Showing 156001 words to 159000 words out of 163724 words

Chapter 53 - WATA_KISHIYA_COMPLETE

27 Aug 2026

82

wani ya dauki nauyin nema mata lafiya a kasar wajen sbda su basu da komi, kuma su ba yan nig

eria bane su yan sudan be.(tade boye musu Ainifin dalilin zuwanta gidan Abdoljalal tade bayyana musu abinds ze bayyanu sauran ta barwa ranta.) Me martaba da salma duk suka karajin tausanta sosai. "Ki zauna damu pls har Allah yayi ikonsa, kakarki ta dawo Ni

geria se itama tadawo nan gidan da zama, harde ubangiji yasa ki koma gidan mijinki knji..." Cewar salma. Ba musu Almuqri'ah tace "Toh...ngde Allah ya biya da Alkhairi ." duk suka amsa da Amin, komi tace suna fahimta dukda da bebanci take magana. Hk kawai

Almuqri'ah taji ta aminta dasu 100% kuma tana kaunarsu 100%.. "Wani suna za asawa yaran naki?'' Me martana ya tambayi Almuqri'ah ganib time nata tafiya bawa yaran wuduba da sunansu ba... Almuqri'ah ta rasa mezatace kawai seta tsinci kanta dacewa "Asa ma m

acen sunan mamana,(shine sunan data bawa salma mamanta take ce mata...) Mazan kuma asa musu sunan daya dace kawai..." Ta fadi da bebanci. Me martaba da salma sukaji dadin karamcin da yarinyar ta musu, ba bata lokaci me martaba yama yarinyar huduba da suna

n salma, mazan daya yasa sunansa, se daya yasa sunan abdoljalal, dayan kuma yasa sunan isma'il wato yarimansa. Seda ya gama musu hudubar kana ya shaidawa salma sunan dayawa yaran, taji ddh sosai kaf kowa yaji dadin hakan musamman Almuqri'ah dataji ansa su

nan Abdoljalal kuma yace sunan dansu ne, ita kuma sunan masoyinta ne wanda ya iya cin gindinta. Almuqri'ah taga ikon Allah sosai , ga sunan dansu da sunan mijinta duk daya, haka kawai itama taji tanaso taga d'an nasu. Byn kwana hudu aka shirya bikin suna

na gani na fadi, kowanni yaro aka yanka mishi sah, wato sah hudu aka yanka ma yaran.ansha hidima ywar jego tasha sutura ta arziki, dan akwati dozin biyu tama mejegon me martaba yamata dozin biyar, sukam jariran ai dozinan kayayyakin da aka musu baze misalt

uba. Anci ansha a suna an raba kayayyaki na Alfarma, harda kudi aka raba na fitar hankali dukde abinda Allah ya ciyar dakai a sunan shi zaka samu.

Paid book ne. Allah yasa mu gama lafiya.

42

Ammah tasamu sauki sosai, dan haka suka tattaro suk

a dawo kasar nigeria, Dr mus'ab ya siyama Ammah gida ta zauna cikin aminci se godiya take masa mara iyaka, nurse mami takoma ga yaranta domin bata da miji tini ya jima da rasuwa, . har gidan mami Ammah tasa dr mus'ab ya kaita ta mata godiya mara iyaka, ha

rda kuka, a zamaninnan ammah bata tunanin za a samu mutane irin Dr mus'ab da nurse mami. Dr yayima mami goma sha tara na dumbin Arziki arziki. Satinsu daya da dawowa kasar Ammah taji dadin jikinta sosai, tanata ci gaba dashan sauran magungunan da likitoci

suka daurata a kai, a halin yanzu jikarta Almuqri'ah kawai takeson gani, tanasan taga a wani hali take ciku zuwa yanzu. Dan haka ta fara tambayar Dr kan yaushe Almuqri'ah zatazo, ko ita zataje ta ganta... Dr ya fuskanci tana da bktr ganinta sosai, dan hak

a yace zeyi kokarin hakan. Tinda ya dawo kasar beje gidansu ba, shima yanada bktr san ganin Almuqri'ah da Abdoljalal, dan haka ya shirya yau after la'asar ya nufa gidan Abdoljalal,. Tin daga bakin get mus'ab yaga gidan ya chanza masa sosai, securities duk

