Showing 66001 words to 69000 words out of 96103 words

Chapter 23 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

59

ba, ban taSa ?o?arin kashe sa ba. To waye yake son ganin bayansa? Kenan akwai wani bayan ni kenan a cikin gidan nan."

Babu mai bata amsa haka ta gaji ta mi?e ta shiga Waki tana tunanin waye wannan da yake so ya kashe Rehaan kai tsaye haka?.

? ? ?? Washe gari.

Islaha da wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya, duk da bata da aiki amma tana son fita shiyasa ta shirya da wuri dan taje ta dawo kasancewar ranar juma'a ce.

Tana fitowa Falo suka haWu da Hanan, bata ce mata komai ba itama bata ce ba, ta raSa ta gefenta zata wuce Hanan ta ce, "ke ji mana."

Islaha ta yi banza bata kula ta ba, ta shiga kitchen ta fito da ruwa a hannunta tana sha.

Hanan ta ?arasa inda take ta ce, "ba magana nake yi miki ba?."

Islaha ta share ta bata ce komai ba, dan bata da lokacin sauraren shirmen Hanan.

Hanan ta ce, "ke ragowar gidan marayu dake nake magana."

Islaha bata tanka ba, ta yi shiru ta cigaba da abinda take yi bata kula ta ba.

Hanan ta girgiza kai ta cec "lallai baki da kirki wallahi, lallai baki da mutunci. Ina yi miki magana kina yi min banza, Wacece ke?."

Nan ma bata kula ta ba, Islaha ta yi niyar barin wajan Hanan ta jawo ta da ?arfi.? Ta ce, "ina magana kina tafiya?."

Islaha ta kalle ta ta ce, "au dani ki ke? Sorry fa, na yi tunanin haukan na ki ne ya tashi."

"Kut! Ni ki ke cewa mahaukaciya?" Ta faWa tana kai mata mari.

Islaha ta ri?e hannunta ta ce, "kar ki kuskura, matar Yayanki ce ni ko bakya so, dole ki yi min biyayya kamar yadda ki ke yi masa. Wallahi in ki ka sake ko da wasa hannunki ya je jikina da niyar duka, daga ranar zaki fara danasanin sanin wacece Islaha a rayuwarki."

Hanan ta fizge hannunta ta ce, "in na mare ki Win uban me zaki yi?."

"Ki gwada ki gani, na rantse da girman Allah in ki ka sake Waga hannu zaki mare ni sai na saSa miki kammani."

Hanan ta girgiza kai ta ce, "lallai baki da kunya, baki da mutunci wallahi. A gidan ubana, a gidan da aka haife ni zaki kalle ki ce zaki saSawa kamanni?."

Islaha zare mata ido, cike da tsiwa ta ce, "a gidan uban naki, ki gwada ki gani, ni kuma sai na baki mamaki ba."

"Baffa ki ke zagi dan baki da mutunci?."

Islaha ta harare ta bata ce komai ba, zata bar wajan ta ji Mama ta ce, "bar ta Hanan, sai ta zagi Baffa sannan zata nuna mana ita Win ba ?arsa ba ce, tsintacciya ce, daga gidan marayu aka kawo mana wahala."

Islaha ta kalli Mama ta ce, "Mama ban zagi Baffa ba, bazan taSa iya zaginsa ba har abada."

"Da ban ji ki da kunnen ba, da sai ki ce baki yi ba, na ji lokacin da ki ka zage sa. Kuma tsaf zaki aikata, dan ba tarbiyya ce ta ishe ki ba."

Zuciyar Islaha ta zo wuya, ta fusata sosai, duk da tana ?o?arin Soyewa amma sai da ta kasa ta ce, "ni ban zagesa ba, in na yi bazan ?i faWa ba."

Mama ta ce, "?arya nake yi kenan?."

"A'a, ban ce ba."

Hanan ta ce, "zata iya faWa ai, ba tarbiyya ce da ita ba."

