Showing 60001 words to 63000 words out of 96103 words

Chapter 21 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

69

zan dire su in yi tafiyata."

Atika ta ce, "abinda zan ce miki kenan, da ?arfin ki da lafiyarki ki tsaya ana Sata miki rai da lokaci?. Meye amfanin ki, meye amfaninki in ba ki je ba?."

Umma ta ce, "Atika ba Baban Safeera nake ji ba, mutanen Katsina nake ji. Baza su Waga min ?afa akan haka ba, Yayanmu fata-fata zai yi min."

"In sun sani ba, sai ki tafi ba tare da sun sani ba. In dai kin je ba shikenan ba?."

Umma ta Wan ti jimm alamun tunani kafin ta ce, "Ina son zuwan nan wallahi, amma ban san ya zan yi ba."

"Maimuna ki daina tunani, ki ajjiye ?a?an nan ki, ki je ki tara kuWin auren Safeera. An kawo kuWinta fa, ko yaushe za a iya maganar aurenta. Me Baban nata yake dashi, ke me ki ka tara da zaki aurar da ita?."

"Babu Atika."

"Amma kin samu dama zaki bari ta gudu?in wannan damar ta kubce mana a ina zamu samo kamar ta?."

"Babu."

"Ki rufe ido kawai ki yi, indai kin je Win dai ba shikenan ba? Duk faWan da za a yi sai ayi, tunda kin je ai komai ya ?are. Shi kuma Baban in ya sake ki fa shikenan."

Umma ta buWe ido ta ce, "Saki Atika! Da girmana?."

"To sai ki zauna ai. Kin san in da aurensa a kan ki bazai bari ki tafi ba, in kuwa ya sake ki ba shikenn kin huta ba, ki yi tafiyar ki babu nauyin kowa a kan ki."

Umma ta ce, "Gaskiya ne wannan, kin ?ara min ?arfin guiwa sosai Atika."

"Ahto, akan me zaki bari Baban Safeera yana juya ki? Dan ya hana ?arsa ke ai bai haife ki ba."

"Gaskiya ne wannan, kuma zan iya tafiyata mutanen Katsina basu san na tafi ba."

"DaWina dake akwai Waukar haske."

"Bara in je na same shi" ta faWa tana mi?ewa ta fita ta nufi gidanta.

Tana zuwa ta samu Baba ya dawo, ta zauna tana sake yi masa magana a kai.

Baba ya bi Umma da kallo ya ce, "amma na faWa miki bana son wannan maganar ko? Na faWa miki kar ki sake gangancin yi min irin wannan maganar ko Maimuna?."

Umma ta ce, "kuWin nan fa in an samu ba ni kaWai zan saka a gaba na cinye ba, amfani zamu yi dasu in auren Safeera ya tashi. Baka dashi, kuma baka da hanyar samu, laifi ne dan na nemo mafita domin gaba?."

Bab ya ce, "to baza a yi ba, babu inda Safeera ko wani a gidan nan zai je, wallahi."

Umma ta kalle sa cike da mamaki ta ce, "harda wallahi?."


"Wallahi Allah baza su je ba, matu?ar ni na haifesu babu wacce zaki Wauka ki kai wata ?asar neman kuWi."

Umma ta girgiza kai ta ce, "na ji, kai ka haifesu kana da iko dasu. Amma ni ai ba kai ka haife ni ba ko?."

Baba ya bita da kallon mamaki jin abinda ta ce, ya gyara zama ya ce, "bani na haife ki ba, amma akwai aurena a kanki. Yadda na isa da ?a?ana haka na isa dake, kafin na samu ?a?an ke na samu, kafin na faWa su ji, ke zan fara faWawa ki ji. Dan haka kema babu inda zaka je."

"Ai kuma baka isa ba, wallahi baka isa ba. Ka hana ?a?ana zuwa nima ka hana ni? Kaima ka san ai bazai yu ba. ?a?anka ka ke da iko dasu amma bani ba, ?a?anka zaka hana tafiya bani ba. Aure da ka ke magana aki kalma uku zata warwaresa, daga nan babu komai tsakanina da kai, zan je duk inda na ga dama."

