Showing 6001 words to 9000 words out of 96103 words

Chapter 3 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

47

sai Saheer sai babbar gidan wacce ta yi aure. Baayan su babu wanda yake nuna mata so.

Ta san ita ba kowa ba ce a gidan, bata da kowa sai Hamma Saheer, shine uwa kuma shine uba a gare ta, Yayanta kuma mijin da zata aura.

Kallonsa kaWai yana ?ara mata farin ciki da jin daWi a zuciyarta, shi kaWai ne mai tausayawa rayuwarta da son ganin ta je matakin nasara. Ya jure ?alubale da yawa akanta, ya jure Satawa da kowa kawai dan ya ri?e ta a gidansu ba tare da sun haWa jini ba.

Bata san shi ba, shima bai santa ba. Sanadin zuwa gidan marayu ziyara ya haWa su, daga nan ta tsinci kanta a cikin gidansu da amincewarta.

Saboda shi take Wagawa Mama ?afa, tana sharewa in aka yi mata ba daidai ba. Amma ba dan shi ba, wata ran sai dai azo aga tana dambe da Hanan ko Labiba. Bata son raini da wula?anci ko kusa.

Saheer kuwa Waki ya shiga wajan Mama, ya same ta zata fito daga Wakin, bata kula sa ba ta dawo falo ta zauna, shima ya zauna.

Ya ce, "Mama barka da dare." Bata kula sa ba ta yi masa banza.

Saheer ya ce, "ki yi ha?uri, na shiga kina sallah."

"Sai da ka gama gaisawa da ?ar gold sannan zaka zo inda nake ko Saheer?."

Ya sauke numfashi ya ce, "ba haka bane Mama, wallahi na shiga kina sallah."

"?arya ka ke yi Saheer, ka nuna min son da ka ke yi mata ya fi wanda ka ke yi min. Ka ga in ka aure ta, wata ran ma daina kula ni zata ce ka yi."

Saheer cikin damuwa ya ce, "ki yi ha?uri Mama."

Ta ja tsaki cikin faWa ta ce, "ni fa tun yarinyar nan bata kai haka ba ba sonta nake yi ba, saboda kai na amince take zaune a gidan nan tun ba a kai haka ba. Haka kawai babu dangi uba da uwa, ka kwaso mana yarinya ka kawo mana?."

"Mahaifinka da yake bakin ku Waya, ya goya maka baya harda shige maka gaba a aurenta. Wata?ila yarinyar nan mayya ce, wata?ila ba ta hanyar aure aka same ta ba. Tun farko laifina ne da na amince wallahi, gashi yarinyar tana neman ?wace min kai, tun kafin ka aure ta!."

A sanyaye ya ce, "har abada babu wanda zai ?wace miki ni, ke ki ka haife ni fa Mama, bani da wata sama dake."

"?arya ka ke yi, ka fi sonta dani."

"Ina son Islaha Mama, amma bata kama ?afar son da nake yi miki ba. Ki yi ha?uri" ya faWa yana saka hannu a aljihu ya Wauko rafar Wari biyar ya ajjiye mata.

Sannan ya ce, "a yi ha?uri Mama." Dan ya san indai da kuWi yanzu zata sauka.

Ganin ya ajjiye mata kuWi masoyanta, sai ta basar ta girgiza kai, ta ja kuWin kusa da ita ta ce, "shikenan ai. Ka je ka huta."

Ya mi?e ya fita, yana so ya ga yanayin da Islaha take ciki, dan yana da tabbacin ta ji kalaman Mama.

Islaha ba jimawa ta gama girkin, ta fito ta wuce Waki ta Wauki wayarta a lokacin ta ga kiran chairman.

Kiransa ta yi, yana Wauka ya ce, "Islaha gobe ki zo office da wuri, akwai aikin da nake so mu yi." Ta amsa da to ta kashe wayar ta ajjiye tana sauke numfashi.

Falon ta dawo ta tarar kowa ya zuba abinci yana ci, bata ce komai ba ta zuba nata ta zauna a gefe tana ci a nutse. Tana ganin irin kallon da Saheer yake yi mata, amma ta basar ta cigaba da cin abincin ta bata sake kallonsa ba. Bata so ya jawo mata hayaniya, dan Mama bata raina ?aramin abu.

