Showing 84001 words to 87000 words out of 163724 words
ta fahimci kwanton mage Larai
zata mata kuma bazata saki jiki ba, a ankare take, tin kafin tazo gidan an zana mata zance tsaf. Ba tare da larai taci gaba da magana ba ta tashi ta nufa kofar dakin ta rufe, kana ta dawo ta zauna tayi low da voice dinta ta yadda bame ji se ita al-muqri
'ah din kawai, saboda larai tsoron ma daga murya takeyi, Dan wannan magana data fasu kwara larai Ajita a bakinta kwara ta mutu har lahira shi zefi mata alkhairi. "Dan Allah yarnan ina kikaje ne? Kwana biyu ina ziryar side dinnan naki naga banganki ba, ba
nan kike kwana ba shin ina kikaje ne harda kwana?"' Larai ta jero mata tambayoyinnan, cikin kwarewa a jin kwakwaf da zallar munafunci. Al-muqri'ah ta dago ta kalleta jin tambayar datakeyi mata , nan da nan hantar cikinta ta kad'a da tashin hankali, tayi sh
iru yayinda gabanta ke dukan uku uku. Larai ta fahimci halin data shiga tini , nan take ta kara tabbatar da zarginta, ta tsure yarinyar da kallon mamaki, "kizo har gidan mace kiyitama mijinta shishigi har kuna fita da mijinta, mijin Saude bala'i saude muts
iba.. a matsayinki na yar aiki ban taba ganin inda akayi wannan karfin halin ba, barawo da sallama...miji kuma bana kowa ba miji na saude drum din yaukin ruwan mutsiba..." Larai ta fadi a ranta, ita da kanta tashiga tsananin tashin hankali, sbda tana hango
ma yarinyar wulaknci nr tsanani. "Ina kike kwana ne yarnan ki bar amsata knji bakomai ki dauka tamkar ni na haifeki dan inada kamarki a gida, ni me dasa miki tarbiya ce daga inda iyayenki suka tsaya, d'a na kowa ne bawa kuma semeshi..." Cewar larai datayi
mgnr cikin kwantar da kai, ita a dole se taji meke tafiya. "Kiching..." Al-muqri'ah ta fadi da bebanci batare datasanma ta fadi maganar ba, kawai ta fidda kai ce mgnr, a bazata ta fito. zamansu tare zuwa yanzu larai ta fara fahimtar maganganun al-muqri'ah
dan haka tana fadin kiching ta fahimci me take nufi. Shiru larai tayi tana nazarin yarinyar, tasan karya ta mata. "Tabbas tinda ta boyemin akwai wata a kasa, kilama me afkuwa ta afku, in ba ma ta afkuba ina sukaje na tsawon kwanaki biyu....." Larai ta fa
di a Zuciyarta me cike da nazari, ta riga ta fahimci akwai wata a kasa, ita kadaice kuma ta fahimci hakan a kaf gidan itama saboda tanata sa musu ido ne shiyasa ta fahimta, a ganinta kenan ita kadaice kesa musu ido. "Wannan shine matsifa..." Larai ta fadi
a ranta, batare datasan maganar ta fito fili ba, al-muqri'ah ta dago ta kalleta jin abinda tace. "Matsifar me?'' Al-muqri'ah ta tambayeta da bebanci. "Matsifar dazaki sewa kanki da lafiyarki da kudinki..." Larai ta fadi a ranta amma a bayyane ta wayince
tace "au zancen zuci ne ya bayyana,, kinga da mukayi waya da kanwata ne, nasamu wani mummunar labari, daya faru a kauye, wai makwabciyar knwatace ta kona kishiyarta da ranta bayan ta babbaka mata patrol ta kyasta mata ashana, nan take ta kone muruss, hart
a cinye kurmus ba wanda ya iya karasowa ya ceceta saboda matsifar shishiyar tata, to itace a raina shiyasa kkji nace matsifa, ina cikin
jimamin abin ne kwarai da aniya..." Al-muqri'ah tatsureta da ido tana nazarin maganganun data gaya mata, dukda ita ka
