Showing 144001 words to 147000 words out of 163724 words
saude bayan sunyi 3days a kanta, se cikin dare 2:am suka samu tadawo hayyacinta, suka mata Allurori aka
bata daki, tare dasa mata drib. Da Asubahi Abdoljalal nayin sallar asubahi yayi lazimi a daddafe 6;am ya nufo gidansa ya bar Ahamad nan asibitin. se Allah-Allah Abdoljalal yakeyi ya isa gidansa domin ya ga Almuqri'ah d'an cikinsa, zuciyarsa na yawan bu
gu a kanta. Yana isa gidan yayi packing a tsakiyar gidan ko packing space bayajin ze iya isa saboda ya kagara yaganta. Ya fito ma'aikatan gidan se miko masa gaisuwa sukeyi ko amsasu beyi ba hankali da duk tunaninsa yana kan Almuqri'ah da bebynsa. Direct y
a nufa dakin Almuqri'ah, securities dasuke kallanshi ko wannensu seda hankalinsa ya kara tashi, saboda sun san yau zasuci bura ubarsu daman tin tini suke cikin fargaba mara misaltuwa, su basusha cewa Almuqri'ah bazata dawo ba sunsha zataje ta dawo ne, shiy
asa suka barta ta fita ba musu,suna tsoron dktr da ita sbda suna bata girma,, gabako daya de a lokacin basusan meya shiga kansu Ba suka barta ta fita.
Da sallama ya shiga dakin. , idanuwansa suka sauka a kan gadonsu, yaganshi kace kace ba gyara,, nan
take yaji jikinsa ya masa wani iri,zuciyarta tayi ba ddh, dayaga bata dakin seyasha tana toilet ne dan haka ya nufa toilet din ya Ganshi a rufe yashiga toilet din hadi da
kwalo mata kira amma shiru, se yasha ko tana farfajiyarsa tashan iska, dan haka y
a nufa can , yana kwalo mata kira, securities na kallansa duk suka sha jinin jikinsu dacewar yau zasuci durin uwarsu, tin tini basu shiga damuwa ba se yanzu. Jikin Abdoljalal har yana rawa ya isa farfajiyarsa tashan iska be gantaba. "To ko tana dakin wann
an yarinyar .." Wato jimmalo yake nufi. dan haka ya juyo ya nufa part din ma'aikatan mata. da larai yaci karo, be taba zuwa part din masu aiki ba se yau,. sam larai batayi mamakin ganinsa a part dinsu ba, domin zuwa yanzu kaf ma'aikatan gidan mata sun sa
n Almuqri'ah ta gudu a gidan,sun san komi dake gudana a gidan, amma suna nuna kmr basu sani ba, larai dake kawo musu labari ita ke daurasu a darasin su nuna kmr basu san meke faruwa ba a gidan,kaf komi sun sani, harda sanadin kai saude asibiti sun sani sud
e fatansu kada saude tadawo gidan domin inta dawo seta ci bura ubar kowa na gidan.. Da larai tasamu labarin Almuqri'ah ta gudu a gidan a gurin salisu tantiri taji, seda ta rabgada gudar farin ciki daman ita ta tsani yarinyar saboda san da saraki kemata d
a kuma daukakar da Allah yama yarinyar daga zuwanta gidan a gun saraki tinda gata da cikinsa ai tasamu daukaka. Tsugunnawa larai tayi ta gaida Abdoljalal hadi da tambayarsa ya jikin hajiya saude... Ba tareda Abdoljalal ya amsataba yace "kiramin wannan yari
nyar, yasunanta ne wadda kuke aiki tare, me jikinnan..." Larai tace "Jimmalo..." "Kiramin ita yi sauri, in Almuqri'ah na dakin ki kirawomin ita seki bar ita waccan yarinyar..." Cewar jalalu. Larai tace toh hadi da mikewa ta nufi dakin jimmalo se murmushi
larai takeyi a zuciya da zahiri. "Insha Allahu kaida ganin wannan me sunan larabawar har abadan, tanacan kilama ta afka gidan yankan kai..."larai tayi maganar a zuciyarta. A kofar dakin Jimmalo larai taga jimmalon ta kalleta taga idanuwainta sunyi luhu luh
u tayi kuka tagaji. Larai ta tabe baki tace "ohh aiki yasamu gwari...aise ki tashi kije oga na kira.." Jimmalo taji gabanta ya yanke ya fadi jin abinda larai tace a karshe, ta mike tsaye hadi da gyara zaninta wanda ke kokarin kubce mata, tashin hankalin