Wayar Mama aka kira, ta Wauka tana cewa, "Kin faWa mata gobe ne tafiyar?."

Daga can Sangaren aka ce, "eh ta sani."

"Yauwa, ta san tsarin dai?."

"Ta sani."

"Yauwa, sannan ki faWa mata, ni ban damu da alkhairin da fararen fata suke yi ba, kawai a haWa min kuWina. Dan wallahi bazan Waga ?afa ba." Mama ta yanke wayar.

Hanan ta ce, "Mama nima a tura ni aikin nan mana, ana samun kuWi muna zaune a gida?."

Mama ta kalle ta ta ce, "ke da ki ke neman mijin aure ina ke ina tafiya wata ?asar?."

Ta juya? ta kalli Islaha ta ce, "Dama dai Islaha ce sai ta tafi, ko babu komai ta tattara kuWin aurenta."

Saheer ya tarin numfashin Mama ya ce, "Allah ya kiyaye, me Islahaa zata je yi aiki wata ?asar Mama? Babu inda zata je, komai da ake yi na aure zan yi mata."

"Indai babar Islaha ba mayya ba ce, to tabbas jikar ?an bori ce. Ko sun lashe maka kurwa, ko sun tsafe ka" Mama ta faWa tana kallonsa.

Shiru ya yi bai amsa ba, dan baya so maganar ta yi ta tsayi, a Islaha a wajan.

Mama bata dakata ba, ta ce, "tun kafin ayi auren har an asirce min kai? Wato ga mai kuWin banza, kai zaka yi komai ko?." Shiru ya yi bai ce komai ba, kafin ta sake magana ya mi?e ya fita daga falon.

Labiba ta ce, "Mama kin haWu da sirika tun yanzu. Wannan in ta auri Hamm wallahi sai ta hanasa gaishe ki" ta faWa tana nuna Islaha sa yatsanta.

Mama ta ce, "ita Win banza, yaushe aka ?yan?yashe ta da zata hana Saheer gaishe ni?."

"Ga zahiri nan Mama. Kina gani yana katse ki kina magana, yana cewa shi zai yi mata komai?. Wallahi nan gaba zata iya saka ki kuka."

"In tana da iyaye a duniya, ko su ?arya suke yi. In kuma yar titi ce, na fi iyayen nata tantiranci.."

Mama ta kalli Islaha da take aikawa da Labiba harara ta ce, "Ke Labiban ki ke harara?."

Islaha ta haWe rai, cikin Sacin rai ta ce, "bana so su dinga shiga harkata, in kina yi min faWa su daina saka min baki, ai basu ne gaba da Hamma ba, shine gaba dasu."

Labiba ta buWe baki, bata yi mamaki ba, dan ta san Islaha zata aikata fiye da haka.? Ta ce, "TabWi, to ke a su wa?."

Islaha ta buWe idanunta ta ce, "ni a matar Hamma."

Hananan ta ce, "to daman waye zai kwashe ki, Ai sai dai Hamman, in ba shi ba sai wa?. Waye zai Wauki ragowar titi?. Ki bari a Waura Win, kafin ki fara kiransa da mijinki."

"Wanda ya Wauki ragowar titi, shima ragowar titin ne Hanan. Kuma tunda har ake tsayar dake aka ta ya, Islaha ta wuce ace waye zai kwashe ta."

"Kutmar uba! Me ki ke nufi? Hamma ne Wan iska?."

Zata yi magana suka haWa ido da Mama,? sai ta fasa ta Wauke kai daga kallon Mama.

Mama ta ce, "mara kunya, kina gidan ubansu kina cin arzu?i kina yi musu rashin mutunci. Zo nan."

Islaha a hankali ta ?arasa ta zauna, Mama ta bita da harara ta ce,"ban ga kin bani komai ba yau, ko dan kin ga Wazu ban yi miki magana ba, shiyasa ki ka Wauka yau kin ci banza?."

Islaha ta rufe ido ta buWe, ta ce, "Mama aiki na ke zuwa."