sun chanza masa, dabadan Ahamad dake bakin get din ba, da sam Dr mus'ab baze samu shiga gidan ba, sbda su securities din dake aikin ynzu basu sanshi ba. Yanayin packing Ahamad yazo ya bude masa, murfin motar ya fito ya zubawa Ahamad din ido nan take yaga d

uk yayi wani zyru-zuru, to duk hankali ba kwance ba, abinci wannan ma se yayi da gaske yake ci, hakan yake ga gogan shi san yadena cin abinci ma sede ruwa kadai dr ke zuwa yana kara masa, shima ruwan se yaga ze mutu ake kara masa shi, duk yabi ya fice a ha

yyacinsa wanda ya sanshi ada inya ganshi yanzu se yayi da gaske yake iya ganeshi. Saude kam ai tinima ita wannan ta dena ci itama tadena sha se aikin yawan bin malamai kawai takeyi, dukda malaminta ya tabbatar mata da Almuqri'ah ta mutu ita da cikin jik

knta amma bata hakura ba se bin wasu malaman takeyi saboda hankalin mijinta yaki dawowa gareta, tini duk tabi ta sabe tayi wata uwar ramar daba kowa itama yake ganeta ba, sbda mulkin datakeyi yanzu sam bata isa tayishi ba, asirin takeyi amma sam gani ma

takeyi asirin baya Aiki,Hajiya Abulle ta dawo da ita suke yawon bin bokayen amma sam ba nasara Saude tazama kmr zautacciya, ta nemi lambar kande domin taci ubanta amma shiru lamba bata shiga, kaf maaikatan gidan mata da maza banda securities duktasa an mus

u duka jina jina, ta musu cin mutumci na fitar lissafi, kana ta koresu a gidan har jimmalo, gida de ya koma daga saude seme dafa mata Abinci, to yanzu bata ma da kwanciyar hankalin dazata ci abincin dan haka ba abincinma take ci ba, aikin me dafa abinci y

akoma gyaran gidanta kawai. "Ahamad meke faruwa ne duk kabi ka zabge kayi duhu? Gidanma dukya chanza min.." Cewar dr mus'ab da yy mgnr cikin dmwa yayinda jikinsa ke bashi babu lafiya. Ahamad ya fara hawaye, hkn ya kara tadawa dr hankali. "Meke faeuwa? Da

n Allah ka gayamin..." Ahamad ya fara mgna yana kwallah "Ranka ya dade duk mun nemi numbers dinka shiru..." Dr yace "Wlhi bana kasar ne, Dana bar kasar duk se nasa wayoyina a yadda ni zan iya kiranka kawai...kuma na kira Abdoljalal lokuta da dama a kashe

ka gayamin meke faruwa, jikina na bani akwai babbar matsala, ka gayamin meke faruwa dan Allah?..." Nan ahamad ya kwashe labarin komi dake gudana ya gayawa dr mus'ab kama daga kama Abdoljalal A kan Almuqri'ah da saude tayi har zuwa gudun Almuqri'ah a gid

an, har de zuwa yanzu da halin da Abdoljalal yake ciki. Ahamad yaji kansa ya tsananin sara masa jin Ahamad yace masa wai Almuqri'ah ta gudu , seda dr ya koma ya jingina bayansa da bayan motarsa nan take yaji jiri na neman kwasarsa

"Innalillahi wa'inna il

aihirraju'un!'' Itace kalmar data fito daga bakin dr, nan take idanuwamsa suka shiga kokarin daukewa daga gani na wasu yan dakiku. "Ina ta shiga?'' Cewar Dr da yayi mgnr fuska da murya dauke da zallar tashin hankali. "Bamu sani ba, an kai cigiya kaf gidaje

n TV da gidajen redio duk bamu samu tadawo ba, duk inda nake inada tabbacin yanzu ta haihu gaskiya,,, wlhi Oga na cikin tsananin dmwa muje kaga halin da yaje ciki..." Cewar Ahamad. Ba bata lokaci dr yabi ahamad a baya zuwa dakin Almuqri'ah inda nan Abdolja

lal ya koma rayuwa tinda ta bar gidan be leka ko kofar dakinsa ba, yazama kmr mahaukaci. dr nashigowa dakin idanuwansa suka sauka a kan Abdoljalal dake kwance kasan tiles din dakin duk yabi yayi karo-karo dashi se kasusuwa kawai a jikinsa, yayi bala'in bak

