Showing 30001 words to 33000 words out of 96103 words

Chapter 11 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

78

da zuwa."

Ta yi murmushi ta ce, "Hajiya Islaha, tun Wazu nazo aka ce baki dawo daga wajan aiki ba. Gashi har ina niyar komawa dare ya yi."

Ta sake yin murmushi ta ce, "ina yini."

"lafiya lau Islaha, ya aikin?."

"Alhamdu lilah. Ina Nabila?."

"Su Nabila suna gida, suna gaishe ki."

Ta yi murmushi ta ce, "ina amsawa" daga haka ta ?arasa wajan abinci.

A lokacin Saheer ya shigo ya zauna suna hira, ta zubo abinci ta zo zata koma Waki.

Adda Sa'ida ta ce, "Islaha ki zo ki zauna a nan mana."

Ta Wan kalli Mama, ta ga bata harare ta ba sai ta dawo ta zauna, dan tashin hankali ne bata so ita.

Saheer ya ce, "ni mamaki ki ke bani Adda, har nawa Nabilan take da zaki fara tunanin wai bata yi aure ba? GabaWaya shekarun ta ashirin fa, har yaushe ta kai matakin yin auren da zaki Waga hankalin ki?."

Ta taSe baki ta ce, "ku dan ba a gidan kishiya ku ke bane, shiyasa baza ku san abinda nake ji ba, wallahi da Mama tana da kishiya da yanzu Labiba da Hannatu sun Waga hankalinsu akan aure zasu yi. Ana nan ana yar musu da magana kan sun ?i aure, musamman in suna da ?an uwa sun yi sun barsu."

"To a yar mana, duk abinda mutum zai ce ai bai isa ya yi abinda Allah bai yi ba ko? Kuma duk maganar mutum sai dai ya yi ya gama, aure lokaci ne dashi."

Ta kalli Mama ta ce, "Mama Saheer yaro ne, bai san abinda nake ji ba. Tunda aka aurar da yaranta guda buyu sa'anin Nabila, shikenan kullum cikin ba?ar magana nake. Nabila ta yi kwantai bata yi aure ba waye waye. Shiyasa nake so Allah ya kawo mata ta yi auren ta huta."

Mama ta ce, "to ina ruwan ki? Dan ayi mata gori sai me? Duk wanda ya yi nata gorin shi ya jiyo, kuma bazai aurar da ita ba."

Saheer ya ce, "abinda na gani kenan, kar garin farantawa kishiya ki aurar da ?arki ga inda bai kamata ba, ki tsaya ki nutsu ki bawa ?arki miji na gari. In akasin ne haka duk abinda ya zagaya a kan ki zai ?are, kishiya sai ta yi miki dariya, babu abinda ya dame ta."

Ta girgiza kai ta ce, "baza ku gane ba" ta faWa tana cigaba da girgiza kai dan a ganinta basu san yanayin da take ciki ba. Ita ko waye yazo neman auren bashi zata yi dan ta huta da gorin kishiya.

A lokacin Hanan ta shogo falon da sallama, suka amsa duk suka bita da kallo, ta zauna a kusa da Adda ta ce, "wash na gaji wallahi. Adda yaushe ki ka zo?."

Ta harare ta ta ce, "ta ya zaki san nazo kin tafi yawon ta zubar? Tun safe ina gidan nan amma baki dawo ba sai yanzu."

A lokacin Baffa ya shigo falon, ya kalli Hanan ya ce, "ke daga ina ki ke a daren nan?."

Ta turo baki ta ce, "Baffa makaranta na je fa."

"makarantar ce tun safe sai yanzu zaki dawo? Ki faWa min inda ki ka je."

Ta kalli Mama alamun ta saka baki, sai kuwa Mama ta ce, "Baffa ta faWa min zata bi ya dubiyar ?ar ajinsu."

Ya dawo da kallon sa ga Mama ya ce, "ta faWa miki zata bi ya dubiya? Dubiyar ce tun safe sai yanzu za a dawo?."

