Showing 27001 words to 30000 words out of 86237 words

Chapter 10 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

25

*SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATI

ON*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

1



9





Shiga ya yi

ya zarce dakin Ayya ya tarar bata nan sai ya fito ya shiga dayan dakin, daman falo ne mai daki biyu,

Yana shiga ya tarar da ita tsaye , Bak'a kuwa zaune inda ta ajiyeta

Karasawa ya yi yana tambayar lafia?

Ta amsa shi cikin kulawa ta tambayeshi k

wannan iyalinshi

Ya yi murmushi dan ya san Walyn bata zo nan ba kennan wajen matar sarki ta je?

Ayya ta ce" Wardugu, zo ka yi mana fasara da y'ata ka ji? Ina son yi mata magana yanda zata fahimta aman ban lamunce maka ka rikita min ita ba ka ji?

Da

mamaki yake kallonta, daman shine dalilin kiran nasa? Kai? Yanzu Ayya ya zata yi idan baya nan toh?

Kai kawai ya dan girgiza ya karasa inda Agaishat ta kara rakubewa jikinta ya fara rawa ta nuna alamar tsoronsa take ji

Ayya ta ce" Wardugu ka yi wan

i abin mana, ka ga tsoronka take ji, bana so dan Allah

Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya kali Ayya ya kara kallonta, uwa uwa hummm

Karasawa ya yi ya dan rage tsayinsa yana kallon yarinyar, kokari ya yi ya saisaita maganarsa ya ce" me ke damun ki?

Kallonsa take ita kuwa, irin kallon nan na kana jiran gannin me za.ai maka

Wardugu ya dan rontse idannuwansa ya bude ya ce" kin ga, mu fa ba mayu bame, ba mugaye bane kamar yanda kike tunani, mamanki tace mu zo da ke, idan kika kwontar da hankalinki k

ika nutsu sai ina kai ki kina gaishe da mamanki, kinga dai yanda kuka yi da ita ko so kike a mayar da ke ne??

Tsam ta yi tana kallonsa bata bashi amsa ba

Ayya ta matso ta ce" me kake ce mata?

Wardugu ya kali Ayya ya ce" ba komai

Ayya ta ce" to

ka ce mata ta tashi ta shiga ta yi wanka , ko na yi mata da kaina ma

Ido Warsugu ya zaro, sai kuma ya basar, ya kaleta sosai ya ce" kin ce Sofo na koya maki karatu ko?

Kai Agaishat ta shiga daga mai

Ya ce" yawa, kuma sofo ya fada maki tsafta na c

ikin adini? Sai mai tsafta zai shiga aljannah fa

Agaishat ta kara gyada masa kai,

Ya fara jin haushin gyadegyadan kan nan, aman Ayya na wajen ta kasa ta tsare, ya tausasa murya ya ce" toh ki tashi ki shiga bayi, Ayya ta nuna maki kayan wanka ki yi w

anka sosai kin ji?

Kai ta kuma gyada masa ta mike tana kallon Ayya, tunda ta ji yace za yana kaita wajen Annarta zata gwada yi masu biyaya ......

Ayya da jin dadi ta rakata bayin ta kuna mata ruwa masu dumi sosai ta bata sabulu da soso sababi, ta bud

e bruch da maclean ta mika mata ta yi mata nuni da yanda zata yi ,

Har ta juya ta dawo tana nunawa ta ce" ki cuta jikinki lungu lungu sannan ki wanke tafin kafafuwanki kin ji

Kai Agaishat ke gyadawa har Ayya ta gama ta fice

A hankali ta tube kayan j

ikinta, ta yi tsaye gaban ruwan tana kallon yanda yake zuba

Da tsoro tsoro ta tara hannunta ta janye, ta kuma tara ta janye hardai ta yarda da ruwa ne ke zubowa kuma ba zai konata ba

A hankaki ta shiga tana bismillah a ranta ta yi tsaye ruwan ya shiga

kwararun mata a jikinta tun daga kanta dake da kitso kwaya daya tal har jikinta

Sai da ya gama dukanta ta dauki sabulun ta shiga gogawa a jikin soson tana jin yanda kamshinsa ke tashi tana jin dadin kamshin

A hankali ta shiga cuda fuskarta da soson nan

ta cudeta da kyau ta darwaye kafin ta shiga wanke wuyanta sosai da bayan kunnayenta da cikin kunnen ta gangaro hamatarta kamar yanda Ayya ta nuna mata ta daga ta kama dirza ta yi kasa ta wanke jikinta sosai ta bi ruwan nan ya shiga darwaye mata kumfar da

har ta zama baka dan tsabar datin dake jikinta, tana kallo ruwan na bin yar magudadar ruwa yana tafiya

