Showing 21001 words to 24000 words out of 70760 words

Chapter 8 - Mu-Rayu-Tare- complete

27 Aug 2026

22

"kuje ku shirya tun da wuri ki bani passport

ɗ

inki sauran abubuwan da za'a nema duk suna gurina"

Hajiya ƙarama ta miƙe tare da kamo hannun Iffat, "kuna kula da cin abincin

ta kuwa?"

"Eh Alhji"

Kafin suka wuce.

Wani wawan burki ya taka, tare da yin salari, jikinsa na

ɓ

ari yai parking mota, ya fito hankali a tashe yayi kanta  yana ambaton "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un"

Cikin ƙanƙanin lokaci mutane sukayi caaa a

gurin kowa na tofa albarkacin bakinsa, kafin Mahabob ya tallafo kanta yasa a mota, wani mutumi ya riƙe shi cikin masifa yace "wato dan kaga bata da gata shine zaka sanyata a mota ka gudu da ita ko? wlhi tallahi bazamu yarda ba sai munyi ƙararka"

Mahabo

b ya dafe kansa, rai a

ɓ

ace yace "haba malam, duk rashin imanina bazanyi wasa da ran

ɗ

an adam ba,  dan nasa ta a cikin mota shine zakuyi min mummunar fahimta, idan har kuka nemeni kuka rasa ku nemo Alhaji Auwal"

"Alhaji Auwal dai, kake nufi wanda sunans

a yayi shura?"

Mahabob ya hararesu cikin sauri ya shige mota yaja sai hospital,

Tare dashi aka shigar da ita emergency room, sosai zuciyarsa ke bugawa, a hankali yasa yakai hannunsa saitin zuciyarsa tare da lumshe ido, doctor ya kamo hannunsa ya fita

r dashi zuwa Office

ɗ

insa,

"Mara lafiyarka zata farka nan bada jimawa ba, Alhmdulilah batayi mummunan jin ciwo ba, sai dai rauni da taji a ƙafarta, karka damu"

Mahabob yai murmishi kafin ya zaro wayarsa a aljihu, ya danna number mu lovely sisna, Amani

ta

ɗ

aga cikin yanayin damuwa tace "bro lafiya kuwa, tun asuba da ka fice har yanzu gashi ƙarfe biyar 5:pm?"

Murya babu da

ɗ

in sauraro Mahabob yace "wlhi na bige wata yarinya tazo tsallaka titi, a halin yanzu dai muna asibiti"

Cikin tashin hankali Ama

ni tace "barin sanarwa da Abba, ko Kuma inzo"

Cikin sauri Mahabob yace "ba sai kinzo ba zan dawo zuwa anjima"

Yasan ba lallai ya dawo anjiman ba, kawai ya fa

ɗ

i hakanne dan ya kwantar mata da hankali.

Kiran sallahar magriba ne ya sashi miƙewa ya fi

to zuwa masallacin dake cikin asibitin, bayan yayi Sallah ya roƙawa mara lafiyarsa sauƙi a gurin Ubangiji, kana ya miƙe tare da sanya takalmin ya dawo cikin asibitin, haske ya gauraye ko'ina, idan kana ciki bazakayi zaton rana ba ce, office

ɗ

in doctor ya k

oma, ya sameshi yana cike ƴan takardu, jin shigowar Mahabob yasa doctor

ɗ

agowa yace "Barka da dawowa, yarinyar da ka kawo ta farka, zaka iya zuwa ganinta"

Jikin Mahabob na rawa yace "Tom Nagode"

Dama abinda yake sonji kenan.

Fita yayi daga asibiti y

a nufi shagunan da suke jere, ya kalli masu girke-girken gurin, duk mutanen gurin basuyi masa ba, saboda akwai shi da ƙyanƙyami,

Madara ya siya ta gwangawani sai maltina da Apple juice kafin ya siyi sabon cup, yaje gurin masu siyarda kayan marmari, lemu

abarba Apple kankana  gwanda da ayaba duk ya siya, aka sanya masa a leda ya kamo hanya hannunsa niƙi-niƙi da kaya,

Kai tsaye room

ɗ

in da aka kwantar da ita ya nufa, kafin ya ƙarasa ciki, tana jingine da pillo goshinta

ɗ

aure da bandeji, "sannu"

Mahab

ob yace cikin nuna kulawa,

"Yauwa dan Allah ka mayar dani gurin Ummana"

"Am sorry ki duba halin da kike ciki bakiga kinji rauni bane?"

