Showing 12001 words to 15000 words out of 86237 words
kunyar haka .......
Da dare, bayan ya gama salama da kowa ya nufo dakin mai motsa zuciyarsa, ya sani ne ta san sarai itace da shi aman taga damar ya tarar da ta rufe kofarta
Ga mamakinsa yana taba kofar y
a tarar da ita a bude,
Turawa ya yi a hankali ya shiga da salama a bakinsa
Kanta ta dago duda tana jin kunya , ta yi kokari ta amsa salamarsa cikin nutsuwa tana dubansa
Da sauri ya karasa inda take zaune, da alama har wanka ta yi, na menene? Taba ji
kinta ya fara yi hankalinsa a dan tashe ya ce" GAISHAT baki da lafia ne? Me ke damun ki?
Dan bakinta ta turo, kafin take dauke hannun nasa ta kara turo bakin, murya a matukar kasalance ta ce" me ya sa ka zabi
aurena ta hanyar baiwa Abanna damar ya ci ga
ba da tafka tsiya a cikin garinka?
Dakatawa ya yi, ya yi tsai yana kallonta, a hankali ya rungumeta a jikinsa ya ce" ba dai za.a yafe min ba du irin hakurin da nake bayarwa? Ki gane dan adam nake mai cike da izgili da sabo a doron kasa,
Ajiyar zuciy
a ta sauke ta ce" ina so ka bar ni na je gida
Da sauri ya zabura ya cikata yana kallonta, muryarsa na rawa rawa ya ce" zaki tafi ki barni kennan? Yau kin fitar abinda ke cikinki shine zaki yi nesa da ni? Me yasa ba zaki yi mini adalci ba? Ina sane da du
ranar da zan zo gare ki sai kin sha madaciya dan kar ki haihu da ni, na so daukan mataki a kanki aman bana iyawa Gaishat, ki yi mini adalci mana
Dora dan yatsarta ta yi saman lebensa jajaji abinka da jan buzu ruwan sarauta ko na kauye dawisu ne, ta ce"
zama da kai yanzu na fara, ina son zuwa gidanmu ne dan kanwata ba lafia, muna son kaita asibiti, ka bani dama da ikon da zan yi bajinta a lamarin
Ajiyar zuciya ya sauke, ya rungumeta sosai har kamar ta yi ihun zafi, ya mikar da ita yana kallonta ya shi
ga warware lafayar da ta yane jikinta yanai mata kallon maita, haka ya idasa shigar da ita uwar dakanta cike da zumudi, wa ya isa in ba ita ba? Ita kadai yake tardowa har dakinta, hajia Gaishat mai sarkin garin *TIMIYA*
Kamar yanda ya yi alkawari
haka ya bayar da rakumi har goma, ya bata kudi masu yawa ya lamunce mata zuwa gari dan kai kanwarta asibiti inda gari ya dauka ana ta lale lale gimbiya ta karbi soyayar sarkinsu, abinka da kauye har yar salah aka yi ta murnar hakan ...................
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of rea
ders}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1
⃣
1
⃣
........Niamey.......
Gidan Wardugu
Kawata, dan Allah wai da gadke kike? Gaki ga yan kaso w
a.inda suka aikata mugun laifi? Gaskiya oga ya san kan mugunta
Walyn ta ja tsaki ta ce" ke, a dakin nan a nan suke fitsari, mata sai kawai ki ga an dage buje an tsirara fitsari a tsaye, basa kunya basa kyankyamin wajen , kai gaskiya Wardugu ni da shi
akoy tashin hankali, ba ni ya wulakanta ba, walahi sai na rama!
Me zaki yi masa? Wardugu ne fa? Kin manta waye shi? Ko mu da muke gari bama rayuwa da shi mun san waye shi, koda kina kema jinnin tubawa ba lale ki iya da rigimarsa ba, ya hada abubuwa da
yawa ne, kin ga shine da daya kwalin kwal a wajen iyayensa, shine Wardugu mai sunnan rikitatu a cikin ku, shi ne Batube, kuma shi ne Soja! Wardugu kakarfa, tsayaye, isashe, hamshakin......
Ke meye haka? Walyn ta fada tana kallon kawar tata,
Ta ce" ya
zaki tsaya kina koda min miji sai kace wata mai son min miji? Toh bara ki ji mu a yarenmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta cika wa.adin yin hakan, duka duka shekarana biyu da aure da mijina, ko na kai shekarun da yana iya kara wata Wardugu haramiyar wata mac
e ce a nan duniya, ban ki ba lahira idan ya dace da aljanna!
