Showing 87001 words to 90000 words out of 96103 words

Chapter 30 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

58

sai yanzu nake jin haushi da ban mari kuWina ba!" Ta faWa cike da fusata.

Safeera ta ce, "yi ha?uri, ki daiga Waga murya. Amma ki daina irin haka, asibitin nan babban waje ne, kuma na manyan mutane, wata?ila babban mutum ne."

"Allah ya tsinewa manyan mutanen, Allah ya sa Wan shugaban ?asa ne ko shine shugaban ?asar da kansa. Ke ni fa sai dai a kashe ni, amma ko uban waye ya yi min bazan ?yalesa ba wallahi!."

"Wai! Hamma Saheer yana da aiki, wanann tsiwar taki kullum sake gaba take yi, bakya jin nauyi ko kaWan. Ni dai ina guje miki harshen ki, in kin yiwa wani ya share ki wallahi wani bazai share ki ba. A Nigeria ki ke, ?asar da mai kuWi shine da iko ba talaka ba. ?asar da kuWi ya take gaskiya, ?asar da kuWi ya take adalci. Ki dinga shan ruwan alwalar la'asar."

Islaha ta runtse ido ta ce, "flowing nake yi Safeera, marata ciwo take yi."

Safera ta yi tsaki ta ce, "Tunda naga kina wannan masifar na san mai lasisi ce, dan ke indai aka ga kin birkice haka tabbas you are on menstrul blood, a daidai wannan rashin kunyarki take tashi daga matakin goma zuwa Wari. Ina tausayin Hamma Saheer in kun yi aure, in kina cikin wannan yanayin ban san ya zai dinga kasancewa ba, domin rashin kunyar ki ?aruwa take yi kamar ke kaWai ake Satawa rai. Bakya iya ha?uri da komai, komai sai kin tanka."

Islaha bata ce komai ba dan ta kanta take yi. Safeera ta ce, "In Allah ya rubuta wani za ki aura ba hamma ba ya shiga uku."

A fusace ta kalle ta ta ce, "Kamar ya wani zan aura ba Hamma ba?."

Safeera ta toshe bakin ta ta ce, "Yi ha?uri Anti bala'i, wasa nake yi."

Ta yiwa mata banza, Saferra ta ce, "amma ya na ganki babu ciwo yau?."

"Na sha magani tun safe, Wazu dai na ji ciwon sosai, a nan na dinga kuka son raina."

"Banza raguwa, ace ki dinga Waga murya kina kuka saboda baki da juriya. Wannan in aka shiga Wakin haihuwa ban san ya za ki yi ba."

"Baki san me nake ji ban. Ni dai wannan mutumin ya cuce ni, ya fasa min waya a banza."

"don Allah ki bar batun fasa wayar nan, ki zo mu je kar ki Sata a jikinki."

Islaha ta ce, "gida zan je kawai, zazzaSi nake ji sosai."

Safeera ta ce, "zo mu je, na ji labarin asibitin nan a cikin banWakin mata har sanitary pads akwai."

Ta faWa tana ri?e hannunta suka cigaba da tafiya, kafin Safeera ta ce, "jikinki ya yi zafi, Allah ya yaye miki wannan ciwo." Ta amsa da amin suna tafiya a hankali.

Reception suka koma, islaha ta koma ta ma?ale a jikin bango ta ce, "Safeera sanyi."

Saferra ta ?arasa wajan ma'aikatan ta tambaye su suka nuna mata hanyar banWakin, ta ja hannun Islaha suka tafi. Suna shiga banWakin Saferra ta buWe inda suka faWa mata sai ga pads da yawa a leda cikin tsafta, har wasu flowers aka zuba a ciki suna tashin ?hamshi.

Islaha ta bi su da kallo ta ce, "Safeera Allah ya sa ba kallo muka zo yi duniya ba, yadda muke kallon wasu su burge mu, Allah yasa mu ma a kalle mu wata ran, Allah ya azurta mu."

Safeera ta Wauko Waya ta c, "amin ya Allah Islaha, arzu?i ya yi a duniya. Mu je ki yi amafani dashi."

