Showing 48001 words to 51000 words out of 86237 words
, aman ka ga yarinyata yanzu na fi ji da ita kan ku, ai ku maza ne ,
Ya yi
murmushi yana kallon yanda Ayya ke kokarin maido da Agaishat jikinta,
Cika Ayya ya yi ya ce" amini abin kauna,
Mu.azam dake danna waya yana faman blok din yarinyar nan docter, domin ta whatsup sai kuka take masa ta fame shi fa
walahi gatannan zuwa ni
geriar ta dawo da shi a yi masa aiki, ya dan dagawa Wardugu hannu,
Wardugu ya girgiza kai ya ce" tashi ka ja ku bi bayana na raka ku, aiki ne da ni fa ka sani,
Mikewa ya yi inda su Ayya ma suka fice suka nufi mota ba tare da Wardugu ya koma bangaren
walyn ba domin ya san ko ya je wata rigimar ce zasu yi dan haka ya shige dankareriyar sabuwar rangrover dinsa ya ja gaba su Mu.azam na biyr da shi a baya,
Du inda suka zo gilas kawai yake saukewa ya yi nuni fa yana tare da motar su mu.azam har suka kar
aso gidan Ayya
Wata mahaukaciyar mota fara ce fake a kofar gidan, suna karasawa mai motar da ya juya keyarsa ya juyo yana kallonsu waya a kage a kunnesa
Datijo ne dogo fari kal, cikin manyan kaya yake ya yi rawani aman ya bude habarsa,
Gabansa ne
ya yanke ya fadi gannin yaronsa cilo da ya malaka yanda ya fito daga mota ya zama cikenken namiji mai jini a hanci,
A hankali ya hango matarsa, aminiyarsa, mai kaunarsa , ta fito daga bayan motar daya ta karaso wajen wardugu,
A hankali wardugu ya ri
ke hannayenta yana dubanta cikin ido ya ce " mahaifiyata, ban kama matar Marahut dan na hada ki rigima da shi ko dan daukan fansa ba, ta cancanci kamawar ne, ina rokon ki da kar ki biyewa kowa ciki kuwa harda Marahut!
Ayya ta rike kuncinsa , ta sakar m
asa murmushi ta ce" na sani, kaida ba mace ba mai zai saka ka yi aikin mata? Na yarda da kai Wardugu, mahaifinka kai ya zo nema ba ni ba domin ya san wacece ni, ba abinda zai hada shi da ni , ka je aikinka, sai dai ina kara jadada maka ka kiyaye bakin muta
ne , ka yi aikinka domin Allah ,
Wardu ya gyada kansa ya mayar da ita mota inda tuni mai gadi ya bude mu.azam da ya sada kansa kar Aba Marahut ya gane shi ya ja motar ya shige gidan Ayya
Agaishat dake zaune gaban motar a hankali take hangen Wardugu
har ya shige tasa motar ba tare da ya nuna ya ga halitar wani a wajen ba ya tayar ya ja motarsa ya nufi wajen aiki
Murmushi marahut ya yi bayan mai gadi yana kokarin rufe gidan ya dakatar da shi ya tura ya shige daidai Ayya ta fito daga motar,
Kokar
in tafiya take domin ta ga shigowarsa sai dai me,
Muryarsa ta tsinta , muryarsa mai gigitata, a hankali cikin sanyi ya ce" *asalamu alaiki anmi Wardugu!*
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
__________
__________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
_
3
️
⃣
0
️
⃣
Dan jim Ayya ta yi, kafin take dora kafafuwanta ta fara hawa yan matatakala kwaya uku dake sadata da balbalin bangarenta,
A nitse a dake ya kuma furta" du musulmin kirki ya dace ya amsa salama koda iya
abinda zai fada kennan,
Ja Ayya ta yi ta tsaya tinawa da ta yi tare take da su Mu.azam, ko ba komai bata so yarinyar da ta dauko riko, ta dauka tamkar yarta ta cikinta ta yi wani tunani a kanta, dan haka ta ja ta tsaya ta juyo a nitse tana kallonsa ido
cikin ido ta ce" amen wa alaika salam,
A hankali ya kai hannunsa jikin karfen ginnin yana kallonta, matarsa uwar dansa, auren soyaya suka yi ba na hadi ba, auren fahimtar juna mai cike da nishadi, sai dai ya yi sake, ya yarda laifinsa ne hakan ta faru,
a hankali ya ce" wa ya baki izinin yin tafia har kasar agadez kauyen agadez timiya ? Kika je kika yi har kusan wata biyu? Anmi wardugu banda fitar ta cikin garin Niamey yanzu kuma har kin fara yin ta nesa haka? Ba dai a so zuciyata ta huta .....
