Showing 72001 words to 75000 words out of 96103 words

Chapter 25 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

73

azkhar taga kiransa, ta mi?e ta fito ta gansa ri?e da jaka yana kallon ta.

Hawaye suka cika mata ido, haka kawai ta ji bata so ya tafi ya barta, duk da yana irin wannan tafiyar amma wannan karon sai ta ji ta damu.

Ta ?araso a sanyaye ya bita da kallo har ta zo inda yake, ya ce, "Matar Hamma zan tafi, ki yi min addu'a."

Hawaye ya sakko mata, ta Wago ta kalle sa ta ce, "bana so ka tafi."

Saheer ya kalle ta, cikin damuwa da rauni ya ce, "meye na kukan? Kina so na fasa tafiyar ne?."

Ta Waga kai alamun eh, ya gyara tsayuwa yana gifanta da murmushi ya ce, "In na zauna da me zan aure ki? Kin manta kina da tsada, dole sai na dage na nemo sannan zan mallakeki?."

Ta kalle sa har tana Waga hannu sama, ta ce, "ni na yafe maka komai, kawai a Waura auren, ba sai ka bani komai ba."

Ya wara ido waje cikin tsokana ya ce, "duk wannan halittar a kyauta za a bani?."

Islaha ta Waga masa kai alamun eh, dan da gaske bata so ya tafi, da ya tafi gwara a aura masa ita Win ba tare da ya bata komai ba.

Ya yi murmushi ya ce, "DaWin sai ya yi min yawa ai, sai na zama mai son kaina. Ina ni ina Waukar matar Hamma a kyauta? Daraja da matsayin matar Hamma ya wuce haka, dole na fita na nemo na aure ta. Dan tana da tsada sosai, dole sai na dage da neman kuWi."

Cikin rauni ta ce, "Allah ni bana so ka tafi, indai akan neman kuWin aurena zaka tafi gwara mu zauna a Waura auren, ni ko sadakin sai in yafe."

Saheer ya yi dariya mai sauti, ya bita da kallon ?auna ya ce, "Har sadakin sai a yafe min matar Hamma?."

Cikin shagwaSa ta ce, "i'm not joking, Allah so ka je ko ina. Haka kawai yau bana son tafiyar nan, ji nake kamar in ka tafi komai zai canja, don Allah ka zauna."

Ganin da gaske take ba shagwaSar da ta saba yi masa bace sai ya nutsu ya ce, "Meyasa bakya so?."

"Ina ji kamar wani abun zai faru in ka tafi. Kamar...Kamar....ni dai ina jin kamar komai zai canja in baka nan."


"Babu abinda zai faru sai alkhairi, wani lokacin samuwar alkahiri tana zuwa a haka, kafin ya samu haka ake ji kamar abu mara kyau zai faru. Ki kwantar da hankalinki, zan dawo mu yi aure, ki haifa min kyawawa yara, masu irin fatarki, hancinki, girar ki, da bakin ki....."

Ta Wan sunkuyar da kai tana murmushi, shima ya yi murmushi ya ce, "kin san abinda ya fi komai burge ni a fuskar ki?."

Islaha ta Wago ta kalle sa, ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Bakin ki! Yana Waukar hankalina sosai, musamman a yanayi irin wannan."

Ta sunkuyar da kai tana wasa da hijjab Win jikinta bata ce komai ba.

Ya kawar da tunanin da ya zo zuciyarsa, ya ce, "ki yi min addu'a."

"Allah ya tsare ka, ya baka nasara akan duk abinda ka je nema."

Saheer ya bita da kallo, ya kasa jure abinda yake ji, ya Wan matso kusa da ita ya ce, "zan iya pecking Win ki?."

Ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba, dan nauyinsa da kunyarsa take ji sosai.

Saheet ya Wan mtsa baya ya ce, "na bari sai na dawo daga Niger, daga wannan lokacin zan fara rungumeki a ?irjina, matar Hamma..."

