Showing 117001 words to 120000 words out of 163724 words

Chapter 40 - WATA_KISHIYA_COMPLETE

27 Aug 2026

67

ma kuwa ciki na d'a wallahi shika zubar, ai zubar cikinne yasata zubar wannan uban jinin...bincike ya nuna sex ne yasa cikin zubewa, da ace an

barshi koda be zauna a

mahaifa ba , zuwa nan da 2month ze koma ya zauna sosai inda akeso ya zauna din ba, amma tini ka girgizoshi waje..." Abdoljalal yace "Au yanzu cikin ya zube duka kake nufi doctor?'' Doctor yace "Ya zube mana dakai can bakaji me na

ke cewa bane? Kai ciki kawai ka fahimta a maganata, ai cikin ya zube tini..." Wani irin bakin ciki da kunci ya lullube zuciyar Abdoljalal be taba jin bacin ciki da dana sani ba irin na yau, shida yake neman d'a ido rufe amma shine yau Allah ya bashi kuma y

a zubar da kayansa kenan, seya dungume duka lefij ya daurashi a kn Almuqri'ah, ya hade rai tamkar an aiko masa da mutuwa yayinda bakin ciki ya kuma lulkube birnin zuciyarsa. Ya fara mgna a zafafe. "Wannan ai wulaknci ne, ai bata gayamin tanada ciki ba, sab

oda kiyayyata dake zuciyarta, inda tagayamin tanada cikina ai da bazan kusancetaba, kodan tana ganin ni ba Aurenta nayi ba,ai kaddaratace nida ita, kuma ai ko dan shegene ni inasan abuna, tinda ba uban wani ya danneta ya mata cikin ba, ai ciki nawa ne, ni

na fara saninta a matsayin y'a mace wallahi, doctor yarinyarnan ta tsaneni tin a kan cin dana mata na farko na fahimci tabi ta tsaneni ko ganinama batasan yi , dole taki jinina...wallahi se an biyani cikina daya zube..." Doctor mus'ab yayi shiru yana kall

an Abdoljalal shi kallan mahaukacima yake masa sbda magnganun nasa bana masu hankali bane, yaza ayi ace ka zubar da cikinka da knka kuma wai ka hau sirfafa matsifa sbda rashin hankali da rashin lissafi irin nasu na maza. "Gaskiya kaci kai..." Cewar dr. Abd

oljalal ya kara hasala yace " dole kace haka tinda ba cikinka bane... yarinyar nan ta renamin hnkli gabaki daya, kilama mgninsu na yan kauye tasha ta zubarmim da ciki, wallahi wallahi taci arziki daya na SO, da har karar mutum ina iya kaiwa, koma waye ya

bata maganin zubda cikin wlhi in kaishi kara ya biyani cikina, wulakncin bnza da hofi kawai..." Dr ya amshe da "Ko kuma kai a kaika kara ba, kaci yar mutane ka mata ciki baka Auretaba, kuma kana mgnr bnza, kaji mgnr bura uba kai,.." Abdoljalal ya taso masa

kai kace shi ya zubar masa da cikin jikin Almuqri'ah din. "Kai kake mgnr bnza da hofi, aikin bnza aikin hofi kawai, koda nacita ba Aure ai inasan cikin nawa dana mata ko? tinda da ubansa..." Doctor ya tashi a kn kujerar da yake haushin Abdoljalal dukya

rufeshi hkn yasahi tashi tsaye yace. "bakada hnkli,,,wai kayi abu kuma ka daurawa yarinya lefi, kasamu yar mutane kanata haike mata da bura,, yanzu kuma wai ka daura mata lefi, yanzu haka itama batasan ciki bane a jikinta kmr yadda kaima baka sani ba..." D

r ya tasoma Abdoljalal shima kmr ze rufeshi da duka. Abdoljalal yayi tsuki kawai shi a dole Almuqri'ah ce ta zubar masa da ciki, ya tashi ya fice a office din yanajin dr nacewa "Se Allah ya sakawa yar mutane, kanata zurmuqa mata abinda yafi karfinta kuma k

ana mata bura uba, se fadin bnza da hofi..." Shima duk ranshi ya bashi, dmn hk Abdoljalal yake shi murd'ad'en mutum ne sam beda dadin kai. Abdoljalal be sake bi ta kn dr ba Ya nufa dakin da aka kwantarda ita daman Ahamad ya bari a dakin, ya kalli Ahamad

