Showing 42001 words to 45000 words out of 86237 words

Chapter 15 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

27

ne...ta ina ake shigo da hoda har ta gama gari haka? Ya sani ne sai sun sha masifa fa lauyoyi, inda ya san ya shige gabansu harda dan gidan banban lauya baki daya, in y

a yarda ya ce a saki mutane, iyayen yara da manya masu daraja zasu sako shi a gaba ace dan da yaronsa ne !

Kansa ya shiga shafawa ya bude bangarensa ya shige ,

Kamar koda yaushe, sansanyen kamshi ne ya taro shi, wannan fa ba.a wasa da shi,

Agogon

hannunsa ya fara kuncewa yana kokarin karasawa cikin dakinsa na baci dan ya samu ya yi wanka,

Wardugu" ta yi kiran sunnansa tana mikewa ta nufo shi,

Tsayawa ya yi yana kallonta, domin yanzu ya dan saka mata haushinta da yake ji na ta tafi ta bar su

wai ba zata hada numfashi da yar gidan Anna ba,

Karasowa ta yi ta shige jikinsa du da yanda yake tarewa,

Murya a kasalance ya ce" Walyn bari na yi wanka , aiki na yi jikina ba tsafta,

Kai ta girgiza ta kara shigewa jikinsa tana rungume shi sosai a j

ikinta ta ce" baka wari kuwa Wardugu, kamshin turarenka na nan,

A hankali ya raba jikinsa da nata ya ce" aa tsaya na yi wanka, na yi zufa sosai kin ji?

Ya karasa yana mai zaunar da ita saman tsareren bed dinsa mai ruwan zeba,

Bayi ya zarce ya samu y

a shige kasan shower,

Ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa a jikinsa dan yana son jin sanyi

A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin sanyi mai dadi na ratsa shi,

Sai da ya gama ya yi wanka na kirki ya dauro alwallah ya fito daga bayin , zuwa wannan loka

cin har karfe tara ta kusa cikewa,

Yana fitowa , Walyn ta kara nufo shi

Tsayawa ya yi yana kallon yannayinta, magana ke tafe da ita domin batai masa yannayin tana bukatarsa ba,

Dan haka ya zarce ya dauko jalabiyarsa ya saka ya dauko salaya ya shin

fida yana kokarin tayar da sallah,

Wardugu mana! Ta fada da yannayin damuwa,

Juyowa ya yi yana kallonta bai amsa ba,..

Ta karaso ta ce" su Mamanmu ne fa ke zaune a falona ka fito ku gaisa ,.

Wardugu yana kallonta, mamansu, har wannan lokacin?

Bai bata amsa ba ya tayar da sallarsa, dama dan ya yi shafa.i da wutiri ne,

Zama ta yi har ya karasa, ya zauna ya yi doguwar adu.o.insa na tsari da komai ya mike ya cire rigar daga shi sai gajeran wando ya yi bismillah ya haye bed,

Da mamaki take kal

lonsa, ranta ne ya baci ta ce" aman baka ji wace nace maka tana jira ba?,

Domin ta sani ne, yana mugun daraja mahaifiyarya, ko gaisar da ita zai yi sai ya dan duka, aman yanzu ta fada masa ta ga ya wani kwonta abinsa,

Wardugu ta kara kiransa tun karfi

,

A fusace ya dago zaune , murya a bace ya ce" ba zan je na gaisar da mamanki ba, na gaji baci nake son yi ki fice mani a daki!

