Showing 78001 words to 81000 words out of 96103 words

Chapter 27 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

71

kallo bata ?arasa ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta tayar da shafa'i da wutir.

Tana cikin yin sallah wata mata da take gefenta, wacce turaren ta ya cika masallacin da ?hamshi ta mi?e ta fita, sai wata daga gefe ta ma ta fita alamun tare suke.

Islaha ta kalli inda ta tashi, sai ta ga ta bar atm card Winta da key Win mota. Islaha ta mi?e ta Wauka ta zata fito, sai ga wacce ta fita daga baya ta dawo.

Ta kalli hannun Islaha, ta kalli fuskar ta ta ce, "asibitin nan dai ba a sata, daga fitar mu har kin Wauki abinda muka bari zaki gudu?."

Islaha ta kalli matar, babba ce dan ta haifi wanda suka girme mata ba ita ba. A lokacin Mamy ta dawo ta ce, "ba ki Wauko ba?."

Islaha ta kalli Mamy, dan ita da ta ganta a cikin masallacin bata yi tunanin tana jin hausa ba, tunda asibitin akwai fararen fata kala-kala, ta Wauka Mamy tana daga cikin wanda basa jin yaren nigeria. Gashi ta saka ba?ar a abaya, sai ta tashi kamar balarabiya.

?awar Mamy ta nuna Islaha ta ce, "har ta Wauke, ba ban dawo ba da baza mu ganta ba" ta faWa tana sake kallon Islaha. Ta yi tsaki ta ce, "a haka kamar yarinyar kirki, Sarauniya kawai."

Islaha ta Wan lumshe ido, bata jin daWin yanayinta ko kaWan, haka ta buWe ta ce, "ni ba Sarauniya bace, na Wauko dan na biyo ku na kawo muku, ba wai dan in sace ba" ta faWa tana mi?awa ?awar Mamy atm card Win da key Win motar.

Ta karSa tana kallon Islaha ta ce, "Sarauniya ce mana."

"In duniya zaki ajjiye, ban ga abin sacewa ba."

"rashin kunya za ki yi min? Kin san su waye a gabanki?."

"Ko su waye ku Win ina ruwana? Title Winku ne ba nawa ba, dan na taimaka na Wauko zan mi?o muku sai ya zama laifi?. In sace miki atm card da key Win mota in yi me dasu? Na yi miki kama da Sarauniya ne?."

Islaha ba da faWa take maganar ba, a hankali take magana, dan yanayin da take jin numfashinta bazai barta faWa ba, kuma dan taji haushin kalaman matar ne da baza ta saurare su ba.

?awar Mamy ta ce, "ni ki ke faWawa haka?."

Islaha ta ce, "in babba bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki bazai ji nauyi kayar dashi ba."

Mamy kallon Islaha take yi, duk da ba faWa take yi amma mamaki take bata. Bata ce komai ba ta gaji da tsayawa, ta karSi atm Win ta ce, "na tafi" ta faWa tana shiga asibitin ta bar ta wajen.

Islaha bata ce komai ba ta raSa ta zata wuce, ta hana Islaha wucewa ta ce, "kin san wacece ni?."

A ?ufule Islaha ta ce, "wacece ke?."

?awar Mamy mamaki ya hanata magana, Islaha ta ce, "don Allah ki ja girmanki, bana son yi miki abinda baza ki ji daWi ba. Kowa wacece ke wannan ke ya dama bani ba" ta faWa tana fita ta barta a wajen a tsaye tana kallonta.

Babban meeting room ne mai girma sosai, ya tsaru, ya yi kyau sosai. Ga babban table a tsakiya da kujeru, wanda zasu kai guda hamsin ko wanne da abar magana a gaban ko wacce kujera.

Ga tv mai girma da take kallon kowa, sannan ga dispenser da ruwa a kanta.

GabaWaya kujerun babu wanda babu wani a kai, suna zaune sun yi shiru ana jiran shigowarsa. Kowa ya san baza a tashi lafiya ba, dan ba ya Waukar kuskure, ba ya son kuskure ko kaWan. Gashi dai ba yawan zuwa asibitin yake yi ba, amma duk ranar da ya zo sai ya tafi hankalin kowa yake kwanciya saboda gudun kuskure.