Ta koma ta darwaye soson ta kara yin yanda ta yi , ta shiga saba sabulun a tufkeken gashinta na buzuwar usul ruwan nan na dareaye mata,

Abinka da tu

fkeken gashi wani wajen ya wanku sama sama aman cikin kam da datinsa daskare, haka Agaishat ta yi ta wanka tana sakewa tana jin kanta wani sakayau tana kara balbaluwa a cikin ruwan nan tana jin dadinsa abinka da ba sabanba ta wanke tafin kafafuwanta da abi

nda Ayya ta nuna mata nanma ta ga dati sai fita yake , har yatsarta ta saka ta debo datin tana kallo da gaske dati ne ta wanke da sabulu tana daga kanta sama ruwan na shiga idannuwanta yana kara ratsa gashinta da jelar ta sako tana yawo du idan ta juya kan

Fitowa ta yi ta dauki kayanta wa.inda sai a lokacin ta ji suna wani irin bugawa da ta rabu da datin jikinta, har ta shiga tunanin ko ta wanke? Sai wani abin yace mata idan kika wanke ki saka me kuma? Mayar da kayan ta yi ta fito ba tare da ta kashe pan

pan ba domin bata iya ba

Ayya dake zaune tana jiranta domin Wardugu ya tafi abinsa , ta mike tana fadin" eyah Agaishat ki cire kayan nan mana

Agaishat ta yi kasakai tana kallonta

Ayya ta dafe kai ta ce" wani yare kika iya

Agaishat kin iya frenc

ais? Angalais? Ko hausa?

Agaishat dake kallon Ayya ta ce" Ayya, hausa kadan kadan

Ayya cikin itama dan yaren hausar nata ta ce" ouf , mun samu na gaisuwa, ki fida kayan nan ki canza wasu kin ji

Agaishat ta gyada kanta tana kallon wa.inda Ayya ta

nuna mata, sannan ta juyo dan gannin a gaban Ayyan zata saka sai ta ga Ayya ta nufi kofa abinta

Ajiyar zuciya ta sauke ta tube kayan ta dauko wa.inda aka ajiye mata

Tsayawa ta yi tana kallon doguwar rigar abaya baka wace bata san ina ne gabanta ko b

ayanta ba sai dogon wando wanda ta daga tana ta jujuyawa irin na maza ta ayanna a ranta sai dai ba irin na mazan garinmu ba domin wandunnansu tamkar buhu........

Da daurin kirjinta tana tsayen nan Ayya ta dawo ta ga bata saka kayan ba

Nufota ta yi ta c

e" aa ya baki saka ba?

Agaishat ta mika mata ta ce" Anna ban iya ba

Ayya ta yi murmushi ta shiga nuna mata ta juya ta saka wandon da kyar domin ya yiwa jikinta kadan duda fadinsa da yanda kuma yake jayuwa,

Ta dora rigar ta kule yar igiyar dake ciki



Ayya ta juyo tana kallonta, ba laifi kayan sun amsheta sai dai sam wankan nan bai yiwa ayya ba , gani take bata wanku ba da saura duda yanda du wani jirwayi na turkudi da fari fat din nan ya fita

Mai ta miko mata ta shafa , ta miko mata turare ta t

ayata shafawa

Agaishat bata san tana sakin murmushi ba sai da ta waiga wajen madubi

A hankali ta taka ta karasa, hannunta ta mika ta taba madubin tana kallon kanta, a hankali ta juyo wajen Ayya ta ce" na gode Anna

Ayya ta karaso da dan kalabin ri

gar ta kama kanta da bai karasa bushewa ba ta saka mata ribom ta daure mata sannan ta nada mata dan kwalin ya zagaye fuskarta

Kwali ta dauko ta nuna mata da ta shafa , Agaishat ta ce bata iya ba , hakan ya sa Ayya ta saka mata idonta ya fara ruwa ruwa a

bin rashin sabo Ayya tace ta jure karta murje ta kuwa juren

Abin maskara ta dauka ta fitar da shi ta saka wani mouchoir (kyale) ta goge bakin jikin tas tas, ta dauki jagira mai ruwan baka ta gogoga a jikin abin ta samu ta caje girar bak'a, girar ta kwo

nta tsaf a inda ya kamata ba kamar da farko yanda take wawatse ba

Ayya ta juyata wajen madubin ta ce" Agaishat, Tsafta, kwaliya, ya zama wajibi ga macen da ta san ciwon kanta, ki rike wanka , ki kasance mai tsafta kin ji??

