Showing 15001 words to 18000 words out of 96103 words

Chapter 6 - RAGAYAR DUTSE BOOK 1 COMPLETE

25 Aug 2026

54

ba ta fita, dan ta ga yanayin Umma baza ta fahimce ta wuri ba.


? ? ? Islaha tana zaune a kan kujerun da aka yi su na gini a compund Win gidan sanyi yana ratsata, ta ?an?ame jikinta tana rawar sanyi cikin rashin mafita.

Ta kalli ?ofar da zata kai falo, ta Wauke kai tana lumshe ido tana jin numfashinta yana yin sama.

Ta san ko me zata cewa Mama baza ta bar ta ta shiga ba sai ta ga dama. Mama indai akan kuWi ne bata Waga ?afa, bata damu da inda zaki samo ba, ita dai kawaai? ki bata shine kwanciyar hankalinta.

Sau da dama Islaha tana ji har gwara zaman gidan marayu akan gidan Mama. Can babu mai takura mata ta kawo kuWi, in ta gama abinda take yi ta dawo ta kwanta shikenan.

Duk da can Win ma akwai ?ananun ?alubale, ta buWe ido kawai ta ganta a gidansu Saheer, bata san ya aka yi ta amince ta biyosa ba. Dan ta san a dokar gidan marayu, in dai mutum zai yi adopting Winka, kuma ka wuce shekara sha biyu, dole sai da amincewarka kafin hukumar gida ta yarda. Balle ita, da ta kusa gama university a lokacin.

Da kanta ta amince masa ta biyosa, ba ta san meyasa ya yi adopting Winta a lokacin ba, ta san sha?uwar da suka yi ne sila, amma wani lokacin tana danasani.

In Mama ta yi wani abun, sai ta ji kamar ta haWa kayanta ta koma, duk da ta san baza a karSe ta ba, kamar an yaye ta ne. Amma tana da yayyun da ?awayen da suka tashi tare, suka yi aure a manyan gidajen da zata iya zuwa can ta zauna. Kawai bata son zubawa Hamma ?asa a ido ne, da wata ran sai dai ya buWe ido ya ga bata nan.

?ankwalinta ta jawo ta rufe kunnenta ta jin sanyi yana shigar mata kunne ta ko wanne Sangare.

BuWe gate Win aka yi aka shigo, sai ta Waga kai ta kalli wanda ya shigo.

Safeera ta gani, ganinta a zaune a wajan sai ta ?araso da roba a hannunta ta ce, "Islaha lafiya ki ke zaune a nan? Kin san dai wajan nan ba wajan zamanki bane, tunda ba cikakkiyar lafiya ce dake ba ko?."

Islaha ta kalle ta tana ?an?ame jikinta ta ce "Safeera Mama ce ta ce in fito na zauna."

"Akan me?."

"Akan ban kawo kuWin ba, kuma bani da kuWin ne shiyasa. Da meye dubu goma ko ashirin da na bata?."

Safeera ta zauna kusa da ita, cikin fusata ta ce, "Amma Maman nan ?ar...."

Islaha ta dakatar da ita ta ce, "kar ki zage ta Safeera, ta yi min abinda babu wanda ya yi min irinsa a duniya. Duk da ba zaman daWi nake yi ba, amma babu laifi ina kwana na tashi har na ci na sha. ?anta kamar shine bangona, shi nake kallo a matsayin Yayana, aboki, kuma mijin da zan aura. Ta cancanci girmamawa ko ya ya ne."

Safeera a ?ufule ta ce, "to neman maza take so ki fara ko me? Haka kawai namiji zai Wauki kuWi ya ba ki ba tare da kin bashi wani abun ba?."

Islaha ta ce, "duk yadda ki ke tunanin Mama akan son kuWi ta wuce haka. Ita gani take yi haka yaranta suke yi, tunda suna fita su samo mata."

Safeera ta yi tsaki ta ce, "to ki zo mu tafi gidan mu kawai, in ba haka ba kin san sanyin nan zai cutar dake."

Ta girgiza kai ta ce, "a'a, ?yale ni kawai Safeera. Me ya fito dake a daren nan."

Ta mi?a mata pack Win ta ce, "Wainar fulawa ce, na soya shine na kawo miki."

