Showing 159001 words to 162000 words out of 163724 words
daya ba,
kalan yadin ba kalan zaren bane, koda goma ta lalace dole ne tafi biyar albarka, zaki zaki koda kuwa gawarsa ce, in namin daji duka gani se hantar cikinsu ta kad'a. Jalalu ya dinga ma Dr maganganu masu zafi ya hanashi mgna kana a karshe ya fice ya bar fa
lon nasa, byn ya kankara masa warning din in har gobe be fito masa da Almuqri'ah ba an bashi cikinsa ba wlhi sede Kawai dr yaji sammaci. Yashiga mota ahamad daketa kallansa yynda yaketa huci,ahamad ya kara tabbatar da babu lafiya. Yaja motar suka fice a gi
dan, har suka isa gida jalalu na kukan bakin cikin abinda dr ya masa. Ahamad nayin packing jalalu ya fito a daddafe yana mejin jiri ya nufa dakin Almuqri'ah yana shiga yaga dr zaune a gefen bed din Almuqri'ah ,abdoljalal na fita a gidansa shima ya hayo mo
ta ya nufo gidan nasa cikin gudu, shiyasa ya rigasu karasowa gidan. "Dan Allah ka saurare ni frnd pls, wlhi bazan iya cin amanarka ba, duk inda naga wanda zeci amanarka ko ze cuceka wlhi se inda karfina ya kare, har raina zan iya badawa a kanka jalalu, kai
mutum ne kmr yadda mahaifinka yake mutum pls ka saurareni..." Dr ya fadi yana kuka shima yayinda idanuwansa sukayi ja-ja-jawur kmr gauta be taba shiga tashij hnkli irin na yau ba. "Baka da abinda zaka gayamin.." Jalalu ya fadi shima yana kara kwallah kmr
ze haukace yakeji, duniya ta masa zafi, ya zauna kasan dakin ya dafe kansa da hannayensa yana kuka fin tunanin me karatu kmr karamin yaro... Dr ya dinga masa magiya kan ya tsaya ya sauraresa,,da kyar jalalu ya yadda ya tsaya ya saurari me Dr zece masa.dr
ya leka ya kira ahamad suka dawo dakin tare, kana dr ya fara zayyanowa jalalu labarin komi daga farko hatta labarin su Almuqri'ah da ammah (fatima) ta bashi be boyewa jalalu ba, ya kira isma'il a waya, domin shida ahamad ne shedarsa se nurse mami a duniya.
Jalalu ya kara fashewa da kuka amma na farin ciki. "Ashe da Aure a tsakanina da Almuqri'ah,,gaskiya kai aboki ne na amana, kai abokine da babu irinsa a yanzu , ka gamamin komi mus'ab..." Jalalu ya fadi yana kuka hadi da nadamar maganganun daya gayawa mus'
ab,ya rungume mus'ab din a jikinsa sosai, dukkaninsu suka fashe da kukan soyayyar junansu. Abdoljalal yadingama dr godiya mara iyaka, ya dinga rungumarsa kmr ze maidasa ciki seda Ahamad ya koka shima, baya tunanin a duniya akwai mutane irin dr mys'ab a ha
lin yanzu, abokan yanzu duk munafukai,kai inka samu me sanka duniya ka riga dakai saarh, me sanka daya yafi makiyi dubban dubbai, (Ya ilahi dan Annabi SAW ka barni da hubb har abadan Abidina Amin ya ilahi)
Ranar nan gidan dr ya kwana yanata kara bawa
jalalu labarin komi yadda ya gudana. Abdoljalal yaji kmr ansashi a aljannah yaji ddh daya zamana Akwai aure a tsakaninsa da Almuqri'ah, dayasan cewa an biya mishi sadaki ai da bugun dazema durinta seyafi haka,,abdoljalal ya dingama dr mus'ab da isma"il da
ahamad godiya dasa Albarka mara iyaka, a duniya byn iyayensa beda kmr mys'ab da Isma'il da ahamad, da hajiya kande ma, shi kadai yasan meze nusu na Alkhairi, Amma fa adduarsa garesu bazata yanke ba. Adduarhsu daya yanzu Allah ya bayyana Almuqri'ah.