Baba ya bita da kallo, jin tana maganar saki har haka, har tana cewa kalm uku ce ta raba auren ya ce, "shikenan Maimuna, Allah ya taimaka" ya faWa yana mi?ewa ya bar mata wajan, kar zuciya ta tunzurasa ya aikata wani abun da zai yi danasani.

Safeera ta shigo falon a sanyaye ta ce, "Haba Umma, me ki ke aikatawa haka? Ina ke ina tafiya wata ?asar aiki?."

Ta bi ta da harara, cikin faWa ta ce, "ba kin biyewa ubanki ba?."

"Umma ko Baba hana ba, wallahi ni bazan je ba."

"Kar ki je Safeera, kar ki je Win mana. ?ar iskar yarinya mai taurin kan tsiya, wacce bata son abinda uwarta take so. Matsa ki bani waje ko na tsinka miki mari!" Ta faWa a fusace tana kallon Safeera.

Safeera ta ja gefe ta tsaya tana kallon Umma da Wubun mamaki. Bata Wauka abin Umman ya kai haka ba, bata Wauka lamarin Umman ya kai wannan matakin ba sai yanzu. Akan zuwa wannan aiki wat ?asa take ce mata ?ar iska, har take cewa zata mare ta?.

Umma ta ce, "in baki je ba ai ni zan iya zuwa ko? Ina da ?arfi da lafiyar da zan iya yin ko wanne aiki ne. Ki zauna Safeera, ni zan je, bazan taSa ganin arzu?i yana tunkaro ni n tsallake ba. Zan bar gidan nan in tafi, sai ki zauna ki cigaba da kula da ?an uwanki, amma wallahi sai na je!."

Baba ne ya shigo ya dawo Waukar wayarsa da ya bari, ya ji kalaman Umma. Sai ya ga Safeera ta zube a ?asa tana kuka, ta ce, "don girman Allah Umma ki rufa mana asiri, Umma don Allah kar ki tsallaka ki bar mu a nan. Ki zauna a tare damu, kar ki tafi wata ?asar saboda neman abin duniya. Da yawan aikin nan yaudara ce, wahala ake zuwa a sha a can."

Baba ya ce, "?yaleta Safeera, matu?ar da aurena a kanta babu inda zata je wallahi!."

A fusace Umma ta ce, "idan na kashe auren fa? In ka sake ni ba shikenan ba!?."

"Sai dai hakan, dan in dai kin ga kin bar ?asar nan tabbas babu aurena a kanki!."

"Ai daman sakina zaka yi, bazan zauna da auren ka ba nima.."

Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Umma na yarda zan je, na yarda zan je Win. Ki daina faWar wannan maganar don Allah, ni zan je na samo miki duk abinda ki ke so!. Ki zauna dasu Rukayya, ni zan js na samo duk abinda ki ke so ki samo a can"

Cikin tsawa Baba ya Wago Safeera ta mi?e tsaye,? ya ce, "wallahi baza ki je ba! Ni na haife ki, ina da ikon saka ki ko na hana ki, babu wanda zai yi miki dole akan wanann. Baza ki je Safeera, ita dai tunda bani na haife ta ba ki ?yaleta ta je!."

Umma ta ce, "nima ai ban ce ta je ba, ta yi zamanta ita da kai, zan je na yi abinda nake so. Sai ka zauna dasu su maye maka gurbina" tana faWar hakan ta fita daga falon.

Safeera kuka take yi sosai, murya tana rawa ta ce, "Baba don Allah ka bar ni in je, ka ji!."

Baba ya kalle ta cikin sigar kwantar da hankali ya ce, "ki kwantar da hankalinki, barazana take yi miki dan ki ce zaki je, amma babu inda zata je. Ki daina kuka."

Safeera ta goge ido ta ce, "Baba Umma da gaske take, ban taSa ganinta cikin irin wannan yanayin ba sai yau, ni ka bari in je don Allah, ka ?yale ni na tafi don Allah!."

Baba ya girgiz kai ya ce, "babu inda zaki je wallahi, ki bar maganar nan dan ba yuwa zata yi ba."

Ta yi ajiyar zuciya tana goge hawaye, ta juya ta kalli ?annenta mata guda uku duka mata.