din rai a baci yace"Kai bani car key..." Ya Karashe mgnr yana kallan inda take kwance jininsa da ake sa mata yana shiga hannunta a hnkli. Ahamad jiki na rawa ya mika

mata car key din ya amsa ya fice a asibitin, se bura ubar fadin rai yakeyi, zuciyarsa kmr

zata fashe dan takaici, ga jirima na neman kwasarshi, sbda jinin da aka diba a jikinsa, dr yace ya tsaya ya huta amma yaki. Abdoljalal direct ya nufa gidansa yayi wanka, ya chnza rigarsa data baci da jini, da knshi ya wanke motar data bata da jinin ma'ai

kata nata kallan abin mamaki. ya dawo asibitin da duk abubuwan dazasu bukata seda ya tsaya yase musu, kana ya dawo se faman fushi yakeyi har lokacin shi a dole an zubar masa da ciki abinda ya jima yana nema, yadawo ya zauna gefen bed din yacema ahamad k

ai jeka kawai..." Ahamad ya mike a guje ya bar dakin, ganin oga nata muzuran dabe taba ganin yanayinuba se yau. Abdoljalal kam haushin uban kowa yakeji, tunaninsa na kan cikinsa daya zube, se tunani yakeyi a ransa, waiko namiji ne ko macece. Zuciyarsa tafi

bashi macece danshi yafisan diya mace Macen ma kmr Almuqri'ah, sam baya tunanin mezeje ya dawo. da yayi tunanin se ranshi ya kuma sosuwa, hatta da haushin yarinyar seda ya kara lullubeshi shi gani yakeyi ba wani sex dinsa daya zubar da cikin kawaide yarin

ya ta zubar masa da ciki,, wani bakin ciki ya kuma rufesa har dare besa ko ruwa a bakinsa ba, sede ya danyi baccin awanni ya tashi. Bata farka ba se wuraren sha dayan dare, taga daurin karin jini a hannunta hnklinta ya dan tashi, sbda ba a taba mata karin

jinin ba, amma se ta tuna da jinin data zubar. Abdoljalal ya mata sannu,ta kalli fuskarshi nan take taga wani irin yanayi da bata saba gani ba a tattare dashi, duk yabi ya hade rai ciki kunci, ko kallanta yakiyi, itama ta dauke knta a knshi, tana mejin

mararta sakayau yau hatta da ciwon ma tadenaji, , da uban nauyin da mararta takeji ynzu bataji. sede kawai tana dan ganin jiri kadan kadan, dr mus'ab yazo ya dubata tabishi da ido sosai, tana mejin kmr ta tambayeshi wani abu sede ba damar hakan. Dubata y

ayi sosai ya mata allurori, yayinda jinin dake shiga jikinta ko rabi beyi na, ya mata sannu ta amsa da "Yawwah, nagode Allah yasa Aljannarh ce makomarka..." Ta fadi da bebanci, Abdoljalal da dr duk suka kalleta, duk sun fahimci me take nufi dukda da bebanc

i tayi mgnr. Dr mus'ab shi yasan dalilin yin Adduarh tata,. Ya mata Allurori ya kula yarinyar nada dauriya, domin data farka bata nuna raganvci ba dukda bakar whlr datasha. Dr ya kara mata sannu ko kallan Jalalu beyi ba sbda haushi yake basa yanzu seya

dinga abu kmr wani karamin yaro, kai kace wanda be mallaki hankalin knsa bane shi, gabaki daya halinsa ya chnza so yakeyi ya koma mara lissafin karfi da yaji, ko jaririn yaro yakeso ya koma dr besani ba.