Kafin ya

ɗ

auko cup ya ha

ɗ

a madara da maltina guri

ɗ

aya ya miƙo mata, sai yanzu ta tabbatar da rabonta da abinci

tun safe, ta kar

ɓ

a hannunta na

ɓ

ari, ta fara kur

ɓ

a ko cire kofin batayiba, har sai da ta shanye ta miƙa masa kofin, murmishin jin da

ɗ

i yayi, kafin ya bu

ɗ

e babbar ledar tare da

ɓ

are su Ayaba da lemu da duk sauran kasancewar an yanka lemun da gwanda, ya miƙa

mata, aiko taci bana wasa ba, sbda sai da tayi gyatsa kai kace ba mara lafiya ba, kafin ta ture,

Mahabob ya kalli screen

ɗ

in wayarsa da yake ƙoƙarin rufe layin saboda Amani damunsa zatayi,

A aljihu ya sanya wayar, kafin ya

ɗ

ago idanuwansa yasa anata

kafin yace "kozan iya sanin sunanki?"

"Sunana Huda"

A ransa ya mai-maita "Huda"

A fili yace "suna mai da

ɗ

i"

Huda tayi murmishi sai kuma ta ha

ɗ

e rai, tace "ina kular tallan shinkafa ta?"

Mahabob ya dafe kai, kana yace "wlhi nidai banga kula

ba, amma insha Allah idan aka sallameki zan siya miki duk abinda babu"

"Kiyimin kwatancen inda kike?"

Huda tace "Sabon layi"

Mahabob yace "muna sa ran gobe insha Allah zasu sallameki sai dai ina tunanin mahaifiyarki da batasan abinda ya faru ba"

Kiran sallahar isha'i ne ya sanya shi fita, yayo sallah ya dawo,

Ya samu har tayi barci,

Allah Sarki akan dogon bencin dake can nesa da gadon Huda ya kwanta, shima rabonsa da abinci tun na safe, kasancewar ba ma'abocin yawan cin abinci bane, barci ma

i nauyi ya

ɗ

auke shi,

Kasancewar alnyi mata allurar barci bata wani farka ba, sai gab asubha, lokacin shikam barcinsa yakeyi.

Kiran sallahar asbha da akayi ne yasa Huda cewa "

ɗ

an gaye an kira sallah"

Sai da ta mai-maita sau uku sannan yaji, yayi sal

ati kafin yasa takalmi ya shiga bayan gidan

ɗ

akin yayi alwala ya tafi masallaci.

Ita ko tunanin ummanta ya addabi rayuwarta, a inda take jin ƙarfi a jikinta ko yanzu akace ta tashi ta tafi, tafiya zatayi,

Tana cikin wannan tunanin har ya shigo ya gaish

e ta, ta amsa tana

ɓ

oye fuska, kafin ya nemi guri ya zauna, yana tsoron ya ciro wayarsa ya kunna Amani ko Abba ko Aseela su tayar masa da hankali, 

"Zaki iya miƙewa kiyi alwalah kiyi sallah?"

"Eh zan iya"

Huda ta zuro ƙafafunta ƙasa, tare da sanya

takalmi ta sabo wanda ya siyo mata a daren jiya ta nufi ban

ɗ

aki, ta

ɗ

auro alwalah ta cire

ɗ

ankwalin kanta ta kabbara sallah, beyi yunƙurin hanata ba, tunda babu abinda zata shimfi

ɗ

a.

   

             °°°°°°°°°°

"Ganin idanuwan Hajara sun fara kakkafe

wa ya sanya shi sake mata wuyan, da sauri ta fa

ɗ

i ragwab ga wani irin tari daya sarƙeta, da sauri ya koma

ɗ

akin da aka kwantar da Mona, cikin isa yace "ya ake ciki?"

"Fya

ɗ

e akayi mata, amma ya kamata ku

ɗ

auki mataki akan hakan"

"Ubanka ne yace anyi ma

ta fya

ɗ

e?, to bari kaji she's my wife"

Da sauri doctor ya kalli Shahazad, a zuciyarsa kuwa yana jinjina rashin Imani irin nasa, da har zai illata yarinya haka, Aiko Tasha

ɗ

inki sosai, a razane ta farka tana cewa "shine zai kasheni ku taimakeni babu muta

ne a gidanne?"