Rukayya da ta kasance babba mai bin Safeera, ta ?araso ta ce, "Adda ina Umma zata je?."

Baba ya ce, "Rukayya ki zauna da ?ar uwarki, ina zuwa" ya faWa yana fita daga falon.

Safeera kuwa bata iya amsawa Ruky ba, kuka kawai take yi tana tunanin ya zama dole ta je Katsina dangin Umma ta faWa musu halin da ake ciki, dan gaskiya baza ta bari Umma ta aikata wannan Sarnar ba.

*******

? ? ? Suna zaune a compond Win gidan, ta saka hijjab har ?asa shi kuma yana gefenta a zaune. Suna ta hira cikin nishaWi da soyayya.

Saheer ya ce, "na fito dake bayan na san a gajiye ki ke."

Islaha ta Wan murmusa ta ce, "Babu komai, ai na Wan huta kaWan."

"To ya aikin? Kin samu ganin Mr Ray Win?."

"A'a, amma mun ga Mr Jafaar, ko yaushe ance suna tare."

"Good. Sai aka yi ya kenan?."

Ta Wan kalle sa ta ce, "dashi mu ka yi magana, ya tabbatar min da kansa zai neme ni in lokacin hirar ya zo. Amma a yanzu ya faWa min hira dashi bazai yu ba, dan ya faWa min gaskiya bai rufe ni ba."

Saheer ya ce, "hakan yana dakyau, Allah ya taimaka matar Hamma."

Ta yi murmushi ta ce, "Amin ya rabbi Hamma."


Sai ta ja numfashi ta ce, "ka san me na gani?."

Ya girgiza kai ya ce, "sai kin faWa."

Islaha ta ce, "Hafsa na gani a hotel Win fa, kuma da ita kaWai na gani da sau?i, zan iya cewa wani abun ne ya kai ta, amma ita da wani ne har na ga sun shiga Waki."

Ya buWe ido cikin firgici ya ce, "Hafsa dai ta orpahange?."

Ta Waga kai ta ce, "ita fa. Lokacin da na gansu mu kuma lokacin mun fito, sai hankalina bai kwanta ba, sai na koma daga baya. Ka ga" ta faWa tana nuna masa hoton da ta Wauka na Hafsa.

Ya karSi wayar ya yi zooming yana kallon fuskar Hafsa, cike da mamaki ya ce, "ai kam itace. Amma me ya kai ta hotel su da ba a barinsu su fita past six?."

"Ashe ka fahimci abinda yake a raina. Kuma kasan na je gidan, an tabbatr min da kwanan Hafsa biyu bata nan."

Ya bata wayarta sannan ya ce, "waye ya faWa miki?."

"Zainab ce, kuma tana cikin faWa min Fadwa tazo ta hanata, sai hakan ya sake jefa min zargi a zuciyata Hamma."

"Zargin me ki ke yi?."

Ta kalle sa suka haWa ido ta ce, "ina zargin ana aikata mummunan abu a gidan nan, zuciyata tana bani ana fitar ?an matan gidan a kai su inda bai kamata ba."

Saheer ya girgiza kai cike da gamsuwa ya ce, "gaskiya ne wannan, nima kaina yanzu na fahimci zarginki. Amma meyasa da ki ka ?i faWa min?."

Ta rausayar da kai ta ce, "zargi ne ai shiyasa, yanzu da na samu hujja ai na faWa maka."

Ya girgiza kai ya ce, "yanzu what next?."

Ta sauke numfashi sannan ta ce, "zan sake samun evidance mai girma, daga nan sai na yaWa maganar zuwa gaba."

Ya kalle ta kaWan ya ce, "amma in hakan ya tabbata sun ci amana wallahi, Allah ya ba su amana suna ci."

Sai kuwa ta ta sake fusata, ta fara magana cikin kaushi ta ce, "bari kawai, na rantse da Allah babu wanda zan sassautawa, wallahi ko waye yake da hannu a lamarin nan sai na tabbatar da ya tafi gidan yari."

"zan baki goyan baya Wari bisa Wari. Allah ya kare min ke, ya cigaba da baki nasaraa a rayuwarki."

Ta yi murmushi tana kallonsa, ?aunarsa na sake shiga cikin zuciyarta.