*Adamawa yola*
Yau kimanin watanta biyu da kwana goma a gidan hajiya Ummusalma, ba karamin kulawa suke bata ita da yayantaba, yaran sun Fara wayau sosai zuwa yanzu, kasancewar duk sunada girman jiki gasu yan lukataye gwanin ban sha'awah, yara hudu re
ras lafiyayyu, kamannin yaran maza da Abdoljalal ya kara fitowa rass, sannan itama macen kamanninta da ummusalma ya kara fitowa sosai, a kullum yaran na gurin me martaba da ummusalma suke jigilar yaran,yaran dun zame musu farin ciki sun wanye musu kewar j
alalu dake ransu, har ummusalma tayi yar kiba sbda zuwan yaran gidan. Yau ta kasance juma'ah ce, ta tashi sallar asubahi taji wani abu ya fita a jikinta da tsananin karfin tsiya, tayi wata iriyar atishawa, ta duba gabas ta duba yamma bataga kowa ba a dakin
, daman yaranta badasu take kwana ba a gun ummusalma suke kwana dame martaba. Ta nufa bandaki a tsorace, ta kara kiba tayi bul-bul da ita tayi fresh ainun ummusalma na bata kulawa ta musamman tako ina ta kara cika, duk wata gaba ta jikinta ta bude ta kara
kyau surarta ta kara bayyana kmr zata fashe. Tashiga bandaki tana brush, brush din yazo faduwa a hannunta zuwa kasa, tace subhanallahi, mamaki ya cikata jin subhanallahin datace ya fito ba gargada, ta kara fsdi kusan 7tyms, nan take taji alamar bakinta ya
koma dai-dai yanzu ita ba bebiya bace, ta rasa ina zatasa rayuwarta dan farin ciki, a guje ta fice a toilet din, ta dice a bangaren nata yayinda tsoro da firgici suka rufeta, ta nufa pat din su me martaba, tana shiga ta taddasu har daki suna sallah, yaran
ta kuma nata bacci a gadansu. Su me martaba suka idar da sallar shida ummusalma, ta dago ta kalleta cikin tsoro tasha wani abin be yasameta,. Nan Almuqri'ah ta bude baki tayi magana, kaf suk farin ciki ya rufesu suka dinga godiya ga mahalli. Nan Almuqri'
ah ta zube tayi sujjadar godiya ga Allah , bata taba tsammanin bakinta ze bude ba, ai rnr baki har baka dan murna, ga muryarta me azabar zakin tsiya. Mommy ummusalma ranar sadakar datayi dabance, Almuqri'ah kam wuni tayi tana ibada ta godiya ga ubangijin
sammai da kasai.
*Kaduna*
Yau kimanin watansa daya da sanin labarin komi nasa da Almuqri'ah,. Tinda ya tashi yau yaji iyayensa kawai yakeson gani sbda su masa adduarh ya fita a matsifar nan da yake ciki, tayuma ko fushin rashinsa garesu ne ke daw
ainiya dashi. Dan haka da wuri ya shirya yasaka jallabiyarsa, ya kira ahamad yace yase musu jirgi zuwa adamawa yola. Ahamad yashiga mamaki mara misaltuwa hadi dajin dadih kuma, domin ba a mamaki da ikon Allah komi yayi farko zeyi karshe. Ba bata lokaci yas
e musu jirgi zuwa adamawa yola. Abdoljalal ya fito ze shiga mota saude ta fito ta watsa masa wani banzan kallo ta amso asirinta boka ya tabbatar mata da zuwa yanxu jalalunta ya koma yadda takesonshi. "Maci amana, dan iska mazinaci, zanga ai yanzu nida kai
waye ze bar gidannan,, seka tsugunna ka rokeni gafarar cin amanata dakayi kana zakaci gaba da zama a gidannan.." Cewar saude datake tunanin jalalun da ne. Daman Abdoljalal yana ciki da haushinta yanzu duk yabi ya tsaneta sbda sanadinta ne Almuqri'ah ta ba
r gidan, shi a halin yanzu beda abarda ya tsana kamar hajiya saude, ya rasa ma meyasa tashigo masa rayuwa a matsayin mata, shide yasan bashi ya aureta da hayyacinsa ba. "Ke ni kk zagi..." Ya fadi a hasale, kawai ya rufeta da duka harda nauyi a bainar nasi
, ya danneta ya dinga nauyi tana kukan neman agaji, ahamad na gani yaki dakatar dashi,sbda shima yana ciki da haushinta se ci masa mutumci takeyi kullum sbda ta koresa yaki tafiya. Securities na kallo amma basu iya su hana ba, .... Seda ahamad yaga jalal
