Showing 39001 words to 42000 words out of 86237 words

Chapter 14 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

9

sunnan da ta bari doka ke tsalake su, Wardugunma bashi da l

abari , a yanzu wajen ba.a barin yaron da bai kai 18 shiga ba, sai gaga gagan yan duniya, sannan ba abinda ba.a yi a ciki, kan masu bushe bushen su, sai masu aikata zina a fili (wa.iyazubillah) shi kansa mahaifin wardugun bai san takamaimain abinda ake aik

atawa a wajen ba, hasalima baya zama tunda abinnan ya faru da iyalansa ya ji niger din ta fice masa a rai, dan haka yake yawonsa yana kasuwancinsa a duniya, idan ya zo niger ba dan ya jima bane, koda an kawo masa korafi bai wani dubawa dan kuwa baya so ya

baiwa yan tsunguri tsoma damar kawo masa korafin gidansa,

Jikin Agaishat haka yake rawa, gannin irin abinda baba sofo ke fada mata cewar ba kyau yawo jiki a bayane haka sannan ba kyau aikata zina, Ayya ma ta yi mata fadan ko a tv ta ga sun saka mace na

namiji na rungumar juna ta canza tashar ba kyau aikata zina sannan ba kyau kallon tsiraicin wani banban zunubi ne ,

Wajen cin abinci Wardugu ya zame da su, domin daga nan du wani abin hange zai hango shi.

Suna zuwa suka zauna a tsararun kujerun wajen,

kamshi sai tashi yake, yayan sangartatu , yayan masu hannu da shuni, da kuma masu hannun da shuni, yayan talakawan da suka zabi rayuwar hutu da zama a inda Allah ya ajiye su, sai bushasha ake ana tafiyar da lamarin cikin tsarin yan gayu.....

Menu ne aka

kawo masu aka aajiye masu, nan Wardugu da kansa ke a dan duke dan kar wani ya gane shi ya dauki menu dinya kare fuskarsa da ita,

Alhinayet da gabanta ke faduwa na yannayinsa, jikinsa ya nuna ya hau, yannayinsa ya nuna ransa a bace yake,

Ta kali Mu.az

an da ya rapka tagumi bai taba Menu din ba ta kuma mayar da dubanta wajen Agaishat ta ga du a firgice take sai sada kanta take bata son kallon mutanen wajen , abin bako ne a gareta,

Hannunta ta kama ta ce" Agaishat, tashi mu je,

Ai kuwa tamkar jira t

ake ta mike ta bi bayan Alhinayettt suka fito daga dakin cin abincin suka zauna a wata farar kujera inda suka baiwa wannan lamari baya.

A hankali yake karanta menu din, harda porc, da giya kala daban daban, sannan abinda ya fi daukan hankalinsa wani abu

da aka zana fari shi kuwa aka rubuta masa kudi , shi idan dai ka dauke shi dole sai ka biya, kudi masu yawa haka,

Kiran serveuse din mai dan bingilin sket ya yi da hannunsa,

Tana zuwa tana wani irin juyi fa tafia ta karaso ,

Ta saman gilas dinsa ya

kare mata kallo, kafin yake mika mata menu din ya nuna mata abinda yake so,

Kallonsa take dan gane idan har dan hannun ne? Ko kuwa? Domin sunna taka tsantsan sosai bisa umarnin hajiarsu, dan ta fada masu au kula fa, kar su yarda wani mai bakin cikinta

ya yi masu rami su afka, domin abin nan hoda ce, hoda ta shaye shaye,

Jikin wardugu wando ne wanda ya dan dara gwuiwarsa, sai bakar riga wace bata da zanen komai a jikinta, sai hular baka itama wace bata nuna ko ta meye ba ya dorata saman gashin kansa

wanda yake da dan tsayi kadan ba dayawa irin na samarin nan dai na zamani, yannayinsa ta karewa kallo, girkeken namiji, bai yi mata kama da police ba, in ba police ba kuwa wa zai zo masu leken asiri? A tunaninta, dan haka sai ta ce" oga, ka kawo carte din

ka ko kach zaka biya?

Wardugu dake zaune a aljihunsa ba kudi, sai dai a mota, carte dinsa kuwa idan ya bada za.a iya gane ko waye shi tun kafin ta karasa wajen,

Yana tunanin mafita Mu.azam ya mita tasa carte din ta bank,

Karba ta yi ta karanta sunna

n,

Kallonsa take shima, a take ta ayannawa ranta yan hannu ne, wani lokacin likitoci na zuwa siyen abinnan su dai basu san ko me suke da shi ga,

Juyawa ta yi ta tafi dan kawowa ,

Wardugu ya hade jimkaken hannunsa da wanda yake bude ya shiga murza

su a tare,

Sannan yana kara bin wajen da mutanen wajen da kallo,

Table sun kai biyar da ya hango suna fan dukawa su ja wani abin da yake kyautata zaton hodar maye ne a saman plat dan karami mai ruwan zaiba mai shegen kyau kafin su dago su dora daga inda

suka tsaya,

Abin mamaki harda yan mata, kananun yan mata wanda a cikinsu sai ya yi rantsuwar akoy wace bata kai 18old din ba!

