Showing 150001 words to 153000 words out of 163724 words

Chapter 51 - WATA_KISHIYA_COMPLETE

27 Aug 2026

110

zama daya, ki daure ki bamu labarinku..." Ammah taja ajiyar zuciya hadi dayin jim tace "Hakane....mu cikakkun haifaffun yan sudan ne, iyayenmu da kakanninmu duk yan sudan ne," se kuma Ammah tayi shiru. dr mus'ab ya

amshe da "yawwah Almuqri'ah ta sanar damu haka nida nurse tace mana ku yan sudan be, sede bamusan ya akayi kukazo nigeria ba bata sanar damu haka ba, sannan haka aka haifa Almuqri'ah da bebanci?'' Ammah ta daga masa kai alamar eh hadi daci gaba da basu

labari "Mahaifanmu ,mu uku suka haifa a duniya, nice babba, se kanwata Fad'ima, se kanina Aliyu haidar,,, kuna fahimtar hausana sosai kou?'' Ammah ta dakata da lbrin da tambayarsu sbda hausarta kwata-kwata bata fita yadda su suke hausa. Dr mus'ab da mam

i suka amsa da A,,," a lokaci guda.. Ammah tayi ajiyar zuciya kana taci gaba da labari. "Mu uku iyayenmu suka haifa suka rasu, tin muna kanana, suka barni da kanne na, ni na rikesu, kasancewar iyayenmu nada tsananin arziki sam bamu nemi komi mun rasa ba,

munyi karatun Arabiq dana boko. Kana nazo nayi Auri wani balarabe dan makka, na haifi d'ana miji mesuna khalid, daganan ban kara haihuwa ba, har d'ana yayi 8yrs, kana kanwata tayi Aure , haihuwar farko ta haifa diya mace Ummukhaltum, gun haihuwar ummukha

ltum yar uwata ta rasu, ya kasance ni na rike ummukhaltum,bamu da kowa kaf kakanni da iyaye duk dun rasu. Da ummukhaltum ta girma na hadasu aure da khalid wanda ya tashi da kwazon neman na kanshi, yayi arziki na fitar hankali,, kanina haydar ya zamana shi

karatun da yayi ya tashi a banza ya fad'a halakar shaye-shaye, duk sati seya cemin beda kudi na bashi, to dayazo yaga d'ana Allah ya dagashi yayi kudi na fitar hankali, shikenan kullum seyazo yace in bashi kudi se in bashi, wata rana dayazo gidana a buge y

ace na bashi kudi, naki bashi nasa masu gadi suka fita dashi se zagina yakeyi saboda naki bashi kudi, daga haka ya kullaceni ya dena ko zuwa ya tambayeni kudi, abinka da jini sede ni nake aika masa da kudi time to time, sam baya amsa sena kyaleshi,, , kaf

in mu Ankare ya zama babban d'an ta adda wanda Kaf sudan suka sani, amma ni sam ban damu ba se rayuwata nakeyi cikin iyalina ina ma hydar adduarh da kaddarar data samesa domin komi rubutacce ne daga sarkin da baya kuskure, koda na damu ban isa in chanzaw

a hydar khaddararsa ba...munata rayuwa da iyalina har Allah yabawa ummukhaltum ciki ta tashi haihuwa ta haifi Almuqri'ah yarinya me tsananin kyau, ana haihuwarta nasa mata Almuqri'ah,,, data kai 7month muka fahimci akwai matsala a harshenta domin ko gwaran

ci batayi, har takai 9month bata uhum ba um-um, sede kullum baki gum tana kallan kowa da ido kawai,,muka neme mgni tin a wancan lokacin amma sam ba a dace ba, wani malami ya taba shedamin iskokai ne suka shigeta tin tana ciki, kuma yace duk maganin daza mu

yi whlr banza zamuyi baza muci nasara ba, amma ya shaida mna akwai ranar da bakinta ze bude tass ranar da daya daga iskokan dake kanta ta fita wato ita wadda take bebiyar kenan...da mukaji hkn muka fawwalawa Allah, muka ci gaba da rayuwa cikin yadda da kh

addara me kyau ko mara kyau,, da Almuqri'ah tayi 1yrs , iyayenta suka rasu duka ta hanyar hatsarin jirgin sama, zasuje ibada kasa me tsarki, da Almuqri'ah sukayi hatsarin amma sam ita ba abinda ya sameta a gefe ma aka sameta kwance ko kurjewa batayi ba...a

