Showing 69001 words to 72000 words out of 96103 words

Chapter 24 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

65

wannan abun na kwanta na tashi. Ni na amince zan tafi aikin indai zata zauna a gida, amma Baba ya hana, ya ce wallahi baza ni ba. Islaha ta ya zan iya zuba ido Umma ta tafi ?asar waje aikatau ina nigeria? Ni ce babba a gidan fa, ya take so na dinga tafiyar da al'amurana gabaWaya?. Ban taSa jin zafin rasa Hamma Muhammad ba sai yanzu, sai yanzu nake jin zafin rashin Wan uwa babba."

Islaha ta yi bata ce komai ba, Safeera ta ce, "shiyasa zan je Katsina na kai ?ararta wajan ?an uwanta, wata?ila in suka yi mata magana zata ji. Ina Umma ina tafiya aiki wata ?asar don Allah? Abinda mu ke ya?i dashi ni dake, gashi yazo mana har gida."

Islaha ta ce, "gaskiya tunda abin ya kai haka ya kamata a sanarwa da na gaba da Umma su Wauki mataki. Kuma wallahi Mama ce take zugata, a gabana na ji suna maganar. Ke Mama ta wuce duk yadda ake tunani, ni kaina haka aka saka ni a gaba wai sai na tafi aiki. Kin san bazan iya shiru ba, na kalle ta nace wallahi bazan je ba."

Safeera ta ce, "Gaskiya Mama ta cuce ni, tana neman ruguza min rayuwa gabaWaya."

Islaha ta ce, "ki yi ha?uri kawai, ki fara faWa musu ta waya kafin ki je. In zuwan ya kama sai in raka ki."

Safeera ta Waga kai tana dafe da kanta kafin ta ce, "me ya faru, na ji Hamma Saheer yana cewa zaki je gidan Addarsa?."

Islaha ta taSe baki ta ce, "to ni meye ma bai faru ba? Mamansa kin san ba ?aunata take yi ba. Yarinyar nan Hanan ce ta Waga hannu ta mare ni, ai kuwa kafin ta sauke na mare ta har sau biyu. Shine fa Mama wai sai na du?a na bata ha?uri, ke ma kin san sauran."

Safeera ta yi dariya ta ce, "Allah ya shirya min ke Islaha, ?anwar mijin naki ki ka mara?."

"?anwarsa ai Yayarsa ba ce, in ba dan Maman ba akwai wanda zan Wagawa ?afa a cikin gidan nan nasu ne? Wallahi babu wata halitta da zan saurarawa."

Safeera ta ce, "shine ki ka bar gida?."

"Cewa tayi na fita, har tana cewa indai tana da rai aurena da Wanta bazai faru ba. Shine shima yazo yana cemin danasani na bada ha?urin waye waye, ban san na balbalesa da masifa ba, sai da naga yayi sanyi na fahimta."

"Kina wahalar da Hamma, dan kin ga yana da ha?uri da sanyi. Dan kuma kin san yana sonki ne. In ba shi ba, ba ko wanne namiji ne zai Wauki wannan bala in naki ba, da wuri za a yanke miki hukunci.

"A'a fa, dan ina zaune a gidansu bazan Wauki ko wanne wula?anci ba Bestie. Bani na ce ya karSo ni daga orphange ba, shine ya dage ya takura sai da na bar gidan hankalinsa ya kwanta. Dan na dawo kuma bazan Wauki raini ba wallahi."

Safeera ta yi murmushi ta ce, "ni so nake ayi auren a wuce wajan. Ko dan ya yi maganin wannan rashin kunyar nan ta ki."

"Ke ko ni na gaji, so nake nayi auren na huta da wannan tashin hankalin wallahi. Kin san me?."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni fa zargina yana so ya tabbata akan gidan marayun da na tashi."

Safeera ta ce, "me ya faru?."

Ta mi?a mata wayarta, Safeera ta karSa ta ce, "Islaha wannan ba Hafsa ba ce?."