Kai Agaishat ta daga tana

kallon kanta da mamaki, tamkar ba ita ba, ta sawaya hancinta ya wani tafi zuwat, wai a nan Ayya bata gamsu da wankan ba jira take dai su karasa Niamey ta dauki lamarin a hannunta..........

Karfe sha biyu da minti arbadin suka fito daga masarauta suka nu

fi aeroport, ita dai Ayya bata san yanda wardugu ya yi ya samawa Agaishat waje ba bata tambaye shi ba

Sauran minti biyar suka karasa, suna zaune Ayya na kallonsa yanda ransa ke bace, bata ga Walyn ba bata tambayi inda take ba domin ba wani shiga lamarin

juna suke ba, bata san zuwanta ba sai da ta ganta daga ina kwana wani abin bai kara shiga tsakaninsu ba sannan dan yanzu bata ganta ba itama ba zata wani tambayi inda take ba , Allah ya basu zaman lafia ita da mijinta ba abinda ya shafeta da zamansu haka

kuma ba zata shiga dan wani gyara ba!

Ba.a jima ba suka mike domin an fara kiraye kirayen sunnaye,

Ita dai agaishat tunda aka haliceta bata taba gannin jirgin bama bale wai har ta shigeshi

Ta dai bi bayan Ayya da ta kama hannunta ta shiga nuna mata

yanda zata taka matatakalar ta hau suka hau tare tana kara rike Ayya da kyau dan kar ta fadi har suka shiga

Kallon tsarin cikin jirgin take a ranta ta ayanna ba irin na mota ba ,

Nan Ayya ta tsaya sai da Wardugu ya shige kusan madubin domin sam ya hann

ata zama a nan in dai tafiar jirgi zata yi, ita dai sai dai ta yi murmushi kawai irin yanda yaron nata ke sonta ke kokarin kareta har mamakinsa take ,

Yana shiga sai ta saka Agaishat ta shige tsakiya , shi kam bai yi magana ba domin ransa a kololuwar bace

yake, wai Walyn ta bi jirgin damagaran gobe ta bi na niamey ta karasa, shi zata nunawa zuciya ko? Han......

Ayya ma ta zauna ta ja ceinture ta sakawa Agaishat sannan itama ta saka bayan ta kashe babar wayarta ta android

Ba.a jima ba aka shiga fadin

a daura ceinture a kashe waya da yarurukanmu na niger da kuma french da inglish duka , bayan an gama jirgin ya fara tafiya wace suuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu ne saman doguwar hanyarsa har ya zo wajen hatsarin wato tashi da saukar jirgi ba,

Cikin adu.a a

bakin Ayya

Nan fa ake yinta domin abin tashin jirgin nan, kun san ko wanda ya saba sai ya ji cikinsa ya yi kasa bale wanda shigarsa ce ta fari kuma sha.af Ayya ta sha.afa da fada mata abinda kan iya zuwa sannan tace da ita tashi zasu yi sama, ita kuwa

a kauye baba sofo ya taba gaya mata akoy harda wani abin mai tashi sama a birni sunnansa jirgi ,

Ai gaba daya ta shiga jijiga ta damki cinyar wardugu dake gefenta na dama ta damko ta ayya ta bude baki ta........



🤣🤣🤣🤣

ku t

aro su kauyawa a birni

🤣😂😂😂😂😂

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is

to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

2





0





Ido Wardugu ya zaro, ya kai kallonsa kan hannunta wanda ke dauke da

dogayen akaifu domin ba wani cire su take son yi ba

sai baba sofo ya sakata gaba take yanke akaifunta sai tace nai ai susa take da su,

Wardugu bai gama tantance meye haka ba ya ji wani irin ihun da ya yi barazanar tarwatsa masa dodon kunne,

A tare suka

juyo wajenta shi da Ayya ......

Ayya cikin yannayin tashin hankali da yaren tubanci ta ce " Wardugu Wardugu tsoro ne take ji na manta ban fada mata ba, kuma ban riketa ba , mai yiwuwa bata taba ganninsa bama bale ta shiga;

Bak'a da jikinta ke bari

gaba daya ta kwalallo idannuwanta, daurin dan kwalin nata ya kunce , hawaye tuni sun kama zarya, ihu kawai take tana ambatan innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!

Mutanen dake kusa da su harma wa.inda ke dan nesa da su ne hankalinsu ya fara tashi du aka far

a jiyowa wajen su Ayyar da ayyar tambaya da alamun tsoron a fuskokin su....