ka kawomin gawawwakin yarana aka musu wanka aka kaisu makwancinsu, na dauki kaddara nayi musu fatan samun kwanciyar hankali a makwancinsu na gaskiya. ..muka ci gaba da rayuwa a katafaren gidan mu, har Almuqri'ah ta kai 8yrs duk tanata zuwa makarantar isila

miyya da boko, tin a 8yrs tayi saukar Alqur'ani me girma kasancewarta me tsananin hazakha, tanada 9yrs ta gama primary scul sbda kwazonta da hazakarta. A lokacin duk muna cikin daula saboda mahaifinta ya bar dukiya da gidaje da har mu mutu baza muyi tala

uci ba insha Allahu,, a haka har Almuqri'ah ta kai 12yrs zuwa lokacin ta gama JJSS, tana shiga SS1 na fara fuskantar barazana a gurin kanina hydar wanda zuwa yanzu ya kara shahara ya zama babban dan daban da kaf kasarmu ke kara tsoronsa ko hukuma bata ja d

ashi. Ya dingamin barazana kan in ban kawo masa kaf dukiyar da mahaifin Almuqri'ah ya bari ba ze kashemu nida Almuqri'ah duka,,senaji tsoro na kwashi rabi na kai masa, muka samu ya shafa mana lafiya, Almuqri'ah taci gaba da karatunta cikin gata a jirgin sa

ma ma ake kaita scul saboda tsanar dukiya da ubanta keda shi...tin tana 12yrs ta iya komi na girki, saboda na koya mata, ta iya komi kwarai, ga ilmi ga komari, tana SS2 ta zana Jarabawar fita zuwa makarantar gaba,, kwatsam muna zaune a gidanmu sega hydar d

a mukarrabansu, ya nunamin wuka ze kasheni, ya dinga zagina wai na masa karya na bashi dukiya kadan, dan haka yanzu ze kwace komi da Khalid ya bari a doron duniya...aiko hkm yayi ya kwace komi yasa aka jefomu a jirgi aka kawomu nigeria garin Abuja, to bamu

san kowa ba a abuja, dan haka muka fara bara,,daman tin tini inada blood cancer amma abin beyi kamari ba seda mukazo nigeria saboda bani da yadda zanyi insha maganin ciwon, yazamana abinci ma da kyar muke samu muci, Se munyi bara, kayan jikinmu ma se munyi

bara muke samu,, muna barar na fara matsanancin ciwo, gashi bamu dako daki a titi muke kwana a bakin hanya,, tin ina iya tashi har nazo ban iya tashi, kaf jigilata Almuqri'ah keyi wadda maza keta kawo mata hari da iskanci amma inata kafa-kafa itama tanata

kafa-kafa da mutuncinta. tin ina sanin inda kaina yake har yazamana ban gane mutane sosai sbda ciwo daya fara cin karfina,, ana haka wani bawan Allah yazo bamu bara yaga halinnda muke ciki, ya daukemu a motarsa ya kawomin asibitinka aka dubani akaga abin

da ke damuna, yace ze biya kudin komi amma se Almuqri'ah ta yadda ya tare da ita, ni kuma nace inta amince wani yayi amfani da ita ba mijin Aurentaba Allah ya isa ban yafe mata ba... Fir taki yadda da mutumin ganin hakan yasashi kin temakonmu sbda besamu

abinda yakeso ya samu ba a jikin Almuqri'ah...kunji yadda labarina ya kasance, munyi rayuwar kankaci a kasar nigeria bayan da gatanmu, duk Hydar ne ya jefamu a wannan kaddarar, da kuma komi rubutacce ne...nida ubangiji sede ince Alhamdulillahi kawai, amma

munsha wahala kuma munga rayuwa, kuma na hadu da jarabawar ciwo iri iri, but Alhamdulillahi..." Ammah ta karashe maganarta idanuwanta duk sunyi jage jage da kwallah, tana jinjinawa kaddararsu, dukda tasan Akwai kaddarar datafi tasu, amma kowani tsuntsu k

ukan gidansa yasani. Dr mus'ab da jarida duk seda suka zubda kwallah da labarin da Ammah ya basu sun tausaya Ainun. "Mutum nugun icce Ammah, ace kaninka uwa daya uba daya ya jefaka a matsifa..." Dr ya fadi yana meci gaba da kwallah, amma ma kwallar takeyi