Islaha ta kalli Hanan ta ce, "ba dake nake magana ba, ki daina saka min baki. Rashin tarbiyya ya biyo bayan ki, in har ni bani da tarbiya ke ban san me za a ce miki."

Mama ta fara tafa hannu tana ?arasowa wajan ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Islaha rashin mutuncin naki har ya kai haka? Ni ki ke kallo kina cewa rashin tarbiyya ya biyo bayan ahlina?. Kenan nima bani da tarbiyyar ko?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Hanan ta ce, "Mama in ban koyawa yarinyar nan hankali ba bazan ji daWi ba wallahi."

Kafin Islaha ta yi zato ta ji mari akan fuskarta, ai kuwa kafin Hanan ta sauke hannu itama ta sauke mata maruka har biyu.

Islaha ta nuna ta da yatsa ta ce, "ai na faWa miki, in ki ka sake gangancin Waga hannu ki mare ni wallahi sai kin yi danasani. Na faWa baki da tarbiyya, ki yi duk abinda za ki yi."

Mama ta fusata ta nufi Islaha zata dake ta ta bar waja da sauri, dan bazata tsaya a daki banza ba, tunda ba iya ramawa zata yi ba.

Hanan tana dafe da kuncinta ta ce, "na rantse da Allah yau sai na ci ubanki a gidan nan" ta faWa tana nufo islaha zata kamo ta.

Islaha ta bar wajan da sauri. Ta ce, "Hanan kar ki yi gangancin taSa ni, za ki yi danasani mai yawa."

A lokacin Saheer ya buWe ?ofa ya shigo falon da sallama yana kallon su.

Mama ta nuna sa da yatsa ta ce, "sai yarinyar nan ta bar gidan nan dan ubanta, ai ba gidan ubanta bane ba ko? To yau sai ta barsa. Kuma indai ni na haife ka baza ka taSa zama da ita a matsayim mata ba! Babu aure a tsakaninka da ita har abada!" Ta faWa a fusace tana kallon sa.

Saheer ya kalli Islaha sannan ya kalli Mama ya ce, "Mama me ya faru?."

"Ka tambayi ?ar iskar da take kusa da kai, sannan ku bar min gida kafin na aikata abinda zai shafe ka."

Islaha ta ce, "Mama ki yi ha?uri, ni ba dake nake ba, da Hanan nake. Zan jure duk abinda za ki yi min bazan tanka miki ba, saboda matsayin uwa ki ke a gare ni. Amma Hanan ko Labiba bazan ?yalesu ba wallahi, duk abinda suka yi min daidai nake dasu."

"Nima daidai nake dake dan ubanki, shegiya mai zubin karuwai. Har ni zaki kalla ki cewa Hanan da Labiba basu su yi miki ki ?yale ba? Ba dai kina ta?ama zaki auri Yayansu bane shiyasa ko? To na soke auren,? matu?ar ni na haifesa bazai aure ki ba!"

Saheer ya ce, "don Allah ki yi ha?uri Mama. Ke Islaha ki bata ha?uri" ya faWa yana kallon Islaha.

Mama ta ce, "ha?urinta Win banza da wofi, mai ha?urinta zai yi min? Ta gama ci min mutunci da zagina ka ce ta bani ha?uri, wato ta yiwa banza ko?."

Ya yi shiru bai ce komai ba, ta nuna Hanan ta ce, "Wallahi indai tana son cigaba da zaman gidan nan sai ta dur?usa ta bawa Hanan ha?uri, in ba haka ba in ta fita kar ta sake dawo min gida. Ai ba da kuWin babar ta aka gina gidan ba."

"TabWi! Ashe na bar zaman gidan nan kenan har abada, da na bawa Hanan ha?uri gwara na kwana babu ci babu sha!" Ta faWa ba tare da ta san a fili ta yi maganar ba.