Ido ta kwalalo tana kallonsa, kafin take juyawa ranta in yayi dubu a bace yake, tana son tsayawa ta ja maganar aman wani

abin na hanata, dan kuwa dukan alamu sun nuna idan ta yarda ta kawo masa raini komai na iya faruwa ,

Juyawa ta yi tamkar zata tashi sama ta fita a dakin,

Karamar wayarsa ya bude,

Sheik ibrahim ya danawa kira,

An jima tana ringin kafin yake daga

wa da salama,

Wardugu ya gaisar da shi da tambayarsa jama.a,

Sheik ya amsa yana mai tambayar Wardugu Aiki,

Wardugu ya amsa shi a nitse ya ce" Malan, a kara saka mu a adu.a,

Sheik ya yi murmushi ya ce" Wardugu , na ganka a tv, fatan Allah ya tay

aka, Allah ya baka ikon yin aikin kirki, sai dai zan kara fada maka, a duniya karka ce sai ka birge kowa, ka yi lamarinka domin Allah, kar ka saka fushi ko gaba dan Allah ya baka dama mai girma ta jan wanda ka yi niya, ka ci gaba da kawar da kanka a kwaday

i , sannan ka ci gaba da jan istighfari kana kaiwa allah kukanka ka ji?

Wardugu ya amsa a mutunce sukai salama,

A hankali ya lalubo cazbaharsa fara kar tana ta kanshin turaren ruwa ya shiga ja daga kwoncen yana ta jan astghfari,

Me mijinki ke t

akama da shi a duniya Walyn? Ya rasa wa zai rufe sai aban iman? Ko dan yana auren yar yayata ai sai ya daga masa kafa, dan kawai ya kama da shi a wannan wajen, wajen ba na ubansa bane? Zance wajen sunnansa ma gare shi! Me yake tunani? Dan yana sanye da rig

ar iko shikennan ? Ai idan shine yau gobe ba shi bane zai ringa yiwa mutane rashin mutunci! Tunda haka ta faru muke gidannan aman ya zo ki wani zo ki ce wai ya gaji? Gajiyar kaniyarsa, mu da muke nan bamu gajin bane? To idan mijina ya kwana a cel nima na d

auki alkawain sai na tozarta Wardugu sai na saka wardugu ya shiga uku, sai na

Aunty! Walyn ta fada tana daga murya sosai,

Da yatsarta daya ta ce" ke a wa? Wacece ke? Kike ikirarin tozarta Wardugu bayan Allah ya rike? Ke kin san da za.a shige shi da a

n shige shi ba yau ba Aunty! Wardugu baya zuwa maula, hukunci kuwa idan ya kama zai yiwa ko wani dan buro........ba, meye? Takamarki ki yi masa shari, ki hada shi da malame, ko ki same shi ta hanyar abin duniya?

Ban ce sihiri ba zai kama shi ba domin wane

ne shi, sai dai na miki alkwarin tunda kika fadi haka , sai dai mu mutu baki daya,!

Mahaifiyarta ce ta kasheta da mari, rai bace ta ce" kan namiji? Kan namiji zaki ciwa kanwata mutunci? Namijin ne ya kai dan goyo har haka? Ke Wardugun da kafin aurenk

u ma sai da ya karya maki hannu sau biyu shine kike daga jijiyoyin wuya dan ance za.a taba lafiarsa? Kin manta dan ya kauce ki malaki wannan daula na yarda yake tata maki rashin mutunci? Idan kin canza ra.ayi na sani da wuri dan Ubanki!

Wakyn dake yash

e tun marin magaifiyarta, jikinta a mace, takan mance du wani kudirinsu idan tana tsaye gaban gwarzonta, namiji ne Wardugu, can dama tana sonsa sosai, damuwar kuna tana son kudi sosai!

Mu.azam, tashi ka kai ni ya sha maganin bakin nan

,

Ayya ta fada tana nuno masa wani dan kuli wai maganin baki ne dan kar baki ya fada masa

Mu.azam dake zaune kafa tankwashe Agaishat na koyar da shi bakara ya dago da mamaki yana kallo Ayya,

A hankali ya ce" Ayya, idan muka yarda muka fita a yau fa

kama mu za.a yi a rufe, sai karfe takwas na safe za.a tsayar da kamen nan, ki rufa mana asiri Ayya kin j?

