauki kujera ta zauna a tsakar gida ta ce, "Atika kina ina?."

Tana daga Waki ta fito ta ce, "Gani nan, aminiya ta samu ne?" Ta faWa tana fitowa ta zauna akan kujera itama.

Umma ta ce, "ta samu, ga bikin zuwa babu zanin Waurawa ?awata."

"Ina jinki, meya faru?."

"batun tafiya Saudia aikin nan ne, kin ji kuWin da ake samu?."

"Allah ?awata?."

"Bari kawai ?awata. Ga gidan aikin an samu a hannu, kawai ma'aikaci ake nema."

Atika ta ce, "ba kin ce Safeera za ki tura ba?."

Umma ta ce, "Yarinyar baza ta yarda ba, kin san tana tare da Islaha, kullum cikin kushe abin suke. Babanta ma ya ce indai shi ya haife ta bazata je ba. Shine nace masa amma ni ai ba shi ya haife ni ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login