Showing 3001 words to 6000 words out of 96103 words

Chapter 2 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

46



Ta ce, "me ya samu Rehaan Win?."

"Mama yaron nan yana neman wuce tunanin mu, yana so ya zarce inda mu ke tunanin yake."

Cikin fusata ta ce, "dallah ka faWa min, meye ya faru?."

Ya sauke numfashi ya ce, "Sunansa ya dawo na biyu a jerin sunayen masu kuWin africa masu ?arancin shekaru."

Idanu ta buWe tana kallonsa ta ce, "Sameer kar ka yi min ?arya."

"Ba ?arya nake yi miki ba, kalli ki gani" ya faWa yana nuna mata wayarsa.

Bata musa ba ta karSa, ta ga yadda aka yi analysis ga sunansa nan a layi na biyu, saura kaWan ya tarar da na farko.


Ba?in ciki ya mamaye mata zuciya, ta mi?a masa wayar, ta mi?e tana zaga falon cike da tunanin mafita.

Ta rasa yadda zata yi da Rehaan, kuWin da ya kamata ace ?a?anta ne suka yi shine yake mallakarsu. Hakan yana taSa zuciyarta, yana sakawa mata ba?in ciki da hassada.

Mama ta ce, "ya aka yi haka yake faruwa, Ya aka yi abubuwa suke jagule mana ne Sameer?. Rehaan fa, kai kanka ka girmesa da shekara Waya. Ya aka yi yake samun Waukaka, bayan ku ne manya a cikin gidan nan?."

Sameer ya ce, "wallahi zamansa a england babbar illa ce a gare mu, ni ban yarda ba dukiyar Abba ce a hannunsa ba. Ta ya yaro ?arami ace ya mallaki abinda mahaifinsa bashi dashi, Hamma Zayyad da yake babba bashi dasu, mu ma da muka biyo baya bamu dashi. Kina jin wannan kin san haWawa aka yi, gabaWaya dukiyar Abba tana hannunsa, mu muna nan an haWa mu da ?ananun abubuwa na banza. Babu damar mu yi magana sai ace ai shi a nan ya girma ba, shi a a can aka haifesa, a can yake kasuwancinsa da sauran shirme. Mama in muka zuba ido, kaf dukiyar Abba da take can zata zama haram a gare mu."

Mama ta girgiza kai ta ce, "ya aka yi hakan yake faruwa, ya aka yi abubuwa suke lalace min ne?. Meyasa na kasa Waukar mataki akan Rehaan, meyasa yake shigar min hancina na kasa fato shi?."

Sameer ya ce, "dole a san abinda za a yi, bazai yu kina babba a gidan nan, muna manya a gidan nan, ace komai yana hannun Rehaan ba, dole ki san yadda zaki yi ya dawo nigeria, in ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai fi ?arfin mu."

"?arya ne wallahi, yadda ku ka kasance manya a gidan nan babu wanda zai samu Waukaka sama da ta ku, dole a dakusar da Waukakar Rehaan, dole Rehaan ya dawo ?asar nan.."

"?aukaka ta nawa kuma Mama? Sunan Rehaan da labarin Ray ina ne bai shiga ba a faWin ?asar nan?. Sai dai a kiyaye gaba, amma wannan ya riga ya faru. Kai tsaye ki samu Daada da wannan maganr, ki same ta ita kaWai ce zata zama silar dawowarsa ?asar nan har abada."

Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta ce, "yanzu nan zan je na same ta, indai a kan ganin bayan Waukakar Rehaan ne babu abinda bazan yi ba Sameer, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan ganin Rehaan ya dawo ?asa, ku kun hau sama."

Sameer ta mi?e ya fita cikin gamsuwa sa kalamanta. A ganinsa ta ya ya suna manya a gidan, ?aninsu wanda ya zama shine namiji ?arami a kaf gidan, ya zo ya fi su Waukaka.

Mama kuma ta dafe kai cikin rashin mafita, a bayyane ta ce, "Rehaan! Rehaan! Rehaan! Ka shiga rayuwata, ka hanani sakewa Rehaan, ka hanani cika burina....."

