Showing 81001 words to 84000 words out of 96103 words

Chapter 28 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

56

mantawa da matsayina ne?."

Abba ya ce, "tare ku ka yi laifin ai, dan an yi muku faWa a tare ai ba komai bane."

"Komai ne wallahi, zubar min da mutunci ka ke yi a gaban na ?asa dani. Ai na wuce a zaunar dani a cikinsu ayi min faWa, ni sai dai a yi min nawa personal ba a haWa ni dasu ba. Ai inda kara ni zaka yiwa faWan, ni kuma sai in je in yi musu a madadinka. Haka kwanaki ka zauna dani da ?aramar yarinyar nan amaryarka, yarinyar da na haife ta, amma ka haWa ni da ita ka zaunar wai kana yi mana faWa. Raini ka ke jawo min wallahi."

Abba ya murmusa yana girgiza kai ya ce, "ke kuma gaki shugabar masu son girma ko?."

Ta kalle sa ta ce, "ai girman ya kama ni ne, dukkansu a bayana suka tare, babu wacce ta riga ni aurenka, to akan me zaka dinga yi min haka?."

Abba ya Wan taSe baki ya ce, "ni ba wannan na kira ki na ji ba, ki je ki duba Rehaan kawai."

Mama ta ce, "ai zan je. Amma don Allah ka daina yi min haka, uwargida ce ni fa, uwar gida mai capacity."

Sai ta bawa Abba dariya, ya yi murmushi ya ce, "an gaishe ki, uwar gida. Ki je ki dawo zamu yi maganar."

Mama ta ce, "yauwa. Maganar kayan abincin nan da muka yi da kai, na bayar fa, kar ka tambaya ace babu."

"Ikon Allah! Dan na ce zan yi tunani har kin bayar?."

"Kuma kamar kaine ka bayar ba, ko na yi laifi ne?."

Abba ya ce, "Ya zan yi miki tunda kin bayar? Shikenan kawai."

Ta yi murmushi ta tashi ta fita, tana jin daWin yadda take da zuciyar Abba har lokacin a hannunta, soyayyar ?uruciya bata gushe ba tana nan, dan ko ba?o ne yazo ya kwana biyu sai ya san itace take mulki a cikin gidan. Haka take son yaranrta su kasance, ko tsuntsuwa ce ta zo wucewa ta saman gidan, tana so ta zama shaidar ?a?anta sune suke juya gidan. Ita a son ranta, Abban ma ya talauce, ya zama ?a?anta ne suke siyan komai a gidan. Hakan shine girma a gare ta.

? ? ? Da safe Islaha da wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya don komawa asibiti. Tana tsaye a kitchen sai ta kira Mama a waya, Mama ta Wauka bayan sun gaisa ta ce, "Mama akwai abinda za a kawo miki?."

Mama ta ce, "ki taho min da kaya Islaha. Hanan ta dawo gida kuwa?."

Islaha ta ce, "eh ta dawo Mama."

"?arfe nawa ta dawo?."

"Wallahi ban sani ba, na ganta yanzu dana tashi

"shikenan, ki kawo min kayan sakawa."

"Abinci fa?."

"An bani abincin karyawa a nan Islaha, kaya kawai nake so."

Islaha ta amsa tana kashe wayar ta dafa tea ta sha ta fito falo ta shiga Wakinsu dan Waya ta Wauko mata kayan Mama.

Islaha ta tarar dukkansu basu tashi ba, ta yi ajiyar zuciya dan ba shiga Wakin Mama take yi sosai ba, bata son ta shiga aga babu wani abun ace itace.

Da?yar ta daure ta shiga, ta buWe wajan kayan Mama ta Waukar mata doguwar riga da hijjab ta fito daga Wakin. A daidai lokacin wayarta ta Wauki ?ara, a tunaninta Sadik ne sai ta ga Zainab ce.

Ta Wauka ta saka a kunne ta ce, "Zainab ya aka yi?."

"Adda jiya naje office Win Mama na ji tana waya tana cewa kawai a yi maganinki, in ba haka za ki zamar musu matsala. Adda ki dage da addu'a, inda dama ki daina bibiyarsu kar su cutar mana dake, don Allah."

"Yaushe ki ka ji suna wannan maganar?."

"Jiya ne."