Ta sunkuyar da kai tana blushing ta ce, "Amin Hammana."

Murmushi ya yi ya ce, "ina ji kamar na...." Sai bai ?arasa ba ya zuba mata ido kamar yadda ta Wago tana kallonsa.

Ganin kallon da yake yi mata sai ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tare da rufe fusksrta da tafukan hannunta masu matu?ar kyau.

Hannunta ya bi ta kallo, muryarsa a ?asa ya ce, "zaki jira ni in je Waki na dawo?." Ta Waga kai bata buWe fuska ba.

Ya mi?e ya shiga ciki ta bisa da kallo cikin ?auna da soyayyar da take yi masa. Ta sauke ajiyar zuciya, domin kuwa Hamma ya cancanci soyayyarta mai girma, ya zamar mata komai a rayuwarta, bata da wani sai shi Win kawai.

A lokacin ta hangosa yana tahowa, ta tsaya tana ?are matsa kallon yadda yake takawa kamar baya so. Hammanta duniya ne a wajan kyau, kai da ka gansa ka ga jinin fulani gaba da baya. Yana da kyaun fulani, ga kwantaccen gashi ba?i irin nasu.

A nutse ya ?araso ya zauna kusa da ita, ya Waga mata gira ganin yadda take kallonsa kamar bata gane shi ba. Sai ya sake ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Ya yi murmushi ya ce, "?an mata wannan kallon fa?."

Ta rufe fuska da hannunta tana ?ar dariya. Ya yi dariya ya ce, "buWe fuskarki ki ga abinda na kawo miki."

Ta cire hannunta ta ga ya Wauko sisirin bracelet kamar chain Win sar?a, silver colour mai hook a jikinsa.

Ya mi?a mata hannu ya ce, "i brought it for you, only Matar Hamma."

Ta yi murmushi tana kallon abin, ya mi?a mata hannu ya ce, "kawo hannunki in saka miki."

Ta Wan zaro ido ta ce, "In Baffa ya zo wucewa fa?."

Ya Wan Sata fuska ya ce, "ba matata bace?."

"Ba a Waura ba Hamma."

"Amma an kusa ko, matar Hamma?."

Murmushi ta sake yi, ya ri?o hannunta a hankali ya Waura mata bracelet Win a hannunta.

Ya bi hannunta da kallo, kasancewar abin silver ne ya haska brown skin Winta sosai. Ya kalle ta suka haWa ido, ya ce, "Ya yi miki kyau, matar hamma."

Kafin ta yi magana ya kai hannunta bakinsa, ya yi pecking hannun yana kallonta ya ce, "mi yidi maa, debbo Hamma" (Ina sonki matar hamma).

Ta Wan sauke ajiyar zuciya, cikin duniyar masoya ta ce, "miWo kadimi yidi maa, gorko debbo Hamma" (Nima ina sonka, mijin matar Hamma).

Bai saki hannunta ba sai murmushi da yake yi ya ce, "Zan tafi Niger."

Ta kalle sa ta ce, "yaushe?."

"Wata?ila gobe in sha Allah."

"In ka tafi sai yaushe?."

"Zan Wan kwana biyu, zan je in samo kuWin aurenki. Da na dawo nake so a gama ginin can mu yi aure mu huta."

Ta marairace fuska ta ce, "Ni bana so ka tafi."

Shima ya yi yadda ta yi ya ce, "dole na tafi debbo Hamma, zan je na nemo mana kuWin da zamu rayu cikin farin ciki."

Ta Wan sauke ajiyar zuciya ta zame hannunta ta ce, "bana so ka tafi wallahi."

Ya bita da kallo dan ya san Mama tafi takura mata in baya nan, cikin rarrashi ya ce, "ki cigaba da ha?uri Islaha, komai ya kusa ya ?are in sha Allah."

Ta Waga kai ta ce, "ni fa babu komai, kawai bana so ka tafi ne."

"In na tafi ai zan dawo, ki cigaba da yi min addu'a kin ji, My dear wife?." Ta Waga kai akamun to.

Ya kalli agogon hannunsa ya ce, "ki je ki kwanta."

Ta kalle sa ta ce, "?arfe nawa zaka tafi goben?."