i, tako ina jikinsa gashine buzu buzu. Tsabar tsananin tausansa ya rufe dr nan da nan se hawaye ya fara zirya a kan kuncinsa, "mutum ba komi bane..." Dr ya fadi a bayyabe ganin yadda jalalu dan gayu kyakyawa ya koma bashi da maraba da kwarangwal. Abdolja

lal na ganin dr ya taso a hnkli yana me binsa da ido kmr mahaukaci yace "Kaganta? Kaga yarinyar nan? Ta gudunmin da ciki wlhi... Kace tadawomin da cikina.." Dr ya karajin tausansa ya rufesa, seda ya mike tsaye ya kula da kayan Almuqri'ah dinne a jikinsa, t

inda ta bar gidan kayanta yake sawa kullum sune suturarsa, duk yabi ya gigice ya koma mahaukacin karfi da yaji. "Why Abdoljalal....innalillahi wa'inna ilaihi!'' Cewar dr daya kara fashewa da kuka ya rungume Abdoljalal yana fadin "Kaine haka jalalu? Kaine a

nya jalaluna ne kuwa..innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!' Dr ya dinga kuka tamkar ransa ze fita, tabbas ya tabbatar da mahaukacin so Abdoljalal keyima Almuqri'ah, gabaki daya dr ya rikice ya gigice, shima yashiga tashin hankali,,, yana rungume da Abdolja

lal harna tsawon 10mnt yana kuka Abdoljalal dinma na kuka ahamad dake gefe shima yana kuka tamkar ransa ze fice daga jikinsa. Kana ya dago Abdoljalal daga jikinsa suka karasa bakin bed suka zauna, ahamad ya danne tashin hankalinsa ya shigama Abdoljalal na

tsiha kan ya dannewa ransa ya dauki kaddara, ya karashe da tausar masa zuciya kan za'aga Almuqri'ah din, Abdoljalal yajishi ne kawai amma ina be dauki natsiharsa ba ko kadan. Da kyar dr ya iya barin gidan karfe sha biyu na dare byn ya lallaba Abdoljalal y

aci abinci da kyar. Da dr ya koma gidansa rnr sam beyi bacci ba, kwana yayi tsaye cikin tashin hankalin , Allah-Allah yadingayi gari ya waye. Yanayin asubahi ya hau motarsa ya nufa gidan malam nata'alah . tashin hankali, yana isa gidan yaga babu gidan bab

u dalilinsa kmr an shafe gidan se fili kawai ba gida. hnkalin dr ya kuma ninkuwa gun tashi, nan take ya tuna da wata kalma da malam ya taba gaya masa dajimawa, yace masa " akwai lokacin dazeso komi ze rincabe, to a lokacin ne ni bazaka ganni ba har abadan.

.." A lokacin dr besha da gaske bane yasha kawai ya fadi ne, ko yace be fahimci mgnrsa ba se yanzu ya fahimci kanun zancan nasa. Tashin hnklin dr ya ninku ji yakeyi kmr zeyi hauka, ya dinga zagaye turun wada ko zega malam amma ina begansa ba sbda shidin ba

mutum bane aljani ne, daman danya temaki Almuqri'ah ya bayyana, yanzu kuma temako ya kare tinda ta dangana da inda ya dace ta dangana. Se dare dr ya dawo gida cikin tashin hnkli yayi tagumi kawai ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji ddh, yakira Isma'il ya sana

r dashi abinda ke faruwa. Hankalin isma'il dake kasa me tsarki ya tashi ainun, kusan 2month yayi a kasa me tsarki yanata ibada da Addu'ur'i kan Allah ya warwarewa me martaba da iyalinsa damuwarsa, Allah yasa Abdoljalal dansu ya dawo garesu. Dr na gaya mas

a wannan kaddarar data kuma kunno musu kai ya shiga dakin kabah yaci gaba da Addu'ur'i ga ubangijin da baya bacci, a kaf addu'ur'insa seyace Allah ya tarwatsa saude. Me martaba mutum be garesa, yana jibantarsa fin tunanin me tunani, in yace masa yana cikin

damuwa to tabbas seya hau yafishi shiga damuwa me tsanani,, yana tausayawa ga kowa dake kasanshi, shiyasa waziri ke tsananin tausayawa garesa, rayuwa nan da waziri keyi da kodar me martaba daya yake rayuwa,, yayi ciwo me tsanani har kodarsa ta lalace aka

