Showing 21001 words to 24000 words out of 96103 words

Chapter 8 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

51

dry comfort da humra" ta faWa tana fara shiryawa cikim gaggawa.

Babu jimawa ta gama shiryawa, ta fito tsaf kamar kayanta. Islaha ta kalli kanta ta ce, "kayan aro akwai ?arawa mutum kyau, ki duba yadda na fito don Allah." Suka yi dariya gabaWaya, Safeera ta Wauke kayan da Islaha ta cire ta ajjiye sannan suka fita.

A tsakar gida suka yiwa Umma sallama ta masa da?yar suka fita.

Ishala ta ce, "mu je motar Sadik abokin Hamma, yana jiran mu." A tare suka ?arasa suka shiga motar.

Safeera ta ce, "Hamma ina kwana."

Ya kalle ta da murmushi ya ce, "Safeera an tashi lafiya?."

"lafiya lau Hamma."

Ya kalli Islaha ya ce, "kin yi kyau."

Fuska babu walwala ta ce, "kayan aro ne."

Ya yi murmushi ya ce, "na sani ai, a daina tona? mana asiri."

Suka fara tafiya bai ce komai ba. Sai da suka Wan yi nisa sannan ya ce, "Bestie ki bata ha?uri akan abinda ya faru, in sha Allah komai ya kusa ?arewa. Na san bata jin daWin zama a gidanmu, amma hankalina yafi kwanciya ta zauna a gidanmu akan gidan da ta bari."

Ta wani kalle sa ta ce, "meye da inda na bari Win? FaWa maka aka yi gidan marayu gidan cutarwa ne ko me?. Baka san akwai security ba?."

?asa-?asa ta ce, "ba gwara can ba, nan da ake cewa ka kawo kuWin da ba a san a ina ka samo ba fa."

Sai kuma ta ce, "Ni dai da zaka amince zan na bar gidanku, na koma wani wajen daban."

"Baza ki koma ba, kuma ba a barin irin waWanan gidan a sake komawa, ke kam sun yaye ki. Da kaina na saka hannu na yi adopting Winki, hukuma ta shiga, ki ka amince aka bani ke. Kuma sai a ga kin koma?. A gidanmu za ki cigaba da zama, har lokacin auren mu."

"To ko ban koma can ba, akwai ?an uwana da muka tashi tare, zan iya komawa wajensu da zama."

"Baza ki je ba fa."

Ta yi shiru bata ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta yi tana wasa da hannunta.

Saheer ya ce, "Safeera don Allah ki bata ha?uri, na san abinda Mama take yi mata bata kyautawa, amma ta yi ha?uri ranta ne ya Saci kawai."

Safeera ta ce, "babu komai Hamma, Mama ai uwa ce a garemu, dan ta tsawatar akan abinda ya faru shima tarbiyya ce."

Saheer ya ce, "duk da haka ki bata ha?uri, sai fushi take yi ko abimci bata ci ba."

"Kar ka damu Hamma, in mu je wajen aiki zata? ci."

Wayar Islaha ta fara ?ara, ta kalli wayar, sai ta Wan sa ci kallon Saher ta ga ita yake kallo. Ta Wauke kai ta Waga wayar ta saka a kunne ta ce, "uhum zan yi."

Ta sake yin shiru alamun ana bata amsa, sannan ta ce, "A'a, a bar min, zan yi handling" ta faWa tana kashe wayar ta ajjiye a gefe tare da lumshe idonta.

"ke da waye?."

Ta runtse ido jin tambayar da ya yi mata, daman ta san zai tambaya, ta san halin kayanta tsaf.

Ta Wan kallesa ta ce, "daga wajan aiki ne."

Ya Wan zuba mata ido ba dan ya yarda ba, ya Wauke kai suka cigaba da tafiya.

Sai da ya sauke su a bakin gidan tv, sannan ya bawa Safeera kuWi ya ce su su yi abinci suka shiga ciki.....


Nana Haleema
'
*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

_More pages on arewapen@nanahaleema11._

*Book 1*
*Page 006.*


Su Islaha suna shiga gidan tv, kai tsaye office Win Chairman ta wuce kamar yadda ya ce yana neman ta.

Ta yi knocking ya bata dama, ta shiga da sallama cikin nutsuwa da yanga irin ta ta.

"Barka da safiya Chairman."

Ya kalle ta da murmushi ya ce, "barka Ishala, ina ta jiran zuwanki tun Wazu" ya faWa yana nuna mata kujera alamun ta zauna.

Islaha sai da ta zauna sannan ta ce, "na Wan samu matsalar abin hawa ne shiyasa. A yi min afuwa."

"An yi miki. KarSi" ya faWa yana mi?a mata envolope mai kyau, an yi mata ado rubutu mai Waukar hankali.

Islaha ta karSa tana jiran ?arin bayani. Chairman ya ce, "invitation card ne. Na samu labarin Mr Ray yana gab da shigowa Nigeria, shiyasa na saka aka buga min katin gayyata tun yanzu, da zarar ya shigo ?asar nan ko ba a nan ya sauka ba, zamu Wauki nauyin Waukarki ki kai masa ko ina. Tunda mun yi mail babu adadi babu respond, gwara a kai iv."

Islaha ta Wan murmusa cike da jin haushin wannan za?ewa ta ce, "Amma yaushe ake saka ran zuwansa?."

"PA Winsa na Yola, ya ce min babu lokaci, amma tabbas zai zo cikin kwanakin nan. Da zarar ya zo zan nemi alfarmar PA Wina, na haWa ki dashi."

Islaha ta yi shiru bata yi magana ba, tana mamakin wannan zumuWi na Chaiman kamar za a yi interview da shugaban ?asa. Ko gwamna da suka yi interview dashi bai yi zumuWi haka ba.

Chairman ya ce, "in muka samu ya amsa gayyatar mu wallahi kakar mu ta yanke sa?a, ba wai dan kuWi ko wani abun ba, kawai dai bai taSa hira da tashoshin nigeria ba, ba a taSa ji yana yaren fulatanci ko Hausa a tv ba, sai dai english. Kuma mu da hausa zamu yi hirar, dan waWanda ba fulani ba su fahimta. Shiyasa mutane da yawa suke cewa baya jin ko wanne yare sai turanci, ni kuma na san ba haka bane. Da zarar ya amsa gayyatar mu, aka gabatar da yaren da kowa zai ji ai mun gode Allah."

Islaha ta Wan taSe baki ta ce, "To Allah ya kaimu."

"Amin Islaha. Shiyasa na zaSe ki, domin kina da nasara da sa'a a rayuwarki. Ba ki taSa gayyato guest ya yi denying ba, kina zuwa suke saka mana date."

BuWe ?ofar office Win aka yi aka shigo, Islaha ta kalki wacce ta shigo kamar yadda Chairman ma ya kalle ta.

Ganin Islaha a office Win sai ta haWe rai tana bin Islaha da banzan kallo kafin ta ce, "Chairman ba dai ita ka bawa iv ba?."

Ya kalli Ummi ya ce, "ita na nawa."

Cike da takaici ta ce, "Chairman ka ce ni zaka bawa wannan aikin, ka yi min al?awarin gayyatar babban ba?o na gaba, ya kuma zaka tsallake ni yanzu?."

"Na baki damar ai, kin manta na baki dama ki gayyato mana C.E.O Footwear by tiger da yake Kano, kin iya?."

Ta yi shiru bata ce komai ba, Chairman ya ce, "Ba ki iya yin komai ba, muna ji muna gani haka damar interview dashi ta kubce mana."

"Islaha kuwa sa'ar daga jininta take, bata taSa kaiwa wani gayyata bai amsa ba, ko ta waya ko a zahiri, indai itace sai ya mun tattauna dashi ba. Kuma magana ake ta za a gayyaci Rehaan Yola, bazan yi sake na tura ki ba. Islaha zan tura, in ya yi rejecting zamu sake komawa, kuma ita zan sake nema."

Cike da ba?in ciki da hassada ta ce, "Amma Chairman a bayana Islaha ta fara aiki a gidan nan, sai da na shekara biyu ina aiki sannan aka Wauke ta. Kuma kafin zuwanta ni ce a sama, dani ake ji ba ita ba. Yadda ka ke yabonta kana cewa indai ta yi sai an karSa nima haka, ni ce top presenter a gidan nan kafin ta zo. Amma yadda ka ke fifitata kamar ta riga mu fara aiki a nan..."