u na niyar kashe saude dan har ihunma gagar yinsa tayi kana ya kira wasu daga securities suka dagashi a kanta da kyar, ya barta a sume ya shiga mota yanata bambamin matsifa yana durawa sauden ashar, yace ta bar masa gidansa karya bari yadawo yasameta. Aha
mad yace securities su zuba mata ruwa inta farfado su gaya mata sakon oga in kuma bata farfado ba su kaita asibiti. Yashiga mota ya bar saude nan yashe da rabe-raben nonuwanta na guguna, duk tabi ta zabge kibar asarar nan yanzu babu se uban baki datayi, do
min yanzu maima yadena amsarta, hatta da gawayin girki yafita kyaun gani da harke. Ahamad yaja mota suka fice a gidan zuwa Airport. Securities suka zubawa saude ruwa ta farfado da kyar byn an antaya mata robar bottles water guda ashirin da tara. Data farf
ado ta kasa tashi ko ina a jikinta karaya ce ga uban jini nata zuba a goshinta, , ta daku iya dakuwa a gun jalalu. Securities suka kwashi saude daketa kuka tana kiran ohhh yesuuu,,,!! Tana ihu irin na radhin tawakkali , securities suka nufa asibiti da ita
. Suna kaita aka amsheta a zaton doctor din daya dubata ma Assident ne, se tambayarta yakeyi babbar mota xe tifa ta bigeta,,,saude ta dinga dura masa ashar,,, dr yaja baki yayi shiru a zatonta ko ta bugu ne a kwakwalwa, dan haka aka mata dauri tako ina dat
ayi karaya, dr ya mata transfer zuwa asibitin mahaukata, ya kira motar asibitin suka dauketa zuwa can asibitin mahaukatan, sede doctor ya gayawa wadanda suka kawota inda zasuje su sameta.
Suna airport ,suka shiga jirgi, cikin hikimar ubangiji jirgins
u ya lula sama zuwa yola. Haka kawai jalalu kejinsa a farin ciki mara misaltuwa.
Sefa hkri da typing error. Allah yasa mugama lafiya paid book ne 08101626484.
44
Cikin cikon ubangiji suka isa yola,. Abdoljalal da Ahamad suka sakko daga cikin j
irgin, abdoljalal ya kalli ahamad yace "Waze daukemu zuwa gida?'' Ahamad yace "A, sir na kira waziri isma'il na gaya mishi gamu a hanya ya turo a daukemu gasu nan ma sun iso..." Ahamad ya karasa mgnrsa hadi da nuna inda motoci guda biyu sukayi packing. Su
ka karasa ga motocin suka shiga suka nufa gidansu Abdoljalal se numfashi kawai jalalu yake saukewa, yana mamakin kansa wai yau shine zeje gidan iyayansa da kansa, ada baya tunaninma ze gane gidan iyayen nasa se yau yaji sun dawo zuciyarsa sabbi fil,yana
tsananin san iyayensa amma besan meyasa ya banzatar dasu ba ada,. Suka isa gidan dreva yayi packing ya fito, ya shiga bin gidan da kallo kmr bakon duniya. ma'aikatan gidan seda sukayi da gaske suka gane Abdoljalal ne sbda lalacewar da yayi,ya kasa takawa d
aga inda ya fito daga motar, maaikatan gidan suka shiga karasowa suna zubewa hadi da kwasar gaisuwa, Amsawa abdoljalal yakeyi yana me binsu da ido... Tini labari ya isarma hajiya Salma wadda ke zaune a falonta bayanta goye da dan Almuqri'ah mesunan me ma
rtaba wanda akece masa nor, se macen wanda akecewa Aflah datake hannunta. Mamaki ya rufe ummusalma da labarin da jakadiya ta kawo mata na Abdoljalal yau a gidan. Kasa daurewa tayi ya karaso ta fito zuwa inda yake still Norr na bayanta Aflah na hannunta, ta
nufo inda Abdoljalal yake gadan gadan. Tin daga nesa taga ya lalace ya rame tamkar bashi ba kawai seta fashe da kuka, Abdoljalal shima yana ganinta ya fasheda matsanancin kuka yana mebin yarinyar hannunta da ita da kallo, besan meyasa ba yana ganin yariny
ar yaji gabansa ya yanke ya fadi. Karasawa yayi ya rungume Ummihnsa yana kuka tana kuka jakadiya ta amshi yarinyar hannun ummusalma da norr dake bayanta.. Sosai jalalu ya rungumeta jikinsa yana kuka me tsuma zuciyar me saurare, kaf maaikatan gidan suka zag
ayesu suma duk suna kuka, banda Almuqri'ah wadda batasanma me akeyi ba tanacan part dinta tana fama da Isma'il da Abdoljalal yau rigima suketayi mata, da ita da nanny dinsu se fama sukeyi dasu.