"Zakici abinci?'' Ya tambayeta yana wani kara h

ade rai kmr ze mutu.. Kwata-kwata Almuqri'ah daman batajin yunwa sam, dan haka ta kalleshi kawai ba tare data bashi amsa ba ta dauke knta, ta juya knta dayan gefen. "Nace zakici wani abin? Ya kuma tambayarta gatsal, murya cikeda zallar bala'i, shi a dole a

nd zubar masa da ciki. Almuqri'ah tasake masa bnza, ya kara tambaya a karo na uku "Ke bada ke nake mgna na..." Ya fadi cikin fushi. Almuqri'ah ta juyo ta kalleshi duk yabi ya rikirkice da bala'i. "Banjin yunwa..." Ta bashi amsa a

taikaice da bebanci. Ya ka

ra hade rai, zuciya fal haushi. Washe gari ya kasa hkri, da sassafe tana tashi a bacci shi ko baccin dmn beyi ba, ya hau matsifa.."dan wulaknci ashe kinsan kinada ciki har kika zubarmin da abuna, ni bnsani ba, kawai dan wulakanci, ai ni dakin barmin abuna

, se in biyaki kudin renon cikina ki adanamin abina in kika haihu ki bani, kayana,ai bnsan kiyayyar da kikemin ya kai haka ba,, ashe haka kika tsaneni kmr ki kasheni, wannan ma ai zaki iya kasheni tinda kin kashemin jinina..." Almuqri'ah tayi shiru tana na

zarin klmnsa ita sam bata fahimceshi ba, har ya gama haushnsa sam bata gane me yake nufi ba, zuwa can kuma tace "Wani cikin?'' Da babanci.a hasale Abdoljalal yace "bansani ba, cikina mna da kika zubar, cikina na jikinki da kika zubarmin da kayana dan tsab

ar wulaknci dacin mutumci...." Har yanzu de Almuqri'ah bata fahimceshi ba, tayi shiru kawai,ta zubawa sarautar Allah ido. Dr mus'ab ya shigo ya sameshi yanata sababi, bebi ta knshi ba ya duba Almuqri'ah , yaga jinin dake jikinta yayi rabi, ya zauna ya mata

bayanin ciki ne da ita amma ya bare. Seda dr ya mata bayanin ta fahimci dalilin matsifar Abdoljalal, watoma sharri ze mata ya zubar da cikinsa da knsa, yace itace dan itade tasan batasha komi ba, tinda ya sadu da ita ya sauka dasafennan bata kara gane k

ntaba. Dr ya fice a dakin byn ya gama dubata, ya bata magunguna ya cire mata jinin yace ma Abdoljalal ya bata abinci shine kawai mgnr data hadashi da Abdoljalal, wanda keta faman kumbure kumber. Brush ya taimaka mata tayi, itama haushinda takeji dande ba

ta da yadda zatayi ne dole sede dan tayi take iya tafiya, sbda jirin datake dan gani..., ya bata abinci taci kadan sbda bakinta ba ddh, se kumbura yakeyi shikam yana niyar fashewa. Kwanansu goma a asibitin dr ya sallamesu, duk kwanakin dasukayi a asibitin

yana bata kulawa sosai, ammfa be bar kumbure kumbure ba, dan daya kalleta se haushi ya rufesa shi a dole ita ta barar masa da ciki. Sam Almuqri'ah taki bi ta knsa sbda dr yace mata ta kyaleshi da kanshi ze gane kuransa tinda ba a kan gaskiya yaketa bambam

in tsiyar ba...duk rashin cikin da yyne yaketa wannan haukan, abinka daba sabam ba.... (sadda Abdoljalal benan ne a asibitin yaje gida ya dawo, dr ya samu dmr gaya mata wannan mgnr).

Paid book ne 08101626484

29

Adamawa yola.

Cikin

temakon mahaliccin sammai da kasai, ubangijin da ba'a dogaro dashi a tabe, sede a fuskanci jarabawa, kuma Allah baya jarabtar wanda ba mumini ba, domin gwajin karfin imanin

bayinsa mumina. Hajiya salma tasamu saukin jikinta sosai, sede fa akwai ciwon da ba

ze warke ba a zuciyarta wannan sede mahalicci inya yanke mata shi, Shine soyayyar danta da tsananin kwad'ayin san ganinsa.