"Itace, a hotel."

"Hotel kuma? To meye abin Waga hankali a nan? Kamar ni dake muna ya?i akan ba iskanci ne kawai yake kai mace hotel ba. Kema jiya kin je ai ko?."

Islaha ta bata labarin duk abinda ya faru kafin ta ce, "so nake na haWa hujja mai ?arfi, so nake na tabbatar da zargina ya zama gaskiya. Wallahi sai mun shiga kotu, sai na san yadda na yi maganar nan ta je gaban gwamna, dan na san irin waWannan bada?alar bai san yana faruwa ba."

Safeera ta ce, "gaskiya ne wannan, in dai maganar ta tabbata wallahi kar ki bari."

"Sai ma kin ce, wallahi bazan barta ba. Shiyasa har na yi magana da Brr Suraj, na shigar da lauya cikin maganar, dan ba ?aramin abu bane ba."

"Gaskiya ne wannan. Allah ya taimaka."

A lokacin Saleem ya shigo ya kalli Islaha ya ce, "islaha yau me yake damun masoyiyata ne? GabaWaya ko kallona bata yi ba."

Ta Wan yi murmushi ta c, "bata jin daWi ne shiyasa."

Ya kalli Safeera ya ce, "Sannu." Sai ya bata dariya ta Wan sunkuya tana dariya kaWan.

Muslim ne ya shigo yana faWin, "Islaha wai an canja kati jiya?."

Islaha ta Wauko katin ta ce, "Muslim in ba dan Allah ya kiyaye bai karSa ba, da yanzu ina cell."

Sauka yi dariya gabaWaya, ya karSa yana dubawa ya ce, "ikon Allah, ko waye da wannan aikin oho."

"Koma waye dan kansa Muslim, ni aka so a tozarta Allah ya nuna musu basu isa ba. Tunda Allah ya kare ni ban damu na san waye ba, su suka sani" ta faWa tana mi?ewa tsaye.

Saleem ya ce, "gaskiya ne, koma waye Allah ya mayar masa da muguntarsa kansa." Ta amsa da amin ta fita daga office Win. Da Ummi suka haWu bata kula su ba ta wuce.

Ummi office ta shiga ta kira Muslim a waya, babu jimawa ya shiga wajanta ta ce, "kaga kallon rainin da yarinyar nan take yi min? Yanzu haka zamu zuba ido tana yin abinda taga dama a gidan nan muna gani?."

Ya kalle ta ya ce, "ta tsallake jiya, amma baza ta tsallake tarko na gaba ba wallahi."

"Na gaji da ganin yarinyar nan wallahi, bana so na buWe ido na ganta a cikin gidan nan."

"Ki ?yale ni, na san abinda zan yi mata. Dashi Mr Jafar Win da ta haWu dashi zan haWasu, wallahi sai ta yi danasanin abinda zan yi mata."

"Ka dai yi da gaggawa, dan wallahi na tsane ta."

"Na fi ki tsanarta, sai da na shekara biyar a gidan nan sannan yarinyar nan tazo. Amma tunda tazo ta mamaye komai, komai ta mamaye, komai itace, kamar ba a bayan mu take ba. Ko shekara uku bata rufe a gidan nan ba, amma itace sama da kowa. Ta ya zan barta?."

Ummi ta girgiza kai ta ce, "duk abinda za a aikata ayi,? indai har zata bar gidan nan." Ya kalle ya girgiza kai bai ce komai ba ya fita.

Islaha bata jima da fita ba ta koma office Winsu Safeera ta tarar da Saleem a zaune yana ta aikin rarrashinta.

Ta yi murmushi ta ce, "masoyan asali."

Saleem ya ce, "mun kai ki, keda Hamma?."

"Mu ai haWin Allah."

Safeera ta ce, "mu kuma haWin ki ne?."

Ta yi dariya ta ce, "HaWin offfice. Wayata manta a nan."

