Showing 18001 words to 21000 words out of 86237 words
to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1
⃣
4
⃣
Bayan sun shiga garin timiya mutane suka ringa gudu suna kururuwa, wasu na fadawa gidajensu wasun kuwa na nufa gidan sarki wasu kuwa na kokarin neman hanyar da zata fitar da su daga garin ta barauniyar hanyoyi domin dai garin b
a wani rufe yake ba
Da mamaki suke kallon reaction din mutanen, Warsugu da sojan dake jansu ne kawai basu yi mamaki sosai ba duba da yannayin garin motar lafia dai bata shiga sai ta sojoji ko kuwa motar mugayen mutane masu zuwa su kai hargitsi su kashe
mutane
Kallonsa ya maida wajen Ayya wace ta dafe habarta ta wara idannuwanta tana mamakin nan yake mutumen kuwa? Aman gudun me suke?
Labari ya kaiwa sarki a yar fadarsa,
Tabas gabansa ya fadi da jin wannan lamari, ba a taba ba, mota har nan bata fa
ra shiga ba,
Mikewa ya yi da dukan kokarinsa ya tatara karfinsa inda dogarawa suka shiga kabara sunai masa kallon jarumi mai tausayin talakawansa da kuma kallon marigayi
Du a bayansa suke inda yake daga kafafuwansa da kyar yana kara tunkarar motar, gan
nin motar ta sojoji ce hankalinda ya kara tashi, domin dai shi ya san motar tunda yana shiga gari kai gaisuwa fada, kai harma ya tafi kasa mai tsarki, me ya kawo motar sojawa Timiya? Shine tambayar da yake yiwa kansa,
To ko dai sojojin ne a cikin motar k
o kuwa mugayen mutane domin idan sun kai hari ai suna karbe motocin sojawan
Wardugu ne ya bude gefen da yake zaune ya karbe hannunsa daga rikon da walyn ta yi masa ya diro daga cikin motar tsaye kan kafafuwansa
Jibgi, dankari, in ba wardugu ba zaka sh
iga kauye sai ka je da wando tree Carter? Sai rigar sojawa irin body din nan damatsunnan hannayensa a fili, yar karamar bindiga marar karan sautin harbi ce a kugunsa inda ya rufeta da wannan rigar ta jikinsa ya saka belt kalar kayan sojojin ya daure tam a
binsa
Kansa sanye da hula baka kalar wandon sai takalminsa sandal wanda ya daura abinsa
Sun karbe shi, sun amshi jikinsa, sun kawata shi
Taku ya shiga yi da karfin jiki ya nufi Sarki da ya ja ya tsaya jikinsa na bari, ta faru ta kare, jita jitar Ashta
kanwar matarsa ta kashe kanta wani ya kai birni an zo kama sirikinsa, mutuwar yau har kwana takwassss tabas wani ya kai, shikennan Alghabiitttt ya bani domin a hoto kuma a tv a birni Yana gannin wannan mutumen, an ce shugaban sojoji ne, shi da kansa ya zo
kama algabiit? Algabitt ya ji haushin rayuwarsa, tunanin da Sarki ke yi kennan inda ya daskare da tare da bugun zuciyar ko wani taku na Wardugu dan nufo shi (
🤦
♀ in ba kauyanci irin na sarki ba, a rasa mai zuwa kama Algabiit karamin kwaro sai Wardugu? Za
dai ka san waye shugaban sojojin nan hangensa kake!)
Yannayin shigarsa ta tabatarwa da Wardugu shi ne magabacin garin, dama irin haka idan an zo sarkin gari ko mai garin gari ko kuwa tsageran gari wanda ya gagari uban kowa ke zuwa ya tarbi mutanen, in d
a karar kwana a kansu ake farawa
Salama ya yiwa sarkin yana mika masa hannu sannan tar yana kallonsa ido cikin ido
Jiki na bari Sarki ya karbi gaisuwarsa yana tambayarsa hanya da zarcewa da magana kamar haka" mai gida, na san ba auren iri ka zo nema
a wannan jeji namu ba? Koma wa ka zo kamawa ka yi hakuri, a yi mana sasauci kar a kashe mu, a kama iya mutumen a tafi, ni kaina inada kankannan yara da mata, idan aka tsame masu ni wa zai ji da su?
Da mamaki Wardugu ke kallonsa , aman da yake Wardugu da
n duniya ne sai ya ce" Kai, baka san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi ba?
