Showing 9001 words to 12000 words out of 86237 words
auren da ka yi mini!
Idannuwa ya zaro ya daga wukar nan nasa ya. Nufota ya saro daidai ita sai aka yi rashin sa.a Anna ta saka hannunta ta tare wukar ta
yi mata muguwar sara a gefen hannunta ta yanketa sosai nan da nan jini ya bale
Ihu yayan suka kwasa, da sauri mariama ta karbe wukar ta yi jifa da ita ta hayayako masa da mugun bacin rai da nuni da zata iya aikata komai ta ce" ka je, kar jini ya biya
jini!
Juyawa ya yi da sauri yana mamakin Kaf yayansa idan ya yi magana a da jiki na bari suke aikata abinda yake so aman kwanakin nan yana haduwa da hari kala kala da wajaje daban daban a cikin yayansa bale Mariama yarinyar na da zuciya ........
Labari bak'a ce labari ne kirkirare bisa lamarin da ba kirkirare ba, labarin yana tafiya ne bisa gaskiyar lamarin abinda ke faruwa , tabas na shiga kuma sai na fada......ku mu je zuwa a labarim bak'a ce in sha Allah
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫
🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://
www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
8
⃣
Yana fita Bak'a ta cire daurin dake kanta ta daure hannun mamansu da fan kwalin du suka zauna jigum jigum suna kallon Fatimata
A hankali ta dora kanta kan cinyar mamansu da take jin zuciyarta na yi mata nauyi sosai ta ce" a ranar da aka dora ni saman Amale (Rakumi) daga ni sai mata hudun da suka zo a matsayin fagin mijin da aka aura mini muka tafi
Mun shiga garin agadez d
aga nan muka dauki hanya muke tafia tamkar ba zamu tsaya ba
Sai da muka je Damagaran daga nan muke mike muka dauki hanyar kano
Muna zuwa kanno muka kwana guda muka dauki motar asuba suwa Abuja
Tafiyarmu tamkar ba zata kare ba, tsakanina da su ido ne s
u basa jin yarena nima bana jin nasu ya kasance muna tafiyar kurame ne sai dai abinda na lura da shi tamkar masu jin haushina domin ko abinci zasu bani sai dai su wulo mini su fadi wata kalma sannan su yi mini nuni da in ci
Ba mu mu isa garin nan ba sai
da safe domin da mukai dare muka tsaya muka waye a wani garin kafin mu karasa
Gida ne tafkeke, ya tsaru, ya hadu iya haduwa
Muna zuwa kowace ta yi tafiyarta aka barni a wani tankamemen falo ina zaune ni guda
Ban jima sosai ba na fara gannin wasu ma
ta masu kyau suma kowace ta sha kwaliya sai baza kamshi take sun fifito sun layu saman kujera gefe da gefena hakan ya saka na takure waje guda
Ba.a jima ba wanda aka aura min da sunan mijina ya fito ashe yana cikin dakin du zaman nan da na yi ya zo ya
zauna saman kujerar dake kallon tamu ya dora kafa daya kan daya
Walahi Anna mutumin sam ba annuri a tare da shi, mumuna ne, garjejen kato ne fuskarsa ba anuri ba fara.a ba haske ko kadan a nan ya kuna taba domin ba sigari bace taba ce ya kuna ya shiga ja
wace nan take wajen ya garwaye da warin kwaya
Wasu maza ne suka fara shigowa, suka zauna suma inda suke hangen mu da kyau abin mamaki matan nan sai su ringa mukewa daya bayan daya su jujuya gaban mutanen nan wasu har su dakan masu duwawu su mamatsa a ga
banmu a gaban kowa shi kuwa yana hakimce idan mace ta yi maka sai su hau ciniki cikin jarshen turanci a dauki mace a tafi da ita kwana wato Bariki
Nan wani yace wannan fa? Wato ni domin sun ga sabuwa ce a wajen
Da sauri na mike domin nunoni ya yi kafin
yake yin maganar, koda ban ji me yace ba idannuwana sun nuna mini abubuwan da suka faru na ga komai na gane komai
Magana ya yi masu wace ban san me yake nufi ba suka gama kasuwancinsu ya cashi kudinsa sosai kafin suke tafiya
Sai da ya gama shaye sha
yensa ya taso kusa da ni sosai da muryar mashayi ya ce" ke fa sai na yi maki filafila dan kuwa an caje ni kudi kafin a bani ke kuma dan iskanci aka kawo ki daga ke sai wannan bakin kayan
Tashi ki tube
Da mamaki nake kallon shi, in tube, wai ina ne n
an? Me hakan ke nufi? Matan nan su waye? In tube haka kai tsaye ai ko matarka ce ni koda mun saba da sannin juna fitsara ne gatsal ka kale ni ka ce mini tube
Mikewa na yi da yarena na rufe ido na shiga zazaga fitsara ina son sannin inda ya nufa
Ta y
i shiru tana sauke ajiyar zuciya kafin take kara sakin wani kukan mai karfi ta ce" Anna matan nan da suka fita bayan ya amshi kudaden karuwanci da zasu fita su kwana da karti ashe gaba dayan su suna zaune a matsayin matansa mace har bakwai ni ta takwas cik
insu ba daya ta yarwa sannan ba daya da ta san hanyar gidansu
A wannan ranar da katsa ya dake ni kafin yake zuwarmini da wata irin sufa yayi anfani da ni ba imani yana gamawa ya wawatsa kafafuwana ya goge gaba daya najasar nan ya shafe a fuskarsa harda ji
ni jinin nan ya side hannayen nasa ya fice
Anna a wannan ranar.kafin gari ya waye sau tara yana zuwar mini
Mariama ce ta dauko kwan fitilar sosai ta haska wajen kafafuwan Fatimata, ruwa ne ke yawo wanda ya saka Mariama cewa" Anna ruwan nan kuma na mene
ne?