"Dan aiki ki ka je ina ruwana? Aiki ke ya dama ba ni ba, abinda na sani ki bani kuWin yau kawai."

Islaha ta ce, "Mama ni bana zuwa wajan ko wanne namiji balle ya bani kuWi."

Mama ta wara hannayenta ta ce, "ni na hana ki? Ai ban hana ki samo min kuWi ne. Dan haka ki fito da dubu hamsin yanzun nan."

Islaha ta wara ido ta ce, "Wallahi Mama bani da dubu hamsin, sai dai in an yi salary....."

kafin ta karasa Mama ta katse ta, ta ce, "Keda salary na ci ubanku, sa'ar wasanki ce ni Islaha!?."

Ta girgiza kai ta ce, "ki yi ha?uri, kuma kin san ina? kawowa duk sati, yau Win na aiki ne ya yi min yawa, shiyasa ban fita."

Mama cikin tsawa ta ce, "Wannan ke ya dama, ki bani kuWi kawai. ?a?an gida suna fita su kawo, ke da ake ciyar sake a sadaka ki ce baki dasu ba. Baki isa ba Islaha."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Allah ya sani da tana da dubu hamsin da ta bawa Mama ta huta, amma bata da komai sai dubu biyar, Wazu Safeera ta karSi rancen dubu talatin Win da ta rage mata, da in ta bawa Maman ta san zata dan sauka kaWan.

Bata son wannan Wabi'ar, ace burin Mama kawai ka kawo mata kuWi, bata damu da inda zaka samu ba. In ba dan dole ba ya za a yi ta zauna a gidan nan? Shi kansa Hamman in zaka biye ta Mama, ai ba mijin aure bane.

Mama ta katse ta ta ce, "bani."

Islaha ta ce, "wallahi Mama...." Mama ta kai mata mari, Islaha ta kauce.

Mama ta ce, "kin isa..? Wacece ke da zaki kwana a gidana ya baki kawo komai ba?."

Ta nuna su Labiba ta ce, "?a?ana ne na cikina, sun fita sun nemo kuma sun bani, balle ke bari karan kaWa miya, kwashe, shara, ragowar gidan marayu?. Ki shiga hankalin ki Islaha, ki daina ganin ina wasa dake ki samu damar raina ni."

Islaha ta haWe rai, duk da ta saba da kalaman Mama amma ko yaushe in ta faWa bata jin daWi.

Ta ce, "ki yi ha?uri."

"Tashi ki bar min falo, ki fita harabar gidan nan ki zauna sai na neme ki."

Islaha ta karyar da kai ta ce, "Mama ana sanyi sosai, don Allah ki bari gobe zan nemo na kawo miki, duk inda zan samu kuWi zan samu na kawo miki."

Labiba ta ce, "Raini, Mama tana faWa kina faWa?. Lallai Mama kina da aiki, duk ranar da Hamma ya auri wannan kin mutu."

A fusace Islaha ta ce, "Labiba bana son shirme."

Labiba ta ce, "ya za ki yi dani?."

Mama ta ce, "Fita ki bani waje."

Islaha zata sake magana Mama ta ce, "Na ce ki fita!."

Abinda Islaha ta tsana a duniya shine tsawa, ta ta fita da Wan sauri tana sauke numfashi.

Mama ta bita da harara ta ce, "shashasha Mara hankali, ni za ki mayar ?aramar yarinya? Wanne kalar iskanci ne bakya aikatawa? Dan kin raina ni, naira dubu hamsin ce zata gagare ki?."

Hanan ta ce, "Wallahi Mama kuWi yarinyar nan take samu, ba ki ga manyan mutanen da take hulWa dasu ba. Hotels kuwa, babu inda bata zuwa."

Mama ta ce, "na sani Hanan, duk wani iskanci da take aikatawa na sani wallahi."

"A haka kuma zaki bari ta auri Hamma Saheer? Ta gama watsar da kanta a titi, ta gama raba jikinta ki bari ta aure sa?."

Mama ta kalle ta tana wani shegen murmushi, ta ce, "mu zuba" ta faWa tana tashi ta shiga daki.