Lokacin da ya buWe ?ofar ya shigo da sallama, duk sai da suka mi?e tsaye ana amsawa.

Sababbin staffs waWanda basu taSa ganinsa ido da ido ba ranar sun ganshi, kowa ya yi tsit ana jira ya ?araso.

Rehaan ya taka a hankali zuwa tsakiyar room Wim, sai ya tsaya ya jingina da bango yana kallonsu, kafin ya yi musu alamu da su zauna.

Duk suka zauna suka yi shiru, ya taka ya je inda kujerar zamansa take, ya zube hannayensa akan table Win ya Wan sunkuya kaWan yana bin kowa da ido. GabaWayansu sun nutsu, kowa da inda yake zaune, dan meeting ne ba iya na Dr's ba, har waWanda aka samu matsala ta Sangarensu.

Ray ta cikin loudspeker ya ce, "What caused the gas cylinder to explode?."

Suka yi shiru basu amsa ba, ya bisu da kallo one by one kafin ya ce, "Who is in charge of that section?

Ta mi?e a sanyaye ta ce, "ni ce Sir."

Ya bita da kallo kafin ya ce, "Explain to me, ya aka yi hakan ya faru?."

Ta Wan gyara tsayuwa ta ce, "Sir it's a mistake."

Ya Wan Wage gira sama ya ce, "mistake!."

Ta Wan girgiza kai ta ce, "yes Sir."

"Who told you akwai mistake a Sangaren lafiya?."

Ta yi shiru tana sunkuyar da kai bata ce komai ba, ya girgiza kai ya ce, "yaushe ki ka fara aiki a nan?."

Jikinta sai rawa yake yi ta ce, "last month."

Ya kalli Dr Abdul da ya yi shiru ya ce, "Why didn't you tell her that I don't tolerate mistakes here before you hired her? Didn't you give her the rules to read?."

Kafin ya ba sa amsa ya Waga masa hannu, ya kalle ta ya ce, "kin san dadin mutanen da suka samu attack, because of your mistake?."

"Im sorry Sir!."

Ya bita da kallo jin ta faWi kalmar da ya tsana a yayin kuskure, ya Wan ja numfashi ya ce, "sorry for what?."

Ta yi shiru bata amsa ba ya ce, "your mistake?."

Sai kuma ya girgiza kai ya kalli Abdul bai ce, komai ba ya mi?e tsaye sosai ya fara takawa zai fita. Sai kuma ya juyo ya ce, "ya aka yi wuta ta Wauke?."

Abdul ya ce, "duk matsalar daga fashewar gas Win ne." Bai ce komai ba ya taka ya fita.

Abdul ya kalle ta ya ce, "ki biyo ni office ki karSi suspension paper Winki, Allah ya taimake ki ma ya ga dama, da yau shine ?arshen aikinki wallahi."

Ya kalli kowa ya ce, "ku kiyaye kuskure in yana nan, daga yanzu har ya bar asibitin nan ku yi abinda zaku burge shi, in ba haka ba wallahi zai watsa kowa ya kawo wasu. Ba ya Waukar kuskure da ha?uri a Sangaren aiki, ku kula" yana faWa ya fita kowa ya fita.

A cikin Wakin ya tarar da Jazy da Mamy suna ta hira, ya tura ?ofar ya shiga da sallama, ya ?arasa ya zauna a kusa da ita.

Ta bishi da kallo ta ce, "ya jikin?."

Ya ce, "na ji sau?i Mamy."

Mamy ta kalli Jazy ta ce, "Yaushe zai bar nan ne?."

"Gobe in sha Allah."

Rehaan ya ce, "Mamy ki yarda na koma hotel, bana son komawa gida gabaWaya."

Ta Wora hannunta a fuskarsa ta ce, "kar ka damu, zan kasance a tare da kai ko yaushe."

Bai ce komai ba Mamy ta ce, "Da gaskiyar Daada, da ta ce ya kamata ka yi aure. Ya kamata ka samo macen da zata dinga kula min da kai."