Ya karash
e yana dan sada kansa,
Mamaki take, al.ajabinsa take, uhum lalema, me yake nufi da ita? Kennan yana bibiyar rayuwarta ko me?
Fuska ta yatsina kafin take fadin" gidan nan ban yarda Wardugu ya saka ko sisinsa ba dan kar watarana ka zo da takamar danka y
a gina,
Marahut ya ce" bayan Allah ya halita min ziyarta inda gonata take a duk lokacin da na yi niya?
Haushi ne ya cika Ayya, yana nufin ita, dan kuwa ai matayenku kamar gonakinku ne,
Dan juyawa ta yi ta ce" ka tarda shi inda yake ba gidana ba,
Dan daga murya Marahut ya yi , domin ta tafi ya ce" ki kiyaye fita kai sake ko dan yarmu da kika dauko kar ta koyi yawo ba izinin miji idan mun yi mata aure!
Wani irin bude kofar ta yi ta rufota da karfin gaske wanda da ba dan glas din mai nauyi kuma
mai karfi bane da kasa zai zubo baki dayansa.
Murmushi ya yi, a hankali ya sauko wajen su Mu.azam dake tsaye cirko cirko,
Mu.azam ya gama yarda wajen wa Wardugu ya yi gadon abubuwa,
Gashi mahaifinsa ya kai shekaru sitin da yan kai aman yana abubuw
a tamkar wani bajimin matashin sarki?
Yana karasowa ya saki fuskarsa sosai ya mikawa Mu.azam hannu,
A mutunce Mu.azam ya gaisar da shi,
Marahut ya amsa yana dubansa kafin yake kai dubansa wajen Agaishat, da yaren buzanci ya ce" ina murna da kasanc
ewa Abanki yarinyata,
Agaishat ta ji abin sabo, abin ya zo mata a bawai, ikon Allah, mutun ya wannan, ya kirata da yarinyarsa, gashi fari karkarkar ita kuwa baka kirin aman bai nuna kyamata ba, harma ya fada mata ya yi murnar kasancewarta yarinyarsa,
B
aki kawai ta saki tana kallon kama, kai har yannayin girman jikin domin Ayya bata da girman jiki irin wannan ,
Hannunsa da ya dora a kafadarta na dama ya ce" sannan ki yi ta kulawa da kanki ki yiwa Ayyarki biyaya, zan yi tafia sai na dawo ...........
Agaishat da wata kwallah ta tarun mata a ido tana kallo ya fice a gidan a kafarsa domin a waje ya bar motarsa,
Yana fita ta juyo wajen Mu.azam, da tsananin murna ta ce" ka ji me ya kira ni? *Yarinyarsa*,
Mu.azam na kallonta shima da murmuahin a f
uskarsa yana kallo hawayen murna ya zubo daga idannuwanta,
Cike da zumudi ta ce" kuma kuma yace ya yi murna da kasancewata tare da su, yaya Mu.azam ni *BAK'A*,
ai bai kai ga bata amsa ba ta cikashi ta shiga taka matatakalar da gudun tsiya dan zuwa fa
dawa Ayya cike da murna,
Sai dai tana shiga ta tarar da Ayya zaune ta hade rai tamkar an yi mata mutuwa, yannayinta ya nuna tana cikin yannayin bacin rai mai tsanani
A hankali ta shiga dan takawa dan karasawa kusa da Ayya,
Tana zuwa ta dan duka tan
a kallonta murya a sanyaye ta ce" Ayya, lafia?
Ayya ta dago ta yi mata wani kallo na ta barta,
Agaishat bata fahimta ba ta ce" Ayya, *WANENE WANNAN?*
Ayya ta zuba mata wani kallon, rai a hade ta ce" ki je dakinki Agaishat!
Agaishat ta mike da
sauri tana kallon Ayya kafin take juyawa da sauri ta nufi dakin nata a matukar tsorace,
Tana shiga ta karasa bakin bed ta tsaya jikinta na rawa, Ayya bata taba yi mata haka ba, dan haka hankalinta ya tashi ainun,............
Wardugu dake tsaye kan k
afafuwansa tun zuwansa wajen aiki yana fama da jama.a, tun daga manyan mutane masu fada a ji da suka biyo sahun nasu, da tsagerun mutane da suka zo belin yan uwansu ko abokai, sai bayin Allah talakawa da yayansu suka kai su inda basu taba tunani ba, suma s
un zo da kokon bararsu kuma cikin ikon Allah wardugu na sauraron mutane du wanda ya ga abin ba wani bane a nan take yake salamarsa da kwakwaran kashedin idan suka kuma hadewa a irin wannan waje ba zatai masa da kyau ba,
Daga karshe dai Wardugu na bincik
e ne cikin nutsuwa yana salamar mutanen da basa bushe bushen nan bisa kashedinsa wanda da kansa yake yiwa mutun ido da ido ba aike ba!