ramar yarinya ce, amma sede ta fahimci maganganun data gaya mata kmr ba gaskiya bane, akwai abinda ke kulle ga zuciyarta, al-muqri'ah ta bita da ido kawai. Larai taci gaba da magana cikin kwarewa, byn ta lura kmr yarinyar bata yaddaba, ta fahimci yarinyar
nada tsananin wayau "wallahi dama seda aka gayawa matar kafin ta aureshi cewa kishiyarta bala'i ce kishiyarta matsifa ce, amma takiji gashi yanzu har abadan an karas mata da rayuwa, ina dadinta..." Al-muqri'ah tayi shiru kmr malam yaci shirwa , abinka da
yarinta nan ta Yarda da labarirrikan larai, tini tunaninta ya juye ta tausaya itama. "Allah ya kyauta ya bata lafiya..." Al-muqri'ah ta fadi da bebanci, Allah ya kyauta din kawai Larai ta fahimta, ta amshe da "Amin...ai shiyasa bahaushe yace in gemun dan
uwanka ya kama da wuta ka shafawa naka ruwa, Allah de ya rabamu da mummunar kaddara, dan ita ke jan wasu, ko kuwa daman ajaline yake kiran hansai oho, kinsan ajali shi kira yake...'' Al-muqri'ah tashiga jimami hadi da tausayawa ita hansai din da abin ya s
ameta, larai ta tabe baki hadi da mikewa bayan ta gama mata jirwaye me kama da wanka amma ita al-muqri'ah bata fahimta ba, setasha ko wanka ne tayi na soso da sabulu ta fita tass, ammafa a bayyane taga hakan a zuciyarta tana me juya wasu kalaman na larai.
Har larai ta isa bakin kofar fita se kuma ta juyo ta kalli al-muqri'ah da tufafin jikinta, daman da batanan, duk seda ta bincike ko ina a dakin taga sabbin akwatuna da kayayyakin da Abdoljalal ya sayawa al-muqri'ah hakan ne ya kara sa larai a tunani tuna
ni, hadi da nazarirrika, ba a tabayin me aikin dako kallanta me gida ya tabayi ba a kaf gidan, tsawan shekara goma larai na aiki a gidan, dan ita jurau ce, kuma tasan yadda take tafiya da saude shiyasa ta jima a gidan... Sosai fa larai tashiga tunani hadi
da dasa ayar tambaya a kan yarinyar dame gida, daman tin zuwanta gidan ta fahimci gaskiya dole ne akwai wata a kasa. "Ki dinga taka tsantsan kina me tunawa da sharuddan hajiya mommy, kada ki bari ta kamaki da wani lefi koda da kwayar zarra ne, domin kuwa
batada digon imani a zuciyarta...ina me baki shawarar daki kiyaye hajiya saude, domin itadin maciji ce amma fa wallahi dafinta yafi na maciji zafi..." Tana gama fadar hakan ta juya ta fice a dakin, yayin data bar al-muqri'ah da nazarirrika a kan kalamanta.
"Tabbas na fahimci dafinta na iya fin na maciji..." Al-muqri'ah ta fadi a ranta, zuciyarta ta tsinke taji jikinta yayi sanyi a kan lamarin dake zaune da ita a gidan "Anya zan iya?'' Zuciyarta ta tambayi kanta, yayinda kalaman larai ke juyi a kwakwalwart
a. Nan da nan damuwa ta hadu tama zuciyarta rubdugu, ta shiga tunano dalilan zuwanta gidan,,,seda tafi karfin 20mnt zaune tana nazarirrika a kan komi daya faru kama daga dalilan zuwanta gidan, har zuwa ynzu da kalaman larai ke neman rusa mata kwarin guiwa
, Tasan tashiga wahala kawai, gashi bata da wanda zata gayawa damuwarta taji dadih, duk saboda kakarta tayi wannan abubuwan, amma fa zuwa yanzu bayan saboda kakarta tayi hakan gaskiya tana bautawa So amma ita bata fahimci ma meye san ba balle tasan tan
a bauta masa,,,
kwanciya tayi hadi dayin lamo, tunaninnika dayawa na damunta a zuciyarta, kawai tana boyewa ne saboda an umarceta data boye din dole,. "Inaso insan a wani hali kakata take ciki..." Al-muqri'ah ta fadi a ranta, wannan damuwar na ya kakarta t