Islaha ta karSa ta ce, "kamar kin san tun jiya nake muradin cinta wallahi, sai dai sanyin nan bazai bar ni ci ba."

Safeera ta ce, "ki zo mu tafi gidanmu, yanzu numfashinki zai ri?e, kin san yanayinki kamar na masu asthama."

Islaha ta ce, "ki bari kawai Safeera, na tabbata yanzu zata ce na zo na koma. Ki je gida, dare ya yi kar Baba ya yi miki faWa."

"Ya san na fito ai, kuma in dai tare dake ne ba ya? yi min faWa."

Islaha ta bita da kallo ganin fuskarta babu walwala ta ce, "wai me ya faru?."

Safeera ta ce, "Umma ce Islaha, wai zata tura ni aikatau ?asar waje."

Islaha ta zaro ido ta ce, "kamar ya?."

"Kamar yadda ki ka ji, kuma na san Mama ce ta zugata."

"Tabbas kuwa, dan Wazu tare na dawo na tarar dasu a falo, kuma na san itace zata yi mata maganar."

"Lamarin Umma ai sai a hankali, ita bata ga bata tura nata yaran ba sai ita zata zugata tura ni?."

Islaha ta ce, "me ki ka ce to ke?."

Ta kalle ta ta ce, "kema kin san ai bazan amince ba. Ni anya topic Win mu na ranar monday baza mu sake maimaitawa akan hakan ba?. Abin ya yi yawa Bestie, iyaye basu san inda yaransu suke zuwa ba, kawai kina nan kin tura ?arki budurwa tana wata ?asar aiki. Babu abinda ya dame ki da a hannun wa ta sauka, aikin me take yi, waye yake bata kuWin, duk babu ruwansu. Kawai ta turo musu kuWi. Wannan abun yana taSa zuciyata Islaha, kuma wallahi iyaye mata sun fi wannan katoSarar

Islaha ta ce, "hmmm! Kamar na fi ki tsanar wannan abun nan Safeera. In kin ga ?an matan da Mama take turawa ?asar waje sai abin ya ba ki mamaki. Kuma laifin iyayensu ne, sune suke bada damar wannan Sarakar wallahi. Kuma da wahala ki ga uba mahaifi ya aikata irin haka, kamar yadda ki ka ce matan ne dai. Dan su za ki dinga gani a wajan Mama, ana washe mata baki zata kai ?arsu Saudia. Zan yi magana da Chairman, zamu sake saka wannan a cikin topics Win mu in sha Allah."

Safeera ta ce, "gwara mu sake tattaunawa, dan da yawan yaran ba so suke yi ba, iyaye mata ne suke takura musu."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "da na je aikatau wata ?asar ba gwara na yi bara ba, Allah ya kiyaye."

Safeera ta ce, "Amin Islaha. bara na wuce, sai mun haWu gobe."

"Kamar kin san Chairman ya kira ni, wai yana so gobe na je da wuri zamu tattauna akan wata magana."

Ta yi ?ar dariya ta ce, "Chairman dai yana ciki, amma na san bashi da space, wajan Hamma Saheer ne."

Ta yi murmuahi ta ce, "gaskiya ne, bana iya kallon ko wanne namiji da fuskar soyayya sai Hammana, ina sonsa sosai Safeera."

Ta yi dariya ta ce, "ya cancanta ki so shi ai Bestie, ya yi miki komai a rayuwar nan."

Safeera ta mi?e ta ce, "sai mun haWu, don Allah ki samu ki shiga ciki."

Islaha ta ce, "To bestie, ki kwana lafiya." Daga haka suka yi sallama ta fita.

Wainar fulawar take son ci amma baza ta iya ba, sanyin ratsa ta yake yi, ga sauro da ya fara kawo mata hari. Duk da wajan akwai haske amma sauro ya dame ta sosai.

Ta mi?e ta ?arasa ?ofar sai ta tarar an kulle ?ofar,? ta Wan yi knocking aka yi mata banza, kuma tana jin motsinsu. Ajiyar zuciya ta yi ta zauna a wajan tana tunani kala-kala.


? ?? "Islaha!"