Ta runtse ido saboda kunyar maganarsa. Ya ce, "Amin, na gode da addu'ar ki, ki cigaba da kula musamman akansu Hafsa, ki cigaba da saka ido, duk abinda ya faru ki faWa min, zan taya ki aikin daga inda nake in sha Allah."

Ta Wan buWe ido ta ce, "zaka jima a can ne?."

Ya Wan Waga mata kai ya ce, "at least wata Waya."

Ta buWe ido tare da rausayar da kai ta ce, "wata Waya! Allah ya yi yawa."

Ya yi murmushi ya ce, "bai yi yawa ba Matar Hamma, da na tafi zaki ga lokacin ya yi na dawo."

Ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya kiyaye."

Ya kalli agogo jin ana yi masa horn a ?ofar gidan, ya kalle ta ya ce, "Amin debbo am, na gode da addu'arki. Dana sauka zan kira ki."

Ta Waga kai ta ?araso ta ri?e masa jaka ta ce, "mu je in raka ka."

Ya Wan tsaya yana kallonta ya ce, "akwai iska sosai, kar ta cutar dake."

Ta ja hijjab Winta ta rufe hancinta ta ce, "zan iya."

Ya ce, "to bani jakar, ta yi miki nauyi."

"Zan iya" ta faWa tana no?e kafaWa kamar yarinya ?arama. Ya yi murmushi suka fara tafiya har suka fita waje.

Sadik da zai kai sa tasha yana zaune a mota, ganinsu tare ya yi murmushi ya ce, "Matar Hamma, kin yi masa rakiya kenan?."

Ta yi murmushi ta ce, "ina kwana."

"Kin tashi lafiya?."

"Lafiya lau. Ga amanar Hammana, ka kai sa tasha lafiya, ka ji?."

Ya yi murmushi ya ce, "in sha Allah, uwar gida."

Ta Wan harare shi ta ce, "Uwar gida kawai?."

Sadik ya rufe bakinsa, ya girgiza mata kai ya ce, "Kuma Amaryar Saheer. Ai ke two in one ce, uwar gida, kuma amarya."

Ta yi murmushi ta kalli Hamma da yake kallon ta yana murmushi ya ce, "ki koma, akwai iska sosai, kar ki samu attack."

Ta Waga kai ta ce, "Allah ya kai ka lafiya, ya dawo da kai lafiya."

"Amin matar Hamma, ki koma. In Mama ta farka ki ce mata na tafi, na shiga tana bacci." Ta Waga kai tana koma ciki jikinta a sanyaye.

Saheer sai da ya ga ta shiga sanna ya sauke ajiyar zuciya ya shiga motar. Sadik ya kalle sa ya ce, "Hamma na Islaha, Allah ya bar soyayyarku."

Ya amsa da amin kafin ya ce, "Allah da na dawo auren nan za a yi, ko meye ajjiyesa zan yi na fuskanci aurenmu. Na kusa gazawa akan ha?urin da nake yi, gwara mu yi a wuce wajen."

Sadik ya yi dariya ya ce, "yanzu ina zamu je?."

Ya harare sa ya ce, "ina ka san zamu je?."

Ya yi dariya ya ce, "Tasha." Bai kula ba sa Sadik ya ja mota suka bar unguwar yana sauke numfashi cikin kewar masoyiyarsa.

_Kamar da gaskiyar Islaha, tafiyar Saheer zata iya canja mana labari.>?-?_

Nana Haleemad'?
'
*RAGAYAR DUTSE.*

?? *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 020.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

__________________

Islaha ko bacci bata iya komawa ba, tana zaune kawai tana kewar Hamma. Har Saheer ya yi mata waya yace motarsu ta tashi, ta sake yi masa fatan alkhairi kafin ta kashe.

A sanyaye ta tashi ta gyara Wakin da take ciki, ta fita ta damawa Baffa kunun kanwa da yake yawan sha, ta dafa tea ta juye a flask sannan ta Wauko doya ta fara gyarawa dan ta soya.

