Showing 48001 words to 51000 words out of 96103 words

Chapter 17 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

71

yanzu dai."

"Mun yi magana dashi, ya ce da kansa zai faWawa ba?on na mu, kuma ya yi min al?awarin ni ce ta farko da zan fara hira dashi."

Saleem ya ce, "good, haka muke fata, Allah ya ba mu nasara."

Ta ce, "Amin. Mu je ko?."

Saleem ya ce, "babu abinda ki ka manta?."

"Eh, ban bar komai ba" ta faWa suna shiga elevetor Win.

Suna sauka Reception suka ba da key Win Wakin suka fita zuwa harabar hotel Win.

Kamar an ce ta kalli gefenta, sai gaban ta ya faWi, ta Wan yi jim tana kallon wajan kafin ta juyo tana kallon su.

Saleem ya ce, "mu je ko?."

Ta Wan girgiza kai ta ce, "ku je, zan biyo ku daga baya."

Saleem ya ce, "kamar ya zaki biyo mu? Me za ki yi?."

"Akwai abinda zan yi, ku je kawai" ta faWa tana komawa da sauri.

Mualim ya ce, "Anya ba shine ya ce ta koma ba?." Saleem ya Wan yi shiru ya bita da kallo a lokacin har ta koma ciki.

Islaha tana shiga ta jawo mayafinta ta rufe fuska, ta saka faacemask Winta ta shiga eleavtor.

A floor 7 ya buWe waWanda suke ciki suka fita itama sai ta fito.

Ta yi hanyar dama su kuma suka yi haggu, kamar wacce ta manta hanya sai ta yi saurin dawowa da baya ta bi baya a lokacin suka buWe room suka shiga.

Ta Wan zubawa Wakin ido tana nazari, dan ko tantama bata yi wannan Hafsa ce, Hafsa ?anwarta ta gidan marayu. Me ya kawo ta hotel har aka shiga da ita Waki?.

Dafe kai ta yi tunawa bata da inda zata zauna ta jira su, sai ta juya a inda take tsaye akwai camera, ta gyara nutuswarta ta ?arasa bakin ?ofar Wakin gabanta yana faWuwa. Kamar zata yi knocking sai ta fasa, ta ja da baya ta koma ta sauka ta koma reception.

A nan ta ga Saleem yana jiran ta, yana ganin ta ya ce, "me kika koma yi ne haka?."

Ta Wan yi jim ta ce, "wata na gani wacce na sani tuna baya, shine na koma muka gaisa. Mu je"

Ta faWa tana yin gaba ya bi bayanta suka shiga mota suka tafi zuciyarta cike da tsananin tunani akan abinda ta gani.

Rehaan bai farka ba sai gab da sallar la'asar, ya mi?e ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya a lokacin aka yi kiran sallah. Ya yi sallah a Wakin ya tashi ya kunna kettel ya haWa tea yana sha.

A lokacin Jazy ya shogo ya bi sa da kallo ganin bashi da alamun shiryawa ya ce, "Malam ka tashi mu tafi. Na gaji wallahi."

Ya Wan lumshe ido ya buWe ya ce, "baza mu bari sai dare ba?."

Ya girgiza kai ya ce, "A'a, yanzu zamu tafi. Tashi" ya faWa yana rufe masa box Winsa yana kallonsa.

Rehaan ya ajjiye mug Win ya ce, "ka kasa gane bana son komawa gida."

Ya kalle sa ya ce, "wallahi dole ka koma, in ba haka ba zan yi tafiyata na ?yale ka. Ya zaka dinga raina min hankali kamar wani yaronka, dan ka ga ina biye maka sai ka dinga yin abinda ka ga dama?."

Ya Wan yi tsaki ya mi?e tsaye, ya Wauki face cap Winsa ya saka, ya saka facemask ya Wauki wayarsa ya ce, "mu je" ya faWa yana yin gaba.

Jazy ya ri?o hannunsa ya ce, "dakata malam, waye bawan ka da zai Waukar maka jaka? Ka san dai baka isa ba ko?."

Bai ce komai ba ga dawo da baya ya Wauki box Win, har zai fita sai ya dawo ya cire charger sa ya fita daga Wakin zuwa ?ofar Wakin yana danna waya.