Ya faWa yana ?arasowa wajan da sauri. Ta kalle sa, bata yi magana ba har ya ?araso. Ya bita da kallo ya ce, "me ki ke yi a wajan nan a zaune ga sanyi? In ki ka samu attack fa?."

Islaha ta karyar da kai, cikin shagwaSa ta ce, "Mama ce ta ce in fito."

Da mamaki ya ce, "ki fito kuma, to akan me?."
Ta girgiza masa kai alamun bata sani ba.

Ya Wan yi tsaki ya ?arasa yana buga ?ofar falon Mama amma aka ?i buWewa. Ya kira Maman a waya bata Wauka ba, ya kira ?annensa duk suka ?i Wauka. Ya dawo kusa da ita ya ce. "Taso."

Ta mi?ewa tsaye, ya ri?e mata pack Win ya ce, "mu je Wakina ki zauna, in wannan sanyin ya yi miki illa fa, mai lafiya ma ya cika balle ke?."

Islaha ta bi bayansa, a hankali dan gaskiya bata son sanyi, tana da wani irin ciwo kamar asthma, duk da Hamma ya ce asthma ce, dan alamominta gabaWaya ya bayyana a kanta, amma an je ayi test an ce babu. Hamma dai ya ce ?arya suke yi, asthma ce da ita.

?aki ne babba mai Wauke da gado da komai na kayan gado, gashi a gyare babu tarkace sai takalmansa da laptop Win da yake aiki da ita.

Ya nuna mata gefen gadon ya ce, "ki zauna."

Ba musu ta zauna ya ce, "me zaki ci?."

Ta fara sosa kunnenta da sanyim ya shiga ta ce, "Zan ci wainar fulawa, Bestie ce ta kawo....." ta kasa faWa saboda atishawar da ta zo mata.

Saheer ya fusata, cikin faWa ya ce, "meyasa ba ki zo nan kin zauna ba za ki bari sanyi ya yi mili illa? Gashi nan har kin fara atishawa, kin manta kina da asthma ne?. Haba Islaha, meyasa baza ki faWa min ba?."

Cikin sanyin murya ta ce, "ka yi ha?uri. Kuma har yanzu ba a tabbatar asthma ba ce."

"Ni na tabbatar. ?arya likitocin suke yi, duk wanda ya ga yadda ki ke yi ya san itace."

Ya sake yin tsaki ya ce, "ki ci wainar, zan fita na samo miki magani. Akwai ruwa a fridge ki Wauka ki sha. Akwai abinda ki ke so in kawo miki?." Ta girgiza kai alamun babu sannan ya fita.

Tashi ta yi ta buWe fridge ta Wauki ruwan da babu sanyi sosai. Ta dawo a hankali ta zauna ta fara cin wainar ta hankali a kwance.

Bayan ta gama ta wanke hannunta ta goge da tissue ta sha ruwa.

Tana zaune ta yi shiru sai ta ji wayarsa da ya bari tana ?ara, ta duba gefenta ta ganta ajjiye, sunan boss yana yawo a kai. Bata Wauka ba ta Wauke kai, ta saka hannu ta jawo bedside drawer ba tare da zata yi wani abun ba.

Har zata rufe sai ta sake buWewa ganin abinda yake ciki, ta saka hannu ta takadar tana kallo. Copy visa ne na mata da yawa, ta dinga bi tana karantawa wasu an tura su ?asar larabawa, wasu ta turawa. Amma ?an Saudia duk sun fi yawa.

Ta girgiza kai ta ce, "Hajiya Mama, ashe abin ya bun?asa haka."

A lokacin ya buWe ?ofar ya shigo, ta kalli ?ofar shima ya kalle ta, ya ?araso ya ce, "har kin gama ci?."

Ba tare sa ta mayar da abinda ta Wauko ta ce, "na gama."

Ya bata magani ya ce, "ki sha." Ba musu ta sha maganin, takardun suna cinyarta.

Ya kalli abinda ta ajjiye a jikinga ya ce, "kina kallon copy visa ne?."

Islaha ta ce, "uhum, kawai na gansu ne. Na ce ashe Mama har kai take bawa ajiya."

Ya yi murmushi ya ce, "Hajiya Mama kenan."