Wajen a da kafin ya dawo haka yake etablissement privรฉ, wanda etat gwomnati ta san da zamansa ta bada amanar a bude shi, bisa

takardun fa aka gabatar a da an gabatar ne kan irin wancen tsarin na wajen hutun yara da iyayensu ranar da ba.a karatu, aman a yanzu ta sauya zani wanda shi dai da hannunsa bai saka hannun a bude haka da shi ba,

Kansa ya girgiza, yau ko uban wa ya daure

masu zasu ci ubansu!

Dubansa ya kai waje, nan ya hangi su Alhinayet suna fan taba hira da Agaishat,

Idannuwansa ya tsaida kan Agaishat wanda bai ma san ya yi hakan ba, kallon me yake mata? Sho kansa bai sani ba ko yannayinta ne ya fi yiwa idannuwansa

dadin kallo?

Yana tsaka da kallon nan nata aka gabatar masa da harakar gabansa harda abin ja,

Ajiye carte din ta yi ta juya,

Wardugu ya dago hannunsa ya shiga dubawa da kyau, lale kwarai ita ce, ta ina? Ta ya aka yi take shigowa kasar? A ina take

samu? Ita ke oder ko mijinta ya canza yake samo mata? Wa yake basu? Ta wace hanya ake bi a kawo har nan? Ina polisawan dake bincike a bakin titi ba dare ba rana?, ina tsaron da yake takamar ya baza a sauran garuruwa ma bale a garin da yake ciki?, ya aka y

i ya yi sake haka har wannan lamarin ya cin masa da ransa da lafiarsa?

Yana tsaka da tunanin ne sai gata ta shigo,

Mace har mace, farar buzuwa mai shegen kyau, ta sha wasu mahaukatan sket da riga kanta ko dan kwali babu, ra sha wani dogon takalmi mai ts

ini, tana tare da wani balarabe ya sha jalabiyarsa hannunsa rike da makulin mota ,

Wani na biye da su da jaka baka suka shige tana dan dadagawa mutanen da sukai sabo hannu,

A hankali Wardugu ya mikowa Mu.azam ky din motar da suka zo da ita,

Murya a

bace ya ce" ka tashi ka dauki yarwn can ku koma gida, minti talatin na baku ku shige gida da abin hawan nan, ko ku je gidan su Alhinayet dan ya fi kusa da wajen nan, domin idan kame ya ritsa da ku sai kun kwana a cel!

Ido Mu.azan ya zaro, kame a karfe

uku na yama? Gashi ranar asabar ne ranar da mutane da yawa kan fita dan shakatawa, aman me ya sa zai yi kame har cikin gari bayan a cikin nan ne ake badalar?

Yar karamar wayarsa ya dauka ya dana kira,

Daga dayab bangaren aka daga ana mai fadin' Chef

๐Ÿ‘ฎ

๐Ÿป

โ€โ™‚

๏ธ

(Sir),

Wardugu ya ce" ina so yanzu ka yi kira wajen Gn na Gendaremeri, sannan ka hado min mahaukatana, ina son motoci masu yawa su cika gari, ina son mahaukatam su karaso nan Wardugu place, kana jina da kyau, polisai su kama du wani wanda ya yi

masu shige da suspect, ba zancen takardunka ko wani abin yau kamun yannayin mutun nake so a yi! Na fitar maka da iyaye mata wa.inda suka bayar da kwakwaran hujar daga inda suke, sai wa.inda suka kai yarensu wani wajen, bayan su a kama a cike mani cel!

Da a vos ordre ya amsa yana katse kiran ya mike ya shiga aikatawa ba jira,

Mu.azam mikewa ya yi da sauri ya fice ya tisa su a gaba da adu.ar Allah ya kai su inda zasu je lafia kar abin nan ya ritsa da su , duda motar Wardugu ne, da lambar shaida shi ne

, ba zai hana a bincike su ba domin matarsa ta saka ya dora dokar ko motarsa a ringa bincikawa a gari! .........