Murmushi ta yi tana kallonta ta ce" dadina da ke saurin hawa , toh yi hakuri ni ban kai abin can ba ..........
Bakinta ta tabe ta ci gaba da shafa cream dinta kan kurajen cizon sauron d
a suka yi mata cin balaki a cikin cel din nan, rabonta da ta saka kafarta kofa tunda abin nan ya faru, gashi ta rasa Wardugu a waya kwata kwata, !
Dogo ne fari kar, datijo ne christa sunansa Docter Lucien, kwararen likitan mata kennan wanda ya karanci a
bin kuma ya lakanta,
Allah ya taimaki su Anna sun samu gannin Docter Lucien a dasha kuma tausayin irin ciwon da ya gani bayan ya sha fada ya karbe su ya shirya shiga tiyata da ita a washe gari wanda cikin ikon Allah sai da ya dauki awa shida kafin yake
fitowa daga dakin tiyatar da ita shi ya hada zufa hakama masu kama masa wanda ba.a jima sosai ba aka gurgurota a gadon mararsa lafia aka kaita dakin da ake kontar da masu yoyon fitsari
Jigum suke zaune suna mamakin wai asibiti ce haka, su kam tunda suka
shigo garin a tsorace suke da yannayin tsarin gari, gini ne kala daban daban bene kai kasa na cin kudin masu kudin birni ....
A hankali ta shiga bukar tana dube dube kafin take kallo shi, a kwonce yake , idannuwansa a rufe kamar marar lafia
Da sau
ri ta karasa ta ce " Sofo?
Firgigit ya buda idannuwansa ya sauke saman kanta,
Kokarin tashi yake wanda da kyar abin tsufa ya samu ya zauna yana kallonta, murya na rawa irin ta tsufa ya ce" ina kika shiga? AGAISHAT zuciyata ta rikice na rashin gannin
ki, na damu na kasa baci, kin ji har zazabi nake dan bana ganninki yata, ina kika je kwana biyu? Kin san ke nake gani ina jin dadi, kece mai daukana tamkar mahaifi, zo zo na ji me akai maki? Wa ya taba min ke ?
Karasawa ta yi tana sakar masa murmushi
ta kamo hannunsa ta damka masa goron da ta siyo masa tun wancen ranar, murya a nitse ta ce" mun fuskanci matsaloli ne a gida Sofo, aman yanzu alhamdulilah mun gode Allah, Su Anna sun tafi birni Sofo, muma watarana zamu je? Zaka tafi da ni nima na ga birni?
Ajiyar zuciya ya yi jin ba abinda ya sameta na tashin hankali, ya lalubo karfen gurza goronsa ya mika mata ta mike ta darwaye ta dawo ta raba goron hudu ta maida hankali ta gurje masa shi tas ta mika masa ai kuwa ya hambuda yana tsotsa yana dan juya k
ai irin ya ji dadin goron
Can ya ce" Birni garuruwa,
A birnima akoy garin da dadi ne da shi sannan akoy wanda sam ba zaka so rayuwa ciki ba indai kai din bako ne
Birni tana tatare da abubuwan firgitarwa, murane sun yiwa abin hawa irin mashin mota yar
da, sun yarda da su suna halaka su
Tagumi ta yi ta ce" suna halaka su kamar yaya?
Ido ya dan zaro ya ce" zaki ga dan birni idan zai yi tafiyar da ba wata nisa ba, ba jeji ba, ba abin tsoro a hanya ba, dan tsabar sangarta da son jiki sai ya dare abin
hawa abinsa ya tafi a dan kankanin lokaci in abin ya zo da karar kwana sai ya juyeka tamkar tuwon masara nan zigib ka mace shikennan sai kiyama
Murmushi ta yi ta ce" toh ba kace ajali na tarda mutun du inda yake ba? Mutuwa ai kai ka fada min ba.a gudunt
a kuma ba.a boye mata, kuna Anna ta ce ita mutuwa lokaci ne idan lokacinka ya yi ba tsumi ba dabara zata daukeka ne ko waye kai ko me kake , kai ka ce min mutuwa mai yanke kauna, takan raba da da uwa, miji da mata, kuma kace min kowani bawa da ajalinsa a d
uniya
Tsofo yama ta murmushi yana dan barin jikin nan na tsofafi ya dungure kanta ya ce" haka ne Agaishat, Mutuwa gaskiya ce, Allah ya sa mu cika da imani
Ta amsa da amin...., ta ci gaba da fadin " ka ce a birni suna da wata kalar madara banda irin wan
nan tamu ta rakumi ko shanu? Ina so idan ka je birni ka kawo mini in kaiwa Anna ta sha ta ji itama
Kansa ya girgiza kawai, domin ya lura yau du labari ne a kunshe a bakin Agaishat, wai shi zuwa birni, shi da a yanzu salarma baya iya zuwa masalaci kaf
afuwa sun kiya, ga tsufa me zai je nema birni? Sai dai idan har kadarar makwoncinsa a can wannan kuwa ya san ko ta wani hali Allah zai kai shi..............