A hankali ya fara kawowa wajen masu zuwa dan kawai su kwale, wani saurayi aka shigo masa da shi, yana zuwa ya zube ka
sa ya shiga gaisar da Wardugu,
Warsugu dake kallonsa, kana ganninsa ka san ba wani dan mai shi bane, aman ya tashi ya saka kansa a rayuwar halaka idan an yi magana ace kadara, ace Allah ya dora,
A dake ya ce" tashi ka zauna saman kujera,
Da sauri
saurayin ya tashi ya zauna sai sasada kai yake tamkar ya yi karya gaban sarki, tsoro yake a ransa domin a gaban idonsa akaiwa wata dukan tsiya wanda ya sa har ta sume dan kirikiri ta yi ikirarin ita ko wacece ta tofar da yawu ta dura ashar ta ci alwashin g
yatiminta zai zo ya fitar da ita har sai uban gidansu Wardugu ya bata hakuri hakan ya sa su kuwa suka nuna mata da gidan maza ta shigo ba gidan yara ba, suka murza kwonji a jikinta har ta some, labarin da ya kaiwa Wardugu da ya fito a gaban mutanen nan na
cel ya zuba mata ruwa da kansa wanda hakan ya farfado da ita, sai dai tana tashi ya wanka mata wani marin da ya mayar da ita duniyar suma sannan ya nunata da yatsa ya ce" ban so tonawa kowa asiri ba shi yasa na saka aka shigarmin da iyayenku daga wancen da
kin wanda ba wanda zai gane in an shigo da kai wanene mahaifinka kuma me ka aikata ba, sai gashi kin tonawa mahaifinki asiri a matsayinsa na dan siyasa kin kama sunansa har kin nuna mana halin kodin! Dole mu kai kararki wajen alkali kin zagi soji!
Haka a
ka kwasheta aka jefata cikin cel din ya koma ya ci gaba da aikinsa dan haka ne ya sa wannan saurayin kamar ya kwonta dan kadabi,
Wardugu ya ce" yaya sunanka?
Saurayin ya kalo shi kadan ya sada kai ya ce" sunana Murtala Tasiu,
Wardugu ya gyada k
ai ya ce" tun yaushe kake zuwa wardugu place? Kai da wa kuke zuwa? A nawa kuke biyan kudin shiga? Du sati sati kuke zuwa? Da yan mata kuke zuwa?
Murtala ya ce" ba.a fi shekara biyu ba,,
Ni da dan gidan Elhaji Dahiru muke zuwa,
Aa ba kowani sati ba d
an kudin shigan da muke biya shima ba kulun yake da shi ba jika goma goma, sannan in mun shiga ga kudin kashewa , aa iya mu muke zuwa a can muke haduwa da yan mata kowani sati akoy a ciki,
Wardugu ya tsare shi da ido ya ce " tun daga bakin lokacin ka fa
ra busa kodin?
Murtala ya shiga raraba ido, ya daga hannu zai fara rantse rantse Wardugu ya ce" murtala, ka fada mini gaskiya mai yiwuwa ka samu sasauci!
Murtala ya ce" oga, ka rufa mani asiri dan girman Allah, mahaifina gajiyaye ne, sai na bi abok
in nan nawa yake bani wani dan abin na je na ciyar da mahifina da kanwata, kanwata bata gani, mahaifina kuwa ya tsufa, ba a son raina nake saka kafata wajen nan ba,
Wardugu ya ce" ban tambayeka labarinka ba Murtala, ban yi niyar wulakanta ba ina rokonka
kar ka wulakantani, kar ka
kawo mani shirme a nan , da farko dai du idan ka ga soji rikeken dan tasha ne domin tashanci koya mana ake mu shanye sai dai muna aiki da shi ne kan tsari, na jima a aikina hakan ya saka ana yi min karya nake ganewa, ka bani ams
ata ko mu baje basirar rainin hankalin ni da kai!.............