"Ita da waye?."

"Waya take yi, ban sani ba. Tun jiyan nake kiran ki wayar ki a kashe."

"Shikenan, ki kwnatar da hankalin ki, duk abinda ya sake faruwa ki faWa min. In kuma kin samu dama, in kin ji ana maganar ki shiga number ta ta whatsapp, ki danna voicenote ki tura min."

"To Adda zan yi."

"Amma fa in baza ki iya ba kar ki yi, kawai ki ji sai ki faWa min."

Zainab ta ce, "Adda ga Fadwa nan, zan kashe" ta faWa tana kashe wayar.

Islaha ta Wan yi shiru ta ce, "har abin ya kai haka kenan? Lallai akwai aiki a gabana, dole a san abinda za a yi."

Kiran Saheer ne yake shigowa ta wahatsapp, ta yi murmushi ta Wauka ta ce, "Hammana."

Daga can Sangaren ya ce, "Matar Hamma."

Ta yi murmushi ta ce, "Ina ta jiran kiran."

"Ba wani nan, bayan ko message Win ki ban gami ba."

"Wallahi abubuwa ne suka yi yawa Hamma, amma kana raina."

"Meye suka yi miki yawan?."

"Aiki ne. Ka je lafiya?."

"Lafiya lau matar Hamma, kina nan lafiya?."

"Lafiya lau Hammana."

"Mama bata tashi ba? Na kira bata Wauka ba."

"Ina jin bacci take yi."

"Baffa ma bai Wauka ba. Kar na tare ki da surutu, ki je ki ci abinci." Ta amsa dan itama so take ta kashe tana jin kiran Sadik yana zuwa.

Tana kashewa ta kirasa, Sadik yake sanar da ita yana ?ofar gida yana jiranta.

Bata tsaya jiran komai ba, ta yafa chatelity veil a kanta, sannan ta Wauko kayan Mama ta fito.

Sai da ta shiga motar ta kalle sa ta ce, "ina kwana Hamma Sadik."

Ya yi murmushi ya ce, "an tashi lafiya matar Hamma?."

"Lafiya lau. Ya gajiya?."

"Alhamdu lillah Islaha. Ke kaWai ce?."

"uhum, bacci suke yi."

Ya ja motar suka fara tafiya ta ce, "Wazu kana kirana muna waya da Hamma ne."

Ya yi dariya ya ce, "tunda na ji call waiting na san shine. Amma baki faWa masa ba ko?."

"Ban faWa masa ba, yana ta tambayar ina Baffa kuma."

"Za a faWa masa, sai mun ji abinda yake damunsa tukunna."

Bata ce komai ba ta sauke numfashi suka cigaba da tafiya har suka ?araso asibitin. Suna tsayawa ta saka facemask dan ac reception Win nan zata iya cutar da ita.

Sadik ya kalle ta ganin ta gama sakawa ya ce, "anya ba asthama ce dake ba, Matar Hamma?."

"To Hamma Sadik an yi gwaji ance babu, babu irin gwajin da ba a yi min ba amma ance ba ita bace. Amma duk wani alamunta ya bayyana a gare ni."

"Gaskiya ya kwmata a faWaWa bincike. Dan ni nasan itace kawai." Ta yi murmushi ta fita suka shiga asibitin.A nan suka tarar da Mama a zaune, suka ?arasa suka gaishe ta amsa.

Mama ta kalli Islaha ta ce, "ina Labiba ko Hanan?."

Islaha ta ce, "bacci suke yi dana fito." Mama ta girgiza kai ta ce, "bacci!" Ta maimaita cike da mamaki. Mahaifinsu yana asibiti cikin wannan yanayin amma su bacci ma suke yi."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta ce, "ai shikenan, mu je wajan likitan ko?."

Sadik ya ce, "Ki fara shiryawar Mama." Mama ta ce, "mu je dai Sadik" ta faWa tana mi?ewa tsaye.

Islaha dai kallon Mama take yi tana mamakinta, ashe duk kafsa faWan da suke yi da Baffa tana son kayanta, ita wallahi bata Wauka zata damu ba, ta Wauka murna zata yi dan Baffa babu lafiya zata samu damar yin abinda take so. Amma sai ta ga akasin haka, sai ta ga ta fi ?a?ansa damuwa, kana ganinta kasan ta damu da rashin lafiyarsa sosai.