Ta yi murmushi ta ce, "Chairman ne ya kira ni dazu, wai gobe yana son ya yi magana dani."

Ya kalle ta ya ce, "wacce magana kenan?."

"Ban sani ba, amma na san baza ta wuce akan Rehaan Yola ba."

"Rehaan Yola da na sani, nake jin sunansa a gari?."

Ta Waga kai ta ce, "Shi fa, ya matsa yana so mu yi hira dashi a channel Winmu. Ya dame ni akan ni zan kai invitation card Winsa, ko ta ya zai amsa gayyararmu ma oho."

"Daman ba mail ku ke turawa guest Win ba?."

"Mail ne mana. Shi sau nawa ana yi masa mail? An yi ya fi a irga, bayan shi har wani Jafar ake yiwa duk a banza. Shine za a je a kai masa Iv."

Ya bita da kallo ya ce, "To Ray Win ya dawo Nigeria ne? Ba fa a nan yake rayuwa ba, ance a Uk ne ko Us ban sani ba."

Ta taSe baki ta ce, "waye ya sani? Tunda ka ji yace nazo maybe ya ji magana akan zuwan nasa. Yana son yin hira dashi, ni kuma nasan bazai amince ba."

Saheer ya yi murmushi ya ce, "ke kin san waye Ray kuwa? Daga ranar da ya je tv ku, ko ya gayyace ku ai kun gama Waukaka Islaha. Har yanzu bai taSa hira da wata channel a Nigeria ba, shiyasa ko wacce channel take marmarin ta fara hira dashi."

Cikin ko in kula ta ce, "Ni fa wallahi ban taSa ganin hotonsa ba, ko maganarsa na ji ana yi zan wuce bazan kalla ba. Ba wai dan ba?in ciki ko hassada ba, ni bai yi ba Hamma. Bana son mutumin da ya cika Waukaka da yawa, kuma yana banzatar da mutane. Kuma ance yana da abubuwan cigaban da in ya kawo Yola, zamu zama na farko a Nigeria da aka fara samu. Amma ya tare a ?asar turai."

Ya yi dariya ya ce, "ke waye ya faWa miki?."

Ta turo baki ta ce, "haka na ji an ce."

"Haka ki ka ji, dan haka baza ki Worar ba. Ban taSa ganinsa, ba amma ana faWa halayyarsa masu kyau. Kuma ya kawo babban asibitin da babu kamarsa a nigeria, kuma ga kasuwar zamanin da in ki ka shiga zaki ce a dubai ki ke. Ai mun je dake kin ga yadda take, zan Wauke ki mu je asibitin ki yi kallo."

"Ni fa ba wani burge ni yake yi ba, in na je ma bazan gani ba."

"A'a matar Hamma. Ki faWi gaskiya."

Ta yi dariya ta ce, "shiyasa ake so na kai masa? invintation da kaina. Tunda sun ce ina da sa a, ban taSa gayyatar wani ya yi denying ba. To ni kasan bana son raini ka sani, in ya yi min wula?anci wallahi ba ?yalesa zan yi ba. Ka san halina, bana Waukar raini. Tsaf zan yi tsalle na gaggaura masa mari."

"In ya saka aka zane masa ke babu ruwana."

"Ina da kai, zaka rama min."

"Gaskiya ne, babu mai taSa ki ya kwana lafiya."

Ta yi dariya. Saheer ya ce, "Ba dan kar na rantse ba, da na rantse da Allah sai ya yi accepting Winki, kin san meyasa?."

Ta girgiza kai tana murmushi, ya kalli idanunta ya ce, "saboda daga jininki abin ya ke, Allah ne ya baki ba wani ba, matar Hamma."

Murmushi ta yi tana rufe fuskarta cikin jin daWin abinda ya ce. Shima murmushi ya yi yana kallon ta cikin soyayya, kafin ya mi?e ya ce, "zan fita, zan koma wajan Sadik mu kwana tare."

Ta mi?e tsaye tana kallonsa ta ce, "fita zaka yi?." Ya Waga mata kai yana kallon idonta.

Ta shagwaSe fuska ta ce, "ni kaWai zan kwana? Allah tsoro nake ji."