A kwanakinnan mafarkinta a kan abdoljalal ya chanza, ada ganinsa takeyi a cikin wani irin duhu wasu muggan mutane na janshi, amm

a a halin yanzu, gabaki daya mafarkanta sun juye ganinsa takeyi a wani irin haske, wanda rabinshi haske ne rabinshi duhu ne, se tadinga ganin shi Abdoljalal din na tinkaro hasken duhun kuma yana tunkararsa, a kullum cikin sadaka take., yau kawai seta tashi

da kwad'ayin san ganin d'anta ko zata samu sassaucin zuciyarta ita koda ganinsa ne tayi ko me ze mata kawai tanaso taga d'anta a yau, koda ze zageta ta uwa ta uba, daman tin tini takeson zuwa inda yake ta ganshi me martaba ke hana shike tausar mata zuci

ya. Bayan tayi asubahi yau ko laziminta data sabayi a kullum batayi ba, ko wanka batayi ba, tasa jallabiya baka, ta fito compound din gidan, tasa dreva dinta ya kawo mota inda take, sauri-sauri takeyi gudun kada me martaba dayaje masallaci ya dawo ya samet

a, sbda yana samunta ze dakatar da ita daga zuwa taje taga danta ita kuma tana tsananin bktr hkn, jiya ma kusan kira goma ta masa wayoyinsa kashe, a kullum seta kirashi koya shiga baya dauka, gabaki daya Saude ta rabasu bawai rabuwar wasa ba, ko lambar mah

aifiyarsa bayaso yagani a saman screen din wayarsa. Dreva ya kawo motarta inda take, ya bude mata gidan baya ta shiga ya mayar ya rufe yana me mamakin ina kuma Sarauniya zataje da asubarnan. Dreva din ya shiga mazaunin dreva ya juyo ya kalleta fuskarsa da

ukeda karin bayanin ina zasuje..."muje abuja..." Dreva ya zaro ido yace "Abuja kuma a mota hajjaju?'' Sbda ko taraba basa zuwa a mota Sede a jirgi tanada jirgi mallakinta ne dashi suke zuwa inda zasuje da dreva din tukin jirgin nata. Hajiya ummu salma tayi

shiru tana naxari, bawai nazarin maganganun Dreva dinta ba, aah nazarin cikin abuja da kaduna a ina zata samu Abdoljalal dinta. "Muje kaduna kawai..." Zuciyarta ta bata hakan Kuma ta furta hkn..dreva yace "ranki ya dade Allah yaja zamaninki matar sarki u

war jalalu saraki, gimbiya yar hajiya jikar hajiya,, gimbiya ai baze yuba muje kaduna a mota ranki ya dade sede a shirya miki jirgi gimbiya matar me martaba, Allah ya kara lafiya..." Ya fadi cikin ladabi. Hajiya salma tace "No muje a motarma is okay ai kas

an gidan d'ana jalalu a kaduna kou?" Se tambayar tata tabawa hassan Dreva tausayi, kaf ma'aikatan gidan sun san halin da take ciki. "Nasani ranki ya dade..." Ya bata amsa cikin ladabi hadi da tausayawa. Hajiya salma ta sauke ajiyar zuciya tana mejin san

danta na kara taso mata tace "Nan zaka kaini..maza ka tada mota mu tafi..." Ba musu hassan dreva ya tada motar, domin dolensa ne yabi umarni. Dai-dai sun iso get din gidan na farko Me martaba yafito daga masallacin dake cikin gidan ganin za a fita da mota

r Hajiya salma kuma yasan ba a fita da motar dole sede in hajiya salmar ce zata fita a cikinta,. Hk kawai ya tsinci knsa da karasowa bakin get din ya hana masu gadi bude get din gidan, hajiya salma ta kalli glass din

motar taga me martaba ne, taji sam bata

ji ddh ba. Tayi kasa da glass din , ya zubo mata ido, itama idan ta zuba masa, kallan mamakin ina zataje da Asubahinnan me martaba yabita dashi."pls ka bari inje inga d'ana koda na yaune pls..." Hajiya salma ta fadi hadi da marairaicewa. Me martana yayi ji

m, daman yasan wannan dalilin ne kadai ze fiddata daga gida a wannan lokacin."tafiya kuma ba sallahma gimbiyata, sakko dan Allah..." Ya fadi cikin kwantar da murya. Ta bude baki zatayi mgna yace "Bakiyimin musu ki sakko kawai..." Ba tare data masa musu ba

ta bude murfin motar ta fito zuciyarta sam ba dadih, me martaba ya tasata gaba zuwa falonta, tana Shiga falon nata ta nufa inda photon Abdoljalal yake, ta dauko hoton dake jikin bango ta rungume a jikinta, nan da nan seta fashe da kuka me martaba na tsaye