"Alhamdulillahi yau jalaluna yadawo gareni ubangini ya A
msa Adduarh ta...ya ilahi na gode maka..."ummusalma ta fadi still tana kuka,,yayinda me martaba ya karaso inda suke shima yanzu labari ya taddashi har part dinsa, ya zubo musu ido bayanta. Shima ya fasheda kuka ganin lalacewar da Abdoljalal yayi, ya karaso
ya rungumesu su duka da jalalun da ummusalma, ya rungumesu sosai shima martaba yana hawaye.... Seda sukayi 30mnt a haka kana suka dunguma zuwa part din me-martaba hajiya salma ta kasa raba jikinta dana Abdoljalal, shima hakan, yau farin ciki mara misaltuw
a iyalan ne martaba suke ciki. "Meya sameka babana dukka lalace haka?'' Ummusalma ta fadi cikin damuwa da zallar soyayyar danta. Abdoljalal ya fashe da kuka sosai hadi da zamewa kasa ya shiga rokon mahaifiyarsa da mahaifinsa yafiya, nan kaf duk sukace sun
yafe masa. Ya kara fashewa da kuka sosai ya shiga gayawa iyayensa irin kaddarar da yake ciki ,da duk abubuwan daya wakana tsakaninsu da isma'il da dr mus'ab, duk haduwarsu Da Almuqri'ah seda ya fadima iyayensa komi be boye musu ba. Me martaba yaji dadin h
akan sosai, ummusalma ma taji dadin hakan, suka dinga sawa isma'il da mus'ab da Ahamad da nurse mami, and kande albarka domin jalalu be boye musu komi ba, sunji ddh sosai domin dasa hannunsu ne da kuma temakon Adduarh jalalunsu ya dawo garesu yanzu sede su
yi fatan Allah ya bayyana matar Abdoljalal din. Me martaba ya kira jsma'il ya masa godiya harda kuka, kana ya kira Mus'ab ya masa godiya yama ahamad dake kusa dashi godiya sosai tamkar ze tsugunna masa, har nurse mami seda me martaba ya amshi lambarta ya
kirata da kansa ya mata godiya nan take ya mata kyautar manyan kudaden data fita a talauci na har abadan. Me martaba ya saje kiran mus'ab yace yanzu yanada bukatar Ammah taxo yola ta zauna dasu.. Mus'ab yace toh..nan take yase mata jirgi ya kawota kasar
yola dmn tini mys'ab ya sanar da ita ba a ga Almuqri'ah ba sbda beda choice fole seda ya gaya mata ammah tashiga dmwa sosai amma ta dauki kaddara. Ammah ta iso duk suka taru a falon me martaba anata jajantawa juna, se yanzu Abdoljalal yaga Ammah ya miko
gaisuwa cikin girmamawa.... Nan de suka shagala a murna har tare suna tareda juna, se 12:am suka rabu, Ammah ta nufa part dinta da ummusalma ta ware mata akwai komi na bukatuwa a ciki. se girmamawa hajiya Ammah akeyi wato fatima tako ina. Duk abunnan da a
keyi Almuqri'ah bata sani ba, seda jakadiya tazo ta shaida mata itama tashiga murna sosai, domin tasan labarin dan Ummihn a gurin ummihn ta sanar da ita komi.... Jalalu yayi kwanan farin ciki a ranar , yasamu ya danci wani abun yau sbda Ammah data matsa ma
sa sosai. yanzu dmwarsa daya Almuqri'ah da cikinsa.