Ya Waga mata hannu ya ce, "Ummi fita ki bani waje, in kin ga dama ki canja wajan aikin, ki ji inda za ki zama sama da Islaha. Babu dole."

Ummi ta bi Islaha da kallon kishi da hassada, ta yi ?wafa, ta ja ?ofar ta fita cikin tsananin ba?in cikin da ya bayyana har akan face Winta.

Chairman ya kalli Islaha ya ce, "ki ri?e a hannunki, komai dare in damar zuwa a kai masa ta zo, zan kira ki."

Islaha ta Waga kai jin wai komai dare, ta ce, "To Chairman."

"Don Allah kar ki bani kunya Islaha, bana jin ki, na san kina da ?o?ari, amma a kan wannan ki ninka. Babban ba?o ne na musamman, ki tabbatar da kin yi masa kalaman da zai saka ya bamu date da time. Don Allah."


"In sha Allah zan yi."

"Kina gani ana nuna miki ba?in ciki ?arara, ki bawa ma?iya kunya, kar su yi mana dariya."

"In sha Allah zan yi."

Ya yi murmushi ya ce, "yauwa na gode. Mun samu labarin an samu gobara a cikin Jimeta, an mutu sosai ta silar hakab, zaku je Wauka. Ki nemi Salim zai faWa miki."

Islaha ta gyaWa kai ta ce, "Na gode" ta faWa tana mi?ewa ta fita.

A waje ta tarar da Safeera tana jiranta, zata yi magana Ummi ta tsaya a gabanta tana aika mata da hararar ba?in ciki.

Islaha ta haWe rai tana bint da kallon up and down ta ce, "lafiya?."

Ummi ta girgiza kai ta ce, "shi ya kawo hakan. Islaha ki tsaya a iya matsayin ki, ki tsaya a inda na ajjiye ki, kar ki yi gangancin shiga gonata. Domin duk wanda ya shiga gonata ya yi irin da na shuka, dashi zan haWa girbe amfaninta."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "Ai na fi ?arfin na shiga gonar ki Ummi, sai dai ke ki shigo tawa. Kuma duk abinda ki ke ji dashi ina ji dashi, banbancin kawai, ni bana nuna ba?in ciki akan abinda Allah ya yiwa mutum."

"rufewa mutane baki, waye bai san asalinki ba? Tsintacciyar gidan marayu, tabbaWaWiyar ?aramar karuwa, wacce masu gadi da ma'aiakta suka gama lalatawa. Har kina da bakin magana?."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "Na gode, kin faWi wace ni. Sau ke, wacece ke?."

Ummi ta sake fusata zata yi magana, Islaha ta ce, "a haka tsintacciyar gidan marayu, kuma ?aramar karuwa ta je matakin da ke ba ki je ba. Nazo gidan nan a bayanki, kuma a yanzu dani ake damawa ba ke ba. Duk inda ki ka shiga a gidan nan, sunan Islaha ake kira, saboda ?arfin da nake dashi wanda ke ba ji da. Kin ga ko a nan an nuna miki banbanci tsakanin tsintaacciyar gidan marayu dake!."

Ummi cikin Sacin rai ta ce, "Islaha sai na yi maganin ki, wallahi sai na ga bayan ki! Sai na Satar dake daga duniyar nan, sai na tarwatsa ki, sai kin bar aikin nan gabaWayaa. Sai na yi miki abinda baza ki sake marmarin zuwa wajn nan ba."

Islaha ta ce, "baki isa ki ga bayana ba wallahi, ba ki isa ki Satar dani ba, dan ke ba wata tsiya ba ce a duniyar. Ina jiran ganin abinda zaki aikata Ummi, ina zuba ido in ga ta ina zai Sullo. In kin cika ?ar halak ki aikata mu gani, in kin cika Ummi daga yau kar na sake zuwa aiki a wajan nan, ki yi min kurciya, na ji na daina sha'awar aikin gabaWaya."

Ummi ta matso kusa da ita ta ce, "Haka ki ka ce?."

Islaha ta ce, "haka na ce."

Ta girgiza kai tare da yin ?wafa ta bar wajan.

Ta kalli Safeera da ta ji ji komai, suka juya zuwa office Win Salim.

A cikin Office Win Safeera ta ce, "Islaha ki tsaya, wannan ba maganar wasa ba ce ba, wannan i?irarin da Ummi ta yi ba abinda za a Wauke kai daga kansa bane ba. Ba wasa bane ba, ba abinda za a yi dariya a wuce bane."


Salim ya kalle su ya ce, "me ya faru?."

Safeera? ta kalle sa ta ce, "Ummi ce ta tare ta tana cewa sai ta ga bayanta. Sai ta Satar da ita daga duniya. Ka ga wannan ai ba maganar wasa ba ce ba."

Salim ya ce, "gaskiya ba ta wasa ba ce, ya kamata a sanar da Chairman. Irin waWanann kalaman suna iya girma a nan gaba, sai ka ga sun haifar da abinda ake gudu."

Islaha ta ce, "ku share ta, babu abinda zata iya wallahi. Ba?in ciki take yi dani, kuma bata iya Soye hassadarta a gare ni, shine kawai."

Ta nuna musu iv Win ta ce, "katin gayyatar Rehaan Yola aka bani, shine gabaWaya ta Waga hankalinta ta kasa Soye haddasarta."

Saleem ya ce, "duk da haka dai Islaha, zahirinta mu ke gani bamu san me zata aikata a bayan idon mu, yana da kyau a tsawatar mata."

Islaha cikin ko in kula ta ce, "ku share ta don Allah. Chairman ne ya ce in zo na same ka akwai inda zamu je."

Saleem ya ce, "yanzu nake niyar kiranki."

Ta kalli Safeera da ta fita damuwa, ta ce, "Safeera kar ki damu fa, babu abinda zai same ni wallahi. Aikin banza, ta Waga hankalinta kawai dan an bani katin gayyatar Mr Rehaan, sai ka ce shi Win wata tsiya ce."

Saleem ya yi dariya ya ce, "wata tsiya ce mana Islaha, ke kin san dawa aka haWa ki kuwa? Kin san wa ake so ki gayyato kuwa?."

"Rehaan Yola, ko na ce Ray, ba haka sunansa yake ba? Bayan haka waye shi?."

Yayi dariya, dan ya san halinta akwai drama, ya ce, "A'a fa Islaha, Rehaan ya wuce ace masa waye shi. Duk inda ki ke tunanin bawan Allah nan ya zarce haka. Ke kanki da aka haWa ki da kati, iya? haWuwa da PA Win nasa ma babban aiki aka baki, balle babbar giwar."

Islaha ta ce, "Kar ka manta Hamma Saleem, ni na yi interview da gwamnan garin nan, na zauna a babban falonsa na gidan gwamnati, aka saka min camera na yi masa interview. Nasan duk capacity da yake ji dashi, bai kai gwamna ba."

Saleem ya kalli Safeera ya ce, "My love da alama Islaha bata san waye Ray ba wallahi, da ta san waye shi da ko kuWi za a bata ta faWi abinda ta faWa bazata iya ba. Amma muna yi miki fatan nasara, in ki ka samu damar ganin Rehaaan, ko ba ki yi hira dashi ba, abin alfahrin mu ne balle kuma a kai ga kin yi hira dashi. Daga ranar zamu sake tsada, ganin mu sai an cike form."

Ta yi tsaki, cike da takaicin yadda ake koWa sa ta ce, "kamar wani sahabi?."

Safeera ta ce, "ke dai Allah ya bamu sa a kawai, amma ya wuce tunaninki wallahi."

Saleem ya yi dariya ya tattara kayansa, dan tunda bata ra'ayi bazata karSi ra'ayinsu ba, sun san halinta kaf, akwai jan magana. Saleem ya kalle ta? ya ce, "ina jiran ki" ya faWa yana fita daga office.

Safeerata ce, "Islaha in tambaye ki don Allah."