ta kasa cewa komi a haka ma bata fayya ce musu komiba sbda rike sirrinta, amma kanin nata seda yaso mata fyade har tsawon 5tyms da kyar ta shallekewa kaidinsa, haka yaso yama Almuqri'ah fyade kusan 4tyms itama Amma Allah dukya tsaresu. "Ranka ya dade ai y

anzu dana kusa dakai ake cutarka, duk duniya babu me kin ci gabanka kmr makusancinka, duniyaR ce kawai tazo karshe, zamaninnan zaka haifa d'a ya kasheka, uwa 9months kana ciki, amma daka fito duniya zaka rasa mezaka sakawa uwa seka kasheta,,ko kaga d'an u

wa ya kashe dan uwansa , ko ya kusanceta, yaran yanzu ma wasu har iyayen nasu shaawah suke basu ta hanyar saduwa, wasuma sesu nemi su haikewa iyayen dasuka haifesu sbda rayuwar dabbobi..." Dr mus'ab dake kuka yace "Me muke nema a duniya? Duniyar data riga

ta kare me muke nema a cikinta? Mutuwa fa dole ce, haka hisabi ma dole ne, kodan haka ya kamata mu guji wannan rud'in duniyar, mu sassauta rayuwarmu lamarin duniya..." Dr ya karashe hadi da fashewa da kuka me tsanani, zuciyoyin kowannensu ya kara cikewa da

tsoron Allah se kwallah kawai sukeyi.

*Kaduna*

Seda hajiya saude tayi sati daya cir a kwance a asibiti kana ta fara gane wanda yake kanta, ta farfad'o kmr gaske, se kuma ta kara suma saboda zallar bala'in tashin hankalin da idanuwanta suka gani b

rain dinta ma rikicewa tayi, asibitin sukaga abu yafi karfinsu dan haka sukayi mata transfer zuwa 44, a can aka samu ta samu kanta bayan tayi 10days kwance kmr matacciya batasanma wake kanta ba. 7:am ta dawo hayyacinta tana bude idanuwanta taga larai ce k

usa da ita, ta lumshe idanuwanta yayinda larai ta bita da sannu, ai bata da hankalin dazata amsa sannu da jikin da larai ke mata gaba daya zuciyarta azabar tukiki take mata. Tinda Abdoljalal ya bar asibitin be kara dawowa ba bema kara saninna wani hali s

auden take ciki ba, yana can yana fama da tashi matsifar dayafi karfin ta saude zuwa yanzu ya fara zama kamar mahaukacn gaske daya ga ahamad seyace "An ganta ne? Ta haifarmin cikinane?an kawomin baby na ne?'' Ahamad na cikin na cikin dmwa shima babba, ya

kira Dr mus'ab kmr zeyi hauka amma shiru, jalalu ma da kanshi ya kira dr mus'ab amma kaf numbers dinsa basa shiga, tashin hnklinsa da jalalu yake ciki a kullum doubles suke zama. A bangaren Jimmali ma tana cikin dmwa har yau bata bar kukan rashin Almuqri

'ah a gidan ba ko ruwa setayi yaki da zuciyarta take iya shama cikinta.

Lumshe idanuwanta ta karayi da tsananin karfi yayinda abinda idanuwanta suka gani suka dawo mata sabo fil zuciyarta tayi nauyi, idanuwanta suka kawo kwallar bakin ciki, kunnuwanta

sukayi dum-dum abinda sukaji basu tabajin irin su ba har abadan,ji takeyi kamar a mafarki take, ta bude idanuwanta ta kalli saman slin din dakin asibitin, batasanma a asibiti take ba se yanzu. zumbur ta tashi zaune jikinta duk ya mutu , tamkar ba ita ba,