Har ta kammala ta yi wanka babu wanda ya tashi, ta fito ta sha tea Winta dan zata je su haWu Zainab a inda ta ce su haWu.

Ta gama kenan Mama ta fito tana amsa waya, Islaha ta tsaya cak har ta ?araso, sannan ta ajjiye wayar tana bin Islaha da banzan kallo.

Islaha ta ce, "Mama ina kwana? Hamma ya ce in faWa miki ya wuce, ya shigo kina bacci" ta faWa lokaci Waya, dan kar Mama ta Sata mata rai ta manta bata faWi sa?on Hamman ba.

"Uwar iyayi, dashi nake waya ai. ?anki ne ko Wana?."

"?anki ne Mama, ki yi ha?uri" ta faWa a sanyaye dan haka kawai take jin kanta babu daWi.

Mama ta bita da harara tana ?wafa ya wuce bata ce komai ba.

Islaha ta yi ajiyar zuciya ta Wauki handbag Winta ta fita daga gidan. Sai da ta fita sannan ta saka facemask, ta kawo cotton ta toshe kunnenta saboda iska, bayan ta saka hijjab har ?asa.


Lokacin ?arfe tara na safe, ta hau napep ta nufi makarantarsu Zainab dan a nan suka yi zasu haWu.

Tana sauka ta yiwa Zainab waya bata Wauka, ta ajjiye wayar tana jiran Zainab. Babu jimawa ta ?araso ta saka ni?ab, dan Islaha bata gane ta ba sai da ta ?araso. Zainab ta zauna a kusa da ita ta ce, "Adda ina kwana."

"Lafiya lau Zainab, na fito dake da sassafe ko?."

"Babu komai Adda. Ki yi sauri kafin a farga bana nan, yau sun san bana zuwa lecture kuma ban sanar zan je yin kitso ba."

"Hafsa ta dawo gida ne?."

"Ta dawo, amma jiya da daddare an sake fita da ita. Hafsa gabaWaya ta canja Adda, kashe kuWi take yi yadda take so. Haka su Sauda suke yi suma, to itama ta shiga sahun su."

Islaha ta ce, "ba ki ga wata alama a tare da ita na rashin gaskiya ba?."

Ta girgiza kai ta ce, "yanzu sun daina hira dani, ko yaushe warewa suke yi ita da Fadwa."

Islaha ta Wan yi shiru tana tunani, Zainab ta ce, "ranar da mu ka haWu dake sai da aka kai ni wajan Mama, ta ce in dai ta sake ganina tare dake wallahi sai ta yi maganina."

Ta kalli Zainab Win ta ce, "ke ba a taSa neman fita dake ba?."

"Na faWa miki lokacin da aka kira mu office Win nida Hafsa cewa aka yi ni na je waje, daga ranar Hafsa ta canja. Dan yanzu ma ance babbar makarantar kuWi zata koma da karatu."

Islaha ta dafata ta ce, "Zainab don Allah kar a kira ki ki aikata wani abun mara kyau, ki taimaki maraicinki, ki cigaba da sana'arki, har ki yi aure."

Ta Waga kai ta ce, "in sha Allah Adda bazan yi komai ba."

Islaha ta ce, "Yauwa, na san ke rainona ce, baza ki yi wani abu mara kyau ba. Na gode sosai, zaki iya komawa" ta faWa tana buWe jaka ta Wauko dubu goma ta bata.

Islaha ta ce, "ki yi kuWin mota, sannan ki siyi abinda ki ke so. Ko da za a ce ina ki ka je, ki nuna kuWin kice kin je kin yiwa wata kitso ne ta baki.

Zainab ta girgiza kai tana ji kamar ta faWa mata matsalar da take damunta amma bakinta ya yi nauyi ta kasa. Daga nan suka yi sallama suka rabu kowa ya kama hanyarsa.

? ? ? Islaha gida ta koma dan bata da inda zata je, bata da aiki kuma baza ta wahalar da kuWinta ta je babu abinda zata yi ba.