Fatimata ta ce" fitsarina ne ba ruwa ba, haka fitsari ke zubar mini bama na sannin yana binna
Anna ta fashe da wani irin kuka kafin ta ture kan Fatimata ta mike ta yi dakin yaren da sauri hannayenta duka biyu saman kanta, *YoYo, YoYon fitsari Fat
imata ke yi*!
A wannan rana yanda suka ga rana haka suka ga dare inda suka cure gaba dayansu waje guda ba mai yiwa yar uwarta magana sai dai suna bin juna da ido , nan Mariama ta mike ta dauko wata leda baka baba ta shinfida ta dauko zani ta shinfida ta
kallo yan uwanta ta ce" ke fatimata taso ki kwonta saman nan, ke Agaishat(Bak'a) tafi wajen Anna, kuma ku taso mu kwonta dare na tafiya kar safiya ta yi mana a nan
A hankali ta samu ta lalaba ta hau, suma du suka samu waje suka kwonkwonta ba dan zasu s
amu yin bacin ba, sun dai yi zuru ne domin Fatimata bata gama basu labarin irin ukubar da ta sha ba aka ga fitsari na binta hakan kuwa ya tayarwa da Annar hankali bata ma tsaya ta ji sauran zancen ba
Anna ce duke kanta kasa ta kai sujada tana ta sheka k
uka ta ce" ALLAH ka san wacece ni, kai ka halice ni, ya Allah ina cikin jarabawarka tun daga yannayin aurena har zuwa yau, na rasa me ke daure da ni da wannan mutumin ainahi Allahna idan ba a cikin sallah ba bana iya tuna wacece ni, menene tarihina, ina da
yan uwa ko haka nake ni daya? Bana son a yi min maganar ko wa ya kawo min zancen zan nuna bacin raina ne, Allah yayana, ka bayannar sauran, wa.inda basu da lafia ya Allah ka basu lafia, wa.inda yake niyar aurarwa dan samun abin duniya Idan da alkhairi a c
ikin auren ka tabatarda, idan kuwa ba alkhairi bane Allah kai ka yi shi ka hana, ka hana ya Allah Allah sannan ka yaye min duhun dake cinkushe min ganina
Ta jima tana kai kukanta wajen Allah kafin take mikewa ta yi tahiya ta salamce ta dora adu.a tana t
a yawaita istigfari domin ba abinda ke saurin yaye kunci irinta
Da safe tana tashi ta dauki sansani (tabar buzaye) a cikin nata ta matsa a bakinta ta yane jikinta ta buga safiya ta fice a gidan
Zugum suke ba mai yiwa dan uwansa magana har wajen ka
rfe tara Anna bata dawo ba, Aba daman tun cikin daren nan ya fice basu san ina ya kwana ba sannan bai dawo ba, sun zubawa sarautar Allah ido ne kawai
A hankali Bak'a ta kali gorin tsofo, ta mayar ta kule a harshen zaninta a ranta take ayanna bawan Allah
ko a wani hali yake? Ko an dauko masa ruwa? Tabas yana cikin damuwar rashin ganninta yau har za.a kwana biyu, sai dai ba zata iya fita ta bar gidansu a wannan halin ba, a hankali ta rike goron ta ce" sofo ina nan lafiata klau, ka ga na saya maka goro ma k
ar ka damu ina nan tafe wajenka
..........inna Anna ta tafi?????