Islaha ce ta yi knocking ?ofar, ya amsa daga ciki suja shiga da sallama. Dr ya amsa yana kallon su ya ce, "Mustapha Maddibo ko?."

Islaha ta ce, "mu ne."

Ya nuna musu wajan zama ya ce, "bismillah ku zauna."

Sai da suka zauna sannan ya ce, "kamar yadda na faWa muku jiya mun yi duk gwaje gwajen da ya kamata. Kuma alhamdu lillah mun kamo bakin zaren."

Dr ya ce, "ya taSa yin ciwon ?oda ne ko sau Waya?."

Mama ta ce, "eh ya taSa yi, amma an fi shekera goma gaskiya."


Ya girgiza kai ya ce, "kuma ya san yana da cutar hawan jini da sugar?." Mama ta girgiza kai ta ce, "hawan jini dai an taSa faWa masa yana dashi, amma sikari gaskiya bai sani ba."

"Yana shan maganin hawan jinin?."

"Gaskiya ba ya sha."

"Kuma yana cin gishiri, kanwa, baya samun isashshen bacci?."

Mama ta girgiza kai ta ce, "gaskiya yana shan kanwa sosai, dan kullum sai an dama masa kunun kanwa."

Dr ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ciwon ?oda ne ya kama shi mai ?arfi Mama, dan har ya kai mataki na ?arshe, mataki na biyar a cikin matakan ciwon. Wanda mu ke kira end stage kidney disease (Eskd)."

Islaha ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma?Dr ya daWe da yin ciwon fa."

Dr ya kalle ta ya ce, "Ko da bai taSa yi ba, hawan jini da sukarin da suka yi masa yawa zasu iya taSa masa ?oda. ?oda bata kamuwa da ciwo haka kawai dole sai da dalili. Ciwon ya bayyana a yanayin da mu ke yiwa take da silent disease, ma'ana yana jin alamomin ciwon amma bai Wauki mataki, su kuma ciwukan da suka haifar masa da kamuwar ciwon ?odar bai san dasu ba, balle ya sha magani ko ya dinga dubawa akai akai."

"Ko yawan shan magani ba tare da umarnin likita ba yana lalata ?oda, kamar haka kawai ka dinga shan maganin ciwon kai, ko na kashe raWaWi ba tare da dalili ba, ko magangunan hausa wanda basu da dose, haka kawai mutum ya dinga zubawa cikinsa. Yawanci alamun ciwon ?oda yana bayyana ne in ya yi nisa sosai."

"Ba haka kawai ake kamuwa da ciwon ba, ana jin alamomin ta sai dai in an raina alamomin, dan ba wani abu bane mai ?arfi da in mutum ya ji zai ce ai wannan babban ciwo bane. ?ananun alamomin ta ana gane su ta raguwar fitsari, yawan yin fitsarin mutum ya ragu, kamar in yana yin fitsari sau goma a rana, sai ya koma yi sau uku wannan Waya ne daga cikin alamominta. Kun san ?oda itace take tace fitsari, shiyasa ba a son yawan ri?e fitsari da mutane suke yi."

"Ka ji mutum yana cewa ai ni sai in yini ban yi fisari ba, hakan ba burgewa ba ce ba, a ?alla ana so mutum ya yi fitsari duk bayan awa uku. Ya zama a rana, mutum yana fitsari sau huWu zuwa takwas. Dan ruwan da ka sha mara kyau ?oda take tacewa kai kuma fitar dashi. Raguwar fitar fitsari alamu ne na ?oda ta fara rage aikinta, ko ta gaza tana bu?atar tallafi. Ko kuma fitsarin ya yi duhu ko ya dinga kumfa. Sannan akwai yawan gajiya da jin rauni, mutum bai yi aiki sosai ba amma sai ya ji ya gaji sosai, shima yana daga cikin alamunta ne."

"Akwai kumburi, ?afa ko ido ko fuska suna kumbura haka akwai. Mussamman da safe, mutum ya tashi aga fuskarsa ta kumbura yana nuni da alamun hakan. Akwai rashin jin daWin jiki, jin sanyi ko ciwon kai haka. Akwai yawan bushewar fata, ?ai?ayi haka mara tsanani ba na Waga hankali ba. Akwai rashin cin abinci, duk wannan ?ananun alamomi ne."