Mama ta ce, "daga makarnata ta bi ya can fa, dole ta daWe ai."

Ya gyaWa kai ya ce, "wa ta duba?."

"?ar ajinsu ce ta gamu da tautsayi, ita ta je dubawa."

Baffa ya bi Mama da kallo itama tana kallonsa kafin ta ce, "baka yarda bane ka ke kallona? Ai ka san bazan yi karya ba. Dubiya ta je, kuma gata ta dawo, ba shikenan ba?."

Baffa ya girgiza kai ya ce, "Ki cigaba kin ji Zulaiha, ki cigaba da goya musu baya, wata ran za kiyi danasani."

Mama ta ce, "babu danasanin da zan yi wallahi, me nayi da zan yi danasani? Dan ?ata ta je dubiya sai ya zama zan yi danasani?. Allah ya raba mu da danasani, ban santa ba, kuma bazan santa ba in sha Allah."

Baffa ya bita da kallo, sai ya yi murmushi ya Waga kai ya fita daga falon.

Sa'ida ta kalli Mama ta ce, "Amma Mama..."

ta dakatar da ita cikin faWa ta ce, "na san abinda nake yi, ba hankali da iya magana ki ka fi ni ba. Ni na haifi Hanan da Labiba, duk abinda zan yi musu babu wanda zai kai ni ?aunarsu. Ya ishe ni, bana son wata magana, in ma a wuta na cilla su suka ?one ?a?yana ne ko?."

Sa'ida da Saheer suka yi shiru basu ce komai ba, Mama ta mi?e ta shiga Waki Hanan ma ta shiga.

Sa'ida ta kalli saheer ta ce, "Saheer na wuce, Allah ya kyauta."

Ya gyaWa kai bai ce komai ba, ta fita shi kuma ya kalli Islaha. A lokacin ta mi?e ta shiga kitchen ya bi bayanta.

Ya same ta a tsaye tana haWa kayan wanke-wanke zata yi. Ya bita da kallon ?auna da soyayya, ya jingina da bango yana kallon ta ya ce, "Boddi am."

Ta juyo kalle sa ya ce, "me ya kai ki orphange Wazu?."

Ta kalle shi da mamakita ce, "Saboda gidanmu ne, na je gidanmu ganin yan uwana da dangina, shine kawai."

Ya girgiza kai ya ce, "Amma ba na ce miki duk lokacin da zaki je ki dinga sanar dani ba? Meyasa ki ka fara tsallake umarnina ne? Bani da daraja ne yanzu ko son da ake yi min ne ya yi ?asa?."

"Babu Waya Hamma, a ganina dan zan je gidanmu ba sai na tambaye ka. Na tashi daga aiki ina ji mararin ganin ?an uwana, shiyasa kawai na je."

"Islaha ni ki ke faWawa dan za ki je gidanku ba sai kin tambaye ni ba? Mijinki ne fa."

"Hamma!" Ta faWa tana jan sunansa tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta.

Ya ce, "na'am."

Ta Wan sunkuyar da kai ta ce, "ni ba haka nake nufi ba, kawai zuciyata tana so ta je ne, shiyasa na je. Amma ka yi ha?uri, bazan sake zuwa ban faWa maka ba."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "kin ga ?an uwan naki da ki ka je?."

Ta girgiza kai ta ce, "Na gansu, amma ban ga sauran ba."

"kin tambaya?."

"na tambaya, amma kamar...."

Ya zuba mata idanu ya ce, "kamar me?."

Ta fara wanke-wanken sannan ta ce, "akwai abinda nake zargi a gidan nan, akwai abinda nake hange yana faruwa kamar ba a so a lura dashi."

Saheer da mamaki ya ce, "kamar me kenan? Kuma meyasa ki ka ce ba a so ki lura dashi?."