Safeera ta ce, "Allah ya taimake ki, dan wallahi yanzu muka dawo office Win, ban kula da wayar ki ba."

Bata ce komai ba ta fita tana faWin, "in kin gama ki yi min magana, ni na gama."

Saleem Wan kira ta da ?arfi, ta dawo ya ce, "kina da labarin an bawa Mr Ray guba?."

Ta Wan zaro ido cike da mamaki ta ce, "guba?."

"Wallahi. Baki ga labaran ?arfe shida ba kenan, Ummi ce ta karanta."

"Ban gani ba wallahi."

"Shiyasa, magana ta yaWa duniya ta shiga ko ina. Jiya a asibiti ya kwana."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Allah ya ba shi lafiya" ta faWa tana fita tana duba wayarta.

Abinda ta gani a wayar ya saka ta zaro ido tana dafe ?irji, cike da tashin hankali da mamaki.

Book 2&3 1k on telegram

Nana Haleemad'?
'
*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ??? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 019.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

_____________

Islaha a kiWime take bincika wayarta amma babu hotunan Hafsa babu alamarsu. Ta duba trash da duk inda take tunanin zata gansu amma babu.

Mamaki da al'ajabi ya kamata, ta ri?e baki zuciyarta tana bugawa cike da tsoro.

Da hanzari ta juya ta koma office Winsu Safeera, tana shiga ta ce, "Safeera kin goge hotunan da na nuna miki ne?."

Safeera da mamaki ta ce, "ban goge ba, ta ya zan goge waWannan hotuna nan masu amfani?."

Islaha ta dafe kai ta ce, "Safeera daga fita ta daga office Win nan an goge hotunan nan, an goge su wallahi."

Safeera ta mi?e tsaye cike da tashin hankali, ta kalli Saleem da yake kallonsu, ta sake kallon Islaha. Cikin mamaki ta ce, "An goge kuma!."

"An goge su, babu inda ban duba ba, amma ban gansu ba."

Safeera ta ce, "Islaha wallahi ban goge ba, ni ban san ma kin bar wayar nan a office Win nan."

Saleem ya ce, "me yake faruwa? Wanne hotuna ne?."

Islaha bata kula shi ba ta ce, "da ki ka fita daga nan waye ya shigo?."

"Ban sani ba, da na san wayarki a nan bazan fita na barta a nan ba."

Ta dafe kai ta ce, "Daga ni sai ke, sai Hamma da Barr ne kaWai muka san da hotunan nan, waye ya san dasu har ya biyo ni office ya goge?."

Safeera ta ce, "Wallahi nidai ban goge miki ba, akan me zan goge to?."

Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "dallah bana zarginki, ki daina yi min rantsuwa. Abin ne ya....."sai ta kasa ?arasawa ta dafe kanta cikin yanayin da bata san meye ba.

Saleem ya ce, "kun barni a duhu, ku faWa min abinda ya faru mana. Wanne hotunana aka goge?."

Islaha ta kalle sa ta ce, "ka yi ha?uri, bazan iya faWa maka a yanzu ba, amma nan gaba kana daga cikin waWanda zasu sani. Safeera in kin gama mu wuce kawai" ta faWa tana fita daga offife Win cikin mamakin wanda ya san da hotunan har ya goge.

A wannan yanayi ta kira Saheer ya zo ya Wauke su a mota suka tafi.

Tunda suka shiga bata ce komai ba, tana tunanin wanda ya goge hotunan nan, tana mamakin ya aka yi aka san dasu har aka biyo ta aka goge?. Kuma gashi a wajen aiki ne, kenan an san ta Wauki hotunan?. Amma babu wanda ya ganta, ko an ganta ai ba a san ta yi hoto da video ba. Lallai akwai lauje cikin naWi, dole ta dage sosai akan lamarin nan, dan taga ba abin wasa bane ba.

Saheer ya katse mata tunani, ya ce, "Baffa ya ce na mayar dake gida, ko gidan Addn kar ki je."

