Showing 78001 words to 81000 words out of 86237 words

Chapter 27 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

11

mai girman gaske , na biyo.....

Bata kai ga karasa maganar

ba walyn ta bushe da dariya tana dubanta,

Hannunta ta nuno mata ta ce" halan saurayinki ne?

Da mamaki take duban Walyn, ashe tana jin french? Da ta zo ba yanda bata yi ba Walyn ta fahimci maganarta aman ta juye yaren tubanci ta yi ta dura mata zagi da

hannayenta kuwa ta nuna bata san yarenta ba, sannan ta daure fuska ta tsare gida ta jefa cingan a bakinta tana taunawa tana kada kafa tana chating.

Walyn bata yi kasa da gwuiwa ba ta ce" wace irin shakuwa ce tsakanin mace da namiji? Ke jiya fa aka daur

a masa aure, jiya suka je suka dauro aurensa,

Walyn! Wardugu ya fada da kakausar murya wace ta saka ta yi shiru tana binsa da kallo sai kikifta ido take uwa ta yi karya,

Kansa ya juya ya ce" ki je dakinki,

Baki ta turo gaba ta mike ta yi wata girg

iza ta juya ta nufi dakinta tana rauda jiki ita matar general,

Tunda ta fadi maganar nan, jikin Khadija ya mutu, ta sada kanta kasa, hankalinta ya gama tashi, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shine abinda take ta fada a ranta, kuka take so ta yi aman y

a ki zuwa,

Wardugu da ya dago ya yi mata kallo daya ya kawar da kansa ya ce" desoler (Sorry),

Wani abin ta hadiye da kyar kafin ta ce" ko ka san da bashi da lafia?

Wardugu ya rintse idannuwansa, ya gyada mata kai,

Ta tatara dukan kuzarinta ta

ce" Wardugu, ana iya yi masa aiki, tabas aikin na da mugun hatsari aman idan Allah ya nufa sai ka ga an dace, ana tashi sosai, wa.inda nasu ya yi mugun tsanani ma sun tashi , ka taimakeni ka saka baki ya biyoni mu je a yi masa aikin nan, bana tunanin idan

ya mace a haka zan iya wata rayuwa, Wardugu ka taimake ni,

Menene tsakaninki da shi mai girma haka? Excuse moi (excuse me), kina magana ne tamkar rayuwarsa na tafe da taki, na san ki, ya min maganarki a matsayin kawa, kawance ne ko da wata maganar? War

dugu ya fada , bai yi niyar yi mata wani kwakwaf ba, aman yannayinta ya tsorata shi, kar dai Mu.azan nada wata ya zo ya auri Agaishat?

Khadija ta sada kanta kasa ta ce" ni ke binsa yana guje min, ya fada mij zai yi aure, kennan dai auren ya yi? Meye la

ifina dan Allah ya dora min soyayarsa? Bani da ja da aurensa, bani da damuwa da matarsa, ni dai burina a yi masa aikin nan, idan da rabo ya samu tsayin rai,

Mikewa Wardugu ya yi, ya dubu wajen Tv din Walyn, kys din motarta ya dauka ya yiwa Khadija alama

da su je,

Mikewa ta yi itama gabanta na faduwa, bayansa ta bi tana tunanin ya zasu kwashe da Mu.azam? Ya zata tsinci kanta idan ta gane shi da wata? Adu.a kawai take a kasan zuciyarta, sannan miskilancin Wardugu ya sakata shiga tatayinta sosai,

Gud

u yake na balaki, jalabiyar nan ta jikinsa baka wace ta mahaukacin haska fatar jikinsa itace a jikin nasa bai canza ba, sai gajeran wandondake kasa, daga su ko yannayin gashinsa bai caje ba, fuskarsa fayau da ita ta bada wani ni.imtacen kyau du kuwa da iri

n yanda ya hade ta.

Da garajen dai ya danna cikin gidan Ayya inda ya fito da tarin balaki ya nufi wajen mai gadi domin ya bar kofar a bude, (za.a dai sauke masa fushi ne)

Nemansa yake bai ganshi ba, hakan ya sa ya dawo wajen motar inda take tsaye tan

a duban ikon Allah,

Tun shigowarsu Mu.azam yake kallonsu, domin yana kasan inuwar tsakar gidan Ayya yana ta tunanin rashin gannin Wardugu da yanda Agaishat ta kaurace masa kwata kwata bai ga fara.arta ba, danma tun dazu Alhinayett ta zo wajenta. Baii ga

fuskar Khadija ba domin ta dayan bangaren ta fito kuma ta ba inda yake baya sai lokacin da Wardugu ya karaso ya yi mata nuni da bayanta ba tare da yace da ita ci kanki ba

Juyawa ta yi, inda likaci daya Mu.azam ya mike tsaye yana zaro ido,

Da sauri ta

nufi wajensa inda shima ya tako suka hade tsakiya suna yiwa juna wani kallo mai wuyar fasara,

Hannunