Showing 9001 words to 12000 words out of 96103 words

Chapter 4 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

48

kallo, ya kaWa kai ya ce, Kai! Kai! Kai!!. Daman haka mu ke da kyawawa ?an mata a garin Yola kamar haka?. Jamila aikin ki yana yin kyau."

Ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Godiya nake yallaSai."

Ya murmusa ya ce, "ku zauna ?an mata adon gari."

Suka zauna gabaWayansu, ya bi su da kallo yana murmushi.

Kafin ya kalli Jamila ya ce, "waWanan sun yi."

Ta Wan rusuna ta ce, "Godiya nake yallaSai."

"Ina fatan komai daidai."

"Komai daidai yallaSai, komai zai tafi yadda ake so. Dukkansu babu matsala, na yarda dasu Wari bisa Wari."

Ya kalle su ya ce, "ai daga ganinsu, wayayyu ne basu da duhun kai. Kuna ji ?an mata?."

Duk suka kalle sa, ya gyara zama ya ce, "Za a kai ku inda zaku samu cigaban rayuwa. Yin karatu a babbar makaranta, hawa mota, ri?e waya mai tsada, kwana a waje mai kyau, da komai za ku zamu. Abinda mu ke so da ku, bama son yawan surutu, ku yi shiru da bakunan ku. Ba ku da iyayen da zasu takura mu ku, abinda ku ke so shi za ku yi."

Jamila ta ce, "in ku ka yi haka, za ku samu abinda baku taSa tunani ba. Fita ?asar waje, da komai ma za ku samu. Kun amince?."

Dukkansu suka Waga kai alamun sun amince. Ya yi murmushi ya ce, "ku shiga ciki, akwai mai dafa abinci, ku faWa mata duk abinda ku ke so za a yi mu ku. Akwai driver a waje, in kuna ?waWayin kayan ciye-ciye duk za a baku."? Suka mi?e suka shiga inda ya nuna musu, ya bisu da kallo yana murmusui har suka Sace.

Ya kalle ta ya ce, "ba a taSa samu team mai kyau kamar wannan ba, kin yi haWi yadda ya kamata. Kuma da alama dukkansu lafiyayyu ne, za a samu abinda ake so."

DaWi ya kamata, ta ce, "sai da na zauna sannan na zaSa, na fiddo su."

Ya ce, "na san za ki iya. Amma ina yarinyar nan da na gani?."

Ta Wan sauke numfashi sannan ta ce, "Hafsa ko?."

Ya Waga kai ya ce, "ita. Ai na faWa miki ina so a haWo da ita, wannan da kaina zan ajjiyeta ba wani wajen zan kai ta ba."

"Hafsa da Zainab bana son taSa su ko kaWan, saboda yaran nan sune na hannun daman Islaha."

Ya bita da kallon mamaki ya ce, "Islaha kuma, ba mun gama da case Winta ba?."

"Mun gama YallaSai, amma ita bata gama damu ba. Daga ranar da ta buWe ido babu Waya daga cikinsu, zata fara yi mana shige da fice a kan lamarinmu. A haka ma dan muna da maganinta a hannu ne, da ba mu san irin Sarnar da zata yi mana ba."

"Wai wacece Islahan nan da mu ka kasa ganin bayanta?."

"Mun yi nasara yallaSai, tunda ta bar gidan nan da jimawa. Barinta gidan shine ya dakusar da ita, har yanzu bata da hujja akan abinda mu ke aikatawa. Iya wannan ma nasara ce."

Ya Wan gyaWa kai ya ce, "A kashe ta mana, meye amfaninta?."

Ta yi murmushi ta ce, "ka bar komai a hannuna, indai ina da rai bata isa ta yi wani motsi ban saka ?afa na fyaWe ta ba. Ai bata isa ta yi wani abu na zuba mata ido ba."

"Na yarda dake Jamila, tunda muka fara harkar nan bamu samu matsala ba. Amma ina so ko ta wacce hanya Hafsa ta zo gidan nan, na yi miki al?awarin mota, da kuWi naira miliyan biyar, da kujerar hajj. bana. Amma in kin kawo min Hafsa kenan."

Ta yi dariya ta ce, "Wallahil azim, ka ji rantsuwar musulmai ko? Islaha ko ita ta haifi Hafsa sai na kawo maka ita, sai ka yi shagalinka da ita yadda ka ke so. Bata isa ta yi komai ba, babu abinda ta isa ta saka ko ta hana."

Ya yi dariya ya ce, "Idon naira, wato tunda na yi al?awari za ki iya."

Ta yi dariya ta ce, "YallaSai babu abinda kuWi ba sa sakawa."

Ya Waga kai ya ce, "wannan karo, baza mu fitar da yaran nan ba, a nan ?asar zamu rabasu. An Wan samu tangarWa akan fitarsu ?asar waje, tunda akwai mutanenmu a nan da suke da kuWi a hannu zamu fanshe komai."

"Babu komai yallaSai, amma kar a barsu a Adamawa ko kusa da Adamawa."

"Haba Jamila, na san abinda nake yi fa."

Ta yi masa jinjina ta ce, "tuba nake yi, matsala ce bana so."

Ya Waga kai ya ce, "na fi ki gudunta."

"YallaSai kowa da Sangarensa, in ka duba yaran nan a hannun mu suke, binciken farko ta kaimu za a fara."

"Na ji. Ki je kawai, ki shirya min haWuwa da Hafsa. Su kuma waWanan, in anjima ko wacce zata san makomarta" ya faWa yana mi?ewa.

itama ta mi?e ta ce, "an gama ranka ya daWe. Amma ina so a bani aron yaran nan mu tattauna." Ya nuna mata hanya alamun ta je, ta ce, "godiya nake."

Tana shiga ta kalle su ta ce, "Kyawawana, ku ri?e amana a duk inda aka kai ku, ban da sata, gulma, ko yiwa babban mutum video da waya. In aka kama Waya daga cikin ku da irin wannan laifin, za a Waure sa ne. In ku ka kwantar da kai, ?asar waje sai ta zamar mu ku wajen zuwa ko yaushe."

?aya daga ciki ta ce, "Baza ki taSa samun mu, da irin wannan abubuwan ba."

Ta yi dariya ta yi musu jinjina ta ce, "sai mun yi waya" ta faWa tana fita..

*****

Tunda ta koma Sangarenta take kuka, ta dafe kai tana zubar da hawaye zuciyarta duk babu daWi.

Bata san me ta yiwa dangin mijinta da basa sonta ba, kawai dan ta kasance ba yarensu ba, dan ta kasance ba ?ar ?asarsu ba, shikenan kowa ba ya sonta?.

Ba ita ta bawa Rehaan Waukaka ba, ba itace take sakawa ya zauna a ?asar waje ba, ta fi kowa son ganinsa a kusa da ita. Amma da an tashi magana, duk laifinsa sai a juye ya dawo kanta gabaWaya.

Babu mai kaunarta a cikin gidan sai Janan, wacce ta kasance age mate Win Riyya. Bayan ita babu wani, sai a fi sati Waya wani yaron gidan bai shigo inda take ba. Sun tsame ta daga gidan, sun mayar da ita kamar annoba.

A lokacin Riyya ta shigo, ganin tana kuka sai ta ?araso da sauri ta ce, "Mamy me ya faru, meyasa ki ke kuka?" Ta faWa tana zama a kusa da ita hankali a tashe.

Ta sake cewa, "Mamy lafiya?."

Bata ce komai ba, ta goge idanunta ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kira min Rehaan a waya."

Ba musu ta Wauki waya ta kira number sa ta ?asar uk amma bata shiga.

Ta kalli Mamy ta ce, "wayarsa bata shiga."

Mamy zata yi magana aka shigo Wakin da sallama.

A tare suka amsa, suna kallon wanda ya shigo Wakin. Riyya ganin Abba ne sai ta mi?e tana kallonsa, ba kasafai aka cika ganinsa a Sangaren matansa ba, sai abu mai mahimmaci musamman rashin lafiya.

Riyya tunda ta gansa, ta san an Satawa Mamy rai a wajen meeting, shine ya biyo ta ya rarrashe ta.

Riyya ta ce, "Abba sannu da zuwa."

Ya kalle ta ya ce, "ina Banisha?."


"Ta yi? bacci." Kai ya Waga Riyya kawai, ta fita daga Wakin ta basu waje.

Abba ya sauke numfashi yana kallom matarsa da take zubar da hawaye har lokacin, kanta yana ?asa bata Wago ba.

Ya Wan gyara tsayuwa ya ce, "NADIRA!."

Bata Wago ta kalle sa ba sai goge idanunta da take yi, ya san an Sata mata rai ne, hakan ya saka ya tako yazo inda take ya zauna.

Ya ri?e hannunta ya ce, "wannan kukan bashi da amfani, kin san bazan ja da hukuncin Daada a gidan nan ba. Kuma ba laifi bane da an ce Rehaan ya dawo gida."

Cikin harshen hindi, da take yi masa magana dashi ta ce, "Amma ka san duk lokacin da Rehaan ya dawo nigeria sai wani abun ya same sa ko? Ka san ba ya taSa zama lafiya indai ya saka ?afarsa a cikin ?asar nan. Meyasa ake so ya dawo gabaWaya, a manta a can yake aiki da kasuwancinsa?. In ya bar komai na sa ya dawo nan kenan ya ha?ura da komai?. Ka san bana son wani abu ya samu Rehaan, bana so ko kaWan."

Ya sauke numfashi bayan ya gama jin abinda ta ce. Duk da ba da yarensa ta yi magana ba, amma a zaman da suka yi ya iya yarenta sosai. Kamar yadda ta iya fulfulde da hausa. Yana fahimtar duk abinda ta ce, yadda ta yi maganar ya san abin yana taSa mata zuciya.

Ya san macece da take da son ?a?anta, bata so ta ga wani abu ya same su. Hakan yana daga cikin dalilin ?inta da Daada take yi, takance bata da fulako da yakana, su fulani ba haka suke nuna tsantsar son yara ba, suna Soyewa. Mamy kuwa bata san Soye son Wanta ba, a gaban kowa take nuna masa soyayyar da iyaye suke nunawa yaransu.?

"Nadira kin san dole gidan nan, shiyasa nake fWa miki zamansa a England bazai yu ba. Dole ya dawo nan ya cigaba da zama kamar sauran ?an uwansa."

"Kasuwancinsa fa? Ka san acan yake yin komai. In ban da yanzu, da ya kawo shopping mall da hospital nan ba, da bashi da komai a nan."

"Zai iya yi daga nan, ba sai a can ba. Muna zamanin da kana zaune daga gida zaka yi meeting, karatu, aika sa?o da komai da komai. Kasuwancinsa bazai dakushe dan ya dawo ba. Aiki da ki ke zance ke kan ki kin san ba yi yake yi ba, sai dai in ya samu contract da wata ?asa ya je ya gama ya dawo. Bai Wauki karatunsa na likitanci da mahimmaci ba, ya fi mayar da hankali akan kasuwanci."

Ya yi murmushi ya fuskance ta sosai, tare da ri?e Waya hannunta ya ce, "Nadira!."

Ya Wago da fusksrta yana kallon kyakykyawar fuskarta ya ce, "na yi miki al?awari, a wannan karo babu abinda zai samu Rehaan, ko da ya yi ciwon da ya saba baza a Wauki lokaci ba zai samu lafiya. Aiki kuma zai cigaba da aikinsa a nan, tunda kin san ya fi mayar da hankali akan aikin in ya zo nan. Harkokin kasuwancina da nasa da suke a ?asar da zai bari, za a cigaba da kula da komai daga nan. Don Allah kar ki samu damuwa, kin ji?."

Ta Waga kai alamun to, ta ce, "Ni daman ba damuwa nake yi akan zuwansa ba, gidansu ne, komai daWewa dole ya dawo. Kawai rashin sakewar da ba ya yi ne bana so, ga kuma yawan ciwon cikin nan na sa."

"Babu abinda zai faru in sha Allah."

"Allah ya sa."

"Amin. Rehaan yana da wacce yake so ya aura ne?."

Ta Wago ta kalle sa tare da girgiza kai, sannan ta ce, "bai taSa bani labari akan hakan ba, sai dai ko yanzu."