Ya yi Wan murmushi ya yi ya kwantar da kansa a kafaWarta ya ce, "ba gaki nan ba, zaki kula dani."

"ba irin kulawa ta, irin ta mata da miji. Ya kama ta samo mata Rehaan."

"Ban san a ina zan samu ba."

Mamy ta ce, "ka buWe ido dakyau za ka gani, ga Jafar ya yi maka wayo."

"shi ?anwarsa ya gani, ni kuma bazan iya ganin ?anwata ba."

Mamy ta yi dariya ta ce, "Shima da farko haka ya ce, ra'ayinku Waya, dan yi magana ku ce baza ku iya aurwn ?anenku ba, amma daga baya ne ya susuce akan Riyya."

Bai ce komai ba sai murmushi da ya yi, itama ta yi murmushi. Jafar kuwa danna waya yake yi yana murmushi bai saka musu baki ba.

Rehaan kamar wanda aka tunawa wani abu, ya Wago ya kalli Jazy ya ce, "ina wayata?."

Bai yi musu ba ya basa wayar ya ce, "Saudi german was alert you, then Alma."

Rehaan ya karSa ya fara duba wayar, ya yi karo da uban messgaes na mutanen nigeria dana ?etare, ya duba wanda zai iya ya share sauran.

Ya shiga gmail Winsa nan ma ya ga abubuwa masu mahimmacin da dole sai ya amsa.

?an tsaki ya yi ya ajjiye wayar, sai kuma ya Wauki wayar ya Wan yi typing kaWan ya ajjiye.

Ya lumshe ido ya buWe a hankali, yana sake ganin fuskar Islaha a idanunsa. Haka kawai yake so ya nunawa yarinyar nan waye shi, yadda ko dan gaba zata kiyaye haWuwar su. Ba ya damuwa da maganar mutane a kansa, ko a gidansu in aka yi masa ba ya tsaya masa a rai balle har ya yi ?o?arin Waukar mataki. Amma ga wata yarinya a waje, wacce bai san wacece ba ta tsaya masa a rai, har yake jin yana so ya nuna mata kuskurenta akan hakan.

Islaha tana barin masallaci office Win Dr suka koma ita da Mama da Sadik. Suka samu likitan yana nan, suka shiga da sallama ya amsa ya ce, "ku nake shirin nema, ku yi ha?uri na shiga meeting na gaggawa ne."

Sadik ya ce, "babu matsala."

Dr ya ce, "ku zauna."

Suka zauna gabaWayansu, kafin ya kalle su ya ce, "an yiwa mara lafiyan ku gwaje-gwaje, an tabbatar mana da yana da matsalar ?oda, matsalar kuma ta yi girma dan ba ?ar kaWan ba ce ba. Amma an yi masa gwajin da zai fayyace mana yanayin da ciwon yake, wannan matsalar Waukewar wutar da aka samu ya jawo machine Win ya Wan samu matsala. Amma kafin awa biyu masu zuwa za a kawo wani, dan haka gobe da safe zan sanar da ku abinda ya kamata ayi."

Sadik ya ce, "shikenan Dr, mun gode sosai."

"Babu matsala, ku je gida, zuwa gobe in sha Allah za a yi komai."

Ba amsa masa suka taso suka fito sai da suka dawo reception. Mama ta ce, "Islaha ku koma gida, ni zan zauna a nan."

Sadik ya ce, "shikenan Mama, ina Labiba?."

"Ta tafi gida."

Sadik ya ce, "mu je na raka ki Wakin da aka ce za ki zauna" faWa yana kallon takardar da aka basa a recption inda za a raka wanda zai zauna.

A tare suka je Wakin, suka tarar da Wakuna ne masu bala'in kyau, babu abinda babu a cikinsa, kuma kawai wanda zai yi jinyar mara lafiya ne zai zauna a ciki. Koda za a samu dalilin da dole sai an nema ka, akwai ta inda za a same ka.