Gyara kimtsi, mai zamani dan sarki jikan sarki, Buzu jinnin sarauta, yaro mai zamani, taka lafia bijimin sarki, taka lafiya gagara gasa, kai ne na uku baban Rabatima, ka shigo a hank
ali yarima, taka sanu sanu sarkina
,
Kirarin da jakadiya ke yi masa kennan tunda ya tunkaro dakin mahaifiyarsa,
dan dakatawa ya yi har ta yi gyaran murya kafin yake saka kai da salama a bakinsa
Dago kanta ta yi tana murmushi ta amsa shi, a hankali
ya karasa yana wata irin tafiya idan ya daga kafa daya kafin ya daga dayar sai ya jima
Dukawa ya yi har kasa kansa kasa ya ce" ta gode Anna, ta gode Amy (Wato mahaifiyar Wardugu aminiyar matar sarki....da Amy suke kiranta bisa umarnin mahaifiyarsu,)
Murmushi take sakar masa kafin ta ce" oh son tashi mana, amynka ce fa ko dan ka daina zuwa wajena ne?
Yana murmushi ya mike ya zauna saman kushin dake wajen cikin nustuwa suka shiga gaisawa da harsen freinsh domin ita ce kawai yaren da zasu yi su jima
suna hira cikib gane abinda suke fadawa juna
Dan jim ya biyo baya kafin yake cewa " Amy ya labarin Oga ne? Na yi na yi ya siyar min da wata mota aman da yake yan rigimar a kansa cewa yayi aa motar ba ta yara bace, ki ji fa Amy
Dariya suka saka gaba d
ayansu, Ayya ta ce" Wardugu, Wardugu baya jin magana Aghali, sai hakuri da murdaden halayen Wardugu
Mahaifiyar Aghali matar sarki ta ce" Kawata, wai ina labarin aban Wardugu ne? Ni kam ina mamakin lamarinku, kawai daga wannan dan laifin?
Ayya ta dago
tana kallonta, a ranta ta ayanna ban ga laifinki ba, ku baku dauki haka a matsayin laifi ba,
A fili kuwa ta ce" manta
Murmushi Mahaifiyar Aghali ta yi, Ayya akoy mulki wannan da gidan sarauta take da an ji jiki domin mace ce mai mulki da isa, ga jan
aji, da yake an dauko hirar da bata so daga haka ta katse hirar ta mike tana yi masu salama dan tana son shiga ciki ta kirayi number Wardugu rabonta da shi tunfa suka karaso jiya ba shi ba labarinsa
...........rashin Comment ne kawai zai saka ni
daukan matakin siyar da novel din nan ko na tsayar da shi,
😊
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand an
d succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
9
⃣
Ayya na zuwa dakin da aka sauketa zauna ta jingin
ar da bayanta jikin kujera ta daga kanta sama,
Ta jima tana tunani, kafin take sauke ajiyar Zuciya a fili ta ce " *MARAHUT*, ina ka shiga? Ka san komai ka tarwatsa rayuwarmu, Marahut ina tausaya maka sai dai mutuncina darajata ba zan yarda ka zubda mini
ba! Ka zabi wancen rayuwar ko? Ba komai ka je sannu duniya zata koya maka hankali,
Ranta ne ta ji yana suya, yama aka yi ta tabo mata wannan mikin, ta sani da gangan ta tuno mata da maganar domin ta fi kowa sannin abinda ya faru, ita kadai sai Wardugu s
uka san takamaimai abinda ya faru aman zatana tuno mata da shi , ita so take sai ta yi hakuri bata san ta rufe babinsa ba kuma ko da jaraba sai ya saketa dan bata fatan idan ta mutu ya kasance shine alwalin gawarta (Toh fa
😳
tubawa akoy zuciya)
Aghali
, dan me ba zaka kara aure ba? Matanka biyu yarka daya mace sai matan daki , ko a cikinsu har yanzu ba wace ta samu ciki bayan ina kula da irin zubin da ake maka ana canzawa du wace ta kwana biyu, ko dai baka zuwa inda suken da gaske? Domin na ji kishin ki
shin cewar wannan matar taka ta shanye min kai,
Mahaifiyar magajin sarki ce ke fada kan ya ki karo aure bayan tana son ya tara yaya
Murmushi ya yi ya ce " zan kara aure, ki kwontar da hankalinki,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take miko masa yar akwa
ti tana murmushi ta ce" ka ga Amynka ta kawowa wannan mumunar ( wato yarsa jikarta)