Dago kanta ta yi ta ce " ka san me?
Ya gorgiza kai alamar aa
Ta ce" wankana sau biyu, su
Mariama sun bani kaya suka saka na yi wanka
Murmushi yake na jin dadi, bai taba yarda a duniya Allah na hada jinnin mutun da mutun haka kawai sai a kan yar yarinyar nan,
Jinta yake tamkar jinninsa, sonta yake har bargonsa, baya son damuwarta, fatans
a Allah ya bata miji na gari komai talaucinsa domin ba zata kasa ratuwa da talaka ba, a hakan rayuwarta ta ginu, gidansu ba laifi su ba talakawanan tukuf bane domin dadaya ne gidajensu ke zagaye a garin aman ita rayuwarta irin ta yayan talakawan nan tukuf
ce masu wadatar zuciya,
Tana ta zubar ta mike ta shiga dan totona dakin kamar yanda ta saba dan dudubawa da kyau ta kashe kunama, domin kunamu na cikin kasa bakaken nan wa.inda idan sukai cizo in ba.a yi gagawar shan magani ba dafin na saurin kashe mu
tun , sune a cikin kasar garin kamar me, yan garin sun iya rayuwa da su, domin sun san inda zasu same su sun iya kashe su tamkar yanda ake kashe cirnaku,
Ta samu ta kashe wajen hudu ta cilar waje ta dauku tulu ta ce" sai na dawo
Hannu ya daga mata yan
a murmushi ya ce" Allah ya tsare ki
Yana kallonta har ta fice , ya samu kansa da zirarar hawaye, ya ce" ya Allah baka barin wani dan wani ya ji dadi, Allah ka sa , ka yarda, ka aminta , ka bani ikon gannin ta shiga hannu mai kyau kafin na koma gareka ..
.....
*Niamey*
Kan Anna kasa take tafiya domin bata son gannin irin yanda mutanen ke cuwa cuwa, a can kauye shiru ne, ba hayaniya , ba komai, sannan mutanen basu fi a kirga ba, hakan ya sa du idan ta fito daga dakin da Fatima
ta take koda dan ta leka ta ga safiya ce rana ne ko dare ne? Sai ta rikice
Ji ta yi ta ci karo da mutun, da sauri ta dago dan bayar da hakuri sai dai me, gani ta yi ya zaro idannuwansa yana kallonta, a hankali ya nunota da yatsarsa sai dai wani abin ya
ce masa Haba docter, haba docter, wacen koda jikin manyanta ya kamata ba zata koma haka ba, kuma ita batuba ce ba buzuwa ba, wannan kuwa buzuwa ce ta sha bakaken kayanta, kai bama zai yiwu ace ita bace,
Da sauri ya ce" yi hakuri baiwar Allah
Bata sa
n ta ina ta iya hausa ba, bata san ya aka yi ta ce" Ba komai yi hakuri kaima
Gaba ya yi yana dan waiwayenta, shi dai rabinsa da wancen dama familynta tunda aka hana masa aurenta, tun suna saurayi da budurwa, muryar wancen da wannan ba daya ba, sannan ka
i ka daina tunani kan matar nan mai yiwuwa matar aure ce
Da sauri ya kawar da maganar a ransa ya nufi office dinsa yana dafe kansa a fili ya furta" ya dace na ajiye aikin nan, na jima ina fama har jikin tsufa ya zo....
Tunda ta koma dakin ta yi shi
ru tana tunani,
Gaishat ce ta salame sallah ta juyo tana kallon maman nata ta ce" Anna me ke damunki ne??
Anna ta dan yi jim ta dago ta ce" wani yare na yi yanzu Gaishat, wanni mutun na kade ya min yare na bashi amsa tartar tamkar na iya yaren
Da mamaki Gaishat ta taso ta zauna kusa da ita ta ce" me kuka ce?????????
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United
we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1
⃣
2
⃣
Cikin yaren buzanci Anna ta maimait
a mata abinda suka ce
Da mamaki take kara kallon Anna ta ce" kuma baki san sunnan yaren ba?