Islaha da Sadik da Adsa Sa'ida suka shiga mota, a lokacin Adda ta ce, "Anya asibitin nan bamu kawo kanmu gidan mutuwa ba? Kana ganin yadda tsarinsu yake kamar a turai, mutanen reception Win ma duk ba hausawa bane, ga likitocinsu ma. Ku duba inda aka kai Mama zata zauna, Anya kuwa zamu iya?."

Islaha ta ce, "Wallahi Adda nima jikina ya yi sanyi sosai, gashi basu faWa mana kuWin komai ba, da alama bill ake yi sai an gama za a faWa mana kuWin."

"Mun shiga uku, kar ace mana miliyoyi fa, a ina zamu samu?."

Sadik ya ce, "gaskiya da tsada kam, amma nan ne maganin matsalar mu, haka zamu yi ha?uri mu lallaSa ko kadara ce mu siyar. Lafiya ai tafi gaban komai."

Islaha ta ce, "haka ne. Amma don Allah koda zaku yi waya da Hamma kar ka faWa masa, ka ga zai tayar da hankalinsa ya ce zai dawo."

Adda ta ce, "gaskiya dai, kar ka faWa masa Sadik."

"Bazan faWa masa ba in sha Allah, ai bai kamata ya sani ba daga zuwan sa ba, gwara a Wan bari ya Wan huta sai ya sani daga baya." Suka yi shiru suna tafiya har suka sauke Adda a gidanta.

Islaha ta kalle sa ta ce, "Hamma Sadik in sha Allah zan nemi loan a bank Wiina in zasu bani, in yaso sai a dinga cire a albashina da kaWan kaWan. Lamarin ciwon nan yana bu?atar kuWi sosai."

Ya Waga kai ya ce, "shawara ce mai kyau wannan Islaha, amma ki bari goben mu ji abinda zasu ce, in yaso sai mu san abinda zamu yi."

Ta Waga kai ta ce, "Allah ya kaimu." Ya amsa da amin ya sauke ta a ?ofar gidan ya wuce gida ita kuma ta shiga.

*******

Tana zaune a office da waya a hannunta, tana magana cikim Sacin rai da ?unar zuciya,ta ce, "Yarinyar bata jin magana, bata daina bibiyar Zainab ba, Wazu an tabbatar min sun haWu da Zainab a wajen gidan nan. Kun ga, in ba mu Wauki mataki akan Islaha ba wallahi sai ta kai mu ?asa."

Da can Sangaren aka ce, "Wai me yarinyar take ta?ama dashi ne?."

"YaWa labarai, ta?amarta ita ?ar jarida ce zata iya yaWa labarin da duk ya zo hannunta. Tana da cikakken iko da damar da zata yi haka."

"Me zai hana baza mu yi maganinta ba, meyasa zamu dinga abu a Soye ne kamar masu jin tsoronta? Mu bayyana mu koya mata hankali mana, ai ba ?arfin mu ta fi ba. Ita kaWai ce fa, ko Waukar ranta muka so yi abu ne mai sau?i."

"Kamar ya kenan?."

"Ke yanzu sai na faWa miki ta yadda za a Wauki mataki a kanta? Sai na buWe baki na faWa miki abinda nake nufi?."

"Zan fi ganewa in an faWa Win ne."

"To ki bar komai a hannuna zan yi maganinta, amma ina so duk abinda ki ka ji ya bayyana kar ki ji tsoro, ki dake ki nuna baki san komai ba. In ki ka tsorata zaki shiga hannun hukuma:"

"Za a iya yi mata komai, mai bata kariyar baya nan. Saurayinta ne, shi zai aure ta, shine ya yi adopting Winta da ga gidan. Ya kulle duk wata ?ofa da za a same ta, amma a yanzu ba ya nan, zamu iya yi mata duk abinda mu ke so ba tare da damuwa ba."

"ki Wauka an gama, kawai ki jira."

"ka bar komai a wajena, zan yi."

"Ki bari na nuna miki abinda ya kamata a yi mata."

"A'a yallaSai, ka bari na koya mata hankali, ta san ni Win wacece."

"Sai na jiki" ta yanke wayar tana sauke numfashi mai nauyi.