Mama ta sake fusata ta ce, "to fita dan uban babanki, fita dan uwarki. Ai ba gidan ubanki bane ko? To fita ki bani waje!."

Saheer ya ce, "Don Allah Mam ki kwantar da hankalin ki, ki yi ha?uri...."

Ta katse sa ta ce, "Wallahi sai ta fita, wallahi yau sai ta bar gidan nan, ai ba gidansu bane!."

Islaha ta ce, "ki yi ha?uri Mama."

Ta faWa tana wuce Waki ta Wauko handbag Winta da wasu kaya ?alilan ta fito ta fita daga falon, dan itama zamam gidan ya fita daga ranta, daman ha?uri take yi, to yanzu ha?urin nata ya zo ?arshe.

Saheer ya bita da kallo, ya kalli Mama ya ce, "ki kwnatar da hankain ki Mama, don Allah ki nutsu."

Mama ta harare sa ta ce, "bazan nutsu Win ba, daman ba ?aunarta nake yi ba, yanzu kuma ta bar gidan, sai ta je ta ?arata, aure tsakaninku babu. In ka ga anyi auren nan bani da rai, amma matu?ar ina da rai baza ka aure ta."

Ganin ta fusata da yawa sai ya juya ya fito da niyar ta huce yaje ya bata ha?uri, ya biyo bayan Islaha da hanzari dan bai san inda zata tafi ba, yana bu?atar tsayar da ita da gaggawa....

Book 2&3 1k on telegram.

Nana Haleemad'?
'
*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ? ? ?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 018.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

_____________


A ?ofar gidansu Safeera ya hange ta a tsaye ta harWe hannu a ?irji ta jingina da bango. Kana ganinta ka san a sama take, ?iris take jira ta fara sauke faWa da masifar da suke bayyane akan fuskarta.

Ya ?arasa wajen yana kallon yadda fuskar ta take a Waure, ta kawar da kai gefe bata bari sun haWa ido ba.

Ya ce, "Islaha meyasa za ki yi haka? Meyasa baza ki jure mu cigaba da lallaSawa kafin Allah ya raba mu ba, meyasa za ki biyewa Hanan? Meyasa Islaha!?."

Ganin ya fara yi mata magana cikin faWa, sai ta yi masa kallon kallon up and down ta ce, "ni fa ban biye mata ba, ta yi min magana yafi sau uku ban kulata ba, da kanta ta jawo ni. Ta ce min karuwa na yi shiru, ta ce mara tarbiyya na yi shiru na ?yaleta, kawai sai ta jawo ni wai zata mare ni."

"Amma da kin sani baki kula ta ba, yanzu gashi Mama tace kin yi mata rashin kunya."

"Marina ta yi na rama, ta ce min mara tarbiyya na ce itace mara tarbiyya ba ni ba. Kuma na bawa Mama ha?uri ai."

"Yanzu ya ki ke so ayi? Ina ki ke so ki je?."

"Dan ni marainiya ce na tashi a orphanage, ba hakan yana nufin zan rasa inda zan je ba, dan suna ganin kamar gidansu ne kawai mafakata, shiyasa suke yi min abinda suka ga dama. Daman nima na gaji da zaman gidan, kafi kowa sanin ha?uri nake yi."

Ya Wan yi tsaki ya ce, "kin Sata komai Islaha, meyasa zaki biye mata don Allah?. Ran Mama ya Saci sosai, kuma bai kamata a gabanta ki dinga faWar kalaman da ki ka faWa ba. Sannan da kin bawa Hanan ha?urin da ba a wuce wajan ba?."

Ta Wan buWe tana kallonsa, ta girgiza kanta ta ce, "Wallahi bazan bawa Hanan ha?uri ba, dan ina cin arzu?i a gidansu bazai yu ta taka ni na ?yale ta ba. Mama kuma na bata ha?uri, ko babu kai bazan iya yiwa Mama rashin kunya ba, saboda ta haife ni, balle akwai ka a tsakani. Duk jurewar da nake yi baka gani ba? Dan yau kawai na tanka shine abin zai zama laifina Hamma?."