Cikin fusata Shahazad ya daka mata tsawa, kafin yace "idan matata ta samu matsala sai na kasheka"

Kafin ya dawo waje inda yabar Hajara a zaune, cikin bada Umarni yace "wuce muje mota zaki tahowa da Mona ruwan zafi mai yawa"

Wani docto

r na bayansu yace "ai akwai gurin matsar ruwan zafi a ciki" to munafiki  jeka munji"

Sai da ya gama ƙarewa Hajara kallo kafin ya sake komawa ciki, ya samu Mona ta barci,

"Wuce muje"

Ya sata a gaba suka wuce mota,

Suna isowa gidan sai da ya bata

umarnin fita kafin ta fice, kai tsaye kicin taje ta

ɗ

ora ruwan zafi kafin ta dawo

ɗ

akinta,

"Hajarrr"

Shahazad ya ƙwala mata kira, da sauri ta fito parlo gurinsa ta durƙusa, jeki gyara

ɗ

akin Mona....

Ayi haƙuri babu yawa

*

💋

MU RAYU A TARE

💋

*

Mom Islam

31-32

Jiki na rawa ta wuce

ɗ

akin Mona, tana hawaye tana gyarawa, bayan ta kammala, ta fara neman turarukan da zasu kawar da ƙarni jin da

ɗ

akin keyi, can ta hango room fresh mai ƙamshi sosai, tabi kowanne lungu da saƙo ta fesa, kamar ance t

a waiga ta hango hotuna a ajiye kan mirror,

Da sauri ta isa gurin ta dauki hotunan guda uku kafin ta kalli na farko, a fili tace "Mona, wannan kuma su waye?"

Tsananin kamar da ta gani  a fuskar mata da mijin ne ya sata zargin ko sune iyayenta,

A ba

yan hoton kuma akwai number waya,

Batakai ga kallon ragowar hotunan ba ta ajiye su tare da ƙurawa number kallo a firgice ta fara tunanin kira,

"Bani da sim card na ƙasar nan"

Tunowa Ai Hassana ta ajiye mata a jakarta ta rataye  yasa tayi ajiyar zuciya,

amma tana tunanin ta inda zata sato hoton ta fito dashi ba tare da mugun ya sani ba,

Dabara ce ta fa

ɗ

o mata ta kunce

ɗ

aurin zaninta ta tura hoton ta cikin riga, kana ta

ɗ

aura zanin akan rigar ta fito sai zufa takeyi,

Da sauri take sauka daga steps

ɗ

in

sam taƙi su ha

ɗ

a ido da Shahazad, cikin kakkausar murya yace "kawo hoton da kika

ɗ

auka"

"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un"

Ta ambata ƙirjinta na dukan uku-uku, tama kasa cewa dashi komai sai rawa da jikinta ya hau yi, zubewa tayi ƙasa jiki babu ƙw

ari ilahirin jikinta yai sanyi babu wani ƙwaƙwaran ƙarfi dake gareta, tace "ban

ɗ

auki komai ba"

"Ehh wato Shahazad Junaid Khan, zaki yiwa ƙarya bayan idona ya ganemin duk abinda kikayi?"

Bata da wata mafita da ya wuce ta bashi hoton, haka kawai ta ts

inci kanta da tura hannu ta saman ƙirjinta ta ciro hoton ta miƙa masa,

"2Game over"

Sam batasan me yake nufi ba, amma tasan wannan murmishin da yakeyi tsaf zai iya aikata mata koma meye tunda shikam baya shayin kowa,

Kitchen ya wuce ya

ɗ

auki ruwan

zafin ba tare da yace "tazo su tafi ba, hankalinta yai mugun tashi, sbda taso su koma taga jikin Mona, amma babu inda ta iya dole ta zauna a gida, tambayarsa wani abun ma ba nata bane, tunda ta samu ya ƙyaleta da ranta beyi mata komai ba, ko kuma da wani s

hirin da yakeyi a kanta ne oho?"

Tana so ta tsananta bincike akan halaiyyarsa yanzu kam guwaiwoyinta sunyi sanyi, ita ba kowa bace zai iya kasheta babu mai

ɗ

aukar mata fansa.

Da wannan tunanin ta koma

ɗ

akinta ta

ɗ

auki sim card na ƙasar tasa, kafin ta

duba number Hassana, ring

ɗ

aya ta

ɗ

aga, kafin hassanar tace "Hajara inata kira sai acemin a kashe, kuma har ku

ɗ

i fa nasa miki"

Hajara ta kawar da zancen ta hanyar cewa "Hassana dama kinsan wannan mutumin mugu ne kika kawoni gidansa?"