"Zan faWa miki Islaha."

"Ka faWa min da wuri, Ina so in yi maka snack ka tafi dashi."

"Kar ki wahalar da kan ki debbo, ba sai kin yi komai ba."

Ta Waga kai ta mi?e a hankali zata koma, sai ta ji ya ce, "Debbo am."

Ta juyo ta kalle sa ya ce, "your monthly pills" ya faWa yana mi?a mata ?aramar ba?ar leda wacce take da Wan tudu sosai.

Kunya ta mamayeta, ta rasa meyasa Hamma baya mantawa da pain reliver Win da take sha every month, da ya rage saura kwana biyu zai kawo mata haWe da sanitary paid da kayan ciye-ciye kamar yadda ya san tana so. Kamar yadda yasan in tana prieod take da son kayan kwaWayi, haka yake haWo mata su da yawa.

Bata ?arba ba, ya mi?e ya ?araso inda take ya ce, "yaushe zaki saba dani ne, Debbo am? Hammanki ne fa" ya faWa yana ri?o hannunta ya saka mata ledar.

Bata ce komai ba ta kwasa a guje ta shiga ciki ya bita da kallon soyayya da ?auna, ya sauke ajiyar zuciya ya shiga ciki da hanzari.

Tana shiga ta ajjiye ledar tana murmushi, ta buWe ta ga sanitary paid ce da chocolates da kuma pain reliver Win da ta saba sha. Ta sauke numfashi, ta Wauki chocolate Waya ta fara sha kafin ta jawo hand bag Winta ta Wazu tana dubawa.

Iv Win da aka bata na Rehaan ta Wauko ta buWe, karantawa ta fara yi tana murmushi kafin murmushin ya gushe daga kan fuskarta.

Bata san ta mi?e tsaye ba, tana buWe ido ta ce, "what! Meye hakan?."

Ta faWa tana sake kallon katin cike da mamaki ganin abinda yake rubuce a jiki.

"Amma wancan ba haka ne a ciki ba, kalamai ne na girmamawa da suke nuni da ana son gayyatarsa. Meyasa wnanan kalaman suka canja suka koma kalaman cin fuska? How?" Ta faWa cike da mamaki tana ri?e ?ugu.

Sai ta girgiza kai ta Wauko wayarta ta kira numbar Saleem aka yi sa a ya Wauka, yana Wauka ta ce, "Saleem don Allah kaine ka canja iv Win jakata ne?."

"Wanne katin kenan?."

"Na gayyatar Mr Ray."

"A'a, akan me zan canja?."

"To abin ne da mamaki, ka ga ashe ba wanda Chairman ya bani bane. Wallahi da ace Mr Jaafar ya karSi katin nan da mun shiga uku, dan cin fuska ne kawai a ciki."

Saleem da mamaki ya ce, "ban gane ba."

Ta Waga kai ta ce, "bara in tura maka ka gani" ta faWa tana kashe wayar tana snaping katin.

Bata jima da tura masa ba ya kira ta, tana Wauka ya ce, "Wallahi ban canja miki kati ba Islaha."

Ta ce, "wallahi na san baza ka yi ba, ni nafi zargin lokacin da na barta a mota aka samu wasu suka canja. Ka san ba kowa ne yake son aikin nan a hannuna ba."

"Eh zata iya yuwa, dan Muslim ma bana tunanin zai canja katin nan."

"Amma ko waye daga gidan tv nan yake, domin komai iri Waya sak aka kwafa, kawai rubutun ne ya banbanta shima sai ka kula. Yanzu ba dan Mr Jaafar ya ce a bar katin nan ba ya kenan?."

Saleem ya ce, "Allah ne ya taimaka ya ta?aita mana wannan abu. Ki ajjiye katin, za ki fito gobe ne?."

"Anya kuwa? Babu program a hannuna."

"In zaki fito sai ki taho da katin a nunawa Chairman."

"Shikenan, na gode" daga haka suka yi sallama ta kashe wayar tana tunanin waye da wannan aikin haka?.


*******

? ? ? A hankali ya buWe ?ofar bedroom Win ya shiga yana mita ya ce, "ka ishe ni da waya, ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login