Ta girgiza kai ta ce, "Baka isa ba wallahi, baka isa Waukakarka ta disashe ta ?a?ana ba, yadda na kasance gaba da kowa a matan gidan nan, dole ?a?ana su kasance gaba da kowa a yaran gidan nan.? Babu wanda ya isa ya sha gabansu, su Win su za a kalla aje ace su bayar, ba kai ba. Tun kana yaro ka ke bani wahala, amma a yanzu bazan barka ba Rehaan, bazan taSa barin ka ba."

A fusace ta ja hiijabi ta fito daga part Winta zuwa part Win Daada.

Daada mahaifiyar Abba ce, tsohuwa mai rigima, duk abinda ta ce a gidan babu wanda yake tsallakewa, duk dokar da ta shinfiWa sai an hau kai ba a karkacewa. Daada mace ce mai fitar da ?o?on usuli, nata nata ne, wanda ba nata ba, ba nata bane. Daada bata son Nadira ko kaWan, duk abinda zata yi zata ce daman ba jinin fulani ba ce ba.

Mama ta shiga da sallama, Daada da take zaune ta amsa mata? zauna a akan carpet.

Mama ta ce, "Daada barka da yamma."

Ta yi murmushi ta ce, "Yauwa Saddi?a."

"Na same ki lafiya?."

"Lafiya lau."

Mama ta gyara zama ta ce, "Daada wata magana ce take tafe dani."

Daada ta murmusa ta ce, "Uwar gida kenan, kina gaba da kowa a gidan nan, kuma kin fi kowa hankali. ina jinki."

Mama ta ji daWi, ta sake samun ?arfin guiwa sannan ta ce, "Yanzu Daada fisabinillahi haka zamu zuba ido abubuwa suna faruwa a gidan nan mu yi shiru, haka zamu cigaba da rayuwa a gidan nan?. Ka yi magana ace ba?in ciki ne, dan ba kai ka haifa ba?."

Cikin rashin fahimta Daada ta ce, "wani abun ne ya faru?."

"Daada akan Rehaan nake magana. Daada wai yaron nan ?arfin ikon ki ya fi a gidan nan ne, da ki ka zuba ido yana zaman wata ?asa, yana watsewa da turawa baki saka ya dawo ba?."

Daada ta ce, "Ko ubansa bai fi ?arfina ba, balle shi."

Mama ta ce, "Daada a cikin ?an uwansa ?anana akwai wanda bai san fuskar ba sai a tv. Yaro Wan dangi, an tsame sa daga dangi ya koma gefe kamar babu shi a gidan nan?. Rabon Rehaan da zuwa ?asar nan shekara Waya kenan, ?ananun jikokun gidan nan duk basu san shi ba. Hakan zumuncin zai kasance? Shi ba aure ba, yana can cikin turawa yana abinda ya ga dama?. Yana zubar da ?imar gidan nan, da mutuncin gidan nan?."

Daada ta giegiza kai tana taSe baki ta ce, "Me ake yi da auren bare? Me ake yi da auren wacce ba jinin fulani ba?. Haka kawai AbdulAziz ya Wauko mana annoba ya kawo ta cikin ahlinmu, ya Wauko mana baragurbi ya haWata damu. Ko da yake ba laifinsa ba ne, asiri ta yi masa. Har a faWawa ?an india tsafi?."

Mama jin ta fara samun nasara sai ta ce, "gaskiya lamarin abin dubawa ne Daada, ke kan ki rabon da ki saka Rehaan a idonki na san an kwana biyu."

"An kwan abiyu kam, tun haWuwar da muka yi dashi lokacin da aka kaini Jedda akan ciwon ?afa, tun daga nan ban sake ganinsa ba."

"Haka rayuwa zata tafi kenan? Yana can yana rayuwa a turai suna lalata masa tarbiyya da al'adarsa. ?anensa mata duk sun yi sun bar shi, Jafar Win da yake ji dashi shima gashi auren zai yi ya bar sa. Shi yana can wata ?asa bai yi auren ba yana mu'amala da turawa. Yanzu sunan gidan nan yana Saci kowa sunanki zai fara kira, a dinga cewa ai kina gani komai ya faru baki tsawatar ba. ?awata ce ta kira ni, take faWa min yadda abubuwa suke tafiya a can ?asar. Shiyasa na taso, na ce zan zo na same ki. Bazan zuba ido ina ganin Saraka, na kama bakina ba."