jikin bangon falon yana kallanta, shi kadai yasan irin damuwar da yake ciki amma yasan ta fishi damuwa a kan d'ansu. "Ki dinga sawa kanki dangana dan Allah Ummusalma..." Me martaba ya fadi da sanyin murya, hadi da nufar inda take tsaye tana rikeda photo

n Abdoljalal tana kallo tana kuka. Ya amshe photon Abdoljalal dake hannunta, ya ajiyeshi hannun kujera, ya jawota jikinsa tana shashekar kuka, yashiga mata natsihohi,...da kyar yasamu ta samu nutsuwa a nan bacci yayi awan gaba da ita mara dadih, me martab

a ya dauketa ya kaita bedroom dinsa, ya lullubeta kana ya dawo falon da knsa ya tattare kaf pictures din Abdoljalal dake bangaren nata duka sbda ya fuskanci in tana ganin photonsa hankalinta kara tashi yakeyi, ya zauna a falansa kawai ya dauki wayarsa yayi

dealing number din Alhaji Isma'il shine wazirinsa kuma babban amininsa, hausawa sunce abokin kuka shi ake gayawa mutuwa. ., bugu daya Alhaji isma'il ya dauki wayar, me martaba yace "Inasan ganin ka yanzu isma'il..." Yana fadae hkn ya katse wayar hadi da

shiga tunannika, damuwar Hajiya salma tana kada masa hankali babban abin damuwar tasa kuma gashi bata da cikakkiyar lafiya, duk lamarinsa ya maidashi kaddara, yanada kudade amma sam beda farin ciki. Ba jimawa isma'il ya iso falon nasa me martaba ya masa i

so, ya karaso Ya miko gaisuwa game martaba ya amsa ya masa izinin zama a kn kujera yana zama me martaba yayi gyaran murya hadi da fara magana. "Waziri na rasa ya zanyi da salma a kan yarannan,..." Ya kwashe komi ya fadu a yau din ya gayawa isma'il kana ya

daura dacewa " wallahi damuwar ta kaini kwano ina tunanin kawai zan nemi Abdoljalal in rokeshi ya dinga zuwa yana ganinta kodan lafiyarta, banasan wani abu ya sameta kwata-kwata..." Ya karashe maganar cikin damuwa. Alhaji Isma'i ma fuskarsa dauke takeda du

mbin damuwa daman tinda ya kirashi yasan tasuniyar gizo bazata wuce ta koki ba. Cikin ladabi Alhaji isma'il ya fara magana "aah me martaba, ai a halin yanzu ko an nemeshi duk hanyar bame billewa bace, sbda bayin knsa bane, adduarh de damuka saba ita zamu C

igaba,, insha Allahu komi me wucewa ne....ita kuma gimbiya abin fa dole se an hada da amso mata adduarh, ranka ya dade dole abin da ciwo d'annan fa daya tilo gareta, wallahi tayi ma try Sosai.." Me martaba yace "Hakane Waziri...Toh shikenan Allah ya datar

damu Amma ni ina ganin kawai kaddaratace haifar Saraki, gani nakeyi kamar a haka ze mutu

bashi ba d'a bashi da jika, ga damuwarsa dake cikin zuciyoyinmu musammanma mahaifiyarsa, wallahi ina tsoron ta mutu ta sanadin bakin cikinsa, ina jiye masa duniyarnan

..." Alhaji isma'il ya amshe da "Ai ba lefinsa bane ranka ya dade,,,, Adduarh de kmr yadda mukeyi a fari ita zamu ci gaba dayi, insha Allahu zansa malam muhammadu ya mata rubutu a kawo mata yau,,Allah ya temakeka insha Allahu aski yazo gaban goshi, yafi

zafi dole se an jure, Allah yaja kwananka sarki jikan sarki...." Me martaba ya girgiza kai kawai, gani yakeyi kamar har abadan hankalin Abdoljalal baze dawo garesu ba. Alhaji isma'il ya dinga tausar Me martaba hadi da dannar zuciyarsa a kan damuwarsa,,me

martaba yana tsananin kaunar waziri Isma'il, wazirinsa ne kuma majibancin lamuransa ne, da zuciya daya yake bashi shawarwari a kan damuwar dake Addabar me nmrtaba shida iyalinsa, wato damuwar Abdoljalal,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login