Ya Wan matso kusa da ita ya ce, "to ya ki ke so ayi, Debbo am?."

"Ka zo mu kwana, sai in kwanta a kan floor."

"Sai ni na kwanta akan gadon ke kina ?asa?" Ya faWa yana bin fuskarta da kallo. Ta Waga masa kai kamar ?aramar yarinya.

Ya yi murmushi, tare da jan hancinta ya ce, "A'a Debbo am, zan je mu kwana da Sadik, ke ki kwana a nan."

Cikin shagwaSar da ta saba yi masa ta ce, "ni dai A'a, Allah bazan iya bacci ba."

Ya sake yin murmushi ya ce, "tsoro ki ke ji?."

Ta Waga kai alamun eh. Ya ce, "babu abinda zai same ki, ki kwanta kin ji."

"Ni dai a'a, don Allah ka kwanta kawai."

"islaha bazan kwana a nan ba."

"Meyasa?."

"Akwai shaiWan Matar Hamma, gwara na baki space, zan dawo da asuba in sha Allah."

"Ni ba ?anwarka ba ce? Ai babu komai."

Ya yi dariya ya ce, "?anwar Hamma. Na san ke ?anwata ce, kar ki damu babu abinda zai same ki."

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san bata yarda ba kenan. Ya sake yin dariya ya ce, "za mu kwana tare wata rana, ranar ba sai kin ce min in zo mu kwanta ba, da kaina zan ri?o hannunki mu kwana tare. Na yi miki wannan al?awarin, indai ranar nan ta zo zan tuna miki. Kin san me zan yi?.

Ta girgiz kai tana Wan murmushi, kanta yana ?asa saboda kunya.

Saheer ya ce, "bazan bari ki kwanta akan komai ba, ni zan zamar gadonki kuma pillow ki. Al?awari na Waukar miki, kuma zan tabbatar miki dashi, Debbo am!."

Islaha ta ji kunya mai tsanani, ta juya masa baya harda rufe fuska da hannunta.

Ya yi dariya ya ce, "kina da aiki gobe matar Hamma, ki kwanta sai da safe. Ki kulle ?ofar kin ji? Sannan kar ki yi alwala da ruwan sanyi." Ta Waga masa kai ba tare da ta juyo ba.

Ya ce, "to ki juyo na ga fuskarki sai in tafi."

Ta no?e kafaWa ta ?i, ya ce, "ki juyo na ganki."

A hankali ta juyo kanta yana ?asa, ya yi dariya kaWan ya ce, "ki kwana lafiya."

Ta Waga ido tana kallon kyakyawar fuskarsa, mai cike da kwarjini ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya."

"Amin matar hamma" ya faWa yana niyar fita.

Sai ta ce, "Hamma!." Ya tsaya cak yana kallon ta, ta juya ta Wauki wayarsa ta ?arasa kusa dashi ta mi?a masa, ta ce, "ka manta wayarka."

Kafin ya karSa sai da ya bi hannunta da kallo sannan ya sake kallon fuskarta, ya murmusa ya ce, "Thank you matar Hamma." Murmushi ta yi ya ja ?ofar ya fita.

Islaha da murmushi ta zauna a akan gadon tana kallon Wakin. Tana jin daWin yadda ba ya za?ewa akanta, soyayya yake yi mata mai tsafta ba ya za?ewa irinta zamani.

Yadda ya ce saboda shaiWan Win nan ba ?aramin daWi ta ji a ranta ba, dan sai mai hankali ne zai tuna da hakan har ya faWa.

Shiyasa a kullum take ?ara ?aunarsa har zuciyarta, domin bata da kowa sai shi, kuma yana yi mata so na tsakani da Allah, ba ya tunawa da ita Win a gidan marayu ta tashi. Yana yi mata so mai tsafta, wanda zata bugi ?irji ta ce ita matar so ce a ko ina. Da wannan tunanin ta Wan kwanta, tana sake kallon Wakin dan bata taSa jimawa haka a ciki ba.

Nana Haleema
'
*RAGAYAR DUTSE.*

? ? ? ? ? ? ?? *Nana Haleema.*

More pages on Arewapen@nanahaleema11.

*Book 1*
*Page 005.*


Saheer yana fita ya shiga motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login