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand a
nd succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
1
️
⃣
Da sauri Murtala ya ce" Eh eh , tun daga l
okacin da muka je abokina ya siya ya saka na taba tun daga lokacin nima nake sha ,
Wardugu ya shiga gyada kai ya ce" kana iya fita,
Dan mikewa ya yi, sai ya mike sai ya dan duduka sai da wani soja ya shigo ya finciko shi ya mayar da shi cel,
Da m
ijin Auntyn walyn aka shigo,
Mutun har mutun, sai sasada kai yake na kunya,
Warsugu ya tsare da da ido, wai tun a nan duniya ka kasa hada ido da mutanen da basu baka ko cin wuni daya ba, ya zaka kare da wanda ya haliceka ya baka dukiya dan gannin ya za
ka tafiyar da ita, ya ara mata lafia, gani da ji, ya baka ikon motsi, ya baka damar magana, ya kaika kasar da ba yake yaken yu da kulun wa.inda zasu iya tayar maka da hankali , ya baka isashen lokaci dan kawai ka bauta masa ka yi masa biyaya, sai gaka tso
fai tsofai a gidan badaka tare da yar shilar yarinya ta tube kusan zindir tana maka rawa tana ciyar da kai gasashen kifi, shine zakana wani sada kai a gabana kai ga
cikenken dan iska! Du wardugu ke jifansa da wani matsiyacin kallo sannan yana ayyana du hak
a a ransa,
Wardugu ya ce" ya sunanka malan?
Mijin aunty da mamaki ya dago yana kallon wardugu ya ce" haba haba wardugu, ai ko me ake a san na gida, a fitar da na gida, ka yi hakuri kure na aikata ba zan kuma ba , ka salame ni na koma ba tare da wani
bama ya ji abin kunya ne ace ka rufe mijin kanwar babar matarka!
Baki wardugu ya dan daga na mamaki, ka ji wani dogon bayani wai mijin kanwar babar matata,
Kai ya girgiza a ransa ya yi murmushi, a fili ya kuma furta" ya sunanka malan!
Yana mai dago
wa da yanayin dakewa,
Mijin auntyn walyn nan ya fara zufa, yana gagawar magana ya ce" tototo, sunana Lawali , Elhaji lawali,
Wardugu ya ce" me ya kai ka Wardugu place? Kai da wa ka je? Me ka je yi? Tun yaushe ka fara zuwa? Me ka lura ana yi a wannan
waje?
Lawali ya ce" ni kam wannan waje na je ne bisa tsautsayi da rabon a yi, domin dai yarinyar nan na so na aura sai take shaida min na kaita mu sha iska, to da muka je shikenan sai muka mayar da wajen wajen zuwanmu lokaci zuwa lokaci yanzun dai an k
ai shekara uku,
Sannan a wannan wajen gaskiya na lura ana abubuwan da bai dace irin ahaye shaye, wannan da ka ganni tana yi wai karamin ne, eh wanda muke yi shine karamin ba Allah ja da kwana....
Ya karashe yana jinjina
Wardugu ya jinjina kai, ya ce"
lawali kada daga Kokin ne?
Da sauri ya dago yana duban wardugu, ya ce" bilahilazi ban taba ba, ai ni ko warinta na ji juwa ke kayar da ni, ka rufa mani asiri rashin jina bai kai can ba,
Wardugu ya dago yana dubansa, wai rashin jinsa, kai ya girgiza d
a hannu ya yi masa nuni da ya fita,
Yana kokarin kara magiya Marahut ya shigo inda sojan nan ya biyo bayansa yana dan kame kame ya rasa me zai yi, su dai ba wanda bai san oga Marahut mahaifin uban gidansu ba, shi ya isa ya masa iyaka ne? Tun daga babar
kofa ya samu shigowa ya ratso du zone na control ba.a hana shi ba sai shi tal dake tsaye dan kula da bude kofa da kuma rufewa da kyau ne zai hana shi shigowa?
Kallon Lawali Marahut ya yi kafin yake girgiza kai yana murmushi daga cikin rawaninsa,,
Kai
sade Lawali ya fice domin ya ji kunyarsa ainun
Marahut ya bi tsararen tankamemen office dan nasa, bMarahut ya ce" ya aka yi ka canza kanshin turarenmu ne Wardugu? Kuma ya aka yi ba hotona a office dinka bayan kai din dan halal ne koda shege ai ado yake
da ubansa bale dan halal ,
Wardugu dake ta cika takardu yana dan dana laptop bai ce da shi ci kanka ba,
Marahut ya ce" Warsugu Abanka ne fa ni ? In ba ruwanka da mutane su ga kana min haka ba ruwanka da Allah ne??
Wardugu ya ajiye biron dake hannu
nsa ya dan shafa kansa ya dago da kallonsa wajen mahaifinsa wanda a kamaninsu haske ne kadan ya dan fi shi domin farin wardugu ba irin cancan din nan bane,
Warsugu ya ce" Aban Wardugu ra.ayi ne ya sa na daina anfani da turaren da ka sanni da shi, sannan
ni ba mace bane da zan kawo hotonka