Showing 54001 words to 57000 words out of 86237 words
fadar adini ku zabawa yayanku iyaye na gari,
Nan fa aka shiga tashin hankali, yarinya ta zo har gida ta tsire ni, nan ta yi ikirarin cewa" AYYA kike ko wa?
Kin dai ganni, kin ga yanda nake, nice farar mace , kwakwa! Dole na shigo gidanki ko a sarakuwarki ko a kishiyar ki!
Abin ya bani mamaki, zuciya ta kama ni na tunkareta kafin take ankara na damketa, ina faman ihun sai na nuna mata ruwa ba sa.an kwondo
bane malalaciyar banza da wofi sai ga Marahut ya shigo da sauri
Kwaceta ya yi daga hannuna kafin yake fadin" ke Zannaba, baki da hankali ne? Kike ikirarin yarinya bata da tarbiya ke kina iya rantsewa waye malamin waye dalibin tsakaninta da dan naki? Ki
shiga tatayinki ki daina abu tamkar wata yarinya karama!
Agaishat , a wannan rana, a gaban wannan yarinya Marahut ya wulakanta ni, ya yi min tas abinda bai taba shiga tsakaninmu ba,
Ke dai kwana biyu tamkar kura ta lafa, domin Wardugu da ya ga na n
ace sai kawai ya basar ya yi biris ya shiga wata sabgar gaban nasa inda ya fara kula Walyn,
Ba.a wani jima sosai ba, domin ba .a yi wata hudu tsakani ba Marahut ya zo da maganar zai yi aure,
Agaishat ban wani nuna halinmu na matan tubawa ba, na ja aj
ina na yi masa fatan alkhairi, na shiga rokon Allah da ya rufa min asiri kar a je dan haihuwana ya tsaya ne wani abin zai tunkaro ni,
Sannu sannu sai abubuwa ya fara bilo mani, halayen Marahut suka shiga canzawa,
Ya fara cika dare sosai a waje kafin y
a shigo, ya dawo ya fara kin cin abincina sai yace baya jin yinwa tamkar wani inji,
A hankali ya kaurace min,
Na sha zuwa na duka nace da shi" menene damuwar? Wani abin na yi ne? Dan Allah ka yi hakuri , har ka manta alkawarin fa ka yi min? Marahut kace
nice lumfashin ka, ka yi hakuri ka dawo min kamar da, ni ban wani hanaka aure ba, aman kar ka tayar min da hankali,
Marahut sai kawai ya yi min murmushi ya mike ya fice,
Du abin nan Wardugu bai san ubansa zai kara aure ba sai wani lokaci ya ji a gari
, a lokacin ya garzayo gida da sanyin safiya ya tambayi uban, ashe auren ma a ranar sauran kwana biyu ni banma sani ba,
A wannan ranar na ga tashin hankali, na ga rikici, domin Wardugu idannuwansa sun rufe hakama na ubansa, ke sai da na fita a guje na
kira direbobi da masu gadi da yaren gida du suka shigo suka yi kokarin shiga tsakannin uban da dan dan kuwa Wardugu ya rike wuka hannunsa yana ta balaki!
Agaishat, wannan bai isa ba sai da aka shigo da amarya Aisata, aisata yar buzaye, aisata yarinya ky
akyawa,
A ranar wardugu ya yi dan karamin hauka, ya ja iska ya zo kusan babansa ya ce" aban Wardugu ka sake ta, ka rufa mani asiri ka saketa , kar ka yarda wani abin ya shiga tsakaninka da ita, Aba, wannan bata da tarbiya, bata da haramun! Abanna ya zak
a kawo macen da ta gama talatarmin da kanta a irin yannayin da ta fado duniya ni danka a matsayin matarka? Haba Abana, me mukai maka da zafi haka?
Marahut ya dube shi ya ce" ita ba mutun bace? Kun haihu da ita ne? Na yi niya ina sonta na aureta da kudi
nka ne? Ka bini
a sannu Wardugu, ni na haifeka kar uwarka ta zigaka ka kauce hanya!
A lokacin ni tuni na fara gannin jiri, ni Marahut? Na sha dukan kirji nace ni mijina dan goyo ne, ba zai wulakanta ni ba, sai gashi haka ta faru, ni ba aurensa ya dame
ni ba, tau da gobe ai sai Allah Allah wacece ni da zan ce ba za.ai min kishiya ba? Damuwana irin auren da ya yi, ya yi shi dan ya nuna min iyakata? Dan ya wulakanta ni? Ko wani abin ke tsakaninsa da yaronsa mai zafi haka?