datake ciki baze misaltuba, ko sadda ubanta ya mutu bata shiga tashin hankalin datake ciki ba a halin yanzu, tin tana ganin yarinyar zata dawo yanzu ta cire raima da yarinyar zata dawo gidan yau kimanin 2days kenan bata gidan, jimmalo kullum kwana da wuni
takeyi tana kuka, tunaninta daya ne ina yarinyar taje?'' Ta tabbatar in Abdoljalal yaji bata gidan tsawon 2days seya fi jimmalo damuwa "wane itama...." A jere jimmalo da larai suka iso inda Abdoljalal yake, jalalu yabisu da ido yaga bega Almuqri'ah ba se
de jimmalon, kallo daya ya mata yagane bata cikin hayya cinta kmr yadda shima baya cikin hayyacin nasa lips dinsa duk yabi ya bushe rakayau se faman jikashi yakeyi da yawon bakinsa.. "Ina Almuqri'ah na?'' Abdoljalal yayi tmbyr idanuwansa na kan jimmalo,
larai taji kmr ta kashe knta dayace Almuqri'ah na. Jimmalo kam gabantane ya yanke ya fadi, ta daburce ta rasama mezatace masa, kawai se yaga hawaye sharr a idanuwan ta..hakan ya bala'in jefa Abdoljalal a tsananin tashin hankali mara misaltuwa , ya tabbar d
a akwai babbar matsala.."nace ina Almuqri'ah da d'an cikina? Ina take? Ina d'an cikina? Kiyimin magana, ina cikina danayi mata? Ina cikina dake jikinta?!!!'' Abdoljalal yayi mata tambayoyinnan cikin tsawar data kada hantar cikin jimmalo ta kalleshi tayi
kasa da kanta, duk yabi ya haukace, a hakama dan beji komi ba kenan. "Ina take nace?!!!! Ina cikina?!!!!" Abdoljalal ya kara tmbya cikin tsananin tsawar da har securities seda sukaji, dukkaninsu suka hada baki gun cewa "Anxo wajen..." Kaf jikinsu ya dauki
rawa, suka kira masu gadin get din tsakiya dana farko duk suka dawo cikin gida sukayi tsuru tsuru, tini wasunsu sun fara zawo.
"Ta gudu,tin washe garin ranar dakuka je asibiti, na nemeta bangantaba wlhi..." Jimmalo ta fadi cikin kuka, ta zube kasan gu
iwowinta hadi da kara rushewa da kukan tashin hankli me tambarin matsifa da bala'in dake tattare da ita ko kwatan Abdoljalal bata kaiba. Larai de na gefe. Jin abinda jimmalo tace yasa kunnuwan Abdoljalal daukewa na wasu dakiku, idanuwansa suka lumshe da ya
na, yaji wani luuuu kmr ze fadi, se kuma ya rike jikinsa sbda shi namijin duniya be yayan namijim zaki ne,sam ba a ganin tashin hnklinsa duka, dan hk yanzuma rabi aka gani a zahiri. "Banji me kikace ba? Ta gudu? Ita wa ta gudu? Almuqri'ah ta gudu? Ta in
a tabi ta gudu? Ina taje? Ina cikina na jikinta??'' abdoljalal yayi maganganun kamar ze haukace saboda rudu da gigita, idanuwansa se lumshewa sukeyi yana kara budesu, tashin hnklinsa baze misaltuba har abadan, kai kace cewa akayi masa Almuqri'ah din ta mu
tu. Jimmalo ta kasa amsa masa tambayoyinsa se faman rusar kuka takeyi. Larai tayi carab tace "ta gudu ranka ya dade, wallahi ta gudu yarinyar nan, ta bakin get tabi ta gudu, suma kansu securities basu san guduwa zatayiba suka barta ta fita , ..." "Innali
llahi wa'inna ilaihirraju'un!!'' Abdoljalal ya maimaita 3ryms hadi da dafe kansa,, idanuwansa suka kara lumshewa. "Ta gudun min da ciki? Ina tajemin da cikina? Ku fada mata ta dawo ta bani cikina dan Allah...innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!''' Abdoljal
al ya fadi kmr saban hauka so yakeyi yayi kuka amma ya kasa, tashin hankali mara misaltuwa ya shiga, zuciyarsa tashiga, fuskarta ta bayyana Dmwar zuciyarsa,. Larai tayi lakur, tana hango bala'in dake tattare ga Abdoljalal. Jimmalo kam se kuka takeyi.