ake ciki yafi komi daga mata hankali , kuma wannan shine dalilin silar yawaitar yin sallar dare,, domin adduarhta kenan daya tak a kan kakarta, tinda ta taso batasan kowa da komi ba se ita, Soyayyarta ce kadai take iya fahimta a matsayin soyayya. "Allah y
asa kina cikin yanayinki me kyau Kakata..." Ta fadi hakan a ranta yayinda kwallah ya cika mata idanuwa nan da nan se kuka, ta dinga kuka da shashsheka....ta kai awa biyu tana kuka kana ta iya mikewa tama dakinta key, ta fada toilet ta dauro alwala, ta dawo
dakin ta hau dadduma ta fara nafilfili, zuwa yanzu harta saba bata da abokin kai kukanta ko wanda take gayawa damuwarta se ubangijin sammai da kasai, saboda yafita sanin damuwarta, dama can ita bata gayawa kowa danuwarta se mahaliccinta, shike amsar kukan
ta kuma shike share mata, ko zuwanta gidannan tasan karfin adduarh ne da ubangijinta ya amsa a kn kakarta, bayan tayi kuka iya kuka, harta fawwalawa ubangiji hakuri da ran datafi kauna wato kakarta, se ubangiji ya kawo musu mafita rana daya tal, tana fatan
zuwa yanzu insha Allahu ran abinda takeso ya kubuta daga wahala me tsanani bayan wadda abinda takeso din tashiga a baya, kawai so takeyi taga kakarta ko taji labarin a wani hali take ciki zuwa yanzu. "Nurse lubna..." Ita ta fado mata rai, nan tasakata a a
dduarhta , domin itama mutumce garesu, kuma baxata mantuba a zuciyar Al-muqri'ah.
** ** ** ** ** ** ** ** ** ** **
Garin Adamawa yola.
Yau ta kasance ranar juma'ah ce, bayan an sakko daga sallarh juma'ah. Dandazon mutane na hango a bakin babban get
din gidan sarki kama daga jinsin mata zuwa jinsin maza,a kalla yawan mutanen yafi a kirga, yawan mutanen ya wuce tunanin duk wani mahaluki me lissafi da tunani a duniya, dukkaninsu nakasassu ne da marasa galihu, suke taruwa a duk ranakun juma'arh domin am
sar temako me tsoka daga matar Sarkin Yola hajiya ummusalma, wanda ta jima tana bayarwa shekara da shekaru. ita da kanta ne tsaye a bakin kofar gidan yayin da take kallon komi dake wakana, tako ina an kakkareta da masu tsaro(securities). Sanye takeda hij
jabi nevy blue har kasa. kallo daya zakama fuskarta ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa, fuskarta na dauke da damuwa me yalwa. Ma'aikatantanta dake dawainiyar raba taimakon a kalla zasukai dari biyu, maza dari mata dari, suke mikawa kowa daki
daki lullubabbiyar takadda wadda ke dauke da kudade kimanin dubu hamsin hamsin, duk ranakun juma'arh setayi wannan sadakar, tana zama sikar yayewa mutane da dama damuwarsu, tana tawassali da wannan ayyukan nata datakewa mutane da damuwar da takeyi itama t
ana fatan ubangiji ya yaye mata damuwarta a kan danta tilo kwara daya tal, wanda zata iya sadaukar da komi nata data mallaka ta hnyar iyayenta a kn danta tilo., iyayenta sunfi mijin datake aure kudi na fitar hankali ma kuwa. Ma'aikata keta aikin wannan r
aban na zallar dukiya ba
tareda gajiyasaba. wasu in sukazo su kawo matsalolinsu na ciwuwwuka da de sauran jarabawar rayuwa, in aka isar da kukansu ga hajiya ummusalma, tace a basu kudade da dama dazeyi musu maganin damuwarsu, a kullum da kanta take tsayuw
a a gaban idanta akeyin komi saboda gudun kada ayi zalinci,tafison sako ya isa ga mabukata direct.