"Dama mutuwa nayi da ganin wannan matsifar..." Ta fadi a bayyane duk tabi ta fada a lokaci kankani se zare ido takeyi, larai ta kureta da ido, matsifa da zallar bala'i kawai ta hango a cikin idanuwanta. "Ina Abdoljalal?'' Itace tambayar data fito daga bak

in hajiya saude wadda tayi tmbyr kmr tayi hauka sbda tashin hankalin datake ciki ya kara dawowa sabo fil idanuwanta suka kara kawo kwallah. Larai ta tabbatar da tashin hnklin da saude take ciki babba ne sbda bata taba ganin tashim hnkli a tattare da ita b

a kmr na yau, dadin da d'awa ga kwallah, bata taba ganin kwallah a idanuwanta ba se yau . "Yana asibiti a farko amma zuwa yanzu yana gida..." Cewar larai da tayi mgnr kmr tana tsoro kasa-kasa. Hajiya saude ta watsa ma larai wani irin mugun kallo ba tare d

atace komi ba, gabaki daya haushin kowa takeji a duniya musammanma su larai, tanada tabbacin sun san komi dake faruwa amma basu ankarar da ita ba seda Hajiya lubah tazo ta ankarar da ita, se yanzu take nadamar cin mutumcin datayi ma hajiya lubar, ta kulla

aniyar kaf ma'aikatan gidan seta musu axaba mara misaltuwa. "Hakkina ne ya tabashi yasashi ciwo....Abdoljalal yaci amanata, wlhi se Amanar Allah tacishi, ..." Cewar hajiya saude,datayi mgnr yayinda zuciyarta ke kuna, hawayen idanuwanta suka kara tsinkewa.

Larai ta bita da ido kawai a zuciya tace "Kede haka zaki mutu cikin rashin wayau...hakkinki din me ya dauka daze sashi ciwo kece de hakki ke dawainiya dake ,haka zaki kare harki mutu, duk abinda ka shuka shi zaka girba..." Hajiya saude ta sauke nannauyar a

jiyar zuciya , ji takeyi daman ranar mutuwarta tagani da wannan ranar data gani , bata tabajin ta gaji da duniya ba kmr yau. "Ke dan bura uban ubanda ya haifo ubanki, tsinannu, yan iska butulu, dukse na hada na kwashewa kaciyar bura ubaku albarka, tsinann

u, yan iska, yayan Allah bani ko yaya ne,,,,ai dani kuke zancen.... Dan bura ubaki tashi jeki kirawo nurse ta ciremin wannan ruwan banga amfaninsa a jikina ba...."hajiya saude tayi mgnr cikin azabar ruwan wutar bala'i da matsifa hadi da tashin hnklin dak

e cike da zuciyarta. Jin irin uban zagin data antayowa larai yasata mikewa jiki na rawa ta fice a dakin, a zuciyarta tace "Ai kadan muka gani,,,nasan duk se kinci ubanmu ko baki fadi ba, tinda baki mutu ba ai tashin hankali be kare ba a gun uban kowa,yanzu

ma aka fara ..." Zuciyar larai ta shiga dukan uku uku, ta nufa inda nurse's suke cikin hanzari.

"Ni saude matar saraki, yau nice mijina kecin wata mace, har yake sambatu, har ya mata ciki, wai kuma ina raye...never! Wallahi senayi kisan kai, wlhi

sena zama rikakkiyar yar daba, sena dauki rayuka da dama koshi jalalun wallahi bazan barshi ba!! ..." Saude ta fadi kmr mahaukaciya bayan fitar larai a dakin. Se kuma ta tashi tsaye zumbur kamar mahaukaciya ta fasa wani irin mahaukacin gigitaccen ihu, se

da kaf asibitin ya amsa gata abu ba kadan ba.

Paid book ne.08101626484

40

Dai-dai ta fasa ihun dai-dai Nurse da Larai suna kofar dakin nata, jin ihun datayi yasasu dannawa cikin dakin a gigice suka ganta tsaye se zare ido takeyi kmr zararriya, id

anuwanta duk sun kumbure, hawayenta ta kasa yi. "Ke dan ubanki karaso ki ciremin wannan tsinanninan drip din..."cewar Saude da tayi maganar da nurse. Abinka da asibitin kudi, kudinma ba yan kadan ba, nan da nan nurse din ta Kara so ta cirewa saude drip di

n jikinta, se uban matsifa takeyi tana zage-zage, ta fice a asibitin kmr mahaukaciya,larai na biye da ita a baya, suka fito harabar asibitin ba mota,. Larai ta kira dreva ba jimawa yazo. hajiya saude ta hau sirfafa masa zagin dabesan dalilinsana,. Ya ding

a bata hkri kawai domin yasan abinda ke cinta a zuciya, dmn sun shiryawa bala'inta tini. Ya bude mata gidan bata ta shiga jikinta sam ba karfi, sun tada mota zasu bar asibitin kenan a guje doctor din dake kula da Hajiya saude, yazo ya dktr dasu daga fita,