Ayya ta zaro ido ta ce" dan ubansa a rufe mun, bafa zai yi baci ba sai ya sha maganin bakin nan yau yanzu yanzu dan haka tashi mu je Mu.azam,

Mu

.azam ya mike yana ayyana ta faru ta kare a ransa, dan ya san in dai suka fita titi za.a kama su ne, za.a rufe su, daga shi har Ayya har Agaishat din,

...........to fah

๐Ÿคฃ๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช

โœŒ

๐Ÿผ

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

*BAK'A CE*

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

Na *SAJIDA*

*ุจุณู…

ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

____________________________________

*

๐ŸŒˆ

KAINUWA WRITERS

โœ

๐Ÿผ

ASSOCIATION*

๐Ÿค๐Ÿป

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

__

__________________________________

2

๏ธ

โƒฃ

7

๏ธ

โƒฃ

Mu.azam ya ce" Ayya, ki bani na je na kai masa, kin ga ko an kama ni kadai ne za.a kama,

Ayya ta ce" yo kai na d'a bane, a hada har mu a rufe, ba yace doka ta hau kowa

ba? Na tabata an hada da iyayen mutane a wajen,

Mu.azam kam ya rasa ya zai yi da Ayya , ta kuwa coge kofar daki inda Agaishat ma ta fito tace ba zai yiwu Ayya ta tafi ta barta ba,

Kallon agaishat yake kasa kasa, a hankali ya ce" idan aka rufe ki Aga

ishana, ba zan iya hakura ba, kar ki biyo mu na roke ki,

Irin na yara ta yi masa da kafadarta irin ta kiya, tama rigayi kowa karasawa wajen motar bayan ta amshi maganin bakin na hannun Ayya,

Haka Mu.azam ya fitar da motar dake da lambar Wardugu, ya d

auko carte dinsa ta shaidar shi likita ne, da carte didentitรฉ dinsa,

Fitowa ya yi da motar Ayya ta shige baya ta hakimce, Agaishat ta shiga gaba aman a ranta a tsorace take, tana tsoron sojojin garinnan, daman ba.a saka soja a lamari a niger sai abin y

a baci, su fa ba ruwansu hade kowa suke, idan ka yi masu gardama su tataka banza su barka nan zubde tamkar kayan wanki,

Tuki yake zuciyarsa kuwa sai adu.a yake, Agaishat ma adu.ar kawai take inda Ayya ke kara buga lambar wardugu aman a kashe, bata shiga

ma bale a dauka,

Danja na tsayar da su aka haske su da cocila dall a idannuwansu,, gaba da baya sojoji suka zagaye su har mutun uku,

Na kusa da direba ne ya kwonkwasa kofa,

Mu.azam ya bude yana dubansa,

Mutumen ya ce" motar Gn ce Oga,

Ya ce"

eh na gane ai,

Ya ce" malan daga ina , kuma ina zaka je? Wa ka dauko? Sannan ka bude mana bayan mota zamu yi bincike,

Mu.azam ya fara bude masu motar, sannan cikin nutsuwa ya ce" ina tare da mamanmu ne, mahaifiyar Wardugu da kanwarmu Agaishat sai ni

kuma amininsa ne, daga gida muka fito zamu je gida wajensa bisa umarnin mamansa,

Menene shaidarka? Sojan ya tambaya ba alamun wasa,

Mu.azam ya mika masa cartocinsa, sannan ya sauke madubin bayan ya dayan ya leka wajen Ayya,

Kwarai kuwa itace, waye

bai san Ayya ba? Mahaifiyar General,

Gaishe da ita ya yi cikin mutuntawa ya ce" yi hakuri mama muna bisa aikin mu ne, ki tabatar mana da abinda ya fada,

Ayya ta ce" eh haka ne, ina son gannin Wardugu me yanzu yanzu,

Sojan ya gyada kai yana kallont

a,

Wanda ke bincika cikin motar ya shaida masu ba komai cikin motar, dan haka ya mika masa takardarsa ya basu damar su fice

Cikin ikon Allah haka sukai ta haduwa da sojojin nan suna kara titsiye su ,

Harda wanda bayan dukan bayannan nan yace ai shi

bai wani san Ayyar ba a bashi shaidar da ta fi haka,

Nan fa aka sha rigima da kyar masu taya shi suka tsawatar masa ya batsu suka tafi,