Daada ta girgiza kai ta ce, "Gaskiyarki ne Saddi?a, kin yi hangen nesa da tunani mai kyau. Bara mijin na ku ya dawo, dole Rehaan ya dawo Nigera ko yana so ko ba ya so wallahi. Dole ya dawo a nema masa mata ya yi aure, ni kaina zan nemo masa mata, dan bazan bari ya Wauko wata ?abilar ya sake haWamu da ita ba. Bafulatana kamar sa zai aura, bazan amince da baturiya ko baindiya ba."

Mama ta taSe baki ta ce, "Allah dai ya kiyaye. Dan kuwa na samu labarin yana can yana soyayya da baturiya."

Sai kuwa Daada ta fusata ta ce, "?aryarsa ta sha ?arya, bai isa ba wallahi, bai isa ba matu?ar ina raye. Jeki abin ki zan yiwa tukfar hanci."

Mama ta yi murmushi tare da cewa, "Godiya nake, a tashi lafiya" ta faWa tana fita kai tsaye Sangaren Salamatu ta biyu ta shiga, kishiyarta kuma abokiyar haWa gulmarta.

? ? ? ?? " " " " " " "

Kyakykawar mace ce a zaune a parlour tana amsa waya cikin murmushi, kallo Waya zaka yi nata ka san ba kyawun fulani gare ta ba, kyau ne irin na foreign countries, ba irin kyau ne irin na mu na gama gari ba.

Kai da ka ganta ka san ba bahaushiya bace, kallo Waya zaka yi mata a fassarata a ?ar india, saboda kamanninta, maganarta, da komai ya gwada hakan.

Waya take amsawa cikin murmushi, kafin murmushin ya gushe daga fuskarta, tana kallon fuskar wayarta alamun video call ta ce, "Jaafar kana saka ido akan Rehaan kuwa? Ka tabbata babu wani abun da yake aikatawa?."

Fuskar wanda take kallo a wayar ya Wan yi murmushi ya ce, "Mamy wallahi babu abinda Rehaan yake yi na ba daidai ba. Ke kin san halinsa, bazai aikata wani abu mai muni ba."

Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ka tabbata babu budurwa a tare dashi, ba ya zuwa club, Bar, chill spots, ko wani romantic vibe?."

"Wallahi ba ya zuwa ko ina Mamy. Ki yarda dani, amma Rehaan ko taba ba ya sha balle ya je Bar. Bashi da budurwa, sai abokan kasuwanci da aiki."

"Jafar ka san ya nake zaune a cikim gidan nan, ka san ?iris ake jira Rehaan ya aikata wani abun a kambbabasa zuwa wani abun daban. Bana so ya aikata abinda zai jawo cecekuce akansa. Shiyasa nake so ka dinga saka masa ido, da ka ga wani abu mara kyau just call me and let me know. I will handle it."

Jaafar ya ce, "Ki yarda dani Mamy, Rehaan ba ya daga cikin abubuwan da ki ke tunani, bussinees da aikinsa kawai ya saka a gaba Mamy."

Mamy ta ce, "Alhamdu lillah. Yaushe za ku dawo ne?."

"Ni dai na kusa dawowa, shi Win ne ban sani ba. Kin san halinsa, kamar an saka masa tsanar zuwa gida."

"In za ku dawo ka tabbatar ka saka ya cire gashin nan na kansa, kasan jama'ar gidan nan ba ?aunar sumar nan suke yi ba, yanzu zaka ji ana magana ana cewa dan babarsa ba bafulatana ba ce shiyasa yake aikata haka. Ka saka ya rage tsahonsa ko ya ya, ka ji?."

Jaafar ya murmusa ya ce, "To Mamy, kin san halinsa akan gashin nan, babu lallai ya amince."


"Zan yi masa magana, bara dai ku tashi dawowar."

"To Mamy."

"Duk da bana son dawowarsa ?asar nan, amma babu yadda zan yi."

Cikin sigar rarrashi ya ce, "Mamy don Allah ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai samu Rehaan in sha Allah."