Islaha ta ce, "Ke ni fa ba dan Hamma ba ko, mai kuWi zan aura wallahi, Ina son lavish life. Amma Allah zai azurta mu tare da Hamman."

"Bazna tanka ba, yanzu na yi magana ki ka harare ni."

Islaha ta yi dariya ta ce, "ai dole sai na canja komai na jikina fa, mu je ku sauke ni a gida sai im dawo."

Safeera ta ce, "amma ki saka sai mu tafi, kar ki Sata jikinki."

"Ba sai na saka ba, kin san yanayin da nake fama baya wani zuwa a ranar farko, sai gobe sannan zan Wan dawo normal, mu je gidan kawai."

Safeera ta ce, "sannu, kina shan wahala sosai."
"Bari kawai, wahala kam ina sha" ta faWa cikin kasala suka fito tare.

Ta ?arasa wajan Mama ta ce, "Mama zan je gida in dawo, bana jin daWi."

Mama ta ce, "Allah ya ?ara sau?i, ki je ki dawo. sanyin wajan nan ma sai ya yi miki illa, in za ki dawo ki sako hijjabi."

Islaha ta bi Mama da kallon mamaki jin tana nuna mata kulawa kamar ba itace mai Waga mata hankali tana zaginta ba. Islaha ta Waga kai ta ce, "to Mama" ta faWa suna fita tare da su Saleem.

Ko a mota mitar fasa mata waya kawai take yi. Ta ?i shiru da maganar, dan da gaske an cuce ta, tunda kuWin screen Win yana da tsada.

Saleem ya gaji da mitar ya yi dariya ya ce, "Islaha kawo wayar, yanzu zan je kasuwa sai in gyaro miki."

Islaha sai ta ji kunya ta kamata, ta Wan sauke kai ?asa tana murmushin munafurcu ta ce, "kar na Wora maka nauyi."

"Babu komai, kawo kawai."

Islaha ta bawa Saferea ta ba shi. Safeera ta yi dariya ta ce, "Allah ya wanke wanda ya fasa wayar nan daga mitar ki. Kai Islaha wallahi ke masifaffaiya ce, Allah ya sassauta miki wannan masifa kafin aure, in ba haka ba Hamma yana ruwa."

Islaha ta ce, "kuma wallahi ban yafe masa ba, in mu ka kuma haWuwa sai na zabga masa mari. Kuma Hamma daman ya san wacce ya Wauka."

Suka yi dariya ita da Saleem suna hira har suka je gida, ta sauka ta shiga gida itama ta shiga gida.

Islaha ko da ta yi wanka ta canja kaya magani ta sha ta kwanta dan zazzaSi ya gama rufe mata jiki, ba jimawa bacci ya Wauke ta.

Rehaan da ya shiga mota kafin ya bar car park Win wajan ya ja ya tsaya, yana hango ta ita da Safeera a wajan a tsaye, da yadda take masifa tana nuna mata waya ya san maganarsa take yi.

Ya sauke nunfashi yana tunani a zuciyarsa, yana so ya nuna mata waye shi, yana so ta san waye, yadda nan gaba in aka ce ta yiwa wani wanda bata sani ba abinda ta yi masa baza ta iya ba. So yake ya koya mata hankali, ya yi mata abinda zata ga ?arfin ikon da yake dashi a ?asar, ya yi mata abinda za a kasa cetonta daga hannunsa.

Babu wanda ya taSa latsa shi a duniya kamar ta, ko namiji gender Winsa ba a taSa samun wanda ya kalli idanunsa ya yi masa wannan shirmen ba. Amma ga mace, yarinya ?arama tana kallonsa tana faWa masa abinda ta ga dama. Ai ko bai yi niyar Waukar mataki ba dole ya Wauka, dan bazai saurara mata ba, dole ta yi hankali saboda gaba.

Ya girgiza kai ya Wauki waya yana dannawa kafin ya saka a kunne ya ce, "track her" abinda ya faWa kenan ya kashe wayar yana kallo suka bar wajan.

Ya girgiza kai yana tunanin irin hukuncin da ya kamata ya yi mata, dan bai taSa jin haushin wani in ya faWa masa magana kamar yadda yake jin haushin ta ba, ko a gidansu in aka yi masa abu baya bari ya dame sa, amma ya rasa meyasa ita abinda take yi masa ya dame shi haka.


