Showing 21001 words to 24000 words out of 86237 words

Chapter 8 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

10

gaba sarki ya shiga suka shishige gaba dayansu Walyn da binsa da kallon meye kuma haka? Shima kallon Ayya dai yake,

Basu zame ko.ina ba sai kofar gidan Algabiitt

...................... ...........

......

Anna, ki yi hakuri haka kin ji? Ki daina damuwarnan kin ji Anna?

Agaishat ta fada tana miko mata gurasa ta kasa da aka kawo sadaka gidan mutuwar

Anna ta lumshe idannuwanta bata karba ba ta bude tana kara bin yayan nata da kallo,

Mutuwar

nan da aka yi bai saka Algabiitt ya yi sanyi a lamuransa ba, ya sako Agaishat gaba dole sai ta yi shafe shafe itama ya samo mata miji kamar yan uwanta tamkar damuwarsa ta yi auren ne,

Yarinyar bata isa ta wulga ba sai ya dura mata zagi

Ya hana a yi zam

an makoki sai yayanta dake zagaye da ita

Amarya kuwa idan yau wannan ya zo ta ce dan uwanta ne , gobe sai wancen ya zo ta ce kaninta ne, ta mayar da gidan filin kawo kwartayenta ba tare da wani dar ba domin mai gidan ya bata lamuni....

Anna murya a sha

ke ta ce" bana so ya kashe mini wani cikin ku,

Mariama ta juyo fuska du ta yi mata ja abin kuka ta ce" to ki biyo mu mu bar masa gidan mana, dan mi ba zaki bi mu mu yi tafiarmu ba? Kin san abinda ke daure mu a nan ke ce,

Hankalinta tashe ta ce" a du

k lokacin da kuka ambata mini abubuwan nan biyu asalina da barin Algabiit bara ku ji na fada maku yau abinda nake ji! Ji nake tamkar lumfashina zai tsaya idan na ji an ce na bar inda Algabiit yake in dai ba da yawunsa ba, ji nake zan fada halaka, ji nake d

uniyara shi ne, ji nake in ba inda yake ba ba ni! Wani duhu ke rufe mini ido kaina ya dauki nauyi idan na takura sai na tuno wacece ni? Nakan fada damuwa mai tsanani juwa ta ringa dibana du idan aka yi maganar dangina, kun ji damuwata

Suke suke kallonta

, Agaishat (Bak'a) kanta na saman cinyar Gaishat, Mariama na zaune gefensu, Fatimata na jingine da garu tana facing dinsu,

Jiki a sanyaye Fatimata ta ce" me ke damunki haka Anna? Wannan ba soyaya bace,

Mariama ta kallota ta ce" wace soyaya? Ai koda a

n yita a baya a yanzu Ya kasheta da kansa, Me ke damun Annarmu?

GAISHAT ta buda baki zatai magana sai ga Algabiit bugum ya fado dakin yana dan dudukewa dan tsayi

Direct ya zarce gurin Anna bakinsa na rawa ya ce" sai dai su tafi da ke da tsinaniyar y

ar ki! Ba wanda zai kama ni, ba abinda na yi!

Da sauri ta mike tana dafe kirjinta, tsinaniyar yarki ke mata yawo a kwakwaluwa, wacece kuma? Me aka yi? Su wa zasu tafi da su?

Bata kai ga tambaya ba ya duko ya dago Bak'a da gashinta ya mikar da ita,



Yawun bakinsa ya tatara mai cike da warin Sansani ya tofa mata a fuska ya ce" ga dan iskan tsohon da kike wuni wajensa tare da sojoji, to ki sani sai dai su kama uwarki

Janyeta Anna ta yi da karfi sannan ta yo fallon nasu da sauri dan jin lafia?

G

aba daya yayan nata suka biyota inda Algabitt ya labe yana leke yana kuma sauraron abinda ake fadi

Da kallo Anna ke bin su, sukai mata salama suka shiga gaisar da ita da yaren buzanci,

Ayya ta kalli wardugu dake karewa kowa na wajen kallo, ta ce" ban

san bama da wani yare zamu tatauna da ita da alama buzanci kawai take ji

Anna dake tsaye ta ji komai abinda aka fada da yaren da ba zata ce ga sunansa ba, kuma ba yaren da suka yi da likitan nan a asibiti bane............................................

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind

of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

1



6



Bata kai ga magana ba dogarai ke sanar da shigowar sarki falon sirikan nasa , daman da baba tsoho

ma shi ke fasara tsakaninsu domin ba komai yake ganewa ba shi kuwa sarki ya zauna da tubawa

Tunda ya shigo Anna ta sada kanta dan kunyar siriki, shima du a wani takure yake inda Gaishat ke binsa da kallo tana tambayar kanta me ya kawo shi ko bakinsa ne

?