wasu daga yawancin mutane da dama, na zargin tana hakan ne saboda danta yaci shugaban kasa a nigeria, nan ko Allah kadai yasan zuciyarta, ita dazata ras
a komi a batta da d'anta dase tafi farin cikin hkn a kan wannan yalwar arzikin da Allah ya mata....jiri taji yana neman kwasarta, dan haka ta koma ta zauna daga tsayuwar datake, nan take taji kanta yayi wani dum-dum kawai kamar an saukar mata da ruwan az
abar ciwon kai, nan da nan kawai taji idanuwanta sun lumshe, cikin hanzari ta mike a daddafe kmr makauniya, hajiya Binta, wato wadda tafi kusanci da ita, jakadiyarta,, na ganin ta mike ta biyota a baya sauran masu taka mata baya sukayi kokarin biyosu haji
ya binta ta dakatar dasu domin tini ta fahimci chanjin yanayin uwar gijiyarta. Karasowa hajiya binta tayi ta dafeta ganin tana niyar faduwa saboda ko gabanta bata gani, sosai. "Ki kaini part din baban jalalu..." Itace kalmar data fito daga bakin hajiya s
alma da kyar. "An gama ranki ya dade..." Cewar hajiya binta, ita ta kamota, suka nufo part din me martaba Sarki, tin kafin su karaso ya fito daga part din nasa cikin hanzari sanye da jallabiya. ya tarbeta domin yana daga window tin sadda take tsaye bakin
g get tana kallon masu raba sadaka, yana kallanta har zuwa yanzu. Karasowa yayi ya amsheta daga rikon da hajiya binta ta mata wadda a kalla zata kai 60yrs. Dukawa tayi har kasa ta korowa me martaba gaisuwa, ina be samu damar ansawa ba, hankalinsa na kan iy
alinsa farin cikinsa. "Salmanah ya akayi? Ko jikinne?'' Ya jefowa hajiya salma tambayar, saboda yau daman ta tashi batajin dadih, dama seda yace mata ma yau ta dakatar da bada sadakarnan ta bari se next friday amma taki. "Kaina ke ciwo..." Ta fadi idanuwan
ta na ciccikowa da kwallah, cikin hanzari ya nufa babban falonshi da ita, yanata mata sannu, ya tabbatar ciwonne ya matsa mata sosai, da bazata taba gaya masaba, tafi karfin 2weeks tana rashin lafiya a tsaitsaye ya tambayeta meke damunta tace masa bakomai,
yayi-yayi a kira dr amma taki amincewa, to tabbas yanzu data bayyana ciwon yacita sosai ne. binta ta juya ta koma bakin get tana me jimamin halin da hajiya salma ke ciki, binta tasan komi, kuma kullum cikin adduarh suke a kan Allah ya karkato da ran
Farin cikin uwar gijiyarsu gareta wato JALALUDDEN.
A kan kujerar 3st suka yada zango, yayinda hajiya salma ta kwanta ta daura knta bisa cinyoyinsa, kwance take kn cinyoyinsa amma yana jiyo heart beat dinta, dan haka hnklinsa ya kuma tashi, ya dauki way
arsa ya lalubo lambar Dr, bugu daya dr rabi'u ya dauka zuciya fal mamakin yau Sarki ne da knsa ke kiransa, be taba kiransa da knsa ba, sede yasa na hannun damansa wazo Zakinsa wanda shine aminin sarki kuma me masa hidima Umar sunansa,. Yana daga kiran Me
martaba yace
"kazo gida ynzu,.." Yana fadar hkn ya katse wayar. Yadda yayi maganar ya kara tabbatarwa da rabi'u ba lafiya. Ba bata lokaci ya iso gidan, direct part din me martaba ya iso, ya nemi iso aka masa iso, ya shigo bakinsa dauke da sallahma yana
me karewa aljannarh duniyar falon kallo, an narka dukiya ainun a falon. Karasowa dr rabi'u yayi cikin hanzari ganin hajiya salma kwance kan cinyar me martaba kallo daya ya mata ya fahimci itace ba lafiya. Ba bata lokaci dr ya dubata kasancewar akwai keba
ntancen asibiti da komi na bukatuwa a cikin gidan, dr yayi mata allurori nan da nan tasamu bacci. Dr ya juyo ya kalli Me martaba wanda ke zaune gadon da hajiya salma ke kwance, yayinda dr ke zaune bisa kujera. "Dr meke damunta?'' Itace Kalmar data fito da