Ya sake kallon mirror ya ga sun bar wajan, ya girgiza kai a bayyane ya ce, "Islaha!."

Ya maimaita sunan da ya ji a lokacin da Safeera ta kira ta. Ya tuna kalmar Allah ya isa da ta yi masa, ya girgiza kai ya cigaba da zama a motar ba tare da ya je ko ina ba.

A lokacin Jazy ya ?araso wajan ya ?wan?wasa glass Win, ya buWe ya ce, "me ka ke yi a nan kuma?."

"Kawai ina nan ne."

"Okay, ni dai in anjima zan koma Uk, in na tafi yanzu baza ka sake ganina ba."

"baza ka je Jedda ba?."

"Bzan je ba gaskiya. Ka yi Alma warning, kar tazo ta dame ni, wallahi maganinta zan yi" ya faWa yana barin wajan, shima ya fito daga motar yana gyara zaman hular kansa suka koma ciki.

Nana Haleema
'
*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 024.*


Islaha bacci ta yi sosai sai lokacin sallar la'asar ta farka, ta mi?e jiki a sanyaye babu ?arfi, ta sake yin wanka ta shirya ta rufe gidan ta shiga gidansu Safeera.

Allah ya taimaka Umma bata nan, daga ita sai ?annenta ta. Islaha ta ce, "Bestie zan koma."

Safeera ta bita da kallo ta ce, "gabaWaya kin canja, fuskarki ta Wan kumbura kaWan. Wannan abu yana baki wahala sosai."

Ta sauke numfashi ta ce, "bacci na yi, ban jima da tashi ba."

"Yanzu ya batun kuWin?."

"Sai gobe in sha Allah."

"To ga wayarki, Wazu ya aiko min da ita ya ce na kai miki."

Islaha ta karSi wayar ta ga an canja mata screen ta dawo kamar dah. Ta yi murmushi ta ce, "na gode sosai, bara in yi masa waya na yi godiya, dan na san ya kashe kuWi da yawa."

Safera ta yi murmushi tana ji suna waya tana yiwa Saleem godiya. Bayan sun gama Islaha ta ce, "Ya batun Umma, Kin yiwa mutanen KT Win magana?."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "na yi magana da Yayan Umma, ya faWa min zai yi mata magana in zara ta ji."

Islaha ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah kar ya bawa Umma ikon tafiyar nan, addu'a zamu dinga yi kawai" ta faWa suna fara fitowa daga falon su Safeera.

Safeeea ta ce, "amin. Akwai abinci in za ki ci."

Ta kalle ta ta ce, "kin san in ina cikin wannan yanayin bana iya cin abinci sosai, na fi son abu mai ruwa da kayan za?i."

"Ai za ki sha gata, tunda wanda zaki aura duk ya san da wannan tsarabe-tsaraben naki, kin ga sai ki sake sangarcewa."

"Kamar kin sani kuwa, kafin ya tafi haka ya bani kayan za?i in ajjiye."

Safeera ta yi dariya, bata ce komai ba ta raka ta har ?ofar gida ta hau napep ta koma asibiti.

? ?? Lokacin da ta koma a nan ta tarar da akwai ba?i yan dubiya, wasu ta san su wasu kuma bata taSa ganinsu ba.

Ta samu waje ta zauna, Sadik ya zo kusa da ita ya ce, "Islaha ya jikin? Mama ta ce bakya jin daWi."


"na ji sau?i sosai. Ya batun kuWin?."

"Abu na farko, an samu mai bada ?odar."

Islaha ta buWe ido ta ce, "da gaske an samu?."

Sadik ya murmusa ya ce, "da gaske Islaha. ?anin Baffa ne, ya ce zai iya bayar da komai akan Baffa. Yanzu jira mu ke yi Dr yazo mu je dashi mu san abinda ya kamata mu yi. Fatan mu Allah ya sa komai ya yi daidai dana Baffa Win."

Islaha ta ce, "Alhamdu lillah! Kai amma na ji daWi sosai."

Sadik ya ce, "nima na ji daWi sosai Islaha, yanzu jira zamu yi ya zo sai a san abinda za a yi."