cireta me martaba ya bashi tasa.. Ba duk d'a ze iya wannan shahadarba musammanma a matsayinsa na shugaba me mulki kuma shahararren me kudi. Dr ya kira mami ya sanar da ita halin da ake ciki , itama tashiga tsananin tashin hankali. IIsma'ildr mus'ab mami

duk suka shiga tashin hankali mara misaltuwa,tako ina aka saka cigiyar neman Almuqri'ah sannan duka dukufa adduarh, duk abubuwannan dake wakana Ammah bata sani ba, sam ba a bari taji komi ba, sbda gudun tashin hankalinta. Dmwar da dr ya shiga tafi ta kowa

ji yakeyi kmr zeyi hauka, zuwa yanzu ko miyaun bakinsa da kyar yake iya hadewa.

Yau tinda Ya tashi yaketa bincike a dakin tako ina, besan dalilin bincikenba, yana binciken yaga kudinnan da dr ya bashi yabawa Almuqri'ah a drower ya dauko kudin ya r

ungume a kirjinsa yana hawaye hadi da tunano reaction dinta data amshi kudin. "Meyasa zaki tafi ki barni a matsifa irin wannan...ya rabbih menayi kayimin wannan jarabawar... Ina sanki wlhi, ya Allah kasa ba hakkin iyayena bane yake bibiyata..." Ya karash

e yana me kara fashewa da kuka kmr ransa ze fita harda shasheka, a kwanakinnan ya fara tunanin anya ba hakkin iyayensa bane ke bibiyarsa yasa yashiga wannan mummunan halin, yanzu fa beda maraba da mahaukaci, dan duk wanda ze kallesa zesha ko mahaukaci ne.

Hannu ya kai ya jawo drower din kasa , se kuma yaga wata takka fara a ciki harda baze dauki takaddarba se kuma yasa hannu ya dauka hannun nasa na rawa, ya bude takaddar yaga rubutu da blue din viro.. "Rubutun dr..." Ya fadi a bayyane ba tare daya karanta

note din dake cikin takaddar ba. Yabi rubutun da ido ko a mafarki aka nuna masa hand writing din dr zesan cewa hand writing dinsa ne. Jikinsa na kakkarwa ya fara karanto note din kamar haka. "Ina fatan kina lafiya Almuqri'ah, wannan kudin naki ne nasan zak

isan kona menene dakinga kudin,, ina fatan zaki tsaya ki nutsu kiyi aikin daya kawoki gidan Abdoljalal cikin Aminci...kakarki tana nan cikin aminci itama, Allah ya bada sa'arh ya dauramu a kan saarh Amin ya Allah..." Abdoljalal yaci gaba dabin rubutun da

kallo yayinda zuciyarsa je tsuma, ya kasa fahimtar me rubutun ke nufi, tabbas de yasan rubutun dr ne, ,abu daya ya fahinta wato aikin da Almuqri'ah tazoyi gidan kenan dasa hannun dr.."to meyasa zeyimin haka?'' Cewar abdoljalal, nan take zuciyarsa ta chanza

lamarirrika, ya mike a zabure yana fadin. "Munafukinka na gindinka..." Ya fice a dakin kafafuwanta ko takalmi babu, sanye yake da jallabiyar maroon ta Almuqri'ah Abdoljalal dinne yase mata.. Ahamad dake zaune bakin get yaga Abdoljalal ya tunkarosa gadan g

adan seya shiga mamakn lafiya, ya mike tsaye zumbur, ya zubowa Abdoljalal ido, yau kusan 2weeks kenan ko masallaci Abdoljalal din be fito yaje ba, a daki yakeyin sallah. "Akwai matsala..." Ahamad ya fadi yayinda zuciyarsa ke dukan uku uku. "Dakko mota da h

anzari kajani zuwa office din dr mus'ab..." Cewar Abdoljalal da takaddar ke hannunsa yanata kara karantawa. Ba tare da ahamad ya masa musu ba, sbda yadda yy mgnr ya tabbatarwa da ahamad wani bala'in ya kunno kai.ya nufa packing space kusan a tarema suka k

araso packing space din abdoljalal yashiga gaban motar, ahamad yaja motar suka fice a gidan yana kallan rigar dake jikin Abdoljalal be dace ya fita da ita ba amma beda yadda zeyi, be isa yace masa ya koma ya cire ba.