Jafar yana fitowa ya ja ta sa box Win suka sauka ?asa zuwa compound Win hotel Win. Suna ?arasawa suka shiga mota suka Wauki hanyar gida.

Tunda suka nufi gida yake jinsa babu daWi ko kaWan, sai kallon hanya yake yi yana ji kamar su koma. A haka suka ?arasa aka buWe musu gate suka shiga.

Jazy zai buWe ya fita ya ri?o hannunsa ya ce, "kar ka ce zaka wuce gida yanzu, ka zauna tare dani."

Ya bisa da harara ya ce, "da yake ga bawan ka ko? Dallah cika min hannu, in na shiga muka gaisa da Abba da Mamy tafiyata zan yi, nima uwata tana son ganina ai" ya faWa yana buWe motar ya fita.

Jazy yana fita suka haWa iso da Janan, ta saki ihu ta nufo sa a guje tana zuwa ta rungumesa tana welcoming Winsa.

Jazy ya yi dariya ya ce, "Janan ya aiki?."

"Alhamdu lillah Hamma Jaafar. Ina Hammana?."

Ya nuna mata side Win da Ray yake har lokacin bai fito ba. Ta buWe ido ta ce, "da gaske tare ku ke?" ta faWa tana zagyawa da sauri ta ?arasa ta buWe masa.

Suka haWa ido ta faWa jikinsa a cikin motar, ya yi murmushi yana zare facsmask Win ya ce, "My little Jan."

Ta Wago daga jikinsa ta ce, "Hamma shine babu labari? Baka faWawa kowa ka shigo ?asar nan ba."

Murmushi ya sake yi ya ja kunatunta kafin ya sakko daga motar. Janan ta kan?ame hannunsa ta ?i saki, tana ta murnar ganinsa ta ce, "Kuma da yake ban ga security guard Winka ba, shiyasa ban yi tunanin kai bane."

Ya kalle ta ya ce, "kina zuwa aiki?."

Ta yi dariya har tana tsalle kamar yarinya ?arama ta ce, "yanzu ma na dawo."

Ya sake yin murmushi tana ri?e dashi cikin murnar ganin favorite brother Winta.

Ya kalli Jafar da ya yi nisa a hanyar apartment Win Mamy. Ya juya yana kallon Janan, kafin ya ce wani abu ma'aikatan gidan sun ?araso wajan ana ta gaishe sa ana yi masa barka da zuwa.

Suka gaisa cikin sakin fuska, aka Wauki box Winsa aka kai apartment Win Mamy. Janan dai tana ri?e da hannunsa suka nufi apartment Win Mamy, sai da zasu shiga sannan ta tuna ta bar abu akan gas ta sake shi ta tafi a guje.

A lokacin Riyya da Banisha suka fito a guje suka rungumesa a tare. Murmushin jin daWin ganin ?annen nasa ya yi, dukkansu kansu babu Wankwali, gashinsu mai tsaho da santsi ya bayyana har gadon baya.

Ya ce, "Riyya za ki yar da ni ba, baki san kina da girma bane?."

Ta Wago tana kallonsa ta ce, "Shine ko ka faWa min."

"Saurayinki bai faWa miki ba?."

Cike da shagwaSa ta ce, "bai faWa min ba."

Ya yi murmushi, ya shafa fuskarta suka shiga ciki har falon Mamy.

Da sallama ya shiga ya samu Mamy a zaune ita da Jazy gaisawa. Rehaan ya bita da kallon kewar mai yawa, fara'arsa ta ?aru sosai. Ya ce "Mamy."

Kafin ya ?araso ta mi?e ta cim masa, ta yi hugging Winsa ta ce, "sannu da zuwa My love."

Ya Wago daga jikinta, yana kallon fuskar ta, cikin harshen hindi ya ce, "na yi kewar ki Mamy."

Itama cikin yaren ta ta ce, "nima na yi kewar ka Rehaan. Zauna." Bai musa ba ya zauna yana kallon kowa da yake zaune a falon.

Riyya ta je ta kawo masa favorite drink Winsa, wanda ta san yana so indai ya zo gida, daman Jafar ya faWa mata zai dawo, shiyasa ta yi masa da kanta.