Anna ta girgiza kai, da yannayin damuwa a fuskarta ta ce" ban sani ba, kuma da dukan alama ba yaren faransanci bane domin likita ya yi ta yinsa a gabana ba wa
ni fahimta nake ba, sannan ba yaren nan da muke ji wajen masu siyar da abinci a garinnan bane wato Zabarmanci, wannan yaren shima daban yake
Gaishat ta mike tana kallon ledar fitsarin fatimata ta ga bata cika ba ta ce" Anna, ko mu koma wajen mutumen ku
kara yin yaren? Anna ko haka na da nasaba da asalinki?
Nan da nan Anna ta ji ranta ya baci, asalinta? Kennan dai yayanta ba zasu daina daga mata hankali da wannan kalmar ba, rai a bace ta ce" ina ruwanki da asalina Gaishat? Ina
ruwanki? Tana gama fada
ta fice a dakin don ji take zuciyarta sai tukuki take mata na bacin rai
Da kallo Gaishat ta rakata, haka ne, komai irin dadin da kake ciki da Annarsu in dai ka yi gigin neman sannin wacece ita? Zata fatatakeka ne ko waye kai komai kusancinka da ita,
Ajiyar zuciya ta sauke ta karasa kusa da Fatimata da yanzu masha Allah sosai take samun sauki dinkinta ana kula da ita sosai, likitan karshe ne , du niger ta wannan fannin da shi muke takama!
A yannayin nishadi ta fito a gidansu, Abanta ya santal
o Amarya yar bariki, irin a nuna masa ana son yayansa har Bak'A bata kyamata tana bata abinci bayan ya cashewa maryama kudaden da ta yi rantsuwar ba za.a shiga da matar ba sai ya bada su ......Algabitt dai na rakashewa fa amarya , yayansa na gefe suna rayu
warsu , inda bak'a ta dan samu inci na kwana biyu a gidansu domin bashi da lokacin wulakantata yana malake da amarya yan uwanta kuwa sosai suka dan sasauta mata tsanar da sukai mata
Yar waka take da yaren buzanci tana saka sunnanta a ciki, fadi take" ni
bak'a yau wa zai so ni?
Bak'a nake wa zai rabe ni?
Yar bak'a haka ne sunana!
Dala biyar babu mai kaunata,
Ta yi dariya ta ce" ni ko a baiwa an rasa mai siyana a kauye da birni,
Agaishat kij cika muni....ta fadawa kanta sai kuma ta yi murmushi tana g
irgiza kai kawai
Algabittt, yar firit din yarinyar da ya auro ta furta kai tsaye
Shi kuwa da yake saman gadon karagarsa ya yi dadaya ya kallota ya amsata da um?
Tasowa ta yi tana juyi uwa bishiya ta karaso tana nuna masa gidan manta na shafawa
ta ce" ka san yanzu muma a kauye mun yi ido, yarinyar nan jikanyar mai siyar da fura nake kawance da ita, ita na baiwa kudina ta siyo min wannan man,
Na ga fatar Agaishat ta dameka, baka son yarinyar dan bakinta, ni kuwa na hango kyakyawar yarinya ce ta k
arshe kawai bakin ne ya yi mata yawa, dan haka ga shawara wace in dai ka yarda ka takurata ta yi a hankali zata dawo farar mace itama mu siyar mu samu kudinmu mu yi tafiyarmu birni mu je mu rakashe mu hau mota mu saka gilashi mu dangwali kaji
Wata zabur
a ya yi daga konce yana kallonta, irin maganar ta fara shigarsa, ya fara aminta da shawarar amaryar tasa
Kara jujuya masa ido ta yi ta mika masa ta ce" ka ga bude ka gani, ai dai ka san wannan uban farin da na kara ba nawa bane wanda har kake son samun
irina ............. ka yi mini ciki na haifa maka mai kyau ko? To sai fa wannan, ka bada na je na kai mata a siyo mata ta shashafa ka ga yanda bak'arka zata dawo yar dagwasssssss
Murmushi ya sakar mata ya jawota jikinsa ya ce" na yarda, in dai ta dawo f
ara sai in baki ki kai a siyo dan ubanta sai ta shafa ko bata so
Dan ture shi ta yi tana jin haushi a ranta, dan jaraba sai ya kama ya jajagulata shi ba wani nisa yake yi da lamarin ba du ya hargitsa mata tunani ya barta, haba ta yi aure ta bar jarumin
maza saurayinta, aman yau sai ta gayato sho gidan nan
Dan dukan kirjinsa ta yi ta ce"