Paid book ne 08101626484

43

"Kai kayi maza maza kayi sauri da motar nan fa..." Cewar Abdoljalal, dayake ganin kmr ahamad baya sauri, shi kuma dukya kagu ya ganshi gashi ga dr mus'ab, kwata kwata beyi tsammanin abinda dr ya aikata garesa ze aikata din ba, ashe maciyinn amana yake tar

e dashi be sani ba.sune kalaman da Abdoljalal keta juyawa a cikin kansa yayinda yakejin zuciyarsa kmr zata fashe. Ahamad ya kara gudun motar sbda mgnr da Abdoljalal yayi. Tafiyar 15mnt ta kaisu office din dr, ko packing ahamad be gama yi ba Abdoljalal ya f

ito daga motar cikin sassarfa ya nufa cikin asibitin yayinda yazama abin kallo sbda rigar jikinsa, wasu suka hau kakkauce masa saboda a zatonsu mahaukaci ne. Direct office din dr mus'ab abdoljalal ya shiga, yaga baya office din. Dan hk ya fito yaga wata n

urse ya tambayeta ina dr?, a tsorace ta bashi amsa da "Beso ba yau..." Tayi hanzarin barin gun sbda itama a zatonta mahaukaci ne. Abdoljalal ya fice a asibitin ya koma mota ya kalli ahamad yace "muje gidansa..." Ahamad ya tada motar hadi da tambayar Abdolj

alal "Meke faruwa ne ranka ya dade.." Abdoljalal yayi banza dashi kmr beji shi ba sam ko mgna ma bayaso yayi sbda azabar turiri da tashin hankalin dake cikin zuciyarsa. Ahamad be kara cewa komi ba yaja motar suka fice a asibitin zuwa gidan Dr mus'ab. Ba j

imawa suka isa sbda gidan da asibitin ba nisa. Ahamad nayin packing abdoljalal ya fito , direct ya nufa part din dr mus'ab zuciyarsa a zafafe. Bako sallama ya fada falon Dr din, ya taddashi zaune kan kujerarsa ta 3ct ya rafka uban tagumi yau ko office be f

ita ba, ya hana kuwa zuwa part dinsa sbda dmwar da yake ciki. Kwatsam yaga jalalu ya fado falon nasa, ya dago ya zuba masa ido,cikin zallar mamaki, yaga yanayin dabe saba ganinsa a ciki ba a kan fuskarsa, kallon bnza kawai yake binsa dashi da kallan kaskan

ci. "Maciyin amana kawai.." Jalalu ya fadi hadi da karaso ya cukumo wuyan dr mus'ab ya dago takaddar dake hannunsa ya nunawa dr din,dr ya kalli takaddar, nan take ya tuna da Sadda ya rubutata da hannunsa yasata a tsakiyar sadakin Almuqri'ah. "Asirinka ya t

onu maciyin amana kawai,,ace dakai za a hada baki anaso a cuceni ..mugu azzalumi,seda na fara zafafa a soyayyar yarinyar kuma seku hada baki kasata ta gudun min da ciki...wallahi ka gaya mata ta dawomin da cikina ko yau -yau dinnan insa a rufeka,, mugu azz

alumi ni na daukeka da zuciya daya ashe kai ba hakan bane azzalumi mugu makiri, aniyarka ta sharri seta bika, nayi nadamar saninka a rayuwata, wlhi da zuciya data nake zaune dakai ashe kai akasin hakan ne..." Ya karashe mgnrsa hadi da fashewa da kukan ta

kaici da zallar bakin ciki, wato besan da makiyinsa yake zaune ba se yau. Dr mus'ab ya bishi da ido cikin zallar dmwa da tashin hankali, yadda abdoljalal ke jefo masa kalamannan cin amana ba karamin dmwa ya jefa dr a ciki ba amma sede yamasa uzuri sbda ras

hin sani ne ke dawainiya dashi wanda yafi dare duhu. "Maciyin amana, Azzalumi insha Allahu se ubangiji yayi kaca-kaca da rayuwarka, kuma wlhi wlhi in baka fito min da yarinyarnan ba, kun bani ciki na ba, wlhi se nayi sharaarh dakai in zanyi yawo tsirara s

ena wulakantaka mugu azzalumi kawai..." Abdoljalal ya fadi still yana kukan bakin ciki. dr ya bude baki domin yama jalalu bayani amma yaki bashi daman hakan gashi ya shakure masa wuya sosai, yana kokarin ya kwace amma sam ya gaza sbda karfinma ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login