Ta ce, "kamar na san zaka dawo na yi cocunut drink, gashi ka sha ta faWa tana mi?a masa.

Ya karba ya ri?e hannunsa, ta zauna a kusa dashi ya ce, "thank you. Ba ki ga saurayinki ba?."

Ta kalli Jafar da yake kallon ta, ta yi dariya tana kwanciya a kafaWar Rehaan cike da kunya.

Mamy ta yi dariya tana kallon Rehaan cikin murnar ganinsa ta ce, "tana murnar ganin ka, ko sannu da zuwa bata ce masa ba."

Ta kalli Mamy ta ce, "Allah na ce masa sannu da zuwa. Ta juya ta Jafar ta ce, "ban faWa maka ba?."

Shi dai murmushi kawai yake yi bai ce komai ba, yana jin daWin ganin iyalan Mamy cikin farin ciki sosai, yana son zama a cikinsu dan kamar ba sirikin Mamy ba haka yake. Tun zamansu a Uk Mamy ta mayar dashi kamar Rehaan, komai tare suke yi, yadda take rarrashin Rehaan haka take yi masa. Zama da ita ya saka yake jin yaren ta kamar yadda Rehaan yake ji, komai in zata yiwa Rehaan zata haWa dashi.

Ya yi tunanin da ya furta yana son Riyya, har maganar aure ta shiga tsakani zata Wan canja saboda kunya, amma sai ya ga shine yake haukansa Mamy ko a jikinta. Yadda take yi masa Win nan dai bata canja ba, wani lokacin har tsokanarsa take yi. Shiyasa shima ya sake, ya daina jin kunyar ta gabaWaya.

Jafar ya kalli Mamy ya ce, "Mamy Abba yana nan?."

"Ba ya nan Jafar, sai dai ka dawo in anjima."

"Shikenan, ni zan wuce Mamy."

"Amma zaka shiga ku gaisa da matan gidan ko?."

Ya Wan yi jim bai amsa ba, Mamy ta ce, "ka je Jafar, kar ka bar shaiWan ya yi galaba a kanka."

Ya girgiza kai ya ce, "To Mamy."

Mamy ta ce, "sai ganin ku kawai na yi, babu labari ko a waya."

Ya yi dariya ya ce, "Rehaan ne wallahi, magiya ya dinga yi min akan kar na faWa mu ku. Tun jiya muka dawo, a hotel muka kwana sai yanzu mu ka zo."

Mamy ta ce, "na yi mamaki da ban ga Rehaan a gajiye ba, ashe kun jima da dawowa."

"Ai da yana nan yana faman furta ya gaji. Rago kawai." Mamy ta yi dariya kawai bata ce komai ba.

Jazy ya mi?e ya ce, "Mamy na tafi."


Mamt ta ce, "ka gaishe da Mummy, ka ce mata zan zo in sha Allah."

Ya Waga kai ya ce, "In sha Allah."

Mamy ta kalli Riyya da take satar kallonsa tana murmushi ta ce, "baza ki raka sa ba?."

Riyya ta mi?e tana Waukar hularta, ta saka ta bi bayan Jazy da sauri.

A lokacin Rehaan ya kalli Mamy da take kallonsa ta ce, "a kawo maka abincin?."

Ya Wan girgiza kai ya ce, "A'a Mamy, zan sha drink Win kawai, in anjima zan ci."

"Me za a dafa maka?."

"Anything from my Mamy i like it."

Ta yi murmushi tana cire hular kansa, gashinsa da ya Suya a ciki ya sauka har bayan wuyansa.

Ta bi gashin da kallo tana shafawa ta ce, "Rehaan ka san jama'ar gidan nan basa son gashin nan ko?."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "Mamy dan ba sa so sai na ?i yin abinda na yi niya? Ni Ina so, kuma babu haramci a ciki, saboda su sai na fasa?."

Mamy ta girgiza kai ta ce, "ka je ka huta, zamu yi maganar daga baya. Banisha Wauki box Winsa ki kai masa Waki."

Banisha da take jikinsa ta mi?e ta Wauki box Win zuwa Waki.