Kafin ya yi magana ta ce, "shikenan, ka ?yale ni zan je na nemi wajan zama kawai, bazan sake zama a gidanku ba."

Ya dafe kai jin ya taSo ta ya ce, "ba laifinki na gani ba Islaha..." ta katse sa cikin faWa, tana kuka har ta manta waye a gabanta.

Ta ce, "to me ka ke nufi? Ka san irin abubuwna da ake yi min a gidan, duk bana Waga kai na kalla, ba dan an fi ?arfina ba, sai dan alfarma nake ci a gidansu. Dan yau an kaini bango na rama shine sai ya zama laifina?. Shikenan mu da muka tashi a gidan marayu bamu da tarbiyya kenan, kowa kallon mu yake a matsayin waWanda aka haifa aka cillar, wasu ne suka tsinta suka kai mu gidan maryu, ko kuma ni ce mara tarbiyyar a cikin gidan?. Dan a can na tashi hakan yana nufin iyayena suka yar dani, kenan ni ba ?ar halak ba ce?."

"Haka aka ce musu duk wanda ya girma a gidan marayu bata hanyar aure aka haifesa? Ko kuma duk wanda ya tashi a cikin gidan yar dashi aka yi?."

"Kullum sai sun ce min karuwa, me na aikata da yake nuna ni karuwa ce?. Ha?uri nake ina cigaba da zama a gidan saboda kai da Baffa, ba wai dan na rasa inda zan je bane. Ina da abokan arzu?i da yawa, wanda zasu iya ri?e ni har abada, ina da wanda zasu jiSanci lamarina babu gori balle cin fuska. Bazan sake komawa ba, nima na gaji da wula?ancin dake yi min. Tunda Mama ta ce baza ka aure ni ba shikenan, zan je na cigaba da rayuwata yadda nake so!" Ta faWa cikin kuka cike da tsiwa da fusata.

Saheer ya sauke numfashi yana kallon hanya, ya sassauta murya ya ce, "ki yi ha?uri, kin ga a akan hanya mu ke. Ki zo mu je na kaiki gidan Adda Sa'ida."


"Bazan je ba, zan je in kama hotel kafin na samu inda zani."

"Sai kin je Islaha. Ki jira in karSo motar Sadik nazo na kai ki, kar ki motsa daga wajan nan, ki jira ni" ya faWa yana juya ya bar mata wajan da sauri.

A lokacin Safeera ta fito daga gidan, fuskar ta babu walwala ko kaWan.

Suka haWa ido Islaha, islaha ta goge ido ta ce, "Safeera lafiya?."

Safeera ta sauke numfashi ta ce, "ba lafiya ba Islaha, ina cikin damuwa. Jiya ko bacci ban yi ba."

"Me ya faru? Kin ga yadda ki ka canja kuwa? GabaWaya kin koma wani iri kamar ba ke ba."

"Za ki raka ni Katsina?."

Da mamaki ta ce, "Katsina kuma, Wajan wa?."

"Dangin Umma, ?arar Umma zan kai musu."

Islaha da mamaki ta ce, "kamar ya ?arar Umma?."

Safeera zata yi magana suka ji horn Win mota, suka kalli wajan a tare.

Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "in kin shirya mu wuce."

Ta Waga kai ta ce, "mu je." Suka ?arasa wajam motar suka shiga.

Ba yabo ba fallasa Safeera ta gaisa da Saheer, daga yadda suka gaisa ya san bata yanayi mai daWi, bai tambaye ta ba suka cigaba da tafiya.

Islaha ta ce, "ka kaimu wajan aiki kawai, in mun dawo sai na wuce gidan Adda Sa'idan."

Ya bita da kallo ya ce, "baki da aiki yau ko?."

"Eh, zan je kawai"

"gwara mu je yanzun kawai."