Tana shiga ta ga Mama ta fito daga Wakin Baffa hankali a tashe tana faWin, "Islaha Baffa ba ya motsi!."

Gaban Islaha ya faWi, bata taSa jin kalmar da ta soki zuciyarta lokaci guda ba sai wannan, ta ji wani iri yarr a jikinta, kanta ya sara, naman jikinta ya fara rawa. Da hanzari ta bi Mama, ta shiga Wakin taga Baffa kwance ya kumbura kamar wanda aka hura. Hankalinta ya tashi ta gigice, ta fito jikinta yana rawa ta rasa ya zata yi.

Waya ta Wauka hannu yana rawa ta kira Sadik, yana Wauka ta ce, "Hamma Sadik! Ka zo gidanmu, kazo gida, Baffa ba yamotsi, ka zo don Allah!."

Tsabar ruWewa bata tsaya ta ji me yake faWa ba ta kashe wayar tana kai kawo, suna tsaye ita da Mama da Labiba da Hanan, Islaha ta fi ce da gudu.

A lokacin Sadik ya shigo a ruWe, ganin halin da Baffa yake ciki ya saka ya fita da hanzari nemo maza biyu a ?ofar gida, suka Wauki Baffa aka saka mota.

Islaha ta shiga gaban motar, Mama da Labiba suka shiga kusa da Baffa aka ja motar suka tafi.

Babban asibiti suka tafi Sangaren emergency, aka karSi Baffa da gaggawa dan yanayin nasa abin tsoro ne, yana bu?atar kulawa da gaggawa.

Sun kasa tsayawa sai kai kawo suke yi ciki kiWima da tashin hankali, Islaha kamar ta shiga ta ga abinda yake faruwa haka take ji. A lokacin take ji ina ma karatun likita ta yi, da yanzu ta san me ake yi a ciki, da tana ciki ana duba lafiyarsa tare da ita. Mintina ashirin da shigarsu, sannan nurse Win ya fito, ya kalli Sadik ya ce, "a je a siyo wannan maganin yanzun nan."

Sadik ya karSa ya fita, ba jimawa ya dawo ya shiga ciki ya kai musu ya dawo ya zauna.

Har azahar ta yi suna wajan a tsaye, a wajan suka yi sallah suna jira su ji abinda za a faWa musu akan Baffa amma shiru.

Sai ?arfe biyu na rana sannan Sadik ya koma yake tambayarsu jikin Baffa. Likitan ya kalle sa ya ce, "yauwa daman ina neman ka, kai Wansa ne?."

Sadik ya ce, "ni abokin Wansa ne."

"Okay, ina iyalansa?."

"Suna waje."

"Kira su."

Sadik ya fita ba jimawa suka dawo dasu Mama suka zauna.

Likita ya ce, "majinyacin ku shine Mustapha Maddibo ko?."

Suka Waga kai alamun eh, ya sauke numfashi yana kallonsu ya ce, "ya taSa fama da ciwon ?oda ne?."

A tare gabansu ya faWi a tare, kowa ya zaro ido jin ana maganar ?oda. Mama ta ce, "bai taSa ba."

Ya girgiza kai ya ce, "Jininsa ya hau sosai, sannan kuma sugar sa ma ya hau fiye da ?a'ida."

Cikin ruWewa Mama ta ce, "daman yana da hawan jini da sugar ne?."

Likita ya Waga kai, ganin hankalinsu ya tashi sosai sai ya ce, "ku shiga ciki ku ga yanayinsa."

Sadik ya mi?e zai fita sai Dr ya ce, "ban da kai abokina, akwai maganin da zaka siyo. Ku je" ya faWa tana kallonsu Islaha.

Islaha ta ?i fita, dan a yanayinsa ta fahimci ba lafiya ba, yana Soyewa ne saboda ya ga sun tayar da hankalinsu daga cewa ciwon ?oda.