Gyaran murya ya yi ya ce" Anna, ina fatan kin san baba tsoho, wanda Agaishat ke zuwa wajensa babanta kennan

Daga inda yake ya daga murya da irin abin haushi haushi ya ce" ya zata manta kwartanta uban yarta? Ai ni dama na san dubunki sai ta cika mun

afuka, yau dai ga zance zai bude

Da wani irin yannayi Wardugu ya kai dubansa daga inda ake maganar, wa ke magana ta rashin da.a haka? Shine abinda yake tambayar kansa din wardugu na jin yaren buzanci kai bama buzanci kadai ba wardugu irin mutanen nan n

e masu kwakwaluwar kwashe yaren da ba nasu ba, yana jin yaruruka da dama, hakan ya bashi damar jin abinda ake fada harma wanda Algabiit ke aikowa daga daka

Sarki ya girgiza kansa kawai, ya san wanene Algabiit farin sani, kuma fa ya san harma gudumuwarsa

wajen Algabiit ya tsula tsiya a garin aman ba komai zai dauki mataki ne tun kafin ya saka a tarwatsa su baki daya

Anna da ta kasa hada ido da shi ta gyada kanta, ya zata kasa gane mutun mai daraja a idannuwanta? Wannan mutumin ko dan tsufansa a girma

ma shi aman Algabiit ke aiko masa da zagi haka? Ta yi imanin ba ita ba ko Algabiit din baba tsoho ya haife shi

Bak'a kuwa tunda ta kyala ido ta ga baba tsoho ta samu ta rakube jikinsa tana dan jefo masa tambayoyi a hankali da alamun tsegumi

Hannunsa ya

saka ya dungure mata kanta yana murmushi, a ransa ya ayyana idan kika tafi,....nishadina, murmushina, zai tafi da ke

Sarki ya ci gaba da fadin" wadinnan mutanen da kike ganni, wannan baiwar Allahm mahaifiyar wannan bawan Allahn ce, sannan ta taso tun da

ga garin da kuka kai Fatimata rashin lafia ta zo Agadez daga nan sun dauki hanya sun zo garin nan dan neman baba sofo da ya baiwa dan nata maganin huka tun yana yaro bisa alkawarin idan an samu lafia sai ta bashi abinda ya samu

Toh Sai aka tashe su Allah

bai yi sun kara haduwa ba, tun daga lokacin take nemansa domin mutun ce mai son cika alkawari abin na tsaye a ranta sai yau Allah ya yi

Dan numfasawa ya yi, ya ci gaba" kin ga, ba a niger ba, ko a kasar waje masu fada a ji ne,

Sun zowa Baba sofo da al

khairi na mamaki sai dai abin mamaki baba ya ce sam shi yanzu ba ta abin duniya yake ba, ya yafe sai dai damuwarsa *AGAISHAT CE*

Anna ta dago da sauri ta ce " AGAISHAT?

Sarki ya ce" kwarai kuwa, Baba ya nemi alfarmar.................................

.....................gaba daya sarki ya kwashe yanda suka yi baba da su Wardugu

ya fadawa Anna dake zaune kanta na kallon kasa sauran yayanta na zagaye da ita Bak'a kuwa na jikin Baba sofo

Da sauri Bak'a ta dago ta kai dubanta wajen Anna da Sarki, ta ma

ida dubanta wajen baba Sofo,

Baba Tsoho ya yi gyaran murya ya ce" shakuwa, da tunani ya hana ni sakun nutsuwa Annar Agaishat, na sani bani da ikon zartar da hukunci kanta domin ban haifeta ba sannan ni ba wani shakikikin dan uwa ba

A duniya adu.ata biyu

ce, Allah ya sa in gama da duniya lafia Aljanna ta zamo makomata , fatan Allah ya nuna min ta zama mutun mai cikaken inci, ta samu nutsuwar zuciya , ta samu zama itama mutun,

Anna Agaishat ta yaya hakan zai faru? A timiya mu duka bamu fi kirgo da yatsu b

a, nan da kike ganina har limamin garinnnan na nemi alfarmar ya aure man ita mana aman ya nuna aa ba zai iya ba

Almajirina ma ya kiye min,

Gashi yau da gobe sai Allah, Agaishat girma take, mu kuwa gajiyawa muke kara yi,

Idan ta fito daga nan ina ta fada

? Me ta ci? Ya ta yi ta samu Allah ne masanin gaibu, ni kam a matsayina da wanda take zuwa wajensa sannan ta daukeni tamkar uba nakan yi mata nasiha, nakan tsoratar da ita, nakan nuna mata karara rayuwa da abinda Allah ya bani ikon sani