Abba ya yi shiru yana kallon ta, sai ta ce, "Daada ta ce ya yi aure ne?."

Ya Waga mata kai ya ce, "ta ce a haWa da aurensu Riyya."

Ta Wan buWe ido ta ce, "Riyya! Bikin Riyya ai ya kusa, har yaushe ya dawo da aka haWa aurensu lokaci Waya?."

Ya Waga kai ya ce, "hakan za a yi Nadira. Za a san abinda ya kamata ayi."

"Ka zaSar masa matar ne?."

"A'a, ke kina da zaSi ne?."

"ko na faWa ma baza a amince ba, baza a so na sake Wauko hindi na kawo cikin fulani ba. Bani da zaSi" ta faWa a sanyaye.

Abba ya girgiza kai ya ce, "is okay, mu jira ya dawo, wata?ila yana da wacce yake so."

Mamy ta ce, "ina so in je gida, na jima ban je canja."

Ya mi?e tsaye yana cewa, "zaki je, amma ba yanzu ba Nadira. Ina jiran zuwa ki, ki kawo min tea" ya faWa yana fita daga Wakin. Mamy ta dafe kai tana tunani.

Tunaninta Waya wacce mata kuma za a zaSa masa a cikin gaggawa haka? Ita fa bata son a aura masa wacce ba ya so, kuma bata so a aura masa wacce zata so shi dan kuWi ko dan kyau. Shiyasa ta fi so ta zaSa masa mata da kanta, amma ta san baza a taSa bata dama ba.

Ko wacece wacce za a zaSa masa, matu?ar baya sonta itama baza ta taSa sonta ba har abada. Abinda Rehaan yake so shi take so, zaSinsa shine zaSinta. Ta sauke numfashi, ta mi?e ta shiga banWaki cikin tunani.

?angaren Daada Mama Saddi?a ta nufa da sassarfa, ta shiga da sallama ta same a yadda suka bar ta.

Ta zauna a ?asa ce, "Barka da hutawa."

Daada ta ce, "Yauwa Saddi?a. Ya ki ke ganin abubuwa za su tafi? Ina so a haWa auren Juwairiyya da Muhammad a lokaci Waya, kuma bana son wani hayaniya, da kaina nake so na zaSa masa matar aure."

Gaban Mama ya faWi, jin kalmar Rehaan zai yi aure, gumi ya keto mata a goshi, ta share gumin ta ce, "Duk yadda ki ka yi daidai ne."


"Kina da matar da ki ke ganin ta cancanci ya aure ta?."

Da sauri ta Wago ta kalle ta, ta Wan yi dariya ta ce, "Hajiya Daada ni kuma, ni zan zaSawa Rehaan mata?. In Nadira tana da rai ai bani da wannan ikon."

"Ni ke na zaSa, kuma ke nake so ki zaSar masa matar aure, amma in kina da ita."

Mama ta yi murmushi ta ce, "abinda ki ka ce daidai ne Daada. ?an mata masu tarbiyya ai baza mu rasa ba, zan bincika in sha Allah."

Daada ta ce, "kar ki samo wata a cikin jikokin abokan zamana. Kar ku ga na amince da auren Juwairiyya da Jaafar, a Wauka za a amince da Wan wanda bani na haifa ba. Ki yi yi tunani mai kyau, ko a danginki ne ki samo masa. Jinin fulani, mai tarbiyya, mai kyau, wacce zata zauna dashi tsakani da Allah."

Ta yi murmushi ta ce, "in sha Allah Daada, za a yi."

"Tashi ki je. Saboda yanayin lokaci, ki yi gaggawar nemowa."

"Ki huta lafiya" ta fada tana fita zuwa Sangaren ta da sauri.

Tana shiga ta cire hijjab Win jikinta ta cillar, yaranta da suke zaune, suka kalle ta. Kafin su yi magana ta ce, "Rehaan! Wannna yaro ya tsaya min a zuciyata."

Babban Wanta mai suna Zayyad, wanda suke kira da Hamma Zayyad ya mi?e tsaye ya ce, "Mama wani abun ne ya faru?."

Ta juyo ta ce, "Aure! aure Daada take so ya yi. Ta ya zamu bari Rehaan ya yi aure? Da zarar ya yi aure ya haihu shikenan mun shiga uku, komai ya sake lalacewa."