"Karya kuke min bata gudun min da ciki ba wlhi,,, se kun nemomin ita tabani cikina wlhi..." Ya fadi yana girgiza kai, ji yakeyi kmr a mafarki yake,. ya juya cikin hanzari ya nufo bakin get securities na ganinsa sukayi kasa da kansu, dmwa da tashin hankal
in dake kan face dinsa basu taba ganin makamancinsa ba a tattare dashi se yau. "Da gaske ne Almuqri'ah ta gudu?'' Abdoljalal ya fadi a haukace byn ya iso inda suke kmr zararre , jijiyoyin knsa duk sun tashi . Duk suka kasa magana sede suka kara kasa da kan
su. Abdoljalal ya daka musu tsawar dabe taba daka musu irintaba se yau "Nace da gaske ta gudun min da ciki?" Jikinsu na rawa suka amsa da "A, sir..tuba muke sir..." Suka hada baki gun fadar hakan. Idanuwan Abdoljalal suka kawo wasu zafafan kwallah, nan da
nan suka karayin jajawur zuciyarsa kmr zata fito fili, jikinsa ya dauki rawa. kaf ma'aikatan suka karayin kasa da idanuwansu, zuciyarsu nata fatt fatt fatt, sun san karshen zamansu a gidan yazo, tini suka fara kokawa kansu. "Ku kuka barta ta fita daga baki
n get?bayan ga cikina a jikinta?'' Abdoljalal ya fadi cikin kuka se yarfa hannu yakeyi sbda rad'adin da zuciyarsa keyi be tabajin irinsaba se yau.. Securities sukayi shiru suka kasa amsa wa.. "Badaku nake mgna ba dan kan babbar bura ubanku ku amsani, karku
karamin shiru, in ba haka ba, wallahi zansa muku bom in kashemu baki daya nida ku, shegu tsinannu, yan iska, nace ku kuka barta ta fita a bakin get, gets hard guda uku ta fice a cikinsu ta gudunmin da cikina a jikinta, dan kutmar babbar bura ubanku?'' Abd
oljalal ya fadi cikin fitar hayyaci da tsantsar tsagwaron ruwan wutar bala'i hadi da gobarar tashin hankali. Duk ma'aikatan suka kara shiga taitayinsu, sbda tashin hankalin dasuke tsammani zasu gansa a ciki se suka gansa a mafiyinsa. Duk suka amsa da yes
s hadi da ban hakuri. "Kuka barta ta gudun min da ciki, har tsawon 2days bata nan, ina taje? Da d'an cikina ta gudu kou? D'an cikina kou? Cikina na jikinta kou? Innalillahi wa'inna ilaihir...!!!''' Be samu dmr karasawa ba ya zube nan kasa sumamme tamkar
an zare masa rai, idanuwansa suka lumshe dmn ba karfi a jikinsa. Hankalin securities din ya matukar tashi, yadda naga fuskokinsu dmwarsu suma bazata misaltuba. Gadan gadan sukayo kansa suka dagoshi, aka kawo ruwa aka yayyafa masa, amma sam be farfado ba
ko ajiyar zuciya beyi ba, hankalin maza ya kara tashi wasu tini idanuwansu sun fara kawo kwallah, wadanda ba musulmai a cikinsu ba se kiran Jesus sukeyi suna ihu suna rawar diskon tashin hankali, tini suka tara kaf ma'aikata mata a gurin kukansu ya jawo
hnklinsu. Tantiri kam si yafi kowa kuka da ihu harda daura hannu yayi a kai yana fadin "Wayyohhhhh mun shiga uku mun lalace !!''' Se rawar tashin hankali tumbinsa keyi.... Nan suka kwasheshi a haukace aka sashi a mota, Almustapha ya rikeshi, da salisu tant
irin daketa kwallah Zuwa yanzu yayi ihun ya gaji har muryarsa ta dishe,, kaf ma'aikatan gidan sunyi nadamar barin Almuqri'ah ta fita a gidan, sbda hkn ya matukar jefasu a tashin hnkli seda kowa kowannensu yashiga tashin hankali. A guje Dreva ya shiga motar
yaja suka fice a gidan, motar securities na biye dasu a baya.