Seda saude tayi 1week asibitin mahauka anata zabga mata Allurori , kana aka gane ba mahaukaciya bace aka batta ta koma gidanta. Tana cike da haushin hajiya Abulle sbda ta kirata yafi sau goma amma sa
m taki xuwa tasa a fitar da ita daga asibitin mahaukatan. Saude dukta lalace ta zabge , amma bata daddaraba taci gaba da neman maganin tsafin dazata kara mallake Abdoljalal, taje wani guri akace seta bada jinin mahaifitarta ba bata lokaci tace ta bada itad
e burinta ta kara malleke Abdoljalal,, . washegarin rabar da saude taje gun bokan ta bada mahaifiyar aka kirata akace uwarta ta rasu, saude ko hawaye batayi ba itade burinta Abdoljalal yadawo gareta ta rama wulakancin dayayi mata. Tini hajiya saude ta fah
imci wacece Abulle yanzu, ta fahimci ashe munafukartace, ta fahimci duk wani plan da Abulle aka hada aka cuceta, bokanta da kansa ya gaya mata sbda ta babe musu da Abulle bata bashi kudin aikinsa ba. Saude tayi kuka kmr ranta ze fita daga jikinta nan take
ta zage bokan tass ta uwa ta uba, kana ta dawo taje gidan Abulle ta dinga zaginta sukayima juna tonon asiri a ti-ti har tsirara saude da Abulle sukayi suna fad'a a ti-tin Allah ta'alah. Washegarin dasukayi fad'an mijin Abulle ya saketa saki uku, sbda fada
nnan da tone tonen dasukayi duk yana nan yaji komi, ya kwace kaf dukiyarsa dake gurin Abulke, dole Abulle takoma gheton gidansu bata tsinanawa iyayenta komi ba datanada kudi,, Abulle tashiga tashin hankali kara misaltuwa ta dauki aniyar ko zata mutu seta z
ama ajalin saude, kisan rai takeso ta mata, sbda ta rabata da mijinta kuma ta rabata da kudadenta da kayan jikinta kawai ta fita a gidan Alhaji. Saude kuwa taci gaba dabin bokaye kan kace kwabo kaf kudadenta sun kare bata da komi , shagunantama da gwala
gwalenta dukta sayar tabawa bokaye kuma ba biyan bukata,, saude ta zama tamkar mahaukaciya ga wata uwar rama tayi, wanda yasanta adama bazece itace yanzu ba, babban bala'in gashi gabanta nata fidda wasu irin manyan tsutsotsi.... Saude tazama mahaukaciya tu
buran ganin hakan yasa sojojin dake aiki a gidan suka sata a daki suka kulle, sbda wari takeyi kuma gashi tsirara take yawo ko ansa mata kaya seta cire, se zonawa kanta asiri kawai takeyi , haukan nata ma mara kyau na dariya, duk abubuwan data yima Abdolja
lal se tonawa kanta asiri takeyi tana ihu tana dariya. A haka kande tazo ta ganta ta dinga salatittuka, dmn tazo gun Almuqri'ah ne domin ta rasa wayarta Kuma tayi jinya ne bataji dadih ba kwata kwata, ganin ba kowa a gidan yasa kande juyawa ta koma inda t
a fito tana mamakin lalacewar da saude tayi. "Duk abinda ka shuka wlhi shi zaka girba, yanzu tin a duniya hakki ke tambayarka base ka mutuba...kadanma kk gani saude..." Cewar kande da hakan ya tsananin mata dadih. "Karahen tika tiki tikkk,,yanzu meye riba
rki kinzo a zero zaki koma a zero,, ya Allah ka rabamu da tabewa, duk wanda yazo duniya ya mutu yashiga wuta yayi asara babba, sbda Allah ya gama mana sitira, inma ta yaye mu muka yayewa kanmu .." Kande ta kuma fadi tana kuka, tana tausayawa kanta, itama n
an data tuba wuyace tasata tuba, domin HIV saurayinta ya kwaso yasa mata, bata saniba seda ciwon yaci jikinta yanzu haka magani kawai taketa amsa tanasha shine ta fara gane ganta.
"Yola**
Kusan satinsa daya yau a garin yola ba karamin kulawa ummih
ke basa ba, sam basu hadu da Almuqri'ah ba, hidimar yaranta tasha mata kai, sbda zazzabi sukeyi again, ummih ce tace ta bari ta natsa kana sesu hadu da d'an