A lokacin Riyya ta dawo shi kuma ya mi?e tsaye, ta ?araso tana sake ri?e hannunsa ta ce, "Ina da labarin da zan baka." Ya sake yin murmushi ya shafa fuskarta bai ce komai ba.

Har zai fita sai Mamy ta ce, "Rahaan."

Ya dawo yana kallon ta, ta ce, "Ka je ku fara gaisa da mutanen gidan, in ku ka gama sai ka wuce Waki."

Bai musa ba suka fita su ukun ta bisu da kallo, tana yi musu addu'ar neman tsari daga duk wani mai nemansu da sharri.

Apartment Win Mama suka shiga da sallama, Janan tana ganinsa ta fito daga kitchen, ta ?araso gare sa suka shigo falon tare.

Ya kalli mutanen da suke zaune a falon, yayyensa maza ne, sai kuma ita Maman da take zaune.

Ya kalle su ya ce, "Barkan ku."

Da?yar suka iya amsa masa, ya kalli Mama cikin harshen fulatanci ya ce, "barka da gida."

Ta bisa da harara tana taSe baki ta ce, "an dawo lafiya?."

"Alhamdu lillah" ya faWa yana mi?ewa tsaye. Kafin su ce wani abun ya ce, "sai anjima" ya faWa yana fita daga falon.

Sameer ya bi sa da kallo tare da jan tsaki, sai kuma ya yi ?wafa ya mi?e shima ya fita bai sake waiwayon kowa ba.

Shi kuwa wajan Umma ya shiga, a nan ya tarar da Yayarsa mace da kuma ?anwarsa wacce ta jima da aure.

Suka gaisa sama-sama, ya fito ya shiga wajan ta ?arshen, itama suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan ya wuce wajan Daada. Har zai shiga sai ake shaida masa bata nan ta fita, ya dawo da baya suka wuce part Winsa shida ?annensa mata guda uku.

Yana saka ?afa a apartment Winsa kansa ya sara, ya Wan yatsine fuska kaWan ya shiga falon ya zauna yana Wan murza goshinsa.

Janan ta ce, "Hamma ya dai?."

Ya Wan girgiza kai alamun babu komai kafin ya ce, "ku je ku yi sallah, nima yanzu zan fito masallaci."

Suka amsa, Riyya ta ajjiye masa drink Winsa su fita.

Ya dafe kai yana sauke numfashi, ya mi?e yana tafiya a hankali, ya shiga ciki zuwa Wakinsa ya buWe yana kallon Wakin kamar ba nasa ba.

Ya ?arasa gaban mirror ya cire agogo ya ajjiye, ya ajjiye hula da glases Winsa ya ya taka a hankali zuwa banWaki.

Alwala ya yi ya fito, bayan ya fito kansa yana juyawa sosai, ya Wan tsaya cak kafin ya zauna a gefen gado yana ji kamar ana juyasa a cikin Wakin.

Kiran sallar da aka yi ya saka shi sauke numfashi, ya koma closet Winsa ya Wauko jallabiyya ya saka ya fito dan zuwa sallah.

Islaha tunda suka Wauki hanya ta yi shiru tana tunanin abinda ta gani wanda ya Waga mata hankali sosai, ta Wan sauke nunfashi a hankali. Sai kuma fuska wanda ya watsa mata tea ya zo idanunta, ta ji takaici ua mamaye mata zuciya.

Ta yi tsaki ta ce, "shirme!."

Saleem da yake kallon ta ya ce, "ke da wa."

Ya Wan lumshe ido ta buWe ta ce, "don Allah ajjiye ni a orphanage, akwai abinda zan yi a ciki."

Muslim ya bita da kallo ya ce, "baki gaji ba kenan?."

"Akwai wanda nake so na haWu dasu, shiyasa nake so in shiga."

Basu jima ba suka ?araso, ta fita daga motar tana yi musu sallama suka tafi ita kuma ta nufi gate Win gidan.

Suka gaisa da ma'aikatan wajan, ta shiga ciki kai tsaye Wakin su Hafsa ta wuce. Zata shiga Zainab zata fito, zata yi ihu ta rungume ta ta yi saurin rufe mata baki suka shiga Wakin.