"ba sai mun je ba, kawai mu wuce wajan aiki."

Ya sake kallonta, ganin fuskarta a Waure alamun tana cikin Sacin rai, ya Wan Wauke ido bai ce komai ba ya cigaba da tafiya.

Sai da ya tsayar da motar sannan juyo yana kallonta, softly ya ce, "ki yi ha?uri, Wazu na yi miki faWa."

Ta sunkuyar da kai ?asa, dan in akwai abinda yake saurin karya mata zuciya bai wuce ya bata ha?uri ba. Sai ta ga babba dashi yana bata ha?uri, yana matsayi mai girma a rayuwarta ya dinga cewa ta yi ha?uri, duk sai ta ji ta damu.

Bata Wago ba ya ce, "ban yi miki faWa dan na saka ki kuka ko dan ranki ya Saci ba, ina so ki dinga ha?uri da komai na rayuwa, zaman gidanmu ya kusa ?arewa. Ba ina yin duk abinda nake yi dan baki da inda zaki zauna sai gidan namu ba, ke kin san waye ni, kin san zan iya sadaukar da komai saboda ke. Mama mahifiyata ce, yi mata biyayya dole ne a gare ni, duk abinda ta ce sai na bi koda bana so. In ta hau sama dole na bari ta sauka ?asa saboda uwata ce, sai ta yi sanyi zan bata ha?uri. Ki yi ha?uri!."

Ta Wago ta kalle sa ta ce, "ka daina bani ha?uri Hamma, komai ya wuce."

"Komai bai wuce ba Islaha, na san na Sata miki rai sosai da sosai. Ku je wajan aikin, in kun gama ki kira ni, zan zo in kai ki gidan Addan ki zauna kafin Mama ta huce."

Ta Waga kai ya ce, "kin cin abinci kuwa?."

Ta girgiza kai ta ce, "bana jin yunwa."

"Kwana biyu bakya son cin abinci, ko baki da lafiya?."

"lafiya lau nake, kawai bana jin daWi ne."

Ya Wan kalle ta sai ya Wauke kai dan ya gano abinda yake damunta, ya ce, "kin sha maganin da na baki jiya?."

Ta girgiza kai ta ce, "ba yanzu nake sha ba."

Ya Waga kai ya ce, "sannu. Ku je." A hankali suka buWe suka fita duka shiga ciki.

Islaha kai tsaye office Win Chairman ta wuce, tunda ta shiga yake tafa mata, ita kuma da yake bata da walwala ko murmushi bata yi ba ta zauna.

Ya ce, "good job Islaha, ina ji dake sosai. Saleem ya bani labarin komai, na ji daWi. Domin an tabbatar min indai ka haWu da Mr Jafar kamar ka ga Mr Rahaan ne."

Ta yi murmushi ta ce, "na gode Chairman."

"Ni zan yi miki godiya, ina jin daWin aiki dake sosai."

Ta yi murmushi bata ce komai ba. Ganin kamar bata cikin walwala sai ya ?yale ta tafi.

Record office ta tafi wajan safeera, ta same ta ita kaWai ta dafe kai cikin damuwa.

Islaha ta zauna ta ce, "Safeera faWa min, meye ya faru?."

Ta Wago ta kalle ta ta ce, "Islaha Umma ce take so na tafi ?asar waje aiki, da Baba ya hanani sai ta ce ita zata je. Islaha Umma tana i?irarin kashe aurenta ta tafi aiki ?asar waje."

Islaha ta zaro ido waje ta ce, "Umman!."

Safeera ta Waga kai ta ce, "jiya faWa suka dinga yi ita da Baba, yana faWa tana faWa. Tana cewa wallahi sai ta je sai dai ya sake ta, shi kuma ya ce indai ta tafi to babu aurensa a kanta."

Islaha ta cw, "innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Mun shiga uku."

"Islaha wallahi bacci kaWan na yi, da tunanim

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login