Ai kuwa gaba daya sarki ya haukace, jiki na bari ya saki kuka ya duka kasa ya rike kafafuwan wardugu ya shiga magiya
Ayya dake cikin mota ta dake lebenta na kasa ta ka
li sojan nan ta ce" ka karasa da mu, na san wardugu wani lamarin ya shiga na tsawatar masa tun kafin abin ya birge shi
Walyn ce ta juyo da sauri ta kalli Ayya, a ranta ta ayanna wai ta tsawatar masa, sai son ta nuna ita kadai ta isa ta juya shi, ta ja t
saki a ranta a fili kuwa ta ce" Hum tana tabe bakinta sosai
Sojan ne ya juyo ya ce" Hajia, ki yi hakuri, nan ya ce na ja na tsaya idan na matsa bai bani umarni ba ni da shi ne
Da haushi haushi ta shiga bude motar wanda sojan bai ankara ba har sai da
ya ji ta bude ya juyo da sauri , har ta sauke kafarta guda ta ga Wardugun ya dawo da saurinsa gefen da take
Yana zuwa ya ja ya tsara mata ya ce" Ayya maman Wardugu, kece ikon mai sanya Wardugu cire wando ta kai, Ayyana kar ki yi fushi kin ji? Koma mota
r mu karasa sai ki yi masa tambayar ai sarkinsu ne
Da mamaki ta saki baki tana kallonsa, sarkinsu? Aman me ya saka shi kuka da dukawa ya kama kafar wardugu?
Dan murmushi ya yi bayan ya saka mata lafayarta ciki ya rufe ya bada umarnin su karasa ind
a sarki yake
Suna karasawa Ayya ta bude tana shirin fitowa sarkin na karasowa ya dan risina yana gaisheta,
Ayya ta kalli wardugu ya dan sakar mata murmushi
Kai ta girgiza ta sauka sosai ta gaishe da sarkin kafin take fada masa abinda ya kawo su
Wata ajiyar zuciya ya sauke a bayane, ya ce" A garinnan Sofo mai bada magani kwaya daya mukeda, ya sufa sosai, gidansa da dan nisa da kasuwarnan sai mun shiga gari sosai
Ayya ta amsawa sarki da ba damuwa su je
A cikin motar nan sarki ya shiga inda y
ake dan hangen Wardugu ta madubi lokaci zuwa lokaci, ya yarda da ake cewa sarkin sojojin fa masifafe ne , bashi da dar, in ba rashin tsoro ba du irin yanda ake tsoron abzinawa da asiri shi a gabansa sai dai ma shi sarkin ya ji gabansa ya fadi maimakun na w
ardugun
ya fadi, lale yaron ya sha ya jiku ya tada kai , rabonsa da kuka tunda aka zo masa da sakon Gaishat ta tafi baban birnin niger inda ya yi tunanin shikenan ta gudu me ta bar shi.....(wani lamarin dan gyara nvl dina ne fa, sarkin abzin ba wasa walahi
🤣🤣
)
Basu zame ko.ina ba sai anguwar baba Sofo
Suna tsayawa mutane suka cika wajen, tunda sun ga sarkinsu a tare da mutanen ai shikenan sai suka sakin jikinsu da su harma ake matsowa a shafa motar sai a kwala ihu da yaren buzanci a ce" nima na taba,
mota mota a garinmu, mota har gidanmu,
Du ja sukai a lokacin da mutanen ciki suka fito gaba dayansu, suna masu binsu da kallo, girma da yannayin tsarin halitar wardugu ta basu mamaki, suna da mutane dogaye sosai sai dai ba masu fafadan kirji da manyan
damatsuna haka ba, sai kuma matan dake tare da mutumen da dayen sojan, kun san dai Ayya gwadar ado ce, bale Walyn farar mace alkyabar mata, walyn farar batuba ce tas tas tas, Ayya ce ma baka domin Ayya baka ce mahaifin wardugu ne farin batube shima tas ta
s tas , sai sojan dake saye da kayan sojoji komai harda bindigarsa da katon takalmin nan nasu da komai sai muzurai yake
Sarki ne ya amsa gaisuwarsu kafin yake kai dubansa bukar Sofo,
Bukar kanta ta tsufa du ta zuzube sai abinda ba za.a rasa ba, ga dati
sosai a dan nesa da wajen domin an yi rasuwa baka bata samu zuwa ta share masa ta gyara masa ba,
Ruwa kawai take zuwa ta dauko masa ta koma
Nuna masu wajen ya yi bayan ya samu ya shiga ya tarar yana zaune saman buzunsa da carbinsa yana ja ya kurawa w
aje guda ido yana ta istighfari(Allah ka bamu nitsatsen tsufa in muna da rai wanda zai kara kusanta mu da kai ya Allah)
Gaishe shi ya yi ya juya inda sofo ke bin kofar da kallon mamaki, me ya kawo Sarki har wajena? Kuma hayaniyar me nake ji haka?