Ta Wan kalle shi ta ga ita yake kallo sai ta ce, "ban gama bincike ba, in na kammala zan sanar da kai."

Ya ce, "yanzu nake so na ji."

Ta Wan sauke numfashi ta ce, "ni kaina bazan ce ga abinda nale zargi ba, amma tabbas akwai wani abun ba daidai ba Hamma. Kuma wallahi bazan zuba ido ba, ko me zai faru sai dai ya faru, matu?ar zargina ya kasance gaskiya sai kowa ya ji labarin nan."

Ya matso kusa da ita yana kallonta, muryarsa a ?asa ya ce, "baza ki faWa min ba kenan ko?."

Ta kalle sa ganinsa daf da ita, ta ce, "na ce maka ban tabbatar ba."

"Ina so na sani, ki faWa min meye ba ki tabbatar Win ba."

Ta kalle sa suka haWa ido ta Wauke idonta, ta kawar da kai gefe ta ce, "Ina zargin kamar an cire yaran nan daga makaranta, ana ajjiyesu a gidan kawai babu karatu" ta samu kanta da Soye masa asalin abinda yake faruwa.

Ya bita da hararar wasa ya ce, "ba yau na sanki ba Islaha, ki daina yi min ?arya."

Cikin shagwaSa da son kawar da maganar ta ce, "ni fa ba ?arya nake yi maka ba, gaskiya nake faWa maka Hammaaaa!" Ta ja ?arshen sunan tana kallonsa.

?auke kai ya yi daga kanta, yana girgiza kai, yana jin wani abu yana fizgarsa game da Islahan tasa.

Ya Wan matsa baya ya ce, "hmm ?anwar Hamma kenan, kin yi wannan shagwaSar a matsayin ?anwar hamma, ki jira ranar da za ki yi a matsayin matar hamma."

Ta yi murmushi tana cigaba da aikinta bata kallesa ba. Daman so ta ke a kawar da maganar, kuma an kawar Win.

Ya ce, "Suraj fa? Ba na hana ki ganin ku tare ba?."

Ta kalle sa ta ce, "Hamma shima kamar Wan uwana yake fa, ka tuna lokacin da nake makaranta shine yake koya min abubuwan da ban sani ba. Kamar Hammana yake a lokacin da nake wancan gidan, ba ya so ya ganni cikin damuwa ko kaWan."

Ya haWe rai ya ce, "ni kuma bana sonsa, ya za a yi kenan?."

Ta karyar da murya ta ce, "to, sai a yi yadda ka ke so."

Ya girgiza kai ya ce, "kar na sake ganin ku tare dashi. Bana so wata magana ta sake haWa ki dashi Islaha, sannan ki goge numbersa."

Ta Wan kalle sa sannan ta ce, "to."

Shiru ya ratsa kitchen Win sai ?arar abubuwwan da take wankewa kafin ya ce, "Ya aka yi da Mama ta bi ki Waki naga ta fito tana fara'a bata sake yi miki faWa ba? Kema kuWin ki ka samo ki ka bata Islaha, waye ya ba ki kuWin da ki ka bawa Mama?."

Ta Wago ido ta kalle sa ta ce, "Hamma meyasa baka karanta jarida bane don Allah? Meyasa ka bar ni ina aikin jarida kai kana nan, Wannan tambayoyi kamar a gaban tv?."


"Kwana biyu bana gane miki ne islaha, kina abubuwan da bakya so na sani. Tabbas na san kuWi ki ka bawa Mama, kamar yadda su Hanan suke bata. Waye ya baki kuWi bayan na san babu kuWi a hannunki?."

"Hamma ni ban bawa Mama komai ba, ha?uri na bata kawai."

"Ban yarda ba wallahi. Na san halinki, na san na Mama"

"Na yi mata al?awarin zan bayar in an yi mana salary, shine kawai."