A bayyane ta ce, "yarinya ?arama tana neman ta zame mana ?adangaren bakin tulu, mu kashe ta mu fasa tulun, mu barta ta Sata mana ruwa. ?aukar Islaha a gidan nan gabaWaya kuskure ne, irin wannan ?aramin abun shi ake kira da Wan hakin da ka raina, ?aramin abinda baka yi zato ba ya zamar mana wahala. Zan iya sakawa a kashe ta kowa ya huta!" Ta faWa tana shiga banWaki.

Zainab da take gab da shigowa dan amsa kiran Maman nasu duk ta ji abinda ta tattauna, gabanta ya faWi sosai, da hanzari ta koma da baya, dan ta kiran Adda Islaha ta sanar da da ita abinda kunnenta suka ji mata.

1k on telegram

Nana Haleema
'
*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ? ? ? ?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 022.*


Abba yana zaune a falonsa yana amsa waya, Umma ta fara shigowa da sallama, kafin ta zauna Mama ta shigo fuskarta a Waure ta nemi waje ta zauna tana cin magani.

Abba sai da ya gama wayar sannan ya kallesu ya ce, "na kira ku ne dan na ji dalilin ku na ?in zuwa asibiti duba Rehaan. Dukkanku kun san guba ya sha, da ace akwai ?arar kwana da yanzu ya jima da barin duniya. Yau kwanansa biyu a asibiti, amma ace babu wacce ta je ta ga ya jikinsa yake. ?aramar cikin ku ta je, amma ku da ku ke manya ba ku je ba. Meyasa?."

Umma ta Wan kawar da kai ta ce, "a yi ha?uri, bana jin daWi ne kawai. Amma yanzu na shirya zan je na dawo."

Abba ya ce, "sai yanzu, sai da dare ya yi sannan za ki je? Tun safe me ki ke yi da baza ki je ki duba sa ba?."

Ta yi shiru bata ce komai ba. Abba ya kalli Mama da take Waure fuska ya ce, "ke kuma fa?."

Mama ranta ya Saci matu?a, ta tsani ya dinga yi mata irin haka a gaban kishiyoyinta, bata so a dinga yi mata irin wannan wula?ancin a gaban na ?asa da ita. Ai ko faWan ne sai ya yi mata nata personal tunda itace gaba dasu, ta wuce ya haWa ta waje Waya da Waya daga cikin matansa ya yi musu faWa tare, ta jima da wuce wajan amma ba ya fahimta.

Mama ta ce, "babu komai" ta faWa a cushe cikin Sacin rai.

Ya girgiza kai ya ce, "kawai saboda bakwa son mahaifiyarsa sai ?iyayya ta shafesa?. Ban ga amfanin keeping malice Win nan da ku ke yi da Rehaan ba, ban ga amfanin wannan Waure Wauren fuskar da ku ke yi a kansa ba. Ko bakwa so Rehaan jinina ne kamar ?a?anku, abinda ku ka saka a zuciyarku, kuke wani tunani a kansa wannan duk ku ku ka sani, abinda ya shafe ku ne, ku ya dama tunda har ku ka Worawa zuciyarku. Wallahi inda Waya daga cikin ?a?anku ne aka kwantar a asibiti, na tabbatar kullum Nadira sai ta je ta dubasa, saboda ita tana zaune daku cikin ruwan sanyi ba kamar ku ba."

Umma ta gaji da maganar, jin sai yabon ?ar gwal yake yi ta ce, "ai na ce zan je na duba sa. In ka yi min izini na tashi in je na shirya." Da hannu ya nuna mata ?ofa ta je, ta mi?e ta fita.

Mama ta kalle sa ta ce, "Abba."

Ya Waga kai ya kalle ta ta ce, "Gaskiya ban jin daWin abinda ka ke yi min. Bana son abinda ka ke yi min a gaban kishiyoyina ko kaWan."?

Bai tambaya ba ta ce, "ta ya zaka dinga zaunar dani kana yi min faWa a kan Waya daga cikinsu? In faWan ne ban wuce shi wajenka ba, amma me zai hana baza ka kira ni ni kaWai ka yi min ba? Meyasa zaka dinga haWa ni dasu kamar wasu sa'annina, kana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login