Daga can kofar masu kula da passenger wata mata mai kulawa da bukatun passenger ta fito da sauri da dan sket dinta, ta sha kwaliya, tana dan sauri tana fadin kowa ya zauna kowa ya

kwontar da hankalinsa ba komai bane , sannan tana nufo wajen su wardugu;

Hannunsa ya daga na dama ya shafa sumarsa, a kasan zuciyarsa ayannawa yake wannan wani irin tashin hankali ne? Shi Wardugu da girmansa da irin yanda duniya ta san shi, shine za.a

yiwa taro da yar kauyen nan! Merde! merde! merde!

Juyowa ya yi wajenta, hannunsa na hagu dake kusa da ita ya saka ya janyota jikinsa, ya sakata a jikinsa da hannun nasa ya karkata fuskarta gefen hannunsa na dama , ya saka hannun nasa na damar ya yiwa

bakin nata mai ihu wata damka ...ai kuwa shiru kake ji ba ihu ba di kira da salamcewa sai dan mutsu mutsu wanda shima da ya kara riketa sai laf tamkar ta lafe ne a jikinsa. (WARDUGU kan keta)

Tambaya matar nan take lafia ? Me ke faruwa??

Wardugu gan

nin bakuwa ce yar amerika, sai ya ciro carte dinsa da hannun hagu dinsa ya nuna mata mai shaidar ko shi waye, sannan da lebensa ya yi mata nuni da mahaukaciya ce kar ta wani damu........

🤔

Ai kuwa ta shiga bada hakuri da iya yi, ta juya ta koma.

Ayya

sai faman ya cika yarinya take aman ya tsareta da ido ya ki yin maganama;

Nauyin da ya ji ta yi ne ya saka shi sasauta rikon, ba.a wani dauki lokaci ba Agaishat ta yi baci sai kace wata baby, bacin tsoro da tashin hankali, bacin wahala, gashi daman dar

en jiya ba wani bacin kirki ta yi ba dan tsoro da zulumi, sai ajiyar zuciya take saukewa du ta goge hawayenta a jikin rigar wardugu.

A hankali wardugu yake kokarin kwontar da ita jikin kujerarta, Ayya ta zabga masa harara ta jinginar da Agaishat a jikint

a tana kara tabata dan tabatarwa in ba suma ta yi ba.

Murmushi Wardugu ya yiwa mahaifiyarsa na alamun bada hakuri kafin ya jingina yana duba agogon hannunsa domin tafiar idan Allah ya yarda ba wata mai tsayi bace a jirgi tsakannin Agadez da Niamey.

A

llah ya sauke su lafia, Wardugu da kansa ya tuka motar da ya je da ita ya ajiye aeroport ,

Bai zame ko.ina ba sai gidan Ayya.

Suna zuwa Ayya ta yi hamdallah ta kamo Hannun Bak'a wace ke kallo da baki da hanci da ido gaba daya

Fitar da ita ta yi ta c

e" mu tafi yar gidan Ayyarta

A hankali ta fito itama kamar yanda Ayya ta koya mata ta bi bayan Ayya tana waiwayen Wardugu da ya fitar da kafarsa guda waje yana ta faman yamutsa gashin kansa, wayarsa ya ciro yar karama ya dannawa abokinsa kira wato docte

r DOCTER MU.AZAM

Yana dagawa ya ce" Ranka ya dade oga *Wardugu Marahut*

Wardugu ya ja tsaki ya ce" Mu.azam ni za ka yiwa rashin mutunci? Yaushe ka fara karya?

Mu.azam ya yi shiru, ......tamkarma ya kashe kiran.

Wardugu ya duba ya ga kiran na t

afia, ya kara karawa a kunnensa ya ce" kai!

Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya ya ce" abokina, ka yi hakuri ka ji? Jikina ne ya tashi aman yau nake fita asibiti in sha Allah da na huta sai na kamo hanya.

Wardugu da ya gama jin abinda ya fada, cikin mutu

war jikin da bai san ko na meye ba ya ce" me ke damun ka ne harda kwonciya hopital? (HOSPITAL)

Mu.azam dake kallon karin ruwan da aka saka masa ya lumshe idannuwansa, jiki a mace ya ce" idan Allah ya kawo ni zan fada maka koma menene,

Wardugu ya sau

ke ajiyar zuciya, bai bashi amsa ba ya katse kiran ya rufo motar ya tayar dan ya samu ya karasa gidansa ya huta

..........................

TIMIYA

Rana ce, karfe biyu na rana ne, aman da dan lulumi kamar yanda garin ya sa

ba,

A kasan innuwa suke zaune su uku suna yamutsa garin kwakwi da mai da yaji da manda (gishiri),

Fatimata ce mai kwadawar, Ayya na yiwa maryama susa a kanta

Mariama ce ta dago ta ce" Fatimata kar ki hade yajin nan duka ki ware min a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login