Nan ma ya bita da kallo alamun bai yarda ba, ta Wan kalle sa suka haWa ido, ganin kallon da yake mata sai ta canja maganar ta ce, "kasan yau Chairman ya bani katin gayyatar Rehaan yola a hannuna, ya ce yana da tabbacin in na basa zai amsa gayyata" ta ?arasa faWa tana murmushi.

Ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "fatan nasara. Yaushe zai shigo?."

"Babu tabbas fa Hamma, an dai yi magana da PA sa ya ce a cikin kwanakin nan zai zo."

Ya ce, "Allah ya bada nasara, zan so ace kin yi hira dashi."

Ta taSe baki ta ce, "ni mamaki nake yi, wai waye shi da ake so ayi hira dashi har haka?. Kaga yadda hankalin ?an gidan tv mu ya tashi, saboda kawai an bani ragamar hira dashi?. Hmmm, Ummi har tare ni ta yi face to face, ta ce sai ta ga bayana."

Saheer ya buWe ido cikin firgici ya ce, "Sai ta ga bayan ki?."

"Wallahi Hamma, kuma akan Rehaan, ni ko gane fuskarsa ma bazan yi ba wallahi. Ko wacce tsiya ce dashi da aka gigice haka ban sani ba."

Saheer ya ce, "Ummin nan itace mai cewa kin zo a bayanta kin wuce ta ko?."

Ta Waga masa kai alamun eh ya ce, "baza mu bar maganar nan ba ai, dole ta je gaban hukuma, ba a wasa da irin wannan kalmar. A gaban wa ta ce sai ta ga bayanki?."

"Ni da Safeera ne kawai a wajan. Amma akwai cctv."

"Za a san abinda za a yi, wannan ba maganar wasa ba ce. Kalmar sai ta ga bayanki har prison sai ta je a kai. Zan yi maganinta."

Cikin ko in kula ta ce, "Ni wallahi ba dan Chairman ba sai in bata aikin, ta je ta ?arata. Bata san kai iv Win ma wahala ne dashi bane shiyasa."

Ya yi murmushi ya ce, "hira da Rehaan babban cigaba ne Islaha, ba kowa ne zai ji an baki ragamar gayyatosa ya ta ya ki murna ba, sai dai ni ko Safeera da saurayinta Salim. Rehaan ya wuce tunaninki, yaro ne mai ji da kuWi Islaha. Kuma yaro matashi, dan bai wuce sa'ana ba, amma ya mallaki abubuwan da ko babansa bashi dashi."

Ta ce, "amma na ji ana cewa ai ba ta hanyar halak yake samun kuWin ba, na ji ana cewa suna safarar ?an mata."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "wannan jita-jita ne, babu wanda ya san asalin gaskiya, dan ba a nan yake harkarsa ba. Zamu san gaskiya ne in ya amsa gayyatar ki, ki ka je ku ka zauna a gaban camera, ku ka tatttauna."

Ta taSe baki ta ce, "?an rainin hankali kawai, an yi masa mails sau babu adadi bai dawo da amsa ba. Ni na tsani wula?anci."

"Ba wula?anci bane Islaha, ni kaina ana yi min message Win da sai in yi sati biyu ban duba ba, ba dan wula?anci ba, sai dan ina da abinda ya fi dubawar mahummacin. Balle shi, da yake harka da ko ina a ?asar nan?.

"Shi dai ya sani, ni dai fatana Allah yasa ba Wan rainin hankali bane, dan wallahi bazai juri raini ba. In naje naga abinda bai yi min ba bazan kyalesa ba. Sai dai ka ji labarin ina police station an kama ni."

Ya yi dariya, dan ya san tsaf zata iya, wani lokacin rashin tsoronta har tsorata shi yake yi, bata tsoron kowa kuma bata jin nauyin faWar komai.

Saheer ya ce, "Allah ya shirya min ke matar Hamma, sarkin tsiwa. Rehaan ba irin mutanen da ake yiwa tsiwa a kwana lafiya bane, tohm ba irin wanda ki ke yiwa suke ?yale ki bane Islaha, shi kwarjininsa ma bazai bari ki yi masa ba."