Insha Allahu zaku jini da daddare. Aski yazo gaban goshi azabar zafinsa nakeji
😂
38
*na gaya muku zan dinga hutun 2days a week kuma ban fadi ranaku ba, to hutuna nayi na 2days d
in,, kinganni nan nasaba da zagi duk wanda ya zageni ya ragemin kayan wahala.... A barni in bi book dina a sannu pls masu sona dan Allah...wadanda basu sona adeyi hkri...*
38
Bata tsaya wata wata ba, Ta buge security din dake kofar get din wanda ya dak
atar da Almuqri'ah daga karasowa cikin gidan, idanuwanta dana Almuqri'ah suka sarke cikin na juna. A lokaci guda dukkaninsu zuciyarsu ta buga da karfin, da basu san zuciyoyin nasu nada irin karfin ba. "Wacece ke?'" Hajiya ummu salma ta fadi out of control
, wani abu taji a zuciyarta gami da yarinyar,.Almuqri'ah tabi Hajiya ummu salma da ido, da tayi mgna se taji zuciyarta ta buga da karfi fin a farko, voice dinta yayi kama da makusancinta amma ta rasa fahimtar wanene wannan din?" Kaf kallo ya dawo kan Hajiy
a ummusalma da Almuqri'ah , kama daga masu neman temako har zuwa kan securities duk suka tsuro musu ido. "Dan Allah wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta kara tambaya hadi da dafe saitin zuciyarta sbda bugun da take mata kmr zata fashe, ta sauke idanuwanta a k
an cikin jikin Almuqri'ah, hk kawai taji wani abu na fisgasta gami da cikin jikin nata. Wani irin murd'awa marar Almuqri'ah tayi ta cije, still kwayoyin idanuwanta na kan hajiya ummusalma, wadda sak kamanninta kema Almuqri'ah kama da wani data sani amma s
am ta rasa tunano waneneshi wannan din. Hannu Hajiya ummusalma ta kai ta shafi cikin Almuqri'ah ba tare data sanma tayi hakan ba, Almuqri'ah ta zabura ta kalli matar, yadda ta shafar mata ciki sak haka Abdoljalal ke shafar mata ciki. "Dan Allah ki gayamin
wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta sale fadi a gigice, data shafi cikin Almuqri'ah se hankalinta ya kara gushewa, ta kasa dauke hannunta a kan cikin Almuqri'ah, ma'aikatanta da kaf da jakadiyarta suka matso kusa kusa,, mamaki ne ya rufesu musammanma jakadiy
arta, nam take zuciyarta ta ayyana akwai wata a kasa. Wani irin ciwon mara ne ya turnike Almuqri'ah wanda ya wuce a daure masa nan ta durkushe kasan kafafuwanta hadi da cije lefe. Nan take hajiya ummusalma ta fahimci nakuda ce,, nan take ta gigice, tasa d
reva ya dakko mota, ta umurci jakadiya data tayata suka kamo Almuqri'ah zuwa cikin gidan, da kyar take daga kafafuwanta, se azabar zufa kawai take karyo mata, suka dauketa da temakon sauran ma'aikatan aka sata a bayan mota, hajiya ummu salma ta shiga bayan
motar ta jawota jikinta, ta kurawa cikin jikin yarinyar data rairaye yayi kasa sosai ido, ita kadai tasan me takeji a kan cikinnan na jikin yarinyar. "Kai yi sauri kaja motar muje asibiti..." Cewar hajiya ummu salma, datayi mgnr da dreva dinta, jakadiyya
ta juyo ta zubo ma Almuqri'ah ido wadda keta faman yarfe hannu tana cije baki idanuwanta a kulle suke gam,, jakadiya ta kalli ummusalma taga cikin jikin yarinyar kawai take kallo, wani irin karatune a kan fuskar hajiya ummusalmar me wuyar karantuwa, nan ta
ke jakadiya ta shiga thinking din wacece wannan yarinyar ?'' Hajiya ummusalma tasaba temakon mata da dama, tanada tsananin imani da tausayi, imanin dake kwance kan fuskarta a wannan karan dabanne. Dreva yaja motar suka nufa asibiti, hajiya ummusalma se san
nu kawai taketa cewa Almuqri'ah,, haka kawai ta tsinci zuciyarta da natsawa sbda kallan dataketama cikin jikin Almuqri'ah.