Ta sauke numfashi ta ce, "Allah ya sa hakan Jaafar, ka gaishe sa in ya dawo daga aiki."

"Okay Mamy."

Ta kalle sa ta Wan yi murmushi, cikin tsokanarsa ta ce, "na hana hira da Riyya ko? sorry ka kira ta, ko na kira maka ita ku cigaba da magana."

Dariya ya yi kaWan ya ce, "take your time Mamy, ba ita nake nema ba."

Ta kalli gefenta, inda wata budurwa ta fito mai kama da ?abilar babarta, tana gyara dogon ba?in gashinta.

Mamy ta ce, "tana jinka, babu ruwana" ta faWa tana murmushi, shima murmushin ya yi yana sake ?aunar Mamy, dan ko kaWan shi mantawa yake yi da ?ar cikinta zai aura.

Mamy ta datse kiran ta kalli Juwariyya cikim harshen hindi ta ce, "in an yi sallah zamu shiga mu gaishe da Daada."

Riyya ta gama naWe gashinta, ta saka hula tana turo baki gaba ta ce, "Mamy ni bana son zuwa."


"Sai kin je, ki faWawa Banisha" ta faWa tana tashi ta Waki.

Riyya ta bi Mamy da kallo, ta sauke numfashi. Bata san me Mamy ta yiwa mutanen gidan basa sonta ba, shiyasa itama bata son shiga cikinsu, ta fi son rayuwa ita Waya, dan bazata jure ?iyayyar da ake nunawa babarta a fili ba.....

Na fara rubuta littafin 3/12/2025.


Nana Haleema
' %?

*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

https://chat.whatsapp.com/IkYPgd4DkXD8mUAAeCIZax?mode=gi_t

*Book 1*
*Page 002.*


Mama tana shiga Wakin ta kalli Labiba ta ce, "ke bana ciki da iskanci, ki bani abinda ki ka samo ko na saSa miki."

Labiba a gajiye da maganar ta ce, "Mama na faWa miki waya zan canja, don Allah ki bar maganar nan. In na samu ai ina kawowa, dan yau kaWai ban kawo ba bazai zama matsala ba."

Mama ta harare ta ce, "wallahi sai kin kawo su, ko kina so, ko bakya so sai kin kawo kuWin nan."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan zan kawo."

Ta yi tsaki ta ce, "ya fi miki."

Mama ta fita ta shiga Wakin da aka mallakawa Islaha. Ta same ta a tsaye tana ninke kayan da ta cire, ta bita da harara ta ce, "saura ke, kar ki ga na yi miki shiru ki Wauka na yafe miki. Dole ki kawo na yau."

Islaha bata son magana, hakan ya saka ta ce,"to Mama" ta fada tana ajjiye abinda yake hannunta ta shiga banWaki.

Hanan da Labiba da suka biyo bayan Mama, suna daga tsaye Hanan ta ce, "wai Mama kanmu Waya da yarinyar nan a cikin gidan nan?."

Mama ta ce, "ta ya zata zama kai Waya da ku? Itafa ?ar ri?o ce."

Labiba ta ce, "Amma itace wacce Hammanmu zai aura ko?."

Mama ta Harare ta? ce, "da zata auri Saheer sai ta zama ?ar gidan nan?. Ke kin ga an yi aurensa da ita din ne, kin ga ya aure ta Win ne, gwana ta gwanaye?" Ta faWa tana harararta ta fita.

A lokacin Islaha ta fito daga banWaki ta saka hijjab ta kalli gabas ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta Wauki wayar ta ta fita daga falon zuwa kitchen.

Aiki take yi tana tunani, dole ce ta saka take zaune a gidansu Hamma, in ba dole ba da yanzu ta tattara kayanta ta gudu. Amma baza ta iya hakan ba, saboda Hamma. In ta yi masa haka bata kyauta ba, kuma ta yi butulci. Bata so ta cigaba da zaman gidan, dan wata ran baza ta iya barwa Mama ba. In tana faWa tana shiru, wata ran bazata iya yin shirun ba.

Hankalinta yana kan aikin da yake gabanta, ga tunanin da yake zuciyarta, tana ta gyara kayan miya tana wankewa.