Tun abin karfe tara sai kusan sha daya suka karasa gidan Wardugu nanma suka tarar da wani balakin an hana iyayen Wa

lyn fita sai dai su kwana a nan in kuwa suka fita aka kama su toh su suka gano, sun izata sai balaki take kan wardugu ya fito ya raka su ko ya basu shaidar da zata sakasu su tafi har gida lafia,

Suma su Mu.azam sai da aka titsiye su kafin suke samun shi

ga gidan,

Mu.azam na tsayawa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon hajia rigima, domin Ayya ta hade rai ta yi kicin kicin da fuska tana kallon yanda suke tsatsaye suna ta magana suna tafa hannu suna balaki,

Mu.azam ya ce" Ayya, kar ki kula koya na roke

ki,

Ayya ta yi murmushi ta ce" oh yarona, yanzu kai ke yi min gargadin kar na kula kowa, ai ka san bana kula mutumen da bai iya tsawatarwa zuciyarsa ba!

Bude motar ta yi ta sauka,

Ai kuwa tunkarar wajensu ta yi direct ba wani tsaye tsaye,

Tan

a zuwa ta ja ta tsaya itama tana yi masu kallon da suke mata,

Da yake akoy wuta ko.ina haske ya garwaye gidan kowa na gannin kowa ne,

Ayya bata fita sai ta shirya ko fitar da a rikice take ne, dan haka yanzuma sai baza kanshi take, ga lufayarta ta nada m

ai ruwan ja da baki, ta sha awarwarenta na zinariya,

Walyn ce ta ce" ina yini,

Ayya ta kai dubanta wajenta ta ce" lafia, sannan ta mayar da dubanta wajen iyayen Walyn din tanai masu kallon ido cikin ido,

Mahaifiyar walyn ta miko mata hannu ta ce"

Hajaju ne, uwar gidan *MARAHUT* ke ce da tsakiyar daren nan??

Ayya ta sakar mata murmushi ta mika mata hannun itama ta ce" wa.alaiki salam maman Walyn, ke ce a gidan Wardugu da wurin nan haka,

Kanwar maman Walyn ta kali Walyn ta kuma kallon sirika

n biyu, ta juya bangaren Walyn tana ayyana taf, lale ana cakwakiya a gidan nan,

Ita kuwa walyn kitson kanta kawai take sosawa, susar da bata san ko ta meye ba,

Ayya ce ta fara cika hannunta ta kuma kallon Walyn ta ce" Aa, Walyn yaron nan yana nan ne

dai ko? Bara na shiga na gani Wardugu sarkin aiki!

Juyawa ta yi ta nufi bangaren Wardugun cike da isa, sai a lokacin Mu.azam ya lalaba Agaishat ya cire mata tsoro suka fito daga motar,

Mu.azam ruwan sanyi sai ya nufi wajen su dan gaishe su,

Waly

n ta daga ta watsar da idannuwanta sannan ta zabgawa Agaishat wata muguwar Harara da kallon kyama ta juya tana riko hannun mamanta suka koma bangarenta,

Agaishat dake dafe da kirjinta jin yanda zuciyarta ke dokawa Mu.azam ya kallo,

Murmushi ya sakar

mata ya ce" mu je Matar Mu.azam,

Ido ta zaro kafin take daga kafa da sauri ta yi gaba tana jin wata kunya kunya da wani irin abu game da Mu.azam din, yakan mantar da ita wacece ita ta halin nuna mata itama mutun ce mai cike da cikeken inci, yana yaba ka

lar fatar jikinta ta hanya kawatata da kalamai masu tsari da sence, yakan ce Allah ya datar da shi samunta, ita Agaishat yar gidan Sofo? Tana so ta biye masa tana tsoron ko wasa yake mata? Tana son ta yarda tana tsoron yan birni,

Ayya na shiga ta zarc

e har dakinsa na baci tana fadin" ina kake janyau, ka hargitsa mana gari ka lafe a gado, tashi tashi kaima ka yi kwanan zaune dan nema kawai!