Ta Wago ido ta kalle sa suka haWa ido, ya Wauke kai ya ce, "Ya kira ki ba ki Wauka ba, ya ba da umarnin in mayar dake gida. Amma in baza ki koma ba ki kira sa ki faWa masa, sai in kai ki inda ki ke so."

Shiru ta yi bata tanka ba dan bata san me zata ce ba, ta ya zata iya yi masa musu akan maganar Baffa? Ai ko bata so dole ta yi ha?uri.

Har suka je ?ofar gidan bata ce komai ba, sai da ya tsayar da motar Safeera ta ce, "Hamma sai anjima."

Ya yi murmushi ya ce, "To Safeera, a gaishe da Umma." Bata ce komai ba ta fita ta shiga gida.

Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ka san meye?."

Ya kalle ta ya ce, "ina jinki."

"Hotunan nan da na nuna maka na hafsa?" Ta faWa da sigar tambaya.

Ya girgiza kai ya ce, "ina ji."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wallahi an goge su Hamma."

Ya buWe ido cike da mamaki ya ce, "kamar ya an goge? Waye ya goge su?."

Ta Wan tafa hannunta ta ce, "wallahi ban sani ba Hamma, abinda na sani na gama nunawa Safeera kenan, sai na bar wayar a office Winsu na fita naje na dawo. Ashe itama ta fita bata san na bar wayar a wajan ba, wallahi dana dawo na duba babu su ko alama."

Saheer ya ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Mu ga wayar."

Ba musu ta mi?a masa ya karSa yana dubawa, kafin ya Wago ya ce, "An goge su gabaWaya."

Cike da damuwa ta ce, "ban san waye ya goge ba."

"Waye ya san dasu?."

"Daga kai sai safeera, sai....." sai bata ?arasa ba tana kallonsa.

Ya bita da kallo ya ce, "Sai waye?."

Ta Wan sauke numfashi ta ce, "Barr Suraj. Na sanar dashi ne saboda shine lauyan da nake so ya yj handling case Win. Kuma na tura masa, amma view once."

Ya zuba mata ido yana kallon ta har ta kai ?arshe, kafin ya ce, "waye ya saka ki tura masa?."

Ta kalle sa ta ce, "Saboda lauya ne, dole ina da bu?atar lauya."

"To yanzu amfanin me hakan zai yi miki?."

Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi tsaki ya ce, "Bakya jin magana Islaha, bakya jin magana kwata-kwata shiyasa bakya jin maganata. Sai da na faWa miki kar kowa ya san maganar nan amma sai da ki ka zagaye ki ka faWa masa. Dan kin faWawa Safeera ba laifi bane, Safeera ?ar uwa ce a gare mu gabaWaya. Amma shi fa?."

Ta rausayar da kai ta ce, "shima Wan uwa ne a gare ni."

Ya harare ta ya ce, "yanzu me gari ya waya? Meye amfanin faWa masa Win?."

Ta sauke numfashi ta ce, "Wallahi bana zargin Barr ko kaWan, na san bazai aikata min haka ba."

Ya kalle ta yana harWe hannu a ?irji ya ce, "tunda shi bakya zarginsa, faWa min ni ko Safeera waye abin zargi?."

Ganin yadda ya kafe ta da ido sai ya bata dariya, ta yi dariya dan ta san yana matu?ar kishi da Suraj, tunda Suraj ya furta yana sonta shikenan Hamma yake jin haushinsa.

Ta kalle sa ta ce, "ni na isa? Wace ni da ce haka?."

Bai ce komai ba ya Wauke kai daga kallonta bai kula ta ba. Islaha ta ce, "duk wanda ya goge ma ya je dan kansa, sun yi a banza dan wallahi bazan bar maganar nan ba."

Ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "hakan alamu ne na ana bibiyar ki, hakan alamu ne da an san kina bincike akan lamarin nan."