ga bakin Me martaba zuwa ga dr, cikin tsananin tashin hankali me martaban yayi tambayar. Dr ya fara da kwantar masa da hankali, dukda be fahimci meke damuntaba saboda ba fanninsa bane amma ya tabbayarda akwai matsala. Me martaba yace "rabi'u, kanata kwan
tarmin da hnkali dan Allah ka gayamin meke damun matata.." Me martaba ya fadi cikin zallar damuwar tashin hankali, yayi mgnr tmkr ba babban mutum ba,. Dr rabi"u ya fara magana cikin muryar kwantarda hankali me dauke da tambarin girmamawa. "Insha Allahu ba
wani babban abu bane, ranka ya dade, ku kwantarda hankalinku ynzu zan kira wani dr ya kara dubata,..." Hnkalin me martaba ya kara tashi yace "Kana nufin baka fahimci meke damuntaba..." Dr rabi'u yace "Ba fanni na bane, amma insha Allahu ba wata matsala bac
e bari in kira dr hassan yazo ya dubata inkun bada permission ranka ya dade.." Ya karashe mgnr cikin girmamawa. Ba bata lokaci me martaba ya bashi izinin kiran dr hassan. Dr rabi'u ya kira dr hassan, ba jimawa yazo ya dubata sosai, kasancewar sunada kaya
n aiki kwararru be wani bata lokaci ba gun gano meke damunta, zuciyartace ta kumbura,. Cikin dabara dr hassan da rabisu suka gayama me martaba, ba karamin tashin hankali me martaba ya shiga ba, dr rabi'u da dr hassan suka shiga kwantar masa da hankali, h
adi dace masa ai warke insha Allahu inde aka daurata a kn magani da temakon Allah.... Haka akayi aka dorata a kn magunguna, yayinda Me martaba yake kwantar mata da hankali akoda yaushe, amma ina taki ta kwantar da hankalinta, seda aka hada da Addu'ur'i ha
di da amsar mata rubutun ayoyin ubangiji kana jikin nata ya farayin sauki amma ta gaza komawa dai-dai, tunaninta da zancenta a halin ynzu duk na jalalu ne,...temakon ubangijine yayi tasiri a knta tasamu ta mike amma badan ta cire tunanin Jalalu ba, yana
nan ga ranta, tasan har ta komawa mahaliccinta , jalalu shine kaf tattalinta da tunaninta a halin yanzu.
USA.....
Babbar asibiti ne, wanda su knsu turawan kasar keji dashi fiyeda kowanni asibiti a kasar, har zuwa kasashen dake makwabtaka dasu, du
k sunaji da wannan asibitin. asibiti ne wanda sukeda kwararrun likitoci masu aiki kmr yankan wuka da
temakon ubangiji,, wannan asibitin duk wanda kagani a cikinsa ba karamin miliyoyin kudade ya sauke ba, domin kuwa zuwan asibitinma bako wanni me kudi ba na
kasar balle na kasashen nigeria, duk wani me karamin karfi yayi kuskura yazo asibitin nan kaf kudadensa zasu kare ba tare dayaga Koda dr ba.
10:pm Wata dattijuwa nagani kwance bisa gadon majinyata, hannunta makale da drib hancinta makale da na'u'rar zu
ko mumfashi wato oxygen, gabaki daya gadon da take kaima na'ura ce ke aiki a jikinta, tako ina a lullube take fuskarta ce kawai a bude, kanta sanyeda hula blue. Fans Gadon majinyatan dakin ma kawai abin kallo ne, ko ina so perfect, akwai komi na bukatuwa
a dakin tamkar kana gida. Wata mace nagani zaune bisa kujerar dake facing gadon da matar ke kwance wadda a kalla zatakai 50yrs, black beauty ce, tanada kyau dukda ta manyanta, tanada matsakaicin tsayi a kallah bazatafi 56 ba lent dinta. Ita kuma wadda ke k
wance gadon majinyatan a kalla zatakai 55yrs wato mara lafiyar tanada tsayin da a kallah lent dinta zekai 60, kaf tsawon nan nata ta mikeshi a kan gadan da take kwance, kai ka rantseda Allah matacciya ce. alamomin wahalar jinya dukya bayyana a tattare da j
ikin wadda ke kwance