Da wani irin sauri ya mike ya diro ya warci doguwar rigarsa yana faman sakawa ta shiga dakin,

Wardugu ya ce

" Ayya, wai yaushe zaki dauna shigo min haka zaraf kawai? Me ya fito da ke a tsohon faren nan? Ya aka yi kika ratso sojawan hanyar nan? Wa ya kawo ki?

Maimakun Ayya ta bashi amsa sai cewa ta yi" baka da sutura a jikinka ne kake kwonciya Wardugu?

Ward

ugu ya dafe kansa ya furrta" Ya Allah,

Bakinta ta yatsina ta ce" fito ina jiranka

Sai da ya saka kayansa ya biyo bayanta,

Yana fitowa ya ga Mu.azam, da bakuwar nan ta ayya da shi ba zai iya fadin sunnanta ba dan bai wani rike ba,

Sai dai mamak

i yake, yanzuma wasu kayan ne jikinta, shi abinda ke bashi mamaki yaushe ta iya saka kayan tubawa har yake bin jikinta haka? Yaushe ta iya saka kayan kansa nema ?

Kawar da kansa ya yi da sauri yana yatsina bakinsa yana ayyana ina ruwanka yo, ba dai Ayy

a ta daure mata ba?

Ayya ta karbi kulin maganinta ta umarci agaishat da ta bude frij dake nan falon ta fauko ruwan roba

Agaishat ta nufi frij tana tambayar kanta ina wajen budewar yake? Domin ba irin na gidan Ayya bane, wannan wani glass nema a jikin

sa ko.ina tar tar yake ana hangen abubuwan dake ciki tar sai dai ba lale ka san wajen kunawarsa ba,

Ja ta yi ta tsaya tana kallo,

Ayya dake jira ta kallo wajenta ta ce" Agaishta kawo mana,

Agaishat ta juyo tana raraba idannu ta ce" Ayya, ina zan

bude??

Wardugu ya girgiza kansa, Mu.azam ya mike ya je ya nuna mata ya bude mata, ta nuna masa wanda take tunanin ruwan ne?

Mu.azam ya ce mata" wannan ai jus ne, gidansa da kamarsa yake yannayin ruwa, aman kin ga jerin ruwan nan,

Nan ta dauko suka d

awo wajen Ayya dake ta yiwa Wardugu fadan ya kwonta bai ci abinci ba dan ba sai ta tambaya ba ta sani ne kwonciyarsa zai yi, aman kwata kwata bata sako maganar matarsa ba ko iyayenta, bata da wannan lokacin,

Wardugu dai kallonta yake, ta bude ruwa ta ts

iyaye fiye da rabi ta zuba maganin ta girgiza ta mika masa ta ce" shanye,

Wardugu ya cee" Ayya meye kuma wannan

?

Ayya ta ce" Wardugu, magannin baki ne, bakin mutane, ka san baki fa ya fi maye mugunta, baki ai ba dan uwa bane, bare yau ka janyowa ka

nka maganar mutane

Robar ya rike a hannunsa ya ce" Ayya, bayan walahaulan da nake yi kuma dai kin bani wannan jike jiken naki?

Ayya ta ce" walahaula hanyarta daban, wannan ma nasa daban, kai harda garin hantiti nake tafe, maza shanye ka dauko min but

a a bayinka na zuba maka ka yo wanka ka turaru sai mu juya,

Ido ya zaro yana kallonta, kafin ya maido dubansa wajen Mu.azam da irin kallon kai ka kawota ko?

Mu.azam ya juyar da kai wajen Agaishat dake zaune kasa yana kallonta, domin kallonta na saka

shi nishadi

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

*BAK'A CE*

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

Na *SAJIDA*

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

____________________________________

*

๐ŸŒˆ

KAINUWA WRITERS

โœ

๐Ÿผ

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login