Toh fa, An tabo Wardugu, an tabo tashin hankali

๐Ÿค”

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

*BAK'A CE*

๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ

Na *SAJIDA*

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…

ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

____________________________________

*

๐ŸŒˆ

KAINUWA WRITERS

โœ

๐Ÿผ

ASSOCIATION*

๐Ÿค๐Ÿป

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_____________

_______________________

2

๏ธ

โƒฃ

6

๏ธ

โƒฃ

Bayan tafiyarsu da kamar minti ashirin, Wardugu dai na nan zaune yana bin kowa da kallo ta kafurin bakin glass dinsa,

Mintuna tsakani sai kukan jiniyar sojoji ta fara yin salama waj

en,

Da farko tunaninsu ficewa zasu yi, sai dai abin kara yi masu salama yake,

Hajia Aisata dake zaune saman cinyar karuwinta suna shagali aka dokowa waya,

Dagawa ta yi da yannayin duniyanci ta ce" Ya?

Masu tsaron kofar Wardugu Place ne daya ya yi k

iranta a tsorace ya ce" Hajia me motocin sojoji ke yi a kofar nan? Na ga sai jeruwa suke suna didirowa da alama wani suke jira,

Ai bata san lokacin da ta diro daga saman kafar mutumen ta ce" me me me ka ce? Sojoji? A nan?

Bata tsayin jin amsarsa ba

ta fito da wani irin gudu ta ce" du wanda ya san da hoda gabansa ya yi gagawar rabuwa da ita ga arnawa a kofarmu!

Nan fa wajen ya rikice, mutane du suka tsorata,

Aka fara kokarin guduwa wasu na nufar motocin su da gudun tsiya wasu na auna tsayin katan

gar sai dai ba halin dirawa domin ga tsayi ga abin kama barawa an zagaye wajen da ita,

Du masu jan mayan nan suka aniya gudu suna boyewa wasu na watsawa cikin ruwa wanda kadan ta rage masa ya janye abinsa, manya manyan masu fada a jin wajrn suka fara nufa

rta suna tambayarta me hakan ke nufi? Dama ba da lamuncewar gwamnati ta bude wajen raba masu eh yane ba? Ba wanda ya daure mata a gwamnati?!

Ita dai ta cire dogon takalmi sai bi take table table tana kara goge dan sauran hodar da wani farin tishu ita da

yarenta masu aikin wajen,

Du sun haukace sai ihu take yiwa mutane kan wa.inda tsiraicinsu ya bayanna sosai sai fadi take su yi maza su saka kayan da ya fi wannan,

Sannan da gudu wata bagwariyar yarinya ta fito da abaya ta kawo mata ta luluba mata daida

i nan tuni sojojin sun cafke masu tsaron kofar sun fara tura su cikin motar wasu kuwa na tsare masu bi ta hanyar da wa.inda ke zuwa a lokacin,

Wani sergent ne ya kali abokinsa ya ce" yau fa akoy buro.uba a wajen nan, domin lamarin na gida ne, fadan gida n

e,

Kai ya girgiza ya ce" ai ba na gida ba, ko na waye ta tarowa kanta dan oga ya yi mata tashi daya!

A guje ta karaso table din wardugu tana babala botiran rigar tana zuwa da mamaki mamaki haushi haushi ta ce" kai waye mai hular nan ne wai? Kai ana

a yi maza a kawar da komai kai kana zaune kikam , to walahi bara ku ji kaf wajen nan dan na lura hoda ta coshe tunanin ku! Du dan iskan da aka kama da ita ba ruwana, tawa kaf ta wajen nan ta bi Wc! Ta hannayen ku kuwa ban sanku bama bale na san me kuka shi

go da shi, kun kuwa san wajen da girma ba lale ne sojojin su yarda da ina iya control din kowa!

A hankali ya dago yana hangen yanda ake shan tsere da mutanen tsakar wajen fa sojoji suna yi masu cafkar fara suna yin waje da su,

Ransa ne ya kara baci ,

me ya kai su kokowa da su? Su saka lasifika su yi magana kan du dan akuyar da ya nemi gudu za.a watsa masa tire a gaz! Aman sai wani guje guje suke da juna harma su yi tunanin mu tsarensu ne!

Gilashin idonsa ya cire a hankali ya dago da jajayen idannuw

ansa ya sauke saman fuskarta , murya a dake a dage ya ce " aman kuwa da kin ci amanar clients din ki *AISATA*, na ji kuna fadin client sarki ne ke kuwa kina ikirarin ba ruwanki dan an kama shi da hoda yana zuka,

Mutuwar tsaye ne Aisata ta yi, mutanen

wajen kuwa gannin mai maganar sannan ya karasa mikewa tsaye du ya saka suka rude abinka da mai laifi suka fara neman hanyar fita,

A rikice ta nuno shi da yatsarta ta kusan baba ta ce" Wardugu? Wardugu! Wardugu,

Ya ce" ki ajiye yatsarki da nuna da

ita, ko ki hade yatsutsanki ki nuno ni da hannun baki daya, rashin tarbiya ne nuna baban mutun da yatsa Aisata!