Annar yara , Ba za

n tirsasa maki ba, ba zan saka ki daukan abinda zaki yi ta nisawa zuciya bata da tabas, aman ina so ki yi tunanin gaba da bayan lamarin, in da hali ki dauki Agaishat ki baiwa wannan mata riko da zuciya daya, ki yi kyakyawan zato, ki saka a ranki alkhairi n

e sannan ki bi da adu.a, na yi imanin koda mugaye ne Allah zai saka mata kaunar yarinyar shari ya juye wa khairi

Wardugu ya yatsina fuska ya dubi Ayya dake zaune tana kallon su, da yaren tubanci ya ce" Ayya, yarinyar nan fa wannan mahaifiyarta ce , kum

a ina jin shegiya ce shi ya sa wancen yake zazaginta haka! Ayya me ya sa suke faman rabuwa da yarinyar? Ayya

Wardugu ya isheka haka , Ayya ta fada tana zaro masa idannuwanta, murya a kausashe ta ce" baka lura da abinda ke faruwa ne?

Ba zato ba tsam

ani muryar Anna, cikin yaren Tubanci ta ce" ba shegiya bace, wannan da ka gani ya shige daki ya labe shine ubanta, yana kyamatarta ne dan ta zo duniya *BAK'AR FATA*

Da mamaki du suke kallonta,

Ayya ta taso ta karasa kusa da ita, hannunta ta kamo tana

kallonta ta ce" batuba ce ke?????

Anna ta lumshe idannuwanta sai ga hawaye sharsharshar ta dan jijiga hannun Ayya ta ce" ban sani ba, ban san ko mecece ni ba,

Damko hannun Ayya ta yi da dan karfi ta saka idannuwanta cikin nata ta ce" ban san ko dan

ina jin yarenki ba? Sai kawai nake ji zan iya sadaukar da y'ata wa ke, zaki rike mini yarinya da gaskiya?

Ayya ta ji gabanta ya dan fadi, matar na tare da wani banban lamari, Ayyan ta jijiga hannayenta itama tana kallonta ta ce" mudin raina

Algabiit

dake ciki sai zaro ido yake, ya shiga ukunsa, ya aka yi Anna bata manta yaren nan ba? Aman abinda ya yi mata *Harta sunnanta ta manta*! Domin kafin ya lulo timiya da ita sai da ya tabata ta iya yarensa, ta iya saka kaya irin nasu, ta iya yan dabi.unsu, sh

igewa ya yi ciki ya zauna jikinsa na dan rawa rawa

Anna ta lumshe idannuwanta, ta ce" thank you,

Wardugu dake tsaye ya kalo su , Inglish kuma? Inglish ta yi?

Hai san ya karasa shigowa dakin da kyau ba sai da ya karasa, inda shigowarsa ya saka du

yan matan suka tsaya kallonsa da mamaki, Bak'a kuwa ta lafe da tsoro jikin baba tsoho jikinta du yayi wani sanyi tana son fahimtar maganar tafiya da wa wai ake? Ina ai ita ba inda zata, ba zata bi wasu mutanen da bata sani ba bata taba gani ba ta je a kash

eta, ya zata iya tafia ta bar yan uwanta da annarta da baba Sofo? Wa zai ringa kawo masa ruwa? Wa zai ringa saya masa gogo yana gurza masa a karfen gurje goro? Wa zai ringa koya mata karatu? Wa zai ringa ce mata itama mutun ce dan tana baka Haka Allah yake

son ganninta ?

Wardugu yana karasowa ya dan duka yana kallon Anna ya ce" di u speak Inglish?

Anna ta dago ta kale shi, ta amsa masa da kanta, a ranta tana nanata inglish? Wani yare ne shi kuwa? Ba irin wanda suke yi da matar bane kennan?

Wardu

gu da mamaki ya ce" ya aka yi kika iya inglish? A ina kika koya? Wa ya koya maki? Daga wani gari kika zo?