"Haba Hajara ina

ruwanki da halinsa, aiki ne ya kaiki ba sa'ido ba"

Tunda Hassana tayiwa Hajara wannan maganar, tace "shikenan"

Ta katse kiran.

Ala-Uddin Samir. durƙushe take a gabansa tana mopping, hankalinsa a zahiri zaka

ɗ

auka akan waya yake, alhalin kuwa rabin h

ankalinsa ya tattara ne ga ƙirjinta dake a bu

ɗ

e ana ganin ilahirin nonuwanta, Sam batasan da hakan ba ita dai tanata aikinta,

"Haseeinaaah"

Ala-Uddin ya kira sunanta da cold voice

ɗ

insa,

"Na'am"

Hassana ta amsa tare da durƙusawa a gabansa,

"Yau Lulu

zata dawo da wuri ne?"

"A'a tace min sai ƙarfe hu

ɗ

u saboda yanzu karatun yayi yawa"

"Okay kawomin Basmati"

Hassana ta miƙe cikin girmamawa ta kawo masa, a

ɗ

an matsakaicin faranti na tangaras me kyau, sai lemo na roba, wanda ya kasance shine ruwan

shansa,

Bayan ta ajiye masa, ya tsayar da ita kafin ya tsiyaya mata lemun a

ɗ

an ƙaramin cup ya miƙa mata,

Girgiza kai tayi alamar "a'a"

Tsawar da ya daka mata ya sata saita nutsuwarta ta kar

ɓ

a,

Sai da ta shanye duka, kafin tabar gurin, koda yaushe

hakan yake yi  mata,

Tana komawa

ɗ

akinta taji barci mai

ɗ

a

ɗ

i yana shirin

ɗ

aukarta, hankali kwance ta kwanta, tare da janyo abin rufa, lokacin ƙarfe 3:pm,

Ala-Uddin ya leƙo cikin san

ɗ

a tare da komawa parlo ya rufe ko ina kafin ya dawo

ɗ

akin Hassana nan

ma ya rufo ƙofa, lokacin da ya shigo har ta

ɗ

ago ido ta kallashi, sai dai kash bata isa ta banbance ko waye ba, idanunta sunyi kamar na mashayiya da tashi

ɗ

aya,

Cikin sauri ya cire gajeren wandon da ya kasance daga shi sai wata riga marar nauyi, Hassana k

uwa riga da sikel ne irin na turawa Amma skel

ɗ

in  ya saukar mata har ƙasa, duka kayan ya ciresu tare da ƙarewa tsaraicinta kallo, can kuma yai saurin afka mata, sbda tunowa da yayi, befi awa

ɗ

aya ne dashi ba, haka ya yi mata rumfa tare da shigarta, har ya

nzu ta farka amma idanunta basa budewa sosai, sannan duk ga

ɓ

o

ɓ

in jikinta a sake suke, haka ya dinga kaiwa da kawowa yana sumbatunsa shi ka

ɗ

ai, already maganin na minti 40 ne yanayi yana kallon waya...

Afuwan

Afuwan

Please akuyi hakuri muna rashin ne

pa wlhi, insha Allah zuwa gobe idan na samu hali zanyi muku mai yawa .

Mom Islam

*

💋

MU RAYU A TARE

💋

*

Mom Islam

33-34

3:45pm ya mirgina gefe, sai yanzu nutsuwa ta fara zuwar masa, ya miƙe da sauri, karo na farko kenan da sukayi ido biyu da H

assana, a razane ta miƙe tare da

cewa "innalilahi wa inna ilaihir raji'un, dama yawan ganin jiƙewa da nakeyi kaine sila?

Meyasa ka za

ɓ

i kayi zina dani bayan Kanada matarka ta sunnah?"