A lokacin Wardugu ya fara wani
irin numfashi, idannuwansa suka shiga canza launi zuwa ja, suka cicika da kwallah, ina gannin hakan na tisa shi gaba da kyar na samu muka shiga motarsa na ja muka nufi gidansa,
Muna zuwa muka tarar da Wakyn ta zo nemansa, a nan ya sauke haushin kanta domi
n sai da ya bala mata hannu du ya kusan canza mata halita baiwar Allah da kyar aka kwaceta,
Kin ji marabina da gidan Marahut domin akai ruwa aka yi iska Wardugu ya hau, ya gindaya rantse rantse, ya juye, nima fushi, mamaki, tsoron lamarin maza ya saka n
a yi watsi da shi na rungumi yarona wanda na san a duniyarnan ni ce duniyarsa ,.....
Ayya ta karasa tana dan shafa kan Agaishat,
Agaishat ta dago fuska shabe shabe da hawaye,, tana duban Ayya , ta sani bata da damar da zata iya tofa wani abin a wanna
n lamari domij ta yi imanin ba komai Ayya ta fada mata ba, tabas ta boye wani abin ko dan karancin shekarunta,
Sai dai wannan lamari ya tuna mata mahaifiyarta, Anna baiwar Allah, yoh ita haka rayuwarta ta kare fa, kuma bata da wani mai dauketa ya matsata
daga wajen da ake cuzguna mata, ita bata san bama marainiya ce ko yar dangi, bata san daga ina ta fito ba, ba abinda ta sani,
A hankali ta mayar da kanta saman cinyar Ayya , daidai lokacin da Wardugu ya shigo dakin da salama,
Daga inda take kwoncen nan
take kare masa kallo, tabas wardugu ko bashi da ko sisi sai mace ta yi haukansa, ko bashi da hali zai mitsa zuciyar mata, dan farin batube mai zamani,
Idannuwanta ta lumshe a hankali wani hawayen ya kuma zubowa daga gurbin su ta mike a hankali bayan ta
share hawayen ta kai dubanta wajensa , kanshin turarensa ya cika mata hanci,
A hankali ta ce" ina yini,
Gaisuwar da tunda suka daukota daga timiya shi dai bai taba jin ra yi masa ita ba, tsumamun idannuwansa ya zuba mata ba tare da ya amsata ba, yana
kallonta har ta fice a dakin dan basu waje su tatauna ta nufi wajen Mu.azam dan gannin ko ya ci abinci?
Ayya ce ta lakato shi tana yi masa murmushi tana saisaita kanta ta ce" dan gidan Ayya, sannu da dawowa,
Wardugu ya juyo da sauri yana dubanta, ya
yi murmushi ya ce" Ayyana, ina yini?
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition i
s to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
4
️
⃣
Amsawa ta yi tana dubansa da madaukakiyar kulawa kafin take mikew
a ta kama hannunsa,
Shima biye yake da ita suka fito daga dakin Agaishat suka nufi dakinta,
Walyn ce zaune a saloon mai suna Tawaye saloon, fitacen saloon ne na manya wanda sai ka isa kake saka kafarka,
Akifunta ake gyara mata bayan an yanyanke s
u an wanke su sosai aka dauko na kanti zako zako din nan aka shiga dora mata,
Kawarta dake gefenta tana karanta magazine, itama ana gyara atach din da za.a yanyara mata kitso ........
Wata mata da ta tsare Walyn da kallo tunda ta shigo ce ta yatsina
fuska, a ranta ta yi murmushi tana ayyana ba laifi , matar tasa bata da laifi,
Kadan ta dan muzguta ta dubi cousint dinta dan daudu wanda suka zo gyaran gashin tare da shi ta ce" ina son aikin General a rayuwana, ina son yanda yake cin uwar kananun yan
iska!
Kallota ya , ya wani yi far da idannuwansa, ya yatsina fuska tamkar mace ya ce" ke kawa, ya iya tata rashin mutunci ne fa, mutumen nan kin san da matar tsohonsa ce ya rufe? Uhum ke ni ko a lahira bama fatan mu hade da General Wardugu domin bashi
da mutunci, ya iya aiki da doka, ke matarsa fa ta yarda ta kai dare a waje sai ta kwana a cel!
Daman inda take so a tabo mata kennan dan haka ta maida hankalinta sosai ta kali dan daudun nan ta ce" kawaliya matar naci ta taba daraja ne?
Walyn dake k
alonsu tana kada kafarta, ta kai dubanta wajen mai saloon din, ta maida wajen kawarta da ta yi kasake itama tana jiran gannin me zata yi? sai sauran matan dake wajen da yan tsirakun ya daudun dake wajen suna suba nasu sha.anin.....