Sameer ya mi?e tsaye ya ce, "Dole mu hana auren nan Mama, in Rehaan ya yi aure a wannna lokacin da yake samun Waukaka akwai matsala."

Mama ta dafe kai ta ce, "Nadira kin cuce ni, kin lalata min shirin da na shekara talatin da biyar ina yi. Yanzu meye abin yi?."

Adda Zuhra da take cikinsu ta ce, "Yaushe ne auren?."

"Ni ta bawa zaSi na nemo matar da zai aura."

"Shikenan faWuwa tazo daidai da zama. Ina Sajida."

Mama ta kalle ta ta ce, "Sajida! Wacce sajidar?."

"Sajida ?ar ?awar ki mana."

"Baki da hankali, a wannan Waukakar da Rehaan yake samu zan bari ya auri Sajida? In ta aure shi ta kere ki fa kenan. Domin Rehaan ya ninka mijinki kuWi, sau babu adadi. Babu yadda za a yi na Wauko ?ar ?awata da kaina, na bata wanda ya fi mijin ?ata Waukaka. Ko labari na ji za a yi, zan shiga na fita na dakusar da auren, balle ni da kaina."

"Inaaa! Har abada wallahi. Ke ko ?anwata da muke ciki Waya, da tana da ?a mace, bazan Wauki ?arta na bawa Rehaan ba. Ke ko ita kanta ?anwar tawa, wallahi bazan iya bari ta auri Rehaan ba. Komai a Wakina nake so ya tare, bana so Waukaka ta tsallake ni ta je wani waje."

Zuhra zata yi magana ta dakatar da ita, cikin fusata ta ce, "ya isa malama, ki bar batun nan bazan amince ba. Babu ta yadda za a yi in bari ta auri mijin da yafi na ki kuWi. Rehaan ga kyau, ga kuWi, ga iko, ga farin jini, ga Waukaka. Ba iya nigeria ba, a kaf ?asashen ?etare babu inda Rehaan bashi da alfarma. A hakan zan bari wata wacce ta raSe ni ta same sa?. Da dai ace akwai aure a tskaninku ne, ko ba ya so sai ya auri Janan wallahi."

Zuhra ta ce, "Kamata ya yi mu zauna ayi magana sosai akan hakan, yanzu dare yana yi."

Sameer ya ce, "Mama ya kamata a san abinda za ayi in, in ba haka ba wallahi muna gani komai zai fi ?arfin mu."

Zayyad ya girgiza kai ya ce, "To ku ?yale Rehaan Win mana, shekara nawa ana wahala a kansa an kasa samun nasara?."

Mama ta kalle sa cike da harara, ta ce, "babban banza, a haka zaka ?are ai. Ina kishinku amma kai kana zuba min ?asa a ido, dama Sameer ko Zubair ne babba ba kai ba."

Ya yi murmushi, bai ce komai ba ya fita.

Mama ta dafe kai ta ce, "innalilahi! Na auri mutum tun yana saurayi, amma saboda tsafi irin na ?an india tana shigowa rayuwarmu ta tarwatsa komai. Ni da nake da ku mu ne manya a gidan nan, amma itace take ri?e da gidan."

Zuhra ta ce, "gabaWaya sunan Abba ya Sata, sunansa ake ambato. Ko ni, in aka ganni sai ace ga ?anwar Rehaan Yola."

Mama ta dafe kai, ta girgiza kai ta ce, "mu zuba mu gani. Sai na dakusar da wannan Waukakar wallahi. Ina zuwa" ta faWa tana shiga Waki da gaggawa.

*****

"Rehaan yana gab da shigowa nigeria, kana da labari?."

Wanda yake zaune a gefensa, ya girgiza kai ya ce, "bani da labari, sai yanzu."

Shima ya zauna yana girgiza kai sannan ya ce, "na sanar da kai yanzu, duk yadda za a yi a wannan lokacin ayi. Kar a saSa saiti, a tabbatar da Rehaan ya daina numfashi. Barinsa duniya kaWai, shine zai zama silar Wagawarmu. Matu?ar yana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login