*******

Yanayin yadda suke zaune a babban falon zai tabbatar maka da ba ?aramar tattaunawa ake yi ba, kowa yana zaune a ?asan carpet, duk sun sunkuyar da kansu suna sauraren umarni daga hajiya Daada.

Ita kaWai ce a zaune a kan kujera, ?afarta tana mi?e tana ?aWawa, hannunta ri?e da jarbi tana ja cikin isa da ?asaita. Shiru falon ya yi, babu sautin komai sai sautin karatun alkur'ani da yake tashi daga tv.?

Kowa a cikin falon farin ciki yake da taron, saSanin Mamy da ta san ?arshen alawa ?asa, ?arshen taron akanta da yaranta zai ?are, tunda ba ?aunarta suke yi ba. Shiyasa kanta yake sunkuye, bata Wago ba balle ta ga abinda zai Sata mata rai.

Daada ta bisu da kallo ta ce, "AbdulAziz kana jin abinda nake faWa ko?."

Abba ya ce, "ina jinki Daada."

"Ka yi shiru baka ce komai ba."

Ya gyara zama ya ce, "ina jira ki gama ne."

Daada ta ce, "na gama, ina jinka."

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Daada ba ?in dawowarsa nake yi ba, abinda nake dubawa a can yake aiki, a can kasuwancinsa ya fi ?arfi, ban da yanzu da ya kawo asibiti, kasuwar zamani, da sauran abubuwa ?asar nan kin san komai nasa yana can. Komai da komai nasa yana can, hatta takardar haihuwa a can take. Dawowarsa nigeria...."

Ta katse sa ta ce, "AbdulAziz ba wannan maganar na kira ka ka yi min, ina bada umarnin dawowar Muhammad cikin gidan nan!. Umarni ne ba shawara ba, komai yake yi ya tattaro ya dawo cikin gida."

"Ban damu da a can aka haifesa ba, ban damu da rabinsa ba Wan ?asar nan bane, abinda na sani Wan cikin gidan nan ne ya samar da cikinsa. In daga lahira aka auro uwarsa ban damu ba, dawowarsa gidan nan kawai nake da bu?ata. Kuma dole ayi ko sa bakwa so."

Abba ya ce, "Allah ya huci zuciyarki, ban faWa dan Sata ranki ba."

Daada ta ce, "in ma ka faWa Win ai na soke yanzu. Ba wani ne ya ce ka auro ?ar wata ?asar ba, kai ka ga zaka iya har ka aikata. Ba tare da shawarata ba ka aure ta, ban san anyi auren ba sai labari na ji, babu albarkata a cikin aurenku."

"Sannan da yake ita ta fi kowa, baza ta zauna a cikin mu ba, sai aka sauke ta a england, saboda baza ta iya zama a nigeria ba. Yanzu kuma Wan na mu ma baza a bamu shi ba? Shima a can burtaniyan zai cigaba da rayuwarsa?. Har yanzu a cikin dangi akwai wanda bai san Rehaan ba, ko ni bazan iya banbance kamaninsa ba, tunda rabona dashi yau shekara huWu kenan."

"Dadda ya zo lokacin ?aramar sallah." Mamy ta faWa jin ana neman Wora masa shekara huWu..

Da sauri Abba ya kalle ta, amma kafin su haWa ido Daada ta ce, "ina magana kina katse ni? Wacece ke ina magana kina kawo min ta ki?."

Ta kalli Abba ta ce, "ka ga rashin tarbiyyar irin na yaran ?asashen waje ko? Baka koya mata a yadda ake magana da manya ba ne? Baka ko ya mata cewa ko kai in ina magana baka isa ka dakatar dani ba?."

A sanyaye ta ce, "Allah ya wuci zuciyarki."

Daada ta ce, "da yazo lokacin bikin sallah kwana biyu ya yi kacal ya koma, Tunda ya gaishe ni sau Waya bai sake waiwaiyona ba, saboda an riga an jefa masa ?in dangin babaansa a zuciyarsa. Ke ga mai Wa, ina magana kina katse ni saboda ke ki ka haifesa."

"Wallahi baza ta saSu ba, dole ya dawo gida, kuma in ya dawo, ba a isa nan da wasu kwanaki ace zai koma aiki ba. Ya dawo aiki a Nigeria, kar na sake ji ance zai koma burtaniya da zama."