Walyn ta saki murmus
hi mai ciwo, ta daga idannuwanta cike da isa da takama ta ce" Wardugu kennan, mijin mace daya, jarimina mai ban tsoro, Warduguna zazafa ne, kawata kin san Wardugu baya bin kadangarun bariki? Ke na yi imanin da Wardugu na bin mata zai je ya zabo zuga zuga n
e, wa.inda idan ya zaga zai dire chek ba wai ya dane karamar yar bariki ya kasa iyanta harda kason shekara sanadiyar rabuwa da mace ba!
Dan daudun nan ne ya sheke da dariya yana duban matar da suka zo tare, wace ta ji abin tamkar saukar guduma domin m
ijinta ne ya jewa wata yar bariki ya ki biya sannan ya yi mata duka hakan ya sa harda su kaso, wani tukukin bakin ciki ne ya taso mata, bata tsamaci jin haka ba , abin ya dake ta,
Kallonta ta yi da yannayin bacin rai ta ce" ke Walyn kike ko wa? Kin san ko
wacece ni?
Walyn ta fizge hannunta daga hannun mai saka mata farcen ta ce" ke ce katuwar yar barki marar aji! Sai me kuma?
Mikewa ta yi itama ta ce" ke din ba yar barikin bace? Ke naki a boye kike yi ko ji kike ba.a sani ba? Meye bambancinki da yar
bariki? Ke kawai bakya yi dan kudi ne aman menene bakya yin? Ko dan kina rufe takunki ne baki san wa.inda kuke labewar da falasawa ba? Ki jika ki ajiye Wardugu General ya fi karfin zama da mace daya wace na sani ne bakima goge a kai shi wata duniyar ba! Za
ki ga aikin gogagiyar yar bariki domin Wardugu katuwar kadara ne wanda malakarsa sai tsayaye ba isa ce zata kai ki ba mu je zuwa!......
Walyn ta yi murmushin rainin hankali kafin take bufe jakarta,
Yan jika goma goma ta fitar dami guda ta bale yar tak
ardar dake zagaye da su wace itama sai kyali take, ta dauki bakin
gilas dinta ta jefa katuwar wayarta a jaka ta juyo sosai wajen matar da sauran mutanen saloon din ta daga kudin nan ta sake su a iska wanda hakan ya saka du suka shiga wawusoso harda mai sal
oon din da yarenta kiwa na nema har wasu suka shiga dambacewa , aman banda wace ake kira da kankana!
Walyn ta bi kawayen da kankana ta zo da su da ido ta ga suma sai wawa suke harda yan daudun,
Yatsina fuskarta ta yi ta ce" abokin mai kanwa ba ya ra
sa burbudi, Wardugu ya daure min a niger tunda ya sakar min yayan banki, na kwana lafia koda Wardugu ya shiga tsakiyar yan bariki ba zata motsa ba domin kyankyaminku yake!
Ta kara taku har gabanta ta zaro idannuwanta ta ce" ki sauke girman kai ki duka ki
kwashi kudi.....su kike kwadayi!
Iska ta ja ta kaiwa Walyn duka warda itama ta damketa suka shiga dukan junnansu,
Sai da suka lilisa junnan su sannan mutanen wajen suka shiga tsakanin su kowace na haki,
Walyn ce ta warce jakarta ta yi gaba inda kaw
ar tata ta biyota da gudu tana kiran ta tsayata, aman ina cikinta take ji yana wani irin hautsina mata, bata san me ke damunta haka ba yanzu, ya kasance tana yawan jin abubuwa a tatare da ita,
Wardugu ya jima wajen Ayya, inda suka tatauna sosai sannan
ta saka shi a gaba kan sai ya ci abinci,
Agaishat na fitowa ta nemi Mu.azam, sai dai bata ganshi ba hakan ya saka ta fice ta nufi wajen runfar Ayya mai wani ni.imtacen sanyi tana neman Mu.azam,
Nan kuwa ta same shi, ya kurawa waje daya ido, ya zurf
afa sosai a tunani wanda yannayin fuskarsa ta nuna ba tunanin dadi yake yi ba,
A hankali ta karasa ta kuma maimaita salamar da ta yi ta yi masa tun daga dan nesa da shi,
A dan tsorace ya kalota kafin yake daidaita yannayin fuskar sa ya amsata yana ma
i kokarin gyara mata kujerar dake kusa da shi,
A hankali ta ja ta zauna tana dubansa, yannayinta ya nuna itama ta shiga damuwar da yake ciki,
A hankali ta ce" me ke damunka ya Mu.azam?
Daman ita yake kallo, dan haka ya bi bakinta da kallo yanda ta
fadi maganar a hankali sannan a cicire domin dai tana faman koyon yarensa ne,
A nitse ta janye idannuwanta daga cikin nasa, domin kallo nr yake mata tamkar zai fada idannuwan nata take ji,
A hankali ya ce" Agaishat,
Ta dago tana dubansa, inda a t
ake ta ji gabanta ya fadi da yannayinsa,
Mu.azam ya ce" kin san soyaya?