Hannu ya saka ya bude ya gani, sarka ne da yan kunaye na zinari masu kyau sosai kirar yara, murmushi ya yi ya ce" zata je ta gaisheta sannan ta yi godiya........ wannan
kennan
Sai da ta bude lulubarta suka ga mace ce bayan ta fada masu ita mahaifiyar Gaishat ce , suka je suka shaidawa sarki ya bada izinin a shigar da ita bangaren Gaishat din yana mamakin zuwanta da fadawa zuciyarsa ba lafia ba domin shekara kusan t
akwas da aurensu bata taba takowa ko aiko da kannen Gaishat din ba duda tana yarta ta fari, itama bata wani zuwa gidan du ta takura rayuwarta da tsoronsa ta mayar da kanta ta daki duda kuwa irin yanda yake daukaka martabarta fiye da iyayen yayansa
Tana
shiga dakin ta nemi waje nan kasa ta zauna ta sada kanta , da kujeru da komai aman ta fi fanewa zama a kasan nan
Da sauri ta fito jin sakon Sarki wai mamanta ce ta zo
Tana fitowa ta karaso da gudu ta riko hannayenta a rikice ta ce" Anna lafia? Anna wa
ya mutu? Anna na shiga uku me yake damunki? Anna me ke faruwa? Me aka maki Anna? Anna.....
Shiiiiit anna ta fada tana dora yatsarta saman leben Gaishat, itama tana kare mata kallo, yarinyar bata wani karu ba a jikinta na da, sai dan girma daga fuska da
ta kara, duda jikinta bai nuna alamar wahala ba aman tana da rama, kanta daure ,
Kunyar Gaishat din ta ji ta kamata, dole ta rikice domin bata taba zuwa alkhairi ko tashin hankali ba, itace ma ke yin kokari idan ta san Abansu baya gari ta leko a tsaitsay
e ta koma shima ba wani zantawa suke sai dai su bi junna da ita
Tunani ta afka shin fada mata zata yi ko kawai ta yi shiru ta juya
A hankali Gaishat ta dago habar mamanta, dara daran idannuwanta na gado ta saka cikin nata ta ce" Anna, me ke damunki? Ki
fada mani kin ji? In sha Allah ko bani da maganin damuwarki zan taya ki da adu.a
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishat, Algabitt ne....ya samarwa su Mariama mazajen aure wa.inda bama a niger din suke ba, kin san bani da labari tghmass ita a niger
din ma aka bayar da ita, jiya Fatimata ta dawo, mariama fatimata ta kamu
da cutar rashin rike fitsari , kin san ba maganinsa a kauye sai asibiti, baki ga fatimata ba, ta dawo wata iri,
Ga irin tsanar Agaishat (BAK'A) , ya sako yarinyar a gaba tamkar ya ka
sheta dan ya san gardawan da yake zuwa da su dan zaben mata ba zasu zabeta ba, shi ya sa nake kara barinta da datinta, mai yiwuwa ita ta tsira daga muguwar rayuwar da yake saka mini yaya
Shiru ta yi kanta sade tana gursheken kuka daga ita har Gaishat di
n,
Ajiyar zuciya Gaishat ta sauke ta ce" Anna zan zo gidan kin ji? Sai mu samo abinda ya samu mu samu shiga asibitin
Ido Anna ta zaro ta ce" ta yaya zaki fita Gaishat?
Gaishat ta yi murmushi ta ce" Anna, ki daina damuwa da damuwata, ni na dorawa k
aina, tabas Aba ya yi auren dole da mutumin da bana so, mai mulkin garina aman shi mutumen jira yake in nuna bukatata a wani abin jiki na rawa yake yi min ko menene , bana tunanin fita zata zama damuwa tsakanina da shi
Anna ta sauke ajiyar zuciya, ta da
go habar Gaishat ta ce" me ya sa toh ba zaki kyautata masa ki kontar da hankalinki ba? Shekarunnan ba fa kwanaki bane, ya ci ace kin zubar da komai kun fuskanci juna, ke Allah ya taimake ki kina cikin konciyar hankali kar ki bijirewa Allah mana
Gaishat
ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Anna na kara nade jikinta da fuskarta wato dai tafia zata yi, ita ba zata ki su dawama a nan suna hira da mahaifiyarta ba
Tana ji tana gani Anna ta yi mata salama ta fice a gidan tana fatan kar ta hadu da wani a kusan
gidan yarta ta fari , haka kawai take jin