Mama ta kalle sa ta ce, "tabbas kwanakin nan duk abinda ka faWa yana faruwa dashi. Dan har wani magani ya samo yana sha, saboda yawan gajiya da raguwar fitsarin."

Likita ya ce, "shiyasa na faWa muku ciwon baya faruwa haka kawai, kamar cancer ce, cancer bata bayyana sai ta yi nisa a jiki, amma zaka dinga jin ?ananun alamomin da zaka raina jinsu."

Islaha ta ce, "yanzu meye abin yi?."

"Kidney transplant!."

Islaha ta ce, "me hakan yake nufi?."

Ya sauke numfashi ya ce, "kamar yadda na faWa muku ciwon ya je matakin ?arshe, ?odojinsa sun daina aiki duka biyun, dole sai an yi masa dashen ?oda!."

A tare suka yi dogon salati, cikin kiWima da tashin hankali mai tsanani.

Sadik ya ce, "Dr dashe fa ka ce?."

Ya Waga kai ya ce, "ta kai matakin da dole sai an cire an saka masa wata gaskiya."

Mama cikim rauni ta ce, "likita babu wata hanya sai wannan?."

"Babu Mama, wannan ita kaWai ce hanyar da za a bi don samar masa da lafiya."

Islaha ta girgiza kai cikin tashin hankali da ruWani ta ce, "Wanne process ake bi dan yin dashen?."

Dr ya ce, "sai an samo wanda zai ba da ?odar, sai ya zo nan ayi gwaje gwaje, in komai ya yi daidai da na wanda za a Wora masa sai a yi."

Islaha ta ce, "Kuma aikin yana kaiwa nawa?."?

Ya kalli islaha ya ce, "daga miliyan biyar zuwa miliyan sha biyu. Tun daga kan gwaje gwaje, da yin aikin har a gama."

Gabanta ya yanke ya faWi jin manyan kuWi, ta kalli Sadik da ya yi shiru ya kasa magana, ta kalli Mama da take zubar da hawaye dan ta san ?arshen rayuwar mijinta ta zo kenan.

Da?yar Islaha ta ce, "Kuma in siyan ?odar za a yi fa? Misali in babu wanda zai bayar."

"A dokance da lafiyance ba a siyar da ?oda, sai sai a samu wani Wan uwa ya bayar a saka masa. Amma siyar da ?oda babban hatsari ne, kuma asibitin nan duk wani abu da ya saSa doka bama yin sa gaskiya. Mai asibitin yana da tsauri da ?a'ida, banbancinsa da bature kaWan ne, dan haka amsar ki ba a siyar da ?oda. Amma za a iya samun wanda zai ba sa ?oda."

Islaha ta yi shiru bata ce komai, kowa ya yi shiru ya kasa cewa komai, sai daga baya ta ce, "yanzu mu zamu bincika inda za a samu?."

Ya Waga kai ya ce, "eh, a cikin ku ko a cikin ?an uwa a duba za a iya samun wanda zai bashi tasa. In aka samu sai ku zo a yi lissafi a biya kuWin, daga nan sai a san abinda za a yi. Amma in aka yi ana samun lafiya, mutum yana cigaba da rayuwa lafiya indai zai dinga shan magani yana aiki da dokar likita."

Sadik ya sauke nunfashi ya ce, "daga nan zuwa yaushe ake so?."

"Ko yanzu in aka samu wanda zai bayar ya zo zamu bincika lafiyarsa. Indai ya kasance lafiyayye wanda bashi da ciwon ?oda, wanda mu ke kira normal kidney function, sannan glomerular filtration rate GFR, ma'ana yawan aikin ta ce jini da ?oda take yi a duk minti Waya, ana so nasa ya zama 90, sannan ya zama babu choronic kidney disease CKD ma, ya zama stage 0 kuma healthy one. In ya sakance yana da CKD koda stage one ne sai an canajwa wani. Amma in ya zama healthy lafiya lau, zai zo mu bashi tsarin abincin da ya kamata ya fara ci kafin aikin, sai a yi gwaje-gwaje a saka ranar yin aiki."