Agaishat ta zaro idannuwanta tana dubansa, tama rasa me zata ce da shi,
Mu.azam ya ce" kin taba yin saurayi wanda kika ji kina so?
Agaishat ta saki murmushi mai kama da na
sakalci, domin ita abin har ga Allah dariya ma ya bata, A hankali ta maimaita kalmomin" *So, Soyaya, Saurayi?*
Mu.azam ya dan kankance idannuwansa ya ce" yeah,
Agaishat ta dube shi, duba na ido da ido kafin take fadin" *Ban san shi ba*!
Da mam
aki yake kallon ta, bata san shi ba tace fa? Aman daga ina Agaishat ta fito haka? Ko dai masu son nata ne basu yi mata ba?
Yin wannan tunanin ya saka gabansa ya fadi, a ransa ya ayanna ya salam, kar dai a je nima ban yi mata ba,?
Muryarsa sanyaye ya ce
" du a maneman soyayar ki ba wanda kika taba jin kina so?
Agaishat dake dubansa itama, bata dago ina ya nufa ba, domin dai ita ba.a taba kamanta za.a ce ana sonta ba, dan haka ta bashi hankalin ta sosai ta ce" ba wanda ya taba fada min ya ake so din ne,
Dariya ya shiga yi kasa kasa yanai mata wani duba kafin yake fadin" ba fa zolayana nace ki yi ba Madame,
Bata san kalmar madame ba, aman ta gane yana nufin wasa take yi masa, dan haka ta ce" ban taba yin saurayi ba, ko an zo zaben yan mata a gidan m
u ba.a taba zabena ba, Ba yace dan na cika baki da muni, ni ba alkhairi bace dan baki ba alkhairi bane, hakan ya sa ba mai zabena bare a biya sadakina, har kanwata an zaba sai dai kafin auren ta rasu ita,
Dubanta yake har ta gama yi masa bayani da kwata
nce da komai dan ya gane da kyau, ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ayanna na godewa Allah ai da basu zabe kin ba da sun saka ni a ukunna,
A fili kuwa ya ce" wa ya fada maki baki ba alkhairi bane?
Agaishat ta ce" da alkhairin ne, da mahaifina bai kyama
ce ni ba da alkhairin ne da nima ana yi min dinkuna irin na yan uwana, da alkhairin ne da jama.ar gari sun mutunta ni a matsayina da dan adam mai daraja a cikin halitun Allah, da alkhairin ne da na yi saurayi koda mahaukaci ne a *Gida*,
Katseta ya yi
da fadin" aman sai na ga kina da ilimin adini sosai, ya aka yi kika kasa imani da haka?
*Agaishat , malamata, wa ya halici fari da baki,?*
Agaishat dake dubansa ta sada kanta a hankali, kafin ta ce" Allah ne,
Shin da ya halici baki ya kawo wata ay
ya a alkur.ani mai girma, a hadissai ko wani litafin na adinin fake nunin bakar fatar nan da ya halita ya haliceta ne dan wani laifi? Ko mai wani laifi?
A hankali ta kuma fadin" aa, ban karanci haka ba,
Mu.azam dake dubanta ya ce" Bilal, bawan Allah,
wacece kalar fatarsa? Ya darajarsa take?
Dago da idannuwanta ta yi ta ce" baba tsofo ya ce shi ne ya fara kiran sallah , ya ce mutun ne mai daraja, makusancin fiyayen halita,
Mu.azam ya gyada mata kai kafin yake ciro wayarsa ya samo hoton ka.aba ya
ce" zo ki ga ka.aba a hoto Agaishat, zo ki gani...
A hankali ta matsa tana kallo, kalar bakin ya tafi da imaninta, abin ya yi mata kyau a ido, a hankali ta kai yatsarta ta dan shafa hoton,
A hankali ya ce" ba wani bawan da ya fi daraja, ya fi kusanci
fa ubangijinsa sai mai yi masa biyaya, mai tsoron shi, mai kiyaye dokokinsa, a cikin nan kin ji an ce *Farar fata ta fi bak'a?*
Agaishat da take jin wani yamyamyam a jikinta na dadi ta girgiza kanta,
Mu.azam ya ce" makafi ne ko kwakwaluwar su bata ja
? Ya aka yi basu yiwa abin kaunata wawa ba?
Da sauri ta kallo shi,
Kansa ya dan sada ya ce" kina da tsararen kyau, fitinanan kyau, baki da tsayi Agaishat...baki da kiba har can, yannayin jikin ki ya tafi da yannayin tsayin ki,
Bakin ki ba mai tabo
bane bare shaida, gaba daya ya tafi iri daya ne baki mai haske mai nutsuwa, agaishat, fuskar ki yar
doguwa ce