Anna da kanta ya fara sarawa ta dafe kanta da sauri , muryarta ya fara rawa rawa ta ce" i...i...i don't know ! Ta fashe da kuka tana rungume hanna

yenta da sauri Gaishat ta karasa tana rungumo Annarsu itama tana kukan za.a kuma raba su da yar uwarsu? Domin ta sani ne , a yanda anna ke jin zafin irin abubuwan da ake yiwa Agaishat , a yanda aba ya tasota a gaba da man bleating kan sai ta shafa ya yi ku

dinta itama , anna na neman koma waye ta bashi aurenta ta tafi ta huta, ta gwamace ta tafi ta auri koma waye da aba ya yi kudinta itama kar a je ta fada irin rayuwar da fatimata ta fada ko ma wace ta fi ta

Sai da Anna ta yi kuka mai isarta, suba bata ha

kuri kafin take share hawayenta ta yafito Bak'a sake kukan yan uwanta da mamanta na kuka

A hankali ta taso ta nufo Anna

Tunda ta taso suka sauke idannuwansu kanta

Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayyana " Eh lale baka ce, tana da baki sosai da

kuma kazanta, a rayuwar kauye dole su tsangwameta domin gari ne mai bambace bambance

Kawar da kansa ya yi, jikinsa ya yi sanyi da lamarin uwar yarinyar, tabas akoy bamban al.amari a tatare da ita, da farko ya so ya cakula abin, ya kasance an watse su yi

tafiarsu ba tare da Ayya ta kwaso masu wani jangom din ba, sai dai ina yanda matar ta yi yarensa tar tar tamkar nata, sannan ta shiga turanci tamkar yarenta shima, kuma ta furta bata san bama sunnan yaririkan da ta yi, harma ta shiga wani yannayi dan za.a

takurata da tambayoyi ya saka shi yin sanyi, a hankali ya furta" sai na san su waye ku!

Anna ta kamo hannunta ta zaunar da ita daf da daf, ta dago fuskarta, abinda bata taba yi ba irin kusancin nan da yar tata, tana so ta yi tana mugun tsoro da kuny

a

Murya a raunane ta ce" Agaishat, Ina son ki

Da sauri Agaishat ta kara kallonta,

Anna ta sakar mata murmushi ta ce" sosai, ina son ki, kuma ina so ki samu canjin rayuwa, bana so ki kare a haka bana so ki kare a ciki duhun rayuwa

Gaishat ta ce

" Anna, Anna

Anna ta kallota ta ce" menen Gaishat? Kar na raba ku da yar uwarku?

Na san muna cikin jimamin mutuwa, muna cikin rudu, aman ku kun fi kowa sannin rayuwar da muke , mutanen nan na tafia in dai ba da ita ba na yi imanin ba zai barta ba tunda

ya saka wannan lamarin a ransa sai ya aikata

Da wa zai hadata? Ina zata fada? Mai yiwuwa idan aka tsilira da ita wani wajen koda ta so guduwa ishrwa ta kasheta a hanya,

Agaishat ta fashe da kuka jikinta ya kwashi rawa ta ce" Anna aa, aa Anna, kar ki

bada ni haka Anna, ku kadai na sani Anna, kar ki raba ni da ku, kar ki yi mini haka Anna, ki barni ina ganninki har in mutu, ki barni ina gannin baba Sofona ina kai masa ruwa yana kiya mini karatu, ni ba ruwana Aba ya yi ta dukan nawa ba komi Anna in dai i

na ganninki ina gannin yan

uwanna ina gannin Baba Sofo ya isheni Anna, kar ki rabani da abinda nakeda a duniya wato ku........

To jama.a ya zama kwashe ne? ............m

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرح

من الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________

________________________

1



7



Anna zuciyarta ta yi mugun karyewa

Hawaye yana shatatar mata muryarta na rawa ta ce " Agaishat, ki yi hakuri ki bi su, ba mugaye bane

Agaishat ta buda idannuwanta da kyau ta ce" k

ina da tabacin ba mugaye bane? Kina da tabacin su din mutanen kirki ne??

Jikin Annan ya yi sanyi ta sada kanta

Gaishat dake hawaye itama ta matso ta dafa hannun Agaishat ta ce" Agaishat....

Anna ta dago ta ce" bani da tabacin halayensu, ba zan ce su

din mutanen kirki bane kuma ba zan fadi akasin hakan ba

Agaishat, ni da na haike ki, ni da na yi rainon cikinki, na haife ki , tunda kika ji na ce ki je, toh ki je din kawai....ba zaki fahimci girman maganana ba sai ranar da Allah ya nuna maki kin haihu,

soyayar dake tsakanina da ke na iya cewa ki je to ki yarda da na yi imani na barwa Allah komai ne, a nan kike ko a wani wajen dama shi ya halice ki, ko wace rayuwa zaki fuskanta shi ya kadaro maki, ni ban isa

na hana ko na saka ba sai dai na yi ta kai kuk

ana wajensa ina neman jin sanyi daga wajensa

Agaishat ta rintse idannuwanta, ita bama bin nasu ba, wannan mutumen da suke tare wanda yake tsaye tunda suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login