Eslaha ta kalle ta ta ce, "ina jin ki."

"don Allah meyasa ake yawan jifanki da sunan karuwa? Wanne abu ne ya faru da hakan yake kasancewa?."

Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "ni kaina ban sani ba Safeera, abinda na sani yana da ala?a da zaman gidansu Saheer. Shiyasa maganar bata damuna ko kaWan, duk yadda ka ke kallona a haka nake, sai me?."

Safeera ta ce, "Haka ne. Amma magana mai kyau daga bakin mutane ma rahama ce Islaha."

Ta taSe baki ta ce, "ki wuce record office, mu mun wuce" ta faWa tana fita daga office Win.

Safeera ta bita da kallo, a bayyane ta ce, "tabbas zamanta a gidan su Saheer zai saka a dinga yi mata wannan zargin saboda kowa ya san wacece Mama. Amma meyasa ake zargin tun a gidan da ta tashi ta lalace? Meyasa bata damuwa?." Babu mai bata amsa, ta yi ajiyar zuciya ta fita daga office Win.


*********

? ?? Mama tana zaune a gabansa malamin duba yana duba mata ?asa, ta yi shiru tana jira ya gama ya zayyano mata abinda ya gano. Yana gamawa ya kalle ta ya ce, "tabbas akwai dawowar Rehaan ?asar nan, nan ba da jimawa ba."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "na ji daWin hakan sosai."

Ya girgiza kai ya ce, "kuma zamu yi nasarar aikin mu a wannan lokacin."

Mama ta yi dariyar jin daWi ta ce, "yauwa, haka nake so. Amma bazai koma ba dai ko?."

Ya sake dubawa kafin ya Wago ya ce, "eh to, akwai yuwar komawar sa ?asar waje gaskiya, amma kafin ya koma za a Wan sha ?alubale kaWan."

Mama ta ce, "ni yanzu abinda nake ka yi masa, ayi masa bazai sake marmarin komawa can ba, sannan yadda yake shiri da Janan, yadda Janan take bashi abu ya ci, a sake haWa ala?arsu ta yadda komai ta ce masa zai yi."

Ya girgiza kai ya ce, "wannan abu ne mai yuwa Hajiya" ya faWa yana juyawa ya Wauko magani ya bata.

Sannan? ya ce, "gashi nan ki ri?e."

Ta karSa ya ce, "wannan jan maganin, a bashi a abinci ya ci, zai yi rashin lafiya mai yawa wacce zai jima a kwance, harkar kasuwancin nasa ma zai manta da ita. Wannan koran kuma a bashi a abin sha, ruwa ko kunu ko dai wani abun, a tabbatar da ya sha. Za ki ga aikin maganin ko ban faWa miki ba."

Mama ta saka maganin a jaka, ta kalle sa ta ce, "na gode Malam. A Waukaka su Zayyad, ya zama yadda suke manya a gidan, su ne dai manya? gaba da baya, ya zama komai dasu za a dinga damawa ba Rehaan ba. Bana son ace Rehaan shine ?arsmi kuma shine a kan gaba, bana ?aunar hakan. So nake yadda na kafu a gidan, ?a?ana ma su kafu, yadda na gagari kowa, suma su gagari kowa malam."

Malam ya yi dariya ya ce, "tunda mu ka iya ya?i da tsafe-tsafe ?an india a kan ki, wannan ?arsmin abu ne a wajan mu."

Mama ta yi dariya ta ce, "Na sha wahalar Nadira, na sha ba?ar wahalar matsafiyar nan. "

"Yadda mu ka yi maganinta shima zamu yi maganinsa. Ko a wajan mijinta bata da wata power, komai yana hannunki."


"Shiyasa nake jin daWin aiki dakai Malam, kana yi min komai yadda nake so."

"Sai maganar matar auren da aka ce na samo masa. Tunda an bani komai a hannuna, zan nemo daidai da ra'ayina. Bana so ya samu mace ta gari, tabaWaWWiyar ?ar iska nake so a samar masa, saboda hakan zai yi min amfani nan gaba."


Ya yi murmushi ya ce, "ki Wauka an gama Hajiya, ki rubuta wannan kamar an yi an gama. Zan yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login