Kafinsu yi magana Dr ya ce, "dan haka kafin a samu ayi dashen ?odar za a fara yi masa dialysis, wankin ?odar kenan, shine kaWai zai ri?esa kafin a samu donar Win, a kuma yi gwaje-gwaje da sauransu. Tunda ciwon nasa ya kai stage Win ?arshe, za a dinga yi masa dialysis sau uku a ko wanne sati, kafin a samu abinda ake nema."

Islaha ta ce, "shi kuma nawa ne dialysis Win?."

"Kin san nan private hosptal ne, dialysis Win mu 300k ko wanne. Kamar shi da za a dinga yiwa sau uku a sati, zai sama duk sati dubu Wari tara. In aka samu wanda zai ba da ?odar sai a zo a tantance ayi aiki."

Islaha ta sauke nunfashi mai ?arfi ta ce, "shikenan Dr, mun gode da bayaninka."

"Babu komai. Kuna ganin a fara yi masa yanzu? A fara wankin ?odar dan a rage masa wasu abubuwan?."

Sadik ya Waga kai ya ce, "a fara Dr. A ina zamu biya kuWin?."

"Za a saka muku a bill, in kuma personal ka ke so ka je reception zasu baka duk abinda ya kamata."

Suka amsa kafin Mama ta ce, "zamu iya ganinsa?."

Dr ya ce, "eh, mu je" ya faWa yana mi?ewa ya fita suka bi bayansa.

Da yake jikinsu a sanyaye yake da?yar suke tafiyar, Dr har ya yi musu nisa.

Suka shiga Wakin da Baffa yake, ganin yanayinsa yake ciki ma kuka ya saka Islaha ta fito tana kuka sosai. Su ma basu jima ba sauka fito daga Wakin, suka zauna duka su ukun, a lokacin Adda Sa'ida tazo aka zauna? da ita don tattauawa.

Mama ta ce, "tsakani da Allah a ina zamu samu kuWin nan?."

Islaha ta ce, "Mama wanda zai bada ?odar shi za ki fara magana."

Ta kalle ta ta ce, "wanda zai ba da ?oda ba shine abinda tambaya ba, ?oda ko ni zan iya ba sa, ?a?ansa zasu iya ba da tasu, ?an uwansa duk zasu iya dan mutum ne wanda ko shine zai yi. KuWin aikin shine abin ji Islaha, magana ake ta miliyan goma sha, ga kuWin wankin, ga kuWin magani, ga kuWin asibitin nan. In ba fashi zamu yi ba a ina zamu same su?."

Adda Sa'ida da take kuka ta ce, "Babu inda zamu samu Mama, sai dai in gidanmu za a siyar."

"Mu koma ina? Kin san shi kaWai ne ya rage mana ko?."? Ta yi shiru bata ce komai ba tana kuka.

Sadik ya ce, "Mama zamu nemi bashin banki ni da Islaha, tunda ma'aikata ne mu zasu ba mu in sha Allah. Gobe litinin za mu je mu san abinda ya kamata mu yi."

Mama ta ce, "Saheer fa? Ku sanar dashi a daina Soyewa, wannan lamari dole sai an haWa ?arfi da ?arfe."

"Ba ma son Waga masa hankali ne shiyasa."

"Dole a Waga masa kuwa Sadik, yanzu ba dan akwai ka Win ba, ba dole ya dawo ba? Kuma in ta kama shi zai zo ya ba da tasa ?odar. Dan haka a faWa masa kawai."

Adda Sa'ida ta Wauki wayarta jin tana ?ara, ta saka a kunne ta yiwa Hanan da Labiba kwantancen inda suke suka ?araso.

Mama ta kalle su ta ce, "kuma zaku iya sadaukar da ?odarku ga mahaifinku ko?."

Hanan ta buWw ido ta ce, "?oda kuma Mama? Baffa za a bawa ?oda?."

"eh. Dashe za a yi masa." Suka yi shiru basu ce komai ba, dan gaskiya ba iyawa zasu yi ba.

Islaha ta ce, "za a san abinda za a yi in sha Allah."

Mama ta ce, "amma mu canja asibiti."

Sadik ya ce, "mu je ina Mama? Ai gwara mu zauna a nan, muna da tabbacin za a yi mana abinda mu ke so. KuWi zamu nemo in sha Allah,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login