Har ta fita ta dawo, likitan ya kalle ta ya kalli Sadik ya ce, "Baban ku yana fama da matsalar ?oda, daga ganin yanayinsa da komai na sa ciwon ya bayyana sosai. Yana bu?atar kulawa ta musamman gaskiya, yana bu?atar ganin likitan da ya ?ware a wannan fannin."

Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!Likita amma bai taSa ciwon ?oda ba, ko Islaha?."

Islaha ta ce, "nidai iya zamana a gidan ban san ya yi ba, ban taSa ji an bada labarin ya taSa yi ba."

Likitan ya kalle ta ya ce, "ina ta so in tuna inda na sanki, yana cewa Islaha na fahimci wacece ke. Ashe presenter mu ce a gabana." Ta Wan yi murmushi kaWan kafin ta ce, "yanzu ya za a yi dr?."

Dr ya Wauko takarda ya yi rubutu ya ce, "Zan tura ku wajan likitan da ya ?ware a wannan fanni, shi gabaWaya aikinsa akan ?oda ne, akan haka ya ?ware kuma yake da sani a kai. Su mu ke kira nephrologist."

"Ana iya ganinsa a nan, amma gaskiya a kan sha wahala sosai, amma in ku ka je asibitin da yake aiki za ku samu ganinsa sosai, zai yi muku bayani yadda ya kamata. Amma asibitin kuWi, asibitin kuWi bana wasa ba, sai dai za ku samu biyan bu?ata in sha Allah."

Sadik ya ce, "to zamu gwada."

Dr ya mi?a masa takardar ya karSa ya ce, "ku je, in kun gansa ku ce Dr Habib ne ya turo ku daga nan babban asibiti, zai yi muku komai yadda ya kamata. Amma ina sake maimaita mu ku, asibitin kuWi ne, iya kwanciya da duba mara lafiya za a yi za a chajin ku kuWi mai yawa."

A lokacin Mama da Labiba suka dawo, a lokacin Sadik ya ce, "zamu gwada mu ji, mun gode sosai likita."

Dr ya ce, "Allah ya ?ara sau?i." Suka amsa da amin. Dr ya kalli Islsha ya ce, "na ji daWin haWuwa dake." Ta Wan yi murmushi bata ce komai ba, dan rashin lafiyar Baffa ya tsaya mata a rai sosai.

Sai bayan sun fito suke faWawa su Mama za a canja asibiti ne, aka basu ambulance suka tafi asibitin da aka faWa musu.

Haka kawai ?irjin Islaha yake bugawa ba tare da ta san dalili ba, tunda suka Wauki hanyar asibitin gabaWaya yanayinta ya canja take ji kamar ba ita ba. Da suka hau kan titin asibitin sai take kallon titi, tana jin kamar akwai wani abun da zai faru, amma ta rasa meye shi.

Tun daga farkon layin da zai kai ka asibitin za a ka san asibitin ba da wasa bane, an zuba masa titi mai kyau, hanyar ta yi kyau kamar kar ka daina tafiya.

Tun daga wajen asibitin take ?are masa kallo, an yi masa wani irin gini da bata taSa gani ba, ga shi tsaho kamar hotel, floor by floor. Babban asibiti ne, kai daga ganinsa ka san an kashe kuWi wajan samar dashi, yana da girma mai ban mamaki tun daga waje, ga kyau da Waukar ido.

NADIRA HOSPOTAL shine abinda yake a rubuce da wani irin front mai kyau, da design mai Waukar hankali. Parking space Win asibitin ma abin kallo ne, yana da matu?ar girma, gashi an samar da duk wani abu da ya kamata a wajen.

Labiba da ta gama ?are masa kallo ta ce, "Hamma Sadik wai wannan asibitin? Anya zamu iya biya?."

Ya kalli Ambulance Win da tuni har ta shiga, ma'aikata sun fito an shiga da Baffa ciki.

Mama ta ce, "abinda zan ce kenan, naji ana zancen asibintin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login