Da sauri Ala-Uddin Samir ya kalli agogon dake

ɗ

aure a tsintsiyar hannu

nsa, ƙarfe 3:46pm alhalin tun ƙarfe 3:40pm da ya wuce ya kamata yayi nesa da ita "whay ya bari ta gansa,  yanzu zata tona masa asiri kenan kokuma zata rufa masa, runtse idanuwanta tayi, sbda kaucewa ganin tsaraicinsa, bayan ya kammala saka ƙananun kayansa,

ya kalleta lokacin ta rufe jikinta da bargo a durƙushe yace "Haseeaina zanyi miki komai na rayuwa zan mayar dake ƴar gata zan fifitaki akan Lulu zan canza miki duniya ba wannan ba, inhar kin amince dani zan yi miki duka wa

ɗ

annan abubuwan"

Hassana ta ka

lli Ala-Uddin Samir cikin kallon bakada hankali tare da fassarori daban-daban ta kawar da kanta, 4:50pm na cika Ala-Uddin Samir ya miƙe jiki na rawa har zai fice sai kuma ya dawo yace "idan kinyi shawara any time ƙofa a bu

ɗ

e take"

Kana ya fice da sauri, m

iƙewa tayi ta fa

ɗ

a toilet cikin dauriy, tayi wankan tsarki kafin tayo alwalahar la'asar, tana fitowa ta shimfi

ɗ

a sallahya ta kabbara Sallah, tana idarwa ta

ɗ

aga hannu sama, tana kuka tana gayawa Allah halin da take ciki.

Sallamar Lulu ne ya sanyata miƙewa

da sauri ta fice, ko ninke sallahyar batayi ba, ta fito parlo.

"Barka da dawowa shugabata"

Cike da izza, Lulu tace "yauwa Barka, bani labari yau Ala-Uddin yayi waya da ƴan mata ne?"

"A'a shugabata, nadaiji yana waya akan kasuwancinsa"

Juyar d

a ido tayi farrr tare da juya mazaunai ta isa

ɗ

akin Ala-Uddin,

Ko jakar makarantar bata ajiye ba ta wuce

ɗ

akinsa, yana zaune hannunsa riƙe da biro da takarda, wani irin zane yakeyi wanda ba kowane zai gane abinda yake zanawa ba, sbda sarƙaƙiyar rubutun.

Tana tsantsar sonsa, hakan yasa idan suna tare take mancewa da komai, ta rungumoshi ta baya, tana cewa "nayi missing

ɗ

inka Hubb"

Ala-Uddin ya zagayo da ita kan cinyarsa tare da cewa "yau kinsha wahala a makaranta meyasa bazaki haƙura da karatunan ba?"

Cikin siririyar murya tace "Hubb inaso in zamo cikakkiyar ƴar jarida domin mu yaƙi masu aikata yawaitar fya

ɗ

e da kidnap da sauran

ɓ

arayi"

Ala-Uddin ya lumshe ido yana shafa gashin kanta, kafin yace "yanada kyau pretty sai dai Ina son rayuwarki kinsan wann

an aikin salwantar da rai ne"

Lulu tayi murmishi, kana tace "ai inada kai shiyasa bana damuwa jarumina".

NIGERIA

Ƙ

arfe 11:am aka sallami Huda daga asibiti, idan ka kalli fuskar Mahabob ya rame sosai, hannunsa riƙe dana Huda suka shiga office, hannun

shi na hagu riƙe da takardar sallama, a rubuce likitan ya rubuta musu dokokin magungunan da

allurai da zasuci gaba da kar

ɓ

a na kwana uku, daga nan Mahabob ya biya ragowar ku

ɗ

in kana suka fito harabar asibitin,

Kai tsaye gurin motarsa suka nufa, ya bu

ɗ

e ma

ta gaba shima ya shiga mazaunin direba, kafin ya tayar da motar suka fara tafiya.

Har sunyi nisa a titi sai kuma yace "wace anguwa?"

"Anguwar rimi"

Suna shigowa anguwar, Umman Huda tana tahowa kanta

ɗ

auke da buhu, cikin murna Huda tace "ga Ummana.."

Da kallon tausayi ya bi Umman nata kafin yai parking a ƙofar gidan nasu, dan Umman nata har ta shige ciki.

Sai da ya fara fitowa sannan ya bu

ɗ

ewa Huda itama ta fito, suka shiga ciki, tana gyara mazaunin hijabinta da ya yage,

Da sallama ta shiga gid

an, Umma ta fito daga

ɗ

aki, tana salati, tare da cewa "au Huda ni na

ɗ

auka kin fara yawon bariki ne?"

Sai kuma ragowar zancen ya maƙale mata a saman la

ɓɓ

a sbda ganin kujewar da tayi a fuskarta,

"Huda tukunna daga ina kika fito?"

"Umma wani yana yi

miki magana a waje wai zai shigo"

Huda ta katse zancen.

"Ce masa ya shigo Allah yasa samuwa mukayi"

Tana fita ta sameshi a jikin mota a jingine, yana latsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login