yace si basu sallametaba. Nan fa saude ta zakalkalo mata ta zagesa tass, dr yaga abu yafi karfinsa ya bata hkri kawai suka fice a asibitin. Se girgiza kawai takeyi a cikin motar har suka isa tana kukan zuci,,ta rasa ma ta ina xata fara, amma ta Ayyanawa

ranta yau seta kashe Almuqri'ah, idanta idanta to tabbas ota ce ajalinsa koda hakan dazatayi shi ze zama na karshe a duniyarta daga nan se a kasheta ta yarda da hakan. Suna isa gidan ko packing dreva be gamayiba saude ta fito tabi masu gadi da ido, taga d

uk an chanzasu, tanaso ta tambayi larai ina wadancan masu aikin amma bala'i be barta ta tayi tambayarba. Ta nufa dakin Almuqri'ah ko kallan gabanta batayi sbda bala'in dake cinta. Tana isa dakin ta banko kofar dakin cikin bala'i da matsifa,idanuwanta cak

suka tsaya a kan Abdoljalal wanda ke zaune kasan dakin duk yabi ya rame ya lalace, jikinsa duk kasusuwa sun bayyana a wuyansa tmkr wanda yayi ciwon shekara da shekaru, yanzu nan dakin yake rayuwarsa gaba daya, sallah kadai ke fita dashi daga dakin, gaba da

ya baya hayyacinsa, ko ruwa besha, tunanintane abincinta tunanintane abinshansa , kukansa kuma shine samuwar sassaucinsa a kan tunaninta, zuwa yanzu ya kwammaci mutuwa a kan rayuwar tashin hankalin da yake ciki, bayasan kowa a duniya for now se ita, daze b

ada uban kowa bnda iyayensa a bashi ita wallahi zeyi hakan, zuwa yanzu ba cikin jkinta Yake bukata ba har itama yana tsananin bukatarta. Abdoljalal ya dago shima ya zubowa hajiya sauden ido, sam ma ya mance da ita in ba yanzu ba daya ganta. Saude ta kara k

uresa da ido zaune yake ya wani rakube kmr maraya sanye yake da jallabiya milk color, wani irin haushinsa ne ya turnike hajiya saude, kishi da zallar bala'i da matsifa suka turniketa. "Maci amana wato yanzuma kana nan dakin nata kenan...wallahi wallahi baz

an barku ba, har kai bazan bari ba, ... Ina ita yarinyar take dan wallahi yau nice ajalalinta..." Cewar saude dake mgnr kmr zata cinye kanta dan zallar bala'i da matsifa, hnklinta ya kara tashi sosai, saboda mijinta data kara gani yau kuma a dakin yarinyar

. "Abdoljalal ka cuceni!'' Ta fadi wasu zafafan kwallah na zubowa daga idanuwanta, yayinda takeji a zuciyarta koda ta kashe yarinyar da Abdoljalal din duka bazata huce takaicinndake zuciyarta ba. Tinda ta fara magana kawai kallanta Abdoljalal yakeyi, se ya

nzu ya kara fahimtar tsoron saude ne yasa Almuqri'ah barin gidansa, haushin saude ya rufe Abdoljalal, be tabajin ya tsani saude ba kmr yau. Saude tana kuka ta shiga dube dube a dakin tana fadinn"Ina take tsinanniyar..." Ta duba toilet taga bata ganta ba, t

a dawo kan Abdoljalal tana haki kmr zuciyarta ta tarwatse. "Ina tsinanniyar take..." Ta fadi da karfi kmr zata tsage dakin. Dago red eyes dinsa yayi ya zubo mata su , zuciyarta ta fara turiri yayinda kiyayyarta ke yawaita a zuciyarsa. "Batanan ta gudu sabo

da ke..." Abdoljalal ya fadi kmr ze fashe da kuka. Kallan rashin fahimta saude tabishi dashi. "Ta gudu kmr ya..." Cewar saude,. Abdoljalal ya tashi tsaye yayinda jiri ke neman kwasarshi kmr zautacce yace. "Ta gudu ta barni sbda ke, ta gudun min da ciki sbd

a ke,...kema yanzu ki fita ki barmin gidana banasan ganinki na tsaneki..." Abdoljalal ya fadi da babbar murya, yayinda kmr ya rufeta da duka. Nan take Saude tayi mutuwar tsaye, yayinda jikinta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login