Ialaha ta ce, "mu je mu duba ko ya dawo." Bai musa ba suka nufi office Win Dr Isma'il. Suka yi? sa a yana nan, suka sanar dashi abinda ya ke tafe dasu, ya ce su je azo donar Win.

Tare suka koma wajan likitan, aka shiga da ?anin Baffa suka zauna.

Dr ya kalle sa ya ce, "Malam ya sunanka?."

Mutumin ya ce, "Sunana Ya?ub."

"Malam Ya?ub ya ku ke da Mutsatapa maddibo?."

"Yayana ne, uwa Waya mu ka haWa."

"Shekarunka nawa?."

"Arba'in da uku."

"Kana da aure?."

"A'a, na taSa yin auren dai amma maatar ta rasu."

Dr ya ce, "ka amince zaka bawa Mustapaha ?oda ba tare da tilastawa ba?."

Ya gyaWa kai ya ce, "na amince, domin ya wuce komai a gare ni."

Dr ya ce, "shikenan. Gobe in Allah ya kaimu litinin, ku zo da safe za a yi gwaje-gwaje dan mu san matakin lafiyar ka, zamu duba ka in komai ya yi daidai, zamu saka ka a tsarin abincin da ya kamata ka ci kafin ayi aikin."

Sadik ya ce, "mun gode likita."

Suka gaisa dashi ya ce, "babu komai, Allah ya ?ara lafiya" suka amsa da amin suka fito daga office Win suka koma suka zauna.

Suna zaune Hanan ta shigo ita da wani saurayi matashi mai ji da iyayi, suka ?araso inda suke zaune. Yana gaida Mama sai wani yatsina yake yi yana yau?i kamar kuSewa.

Ya ce, "Mama ya mai jiki?."

"Mai jiki da sau?i."

"Allah ya ?ara sau?i." Aka amsa da amin.

Ya saka hannu aljihu ya Wauko dubu Wari biyu ya bawa Mama ya ce, "Mama a siyi magani, sannan in akwai abinda ake bu?ata a sanar dani zan bayar."

Ba tare da tunanin komai ba Mama ta karSa tana ta zuba masa godiya, Hanna sai iyayi take yi saurayinta ya zo ya bada kyautar dubu Wari biyu.

Labiba kuwa ta haWe rai, kishi da ba?in ciki suka mamaye mata zuciya. Ba haka take so ba, bata so ta ga Hanan ta fita samo kuWi, bata so ta ga Hanan da samari kala-kala ita kuma ba ko yaushe take samu ba. Hakan yana ?ona mata rai, bata so Hanan ta fita ko kaWan.

Islaha dai tana zaune tana ganin ikon Allah, tana zaune tana ganin yadda ake kishi akan bin mazan kan titi. Tana kula dasu duka, ita Hanan da biyu take wani abun, tana yi tana kallon Labiba. Ita kuma Labiba ga kishin nan ya bayyana a tare da ita. Ta yi tsaki, a bayyane ta ce, "Allah ya kyauta."

*****

Rehaan da ya koma Waki kasa bacci ya yi, duk da baccin yake so ya yi amma ya kasa, so yake ya samu dama ya nunawa yarinyar can waye shi, so ya ke ya yi mata abinda bazata sake ganin wani ta ce masa waye kai ba. GabaWaya abin ya dame shi, ya rasa meyasa ta cushe masa zuciya har haka.

Ya yi shiru ba ya cewa komai, duk da ba hira ake yi ba, Mamy ce kawai a zaune sai Banisha.

A lokacin Jafar ya shigo da sallama suka amsa, ya ?araso ciki ya kalli Mamy ya ce, "Mamy in sha Allah da daddare zan koma Uk."

Mamy ta ce, "da wuri haka?."

"Eh Mamy, akwai aikin da zai mayar dani ne dole in koma."

"Allah ya kiyaye Jafar."

"Amin Mamy."

Rehaan sai a lokacin ya buWe ido ya kalle sa ya ce, "baza ka bari mu tafi tare ba?."

Ya kalle sa cikin harara ya ce, "kai fa Jeddah zaka je daga nan, ni kuma kai tsaye can zan wuce."