"Hakan kuma shine alamar da take nuna min zargina gaskiya ne Hamma. Zamu haWu dasu Hafsan, zan san duk abinda zan yi akan maganar nan."

Ya bita da kallo a sanyaye ya ce, "ki bi komai a hankali, kin ga gobe zan yi tafiya, don Allah ki nutsu."

Ta yi murmushi ta ce, "To Hamma."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "akwai abinci na siya miki" ya faWa yana Wauko ledar ya mi?a mata ya ce, "ki bawa Safeera sai ki ri?e sauran. Kayanki na kai miki Wakinki na ajjiye."

Ta yi murmushi tana wasa da hannunta bata ce komai ba. Saheerya ce, "ya jikin, kin daina jin ciwon?."

"Na daina, daman yanayi ne kawai."

Ya Waga kai ya ce, "ki shiga ciki, zan shigo in anjima."

Ta Waga kai tana murmuahi yana kallon ta. Ya ce, "Debbo am."

Ta kalle sa ya ce, "da na dawo daga Niger za a yi auren mu in sha Allah, ina so na mallake ki nan kusa."

Ta yi dariya ta ce, "Allah ya dawo min da kai lafiya Hamma."

"Amin matar Hamma. Ki je ciki, ki fara shiga wajan Baffa yace yana son ganinki. Nima yanzu zan shigo." Ta amsa da to ta fita daga motar ta fara shiga gidansu Safeera.

Da ?anwar Safeera suka haWu, ta bata abincin ta koma dan bata son haWuwa da Ummansu Safeera.

Kamar yadda ya ce wajen Baffa ta shiga, yana ganinta ya yi murmushi ya ce, "Islaha kin dawo?."

Ta yi murmushi itama, ta ?arasa ta zauna ta ce, "na dawo Baffa. Ina yini?."

"Lafiya lau, ya aikin na ki?."

"Alhamdu lillah Baffa."

"To ma sha Allah. Saheer ya faWa min duk abinda ya faru, ki cigaba da ha?uri kin ji? Ko wanne bawa akwai irin tasa jarabawar, ke taki ga a yadda tazo miki, ki yi ?o?ari ki cinye sai ki dace. Kar komai ya dame ni, indai ina gidan nan baza ki wula?anta ba."

Ta yi murmushi ta ce, "In sha Allah Baffa. Amma Baffa sai na ga kamar baka da lafiya."

"Eh haka ne Islaha, kwana biyu bana jin daWi. Ina fama da ciwon ha?ar?ari, ga zazzaSi. Kin san jikin tsufa, abin sai a hankali."

Islaha ta ce, "Allah ya ?ara lafiya."

"Amin."

"Ki cigaba da ha?uri, kar wani abu ya kuma faruwa ki ce zaki bar gidan nan, har abada nan gidanku ne, kin ji?." Ta yi murmushi bata ce komai ba.

Baffa ya ce, "Tashi ki je, Allah ya yi miki albarka." Ta amsa da amin ta mi?e ta fita daga Wakin Baffan.

Da ta shiga Sangaren Mama bata nan, Sangaren shiru babu kowa. Hakan ya yi nata daWi sosai, ta ci abincin da Saheer ya bata, ta gama duk abinda zata yi babu mai takura mata.

Islaha har ta yi bacci Mama bata dawo ba, hakan ya saka ta yi baccinta hankali kwance ba tare da wata damuwa ba.

Bayan sallar asuba Saheer ya shigo yiwa Mama sallama, ya shiga Wakinta ya samu ta koma bacci.

Yana fitowa ya haWu da Hanan, Saheer ya bita da kallo ya ce, "jiya a ina ki ka yini har dare?."

Hanan ta ce, "muna tare da Mama fa."

Ya girgiza kai ya ce, "ki yi yadda ki ka zaSa Hanan, duniya dai ta ishe ki." Daga haka ya bata waje ya fita yana kiran Islaha a waya.

Tana zaune tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login