Ku
shigo;
Sarki ya fada yana dubansu
wardugu ya ce" anya kuwa? Me zai hana ya fito???
Ayya ta kallo shi ta ce" Wardug.....
Da sauri ya yi gaba ya fara nufar yar bukar sofon a ransa yana ayyana ai idan Ayya ta nadaka toh fa tana yi da kai
Shishiga
sukai banda sojan nan,
Walyn na saka kanta ta yi baya tana kakarin amai da coshe hanci, a fili ta furta" kai ina , ba zan iya ba!
Ayya ta karasa a hankali kusan tsofon dake zaune ya zuba masu ido gaba dayansu yana mai binsu da kallo, ko gezau bai y
i ba daga zaman da yake sannan yana jan carbinsa cikin nutsuwa
A hankali ya amsa salamar Ayya da ta nufo shi cikin nutsuwa ta tsugunna dan nesa da shi aman suna facing din juna
A hankali ta ce" lokaci mai tafiyar da abubuwa, lokaci mai bayanna abubuwa
, lokaci mai rarabe abubuwa,
Baba tsufa ya zo haka? Allah ya sa mu cika da kyau da imani
Murmushi ya yi na gano wacece ita, tabas ya ganeta, idan ba zai manta ba shekaru sun kai talatin da suka shude ya sha kai mata magannin athsma na yaronta da bai f
i shekara hudu a lokacin ba tana karbar masa aman ya ki karbar komai da sharadin sai yaro ya samu lafia
Murya na rawa baba tsoho ya ce" y'ata ke ce a garin timiya? Ya jikin yaronki? Na koma ban same ku ba sai na yi adu.ar Allah ya sa ya warke
Ayya d
a murna ta janyo hannun Wardugu dake tsaye kikam ta ce" baba ai gashi, kana ganni soja ne, cikin ikon Allah magannin nan mun ji dadinsa, nima a raina kake, na nemeka Allah bai yi ba, kwanan nan na yawaita mafarkinka, a sifarka ta da hakan ya daga hankalina
na saka aka nemo min inda kake, shi ne na zo na yi godiya sannan na yi salama kamar yanda na dauki alkawari,
Baba na murmushi yana kallon wardugu wanda shima zuwa lokacin ya risina, yana kallon tsohon yana kidaya shekarunsa a ransa, ya yi imanin a kad
an ya linkasa uku da rabi,
Baba ya maido kallonsa wajenta, kafin yake bin dakin da yake zaune da kallo, ya yi murmushi bai ce komai ba
Ayya ta ce" Baba ka yi magana mana,
Baba ya dago yana dubanta ya ce" kaya y'ata, ki dubi dakin da nake ciki a
zaune a yanzu, me ya rage min? Me zan yi da arziki? Kyakyawan karshe kawai nake nema, shekaruna dari da ashirin da uku a duniya a hasashe mai yiwuwa na fi,
Kallonsa kawai suke suna masu adu.a a ransu, adu.a suke da Allah ya datar da su da irin tsufan n
an, wanda zaka yi ram da kai da carbinka,
Jikin ayya ya yi sanyi sosai , a hankali ta zauna a kasar dake dakin tana kallonsa, murya a sanyaye ta ce" haka ne baba, Allah ya sa mu cika da imani......
Aman na so na yi maka wani abin da zai faranta maka,
da zaka aminta ma da mun tafi da kai mun kula da kai
Baba tsofo da kansa ke kasa cikin rawaninsa ya dago yana kare masu kallo, ya yi imanin wannan matar da muguwa ce da bata bi bayan alkawarin da ta yiwa talaka futuk kamarsa domin ta san bai isa ja da i
ta ba domin zamani ya zama mai abu shi ne sarki, shi ya isa shi ke da magana ya dora doka, aman du ta manta ta tako ta ci gari da gari, ta ratso sahara du dan ta yi masa godiya sannan ta cika alkawarin da ta dauka,? Sannan ya san ba yar yankan kai bace dom
in ba da kansu suke nema ba kawo masu ake har gida, shi kam ji yayi gaba daya ya samu nutsuwa a zuciyarsa da shawarar sa,
Murya a sanyaye ya ce" tabas ina da bukata mau girma baiwar Allah, sai dai ban san ta inda zan fara ba, banma san ko za.a dace ba,
Hankalinta ta maida kansa ta ce" Mecece ita?????????????........
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we sta
nd and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1
⃣
5
⃣
Baba cikin yannayin damuwa ya ce" me z
ai hana na baki auren y'a?
A nitse ayya ta ce" Auren Ya baba?
Baba tsoho ya ce" eh, domin shi kawai zan nema a bada yarinyar dindindin ,
Aman baba wace yarinya ce wannan??
Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" yarinya ce mai tarbiya mai ladabi
da biyaya, yarinya ce mai nutsuwa, bata da kwaramniya, inda aka ajiyeta ta zauna kennan sai an ce ta tashi, yarinyar nan ina jinta a raina tamkar yar da na haifa, a kulun damuwana na mutu na barta a wannan hali, tana cikin halin matsi dan kawai Allah ya y
ita *BAK'A* sai dai ni murnar hakan nake domin fatarta ya sa har ta kai warhaka sai dai har yanzu bata samu mijin da zai aureta ba a kauye ta girma sosai shekarunta goma sha takwas a duniya ,
Jim Ayya ta yi tana kallonsa, kafin take cewa " me dinka ce
Baba?
Baba tsofo ya kalli Sarki dake kallonsa shima cike da rausayawa, da wani ne duda tsufanda in dai yana iya magana yana gane wasu abubuwan da gudu zai karbe makuden kudin da aka baza masa, sai dai shi bawan Allah ta yarinyar fake tare da shi tun ta
na yar shekara shida a duniya yake, irin tunanin da iyaye zasu kwana su tashi da shi na gannin yayansu sun samu mijin aure mai nagarta wanda zai kula da yayansu, toh haka baba tsofo yake kasancewa, du motsinsa itace a ransa, tambayar kansa yake ina? Ta yay
a? Wanene wanda zai rike masa Agaishat mudin ranta cikin mutuntawa da kauna? Ya hanga ya hango bai samu ba, har almajirinsa ya tuntuba aman ya watsa masa kasa a ido, hakan ya saka shi dukufa wajen kai kukansa wajen Allah, yana rokonsa da ya bili masa da ha
nya ta inda baya zato baya tsamani, ya bilo masa da hanyar da zata zamo alkhairi gareta,,,,
Sarki ya ce" kanwar matana ce, Sunnanta *AGAISHAT*
Kana nufin farar buzuwa? Ayya ta tambaya
Sarki ya ce" buzuwar ce tabas, sai dai ita wannan Bak'ar buz
uwa ce,
Ayya ta kai dubanta wajen Baba Tsofo da ya yi kododo yana kallonsu, kallonta ta maida wajen Wardugu dake tsaye ya tsareta da ido yana jiran jin me zata ce,? Ya san halin mamansa, ya san Ayya da daukarwa kai, !
Murya a sanyaye ta ce" Wardu
ggggggggg..........
Fuskarsa a hade ya ce" Lalalalala,
Daga haka ya tamke fuska yana kallon su
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa ta afka tunani (Tabas a al.adar Tubawa ba.a yiwa namiji auren dole, bake Wardugu, sannan idan namiji ya yi aur
e sai matarsa ta yi haihuwa kamar uku zuwa hudu kafin ya yi mata kishiya idan kuwa bata haihun ba sai ta dauki shekaru kafin ya yi mata kishiya, wannan haka
ne ba ja, haka al.adar garin yake, ) Ayya ta kuma kallon su, ya zata yi?
A hankali ta ce" bab
a, wannan yaron shi daya Allah ya bani a duniya,
Sannan bai jima da yin aure ba,
Ban ki ba, ina so idan da hali a bani yarinyar a matsayin yar rikona, yar amanata, in sha Allah zata ci abinda na ci ta kwonta a makwoncin da na kwonta ko wani iri ne, kafa
ta kafarta Har Allah ya bata miji, zan yi dukan abinda ake yiwa ko wace y'a na kaita gidan miji sannan zan bi dukan lamuranta a gidan miji mudin raina
Baba tsoho ya jima yana nazarin maganarta, baya shakun za.a bada AGaishat in dai sarki ya yi magana, d
amuwar shi ne: Agaishat zata so bin bakin fuska duda irin matsin da take ciki? Gida fa gida ne, sannan mahaifiyarta zata yarda da radin kanta a rabata da yarinyarta budurwa ba da wani dalilin aure ba ko dangi na jini haka kawai a tafi da ita tare da mutane
n da bata sani ba? Ko wannan karon ma isar za.a nuna mata a kuma kwace mata *Y'A*?
Duda haka baba ya kai dubansa wajen sarki,
Irin kallon da baba ke yi masa sai da ya saka ya ji kunya, ya ce" abinda za.a yi, zamu kama baba a je da shi da ku baki day
a ga mahaifiyar yarinya da mahaifinta, du yanda hali ya kama zuwa ya fi aike
Sun lamunce da hakan inda Wardugu ya kama baba a hankali ya mikar da shi sarki ya kama masa suka fito yana dan dingisa kafarsa har suka karasa wajen motar inda sojan nan ya bud
e wardugu ya daga baba a hankali ya saka shi gidan