Wani irin juya ta fara ji, hankalinta tashe ta ce" aman kai da kanka zaka tonawa wajen nan asiri? Ka fa san mamalakin wajen,

Sergent Kab

ir da ya shigo da sauri ya zo dan jin me Wardugu zai fada kiran da ya tura nasa ya ja ya tsaya ya sara masa,

Wardugu ya juyo wajensa ya ce" ankwa!

Da sauri ya mika masa, sannan ya kara ja ya kame,

A bainar jama.a Wardugu ya ja hular kansa ya cire

ya nufota ya ce" Madame *MARAHUT AISATA* iko ya kama ki bisa laifin buda gidan badala, yada mugayen ayuka a boye, da siyar da hoda a fili kuma a bayane, ki yi shiru ko dukan abinda kika fada zai yi aiki kan ki, kina da damar tsayar da lauya dan kare kan k

i ko kwato incinki.........

Yana fada ne yana sarkafa mata ankwa irin na an kamo barawo, kafi yake turata gaba da kansa ransa bace ,

Suna fitowa ya daga murya ya ce" lasifikha sergent!

Ai kuwa da gudu aka fita aka kawo masa,

Ana kawowa tuni ya

n jarida sun halarta sun fara dauka abinsu,

Wardugu na amsa daidai kunenta yana rike da ita hannunsana dama ya daga, a dake kalamai a rarabe ya ce" Duk wanda ya yi gigin guduwa daga wannan waje zai jawa kansa rigima, zamu saki batkonon tsohuwa (

๐Ÿคฃ๐Ÿคช

), ko

da kana da rashin lafia kan ka! Ku hade gaba dayanku tsakiyar wajen nan minti biyar na baku, du wanda bai zo ba tawa ce ni da shi!

Ji kake wajen ya dan lafa da iface iface, nan fa dan koke koken yan matan ya fara tashi,, wasu na dora hannayensu a kai su

na ihun sun mutu sun lalace yau asirinsu ya tonu, wasu na kaico da tunanin mai tsaya masu domin dama ba wani abin iyayensu gare su ba , irin sun samu dan masu kudi ne suka zubar da tarbiya aji daraja irin ta ya mace suke bin su ana shan kida, wasu samarin

sun sato motar gida ne an zo a more da yan mata haka ta ritsa su, wasu manyan mutane ne masu iyalai a gida suka baro suka dauko wata yar shilar suka zo a cashe, waje dai ya fara daukan kimtsi, waje ya yi tsit sai iza keyarsu ake ana waje da su,

Murya k

asa kasa Aisata ta ce" Wardugu, ka bar ni na kirayi abanka,

Bindigarsa karama ya daure a kugunsa kafin yake turata itama ya yi mota da ita,

A wannan rana Wardugu bai nufi gidan su Alhinayettt ba sai wajen karfe bakwai na dare,

Yana zuwa bai fita a

motar su ta sojoji ba kira kawai ya yi suka fito ba tare da ya yiwa kowa magana ba suka duru a motar ya ja, inda Alhinayettt ta bi su da kallo ta koma tana shan dariyar mahaifiyarta na fadin" yau fa akoyta, Alhinayettt yau ana rigima a garinnan, kina ji s

hiru ? Ba galama basu fara kade kadensu ba

Alhinayettt ta yi dariya ta ce" Anna (Matar babansu ce), ai sai adu.a kawai, Wardugu Wardugu Kowa Wardugu, ni dai zan yi ta yi masa adu.ar Allah ya tsare shi........

Gidan Ayya ya kai su, wace ke zaune tsaka

r gida da waya a hannunta sai dokawa wardugu kira take aman ba.a dagawa,

Ai tana gannin sun sauko ta nufo wajen su sai dai bai tsaya ba ya yi gagawar juyawa ya fece abinsa, domin ya sani ne yanzu har an fara zuwa wajenta, bayan ta sani shima bai isa ba

, shima yana bin dokar ne !

Gidansa ya yiwa tsinke,

Nan ya tarar da Mota uku a ciki bayan na kofa da aka hana shiga,

Mita daya dai ta mahaifiyar Walyn ce, biyun ne bai gane ba, dan haka ya shige bangarensa yana haharde kafafuwa yana so ya je ya zauna

ya kashe du wata waya dake yi masa kuka a kunne ta hana shi sakat sai doko masa kira ake shi kuwa ba wanda zai daga kiransa domin ba wanda zai saurara, ba tonon asiri ne ya yi niyar yi masu ba, ba huce haushi ne ya yi niyar yi wa mahaifinsa ko matarsa ba,

abin ne ya daje shi, ya diro masa a lokacin da bai yi tunani ba, tashin hankalinsa shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login