Islaha ta ce, "yi shiru, bana so a san na shigo gidan nan."

Zainab ta ce, "Adda Islaha sannu da zuwa."


"Yauwa Zainab. Ina Hafsa?."

Zainab ta yi shiru bata ce komai ba. Islaha ta ce, "magana nake yi miki fa, ina Hafsa take, itama bata nan kamar sauran?."

Zainab ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Adda Islaha Mama ta fita da Hafsa tun jiya, har yanzu bata dawo ba."

Islaha ta gyara zama ta ce, "ina ta je da ita? Meyasa ke ba a tafi dake ba?."


"Wallahi ban sani ba, tunda aka yi wasu ba?i bayan kin bar gidan nan, sai aka kira mu dani dasu Hafsa da Saliha mu ka je wajan, tun daga lokacin Mama ta kira Hafsa suka fita basu dawo ba."

"Su waye ba?in? Mata ne ko maza?."

Zainab zata yi magana cikin tsawa aka katse ta aka ce, "Ke Zainab!."

Dukkansu sai da gabansu ya faWi, dan tsawar ta zo musu a bazata. Suka juya suna kallon wacce ta yi musu tsawar.

?aya daga cikin wacce suka tashi tare ne, da shekaru da komai na su Waya ne.

Ta ?araso ta janye Zainab ta ce, "me ki ke yi a nan? Ba an ta fi dining cin abinci ba?."

Zata yi magana ta daka mata tsawa ta ce, "wuce ki bar wajan nan kafin na yi ball dake."

Islaha ta mi?e tsaye ta ce, "babu inda zata je, yadda ki ke da iko da ita nima haka nake da iko da ita" ta faWa tana ri?o hannunta.

Fadwa ta bi Islaha da kallo ta ce, "Islaha ba da ke nake ba, ki bari na yi abinda aka saka ni. Baki fa iko da kowa na gidan nan, ba a nan ki ke ba yanzu."

"dan ba a nan nake ba, amma ?anwata ce."

"Zainab fita."

Islaha ta kalli Zainab ta ce, "jeki Zeey, kar ki damu." Zainab ta fita a hankali bata sake magana ba.

Islaha ta kalli Fadwa ta ce, "kin bani mamaki, ban yi tunanin haka daga gare ki ba. Me ku ke Soyewa wanda ni ban san dashi ba?."

Fadwa ta ce, "babu ruwanki da abinda mu ke Soyewa, nan gidanmu ne muna da ikon yin duk abinda mu ke so. Bakya cikin mutanen gidan nan, baki da file a gidan nan a yanzu, dan haka ba a gidan mu ki ke ba. Ki daina ?o?arin ganin sai kin nemo abinda aka Soye, babu ruwan ki."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Tabbas sai na nemo abinda aka Soye, kuma in zargina ya tabbata na rantse da Allah kaf gidan nan babu wanda zai sha. Wallahi sai kowa ya kwashi kashinsa a hannunsa."

"Babu abinda zaki gano balle ya tabbata, ki cigaba da tsayawa a matsayin da aka ajjiye ki. Tunda ke kin koma gidansu saurayi da zama ke ki ka sani, sai ki je ki yi rayuwarki, ki bar mu mu yi tamu rayuwar."

Islaha ta yi ?wafa ta ce, "zamu gani Fadwa, na gode da samun information daga gare ki" tana faWa ta fita daga Wakin da hanzari.

Fadwa sai ta tafi tunani, wanne irin info take zance? Wacce irin magana ta faWa da ta zamarwa Islaha information?. Sai ta ji tsoro ya kamata, gabanta ya faWi kar ta je ta faWi wani abun.

Da hanzari ta fita ta nufi office Win Mama, ta samu tana ganawa da ba?i, an kawo gudunmawar kaya masu yawa a rabawa marayu.

Ta jima tana jira su tafi amma basu tafi ba, sai bayan sun tafi sannan ta shiga ta ce, "Mama Islaha ta zo nan."

Mama ta juyo ta kalle ta ta ce, "me ya kawo ta?."

"Na je na same ta ita da Zainab tana tambayarta ina Hafsa take, kuma kin san Hafsa bata gidan nan."

Mama ta ajjiye ruwan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login