*Kaduna*
Suna isa abitin da Abdoljalal ba bata lokaci doctor suka dukufa a kanshi , suka samu ya farfado daga suman da yayi, ak
ayi masa Allurar bacci, bacci ya kwasheshi bashi ya farka ba se 12:am ,ya bude idanuwansa a saman P.O.P din dakin asibitin, tunaninsa ya dawo kansa, "da gaske be ta gudun min da ciki!!??" Ya fadi kmr zararre hadi da tashi zaune zumbur ,idanuwansa suka sauk
a a kan Ahamad dake zaune kan kujerar dake facing dinsa, mustapha ne ya kirashi ya sanar dashi abinda ke faruwa shine yaxo asibitin yakira larai ita kuma take asibiti gun hajiya saude wadda har yanzu bata farka daga dogon baccin tashin hankalin da takeyi
ba. "Sannu sir, ya jikin naka?..."cewar Ahamad da yayi mgnr cikin tausayi da tausayawa. "Kagani ko Ahamad yarinyar nan ta gudun min da ciki? Kana gani ta gudun min da ciki kou?' Kwananta biyu kenan bata nan ta gudun min da cikina...'' Abdoljalal yayi magan
ar idanuwansa na cikowa da zallar kwallar tashin hankali tini ya koma kmr zararre. Ahamad ya karajin tausayinsa sosai, mustapha ya sanar dashi komi. "Ka kwantar da hankalinki sir dan Allah, zata dawo insha Allahu..." Ahamad ya fadi cikin kwantar masa da h
ankali. Abdoljalal ya kalli Ahamad dayayi, ya dawo ya kalli drib din hannunsa, ya girgiza kai still yana kwallar dashi kadai yasan zafinsa yace. "Bazata dawo ba...Ahamad tashi muje ka kaini in nemota, mutuwa zanyi in bangantaba..." Yayi mgnr hadi da tsige
drip din hanninsa nan take jini ya balle ya fara zuba. Hankalin Ahamad ya tashi ya riko hannun nasa yana fadin " sir dakayi hkri drip din jikinka ya kare..." Abdoljalal ya mike tsaye, still jini na tsiyaya a hannunsa,ya fisge hannunsa daga rikewar da Ahama
d ya masa, ya fice a dakin Ahamad ya biyoshi yana fadin "Sir bari a kira nurses su duba maka jinin nan dake zuba a hannunka..." Ina sam Abdoljalal be bi ta kansa ba ya fice a asibitin ma baki daya, ahamad ya kira nurse suka biyo shi wajen a bakin motarsa s
uka samesa har lokacin kuka yakeyi kmr karamin yaro yana fadin "Ta gudun min da ciki...shikenan ta tafinmin da ciki... sena kashe kaf securities din dasuka barta ta fita....a kaina gidan mahaukata, wlhi haukacewa zanyi in bangantaba..." Sune kalaman da Abd
oljalal keta fadi cikin gigitar fitar lissafi. Ahamad da nurse duk sukaji tausansa ya kuma ratsasu, nurse ta karaso domin temaka masa jinin hannunsa ya dena zubowa, amma fir yaki yarda, ahamad yayi-yayi ya tsaya amma yaki tsayawa nurse ta dktr masa da jin
in dake zubowa a hannun nasa. "Ka barni in mutu Ahamad,yarinyarnan ta gudunmin da ciki..." Ya kara fadi kmr ze mutum kokawa kawai yakeyi da numfashinsa. Idanuwan ahamad suka cicciko da kwallah ya zaro waya a aljihunsa yayi dealing number din dr mus'ab amm
a kiran be shiga ba tin jiya yake kiransa amma number taki shiga. Ahamad ya maida wayar tasa aljihu yayinda kwalla suka wanke masa fuska,yana me kallan Abdoljalal ita kanta nurse ta tausaya Ainun. "Dan Allah sir ka bari a duba maka jinin nan dake zuba a h
annunka dan Allah sir, zamu nemota kuma zamu ganta insha Allahu..." Cewar ahamad da yy mgnr yana kuka Abdoljalal dinma na kuka, da kyar ya yadda suka koma ciki nurse aka bashi temakon gaggawa jinin ya dena zubowa a hannun nasa. Suka fito ahamad ya bude mas
a mota ya shiga, shima ya shiga yaja motar suka fice a asibitin. Abdoljalal ya kwanta a kan kujerar motar ya lumshe idanuwansa se kuka yakeyi kmr karamin yaro. Ahamad nata kallanshi shima se hawaye yakeyi tausayin Abdoljalal ya kuma cika masa zuciya be tab
batar