Abba ya ce, "in sha Allah, zai dawo Daada."

Daada ta ce, "ya yi kyau. Kowa ya watse, AbdulAziz ka zauna."

Cikin lokaci kaWan kowa ya tashi daga falon cikin farin ciki, kaf gidan babu mai ?aunar zaman Rehaan a wata ?asa, dan babu mai ?aunar cigaban rayuwarsa kowa so yake ya ga ya Wurkushe. A ganinsu dawowarsa Nigeria babbar na?asu ce a gare sa.

Aka bar Abba kaWai a zaune kusa da ita. Daada ta ce, "AbdulAziz, bana so na sake ji ance zai koma wata ?asar, ya zauna ya cigaba da rayuwa kamar yadda muke yi."

Ya Waga kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah za a yi."?

Ta Waga kai ta ce, "Ya batun auren Juwairiyya da Jaafar?."

Abba ya Wan yi jimm dan ya san bata son batun auren Jaafar, amma sai ya ce, "yana nan yana tafiya yadda ta kamata."

"Da zarar Rehaan ya dawo, a haWa auren harda shi."

Da sauri ya kalle ta ya ce, "Daada ba ja da maganarki nake yi? ba, amma ta ya za a haWa da Rehaan bayan, ko budurwa ma bashi da ita?."

Daada cikin ba?ar magana ta ce, "Ai na Wauka shi Win ma baturiya zai Wauko ko balarabiya."

Ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san shi take faWawa magana. Tunda ya auri Mamy kullum sai an yi haka, an kwashe shekaru da auren amma Daada ta?i saduda.

Daada ta ce, "ina so ka sani, babu yaren da Rehaan zai aura in ba bafulatana ba, wallahi ko ya Wauko wani yaren ba fulani ba sai an soke auren!. Yadda ka auri baindiya ta lalata mana zuri'a, bazan bari a sake maimaitawa ba."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "in Allah ya amince."

"Zaka iya tafiya."

"Sai anjima" ya faWa yana mi?ewa ya fita.

Daada ta yi tsaki ta ce, "kawai ka Wauko mana dangin masu tsafi cikin gida, ?an india me suka iya in ba tsafi ba? GabaWaya ka gurSata mana ahlinmu" ta faWa tana kallon gefenta.

Daada ta ce, "ke Indo?."

Wacce aka kira da Indo ta zo? ta ce, "gani Daada."

"Ki je ki kira min Saddi?a."

"To" ta faWa tana tashi ta fita daga falon.


Nana Haleema
' =?%?


*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

https://whatsapp.com/channel/0029VbC1pVN42DcoY0dAzq46

*Book 1*
*Page 003.*

?an mata guda goma ne a tsaye, kyawawa masu ji da haske. Kallo Waya zaka yi musu ka san jinin fulani ne, duba da yadda suke da kyau mai sanyi. Dukkansu basu wuce shekaru ashirin ba, babu wacce zata Wara daga ashirin, sai dai ?asa da haka.

Suna zaune a babban falo, sai wata babbar mace a zaune tana kallonsu tana murmushi.

Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, "bakwa burin zama a irin wannan gidan don Allah?."

Suka yi shiru basu ce komai ba, ta sake yin dariya ta ce, "ku saki jikinku, babu abinda zai faru a nan. Na san kun ji daWin kuWaWen da ake baku ko?."

A tare suka Waga kai alamun eh, ta ce, "To kun gani. Da kuna gidan marayu kuna rayuwa kamar ta bayi, abinci ma ba wani mai kyau ake samu ba. Ku kalli yadda ku ka canja, ku ka yi kyau kamar ba ku ba. Ni kaina yanzu na tabbatar muna da ?an mata kyawawa, da an dakusar daku a waje Waya."

Gyaran murya suka ji, ta yi musu alamu duk su mi?e suka mi?e tsaye.

Babban mutum ne ya shigo sanye da shadda fara harda babbar riga. Kana ganinsa ka ga alhaji, wanda kuWi ya zauna yake shigowa.

Ganin ?an matan sai ya yi murmushi yana binsu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login