Ta Wan buWe ido ta ce, "Na yi hira da LamiWon Adamawa fa, kwarjinin da ake cewa masu mulki suna dashi ni ban ji ba wallahi. Balle wani karan kaWa miya, wai Mr Rehaan."

"Ni ban san me Rehaan ya yi miki ba, baki taSa ganinsa ba kin tsangwame sa haka."

"Bana son rainin wayo ne, duk an haukace a kansa kamar wanda in aka gayyatosa lada za a samu."

"Ni mamaki ki ke bani, kina ?ar jarida kuma ?ar social media, ace baki san Rehaan ba."

Islaha harda buWe ido don mamaki ta ce, "Hamma duk sharar mutum wani ban san shi ba. Yanzu ba shugaban ?asa ne number one a nigeria ba? Akwai wani yana nan bai san ya fuskarsa take ba. A duniya Annabi Muhammad S.A.W kaWai aka yiwa wannan sanin, shine mutum ko ba addinsa yake bi ba, ya san dashi kuma ya san da zaman addininsa, sai dai ya ?i karSa. Rehaan Yolan waye shi da dole sai na san shi?.."

Ta yi ?aramin tsaki ta ce, "wallahi ka Hamma saka ko hotonsa bazan kalla ba, ranar da na gan shi face to face na sanshi. Da na yi niyar ganin hotonsa, amma yanzu na fasa."

Ya yi dariya ya ce, "na faWa miki in ya saka aka zane ki babu ruwana" ya faWa yana saka hannunsa a ruwa suna wanke-wanken a tare.

"Ba sai ka rama min ba? Ko baza ka rama ba."

"a guje zan rama miki, waye zai taSa min ke ya kwana lafiya?."

Ta yi murmushi bata ce komai ba. Saheer ya ce, "Amma serious kar ki yi wani abu mara kyau Islaha, ki nutsu ki je a yadda ki ke, na san basai ?i amsa gayyatarki ba."

Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya sa."

"Ki yi min al?awarin babu rashin kunya."

Ta Wan dariya ta ce, "To zan gwada in gani" ta? faWa tana cigaba da aikin dan baza ta iya Waukar al?awari ba.

Ya yi murmushi ya ce, "na fa san halin ki, Allah ya shirya min ke."

Ta yi dariya sosai, suka cigaba har suka gama, kafin ya fita ya bar ta a kitchen Win.



Nana Haleema
'

*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ??? *Nana Haleema.*


SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

*Book 1*
*Page 009.*


?? A tsaye yake ya juya baya yana waya, idar da sallar asuba kenan ya dawo daga masallaci ya tsaya yana amsa waya.

Ya sauke nunfashi ya ce, "ta faWa min ta zo, amma bata faWa min dalilinta na zuwan ba. Kuma ni ban ga dalilin da za a ce akwai aibu dan ta zo ba. Meye rashin dacewa dan ta zo nan Win?."

Ya Wan yi shiru yana magana sannan ya ce, "babu damuwa, zan kula da komai. Amma baza ta fasa zuwa gidan nan ba, dan a nan ta girma babu abinda zai saka ace kar ta zo. Ni bazan hanata ala?a da waWanda ta tashi tare dashi ba, ban ga dalilin kirana da asubar nan ana yi min wata magana ba" Daga nan ya sauke wayar yana ajiyar zuciya.

Islaha da ta fito Waukar doguwar rigar Safeera da ta wanke mata ta ji yana waya, sai ta tsaya tana jin me yake faWa, yana juyowa suka haWa ido.

Saheer ya Wan buWe ido ya ce, "me ki ke yi a nan?."

Ta nuna masa kayan ta ce, "rigar Safeera ce ta jiya, shine nazo in Wauka in goge mata kafin a Wauke wuta."

Ya matso kusa da ita yana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login