?hamshin turaren da ta ji a bayanta ya saka ta murmushin farin ciki, lokaci Waya zuciyarta ta mamaye da farin ciki, ta ji daWi kamar ta buga tsalle.

Ta Wan sauke numfashi, cikin muryarta mai daWin saurare ta ce, "Hamma!."

A lokacin kyakykyawan sarauyi fari tass ya shigo kitchen Win yana murmushin. Bazai wuce shekaru talatin da uku ba, yana da tsayi sosai, dan da ya tsaya a kusa da ita sai ta zama ?ar ?arama.

Fari ne sosai, kyakykawa mai kyaun fulani. Yana da hanci dogo, da kyakykyawan gashi a fuskarsa, duk da babu yawa kaWan ne.

SAHEER kenan, Hamman Islaha, abokinta, masoyinta, abokin shawararta.

Ya jingina da cabinet, ya harWe hannu a ?irji yana kallonta ya ce, "ya aka yi ki ka san nazo?."

Ta juyo tana kallonsa ta ce, "tun kafin ka zo turarenka ya ri ga ka zuwa."

Murmushi ya sake yi yana kallon fuskar ta da take fitar da murmushi, ya ce, "Ba wani nan, kin ji shigowata ne kawai."

Ta Wago kyakyawan idaunta ta kallesa ta ce, "A jikina na ji zuwan ka Hamma. Sannu da zuwa, daman yau zaka dawo baka faWa min ba?."

"Na kira matar Hamma bata Wauka ba, sai na ?yaleta na ce kar na je na yi laifi."

Ta jingina da cabinet itama ta ce, "Hammana ba ya laifi a wajena."

Murmushi ya sake yi, cikin ?auna da soyayyarta ya ce, "me ake dafa mana matar Hamma?" Ya faWa yana karasowa kusa ita ya buWe tuukunyar da ta Wora.

Islaha ta ce, "couscous Mama ta ce a dafa. Kamar ta san zaka dawo."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "baki je aiki ba ne?."

"na je."

"Amma ki ke a tsaye a kitchen kina aiki? Ina Labiba ko Hanan, su baza su yi girkin ba sai ke?."

Ta Wan sauke numfashi ta kalle sa, sai ta Wauke kai ta yi murmushi bata ce komai ba.

Ta ce, "Mama ce ta saka ni."

Ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta cikin rashin jin daWin abinda Mama take yi mata a gidan, ya cize baki yana girgiza kai tare da zuba mata ido.

Calmly ya ce, "ki yi ha?uri Islahaa! In sha Allah komai ya kusa ?arewa, da mun yi aure na Wauke ki shikenan babu mai takura miki. Da kaina zan dingayi mana girki, bazan bari ki takura kan ki ba."

Kunya ta kamata, ta saka dogayen hannayenta ta rufe fuska. Sautin murmushinsa ta ji yana kallon hannunta ya ce, "yaushe aka aka miki red henna? Yana yi miki kyau Islaha, Ina so na gansa a hannunki, ke kaWai" ya faWa yana ri?on hannunta yana kallon zanen red hennan da yake fatar hannunta.

? ? ? "Dakyau Saheer! Ashe ka dawo, ni uwarka Ina Waki baki a sake Ina jiranka, ashe kai kana nan ka saka ?ar gold a gaba. Wato ta fi ni mahimmaci a wajan ka, wajanta ka fara zuwa kafin ka zo wajena ko!?."

Da sauri ya saki hannun Islaha, ya juyo yana kallon Mama.

A sanyaye ya ce, "Mama na shiga kina sallah." Ta harare sa, ta juya ta bar wajan.

Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Islaha ya ce, "Zamu yi waya" ya faWa murya a can ?asa yana fita ya bi bayan Mama.

Islaha ta bi sa da kallo kafin ta cigaba da aikinta, rayuwar gidan sam bata yi mata daWi, tana manage kawai dai bata da inda ya fi gidan. Shiyasa take jin daWi in ta fita aiki, wani lokacin ko lokacin barinta aikin ne ya yi bata dawowa, zama take yi a can ta huta da bala'in Mama.

Dan gidan indai ba Baffa yana nan ba ya yi mata daWi. Babu mai sonta a gidan, daga Baffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login