"Ba sai ka raka ni Jedan ba."

"ko ina sai na raka ka? Kai kamar wani Wan ?aramin yaro komai sai an yi maka?. Ka ga Malam, ka ko yi yin abu kai kaWai ba tare dani ba."

Rehaan bai ce komai ba ya Wauke kai daga kallonsa, dan ya san tunda ya ce haka bazai tsaya Win ba.

Mamy kam murmushi take yi, ta san a duk duniya Rehaan Winta bashi da wani in ba Jafar ba. Shiyasa take son Jafar, bata jinsa a matsayin wanda zai auri Riyya, tana yi masa kallon Wanta kamar Rehaan. Dan a duniya in kana so kaga farin cikin ta, ka so Wanta.

Rehaan ya mi?e zaune ya ce, "zamu koma gida, amma ni bazan koma gida ba Mamy, zan je guest house akwai abinda zan yi."

Mamy ta kalle sa ta ce, "ba ka son komawa gidan ne kawai Rehaan."

"A'a Mamy, akwai abinda za a kawo min, in na gama zan dawo gidan in sha Allah."

Mamy ta ce, "shikenan ya yi. Yanzu zamu tafi?."

Ya Waga kai alamun eh ta ce, "to mu je."

Ma'aikatan asibitin da kansu suka shigo, hatta handbag Win Mamy ri?e mata aka yi, aka raka du har inda mota take, suka shiga suka tafi sannan kowa ya watse, ana murnar an rabu lafiya.

? ? ? Islaha basu koma gida ba sai bayan sallar i'sha sannan Sadik ya tsaya a ?ofar gidan da mota. Ta kalle shi da murmushi ta ce, "na gode Hamma Sadik, Allah ya saka maka da alkhairi."

Ya yi murmushi ya ce, "Matar Hamma kenan. Ni da Saheer tare muka taso fa, Baffa babana ne kamar yadda babana yake babansa. Duk mun zama ?an uwa, kar ki damu da wannan."

Ta yi murmushi ta ce, "gaskiya ne. In sha Allah da safe zan je bank saboda zancen loan Win nan, in na samu zan sanar da kai."

Ya yi murmushi ya ce, "Allah ya kaimu, ki kwantar da hankalinki, komai zai zo da sau?i in sha Allah." Ta Waga kai daga nan ta fita ta shiga gida.

Ya bita da kallo yana murmushi, sai kuma ya girgiza kai ya ce, "Islaha ta Saheer. Tana da ?o?ari, yadda ta damu da Baffa ko ?a?ansa basu damu dashi ba. Shege Saheer, ba dai wayo da hange ba, ashe kaWai ya san me yake shiryawa, shiyasa ya ?wamuso ta daga gidan marayu. Ya yi zaSe mai kyau" ya faWa yana dariya ya ja motar ya tafi.

Islaha da ta shiga cikin gidan bata shiga harkar kowa ba, wanka kawai ta sake yi, ta sha black tea ta kwanta. In ta ce zata kula ?an matan Mama faWa zasu ja ayi, ita kuma ba wannan ne a gabanta ba. Da wuri ta yi bacci da niyar gobe ta tashi ta je banki.

? ? ? Rehaan lokacin da suka koma gida tunda suka shiga yake jinsa wani iri, gabaWaya rayuwar gidansu bata yi masa daWi ko kaWan, sai ya dinga jinsa daban kamar wani ba?o. A haka ya zauna a falon Mamy, ya yi shiru yana kallon waje Waya cike da tunani.

Abba ne ya shigo da sallama, Rehaan ya amsa yana tashi zaune sosai. Abba ya ce, "ashe kun dawo gida, yanzu nake shirin zuwa asibitin." Ya Wan Waga kai ya ce, "mun dawo Abba."

Abba ya zaunaa kusa dashi sannan ya ce, "ya jikin?."

"na samu sau?i."

"Allah ya ?ara sau?i, ya kiyaye gaba."

"Amin Abba."

A lokacin Mamy ta dawo, ta mi?awa Rehaan tea ya karSa ta zauna a gefensa. Ta kalli Abba ta ce, "ba mu jima da dawowa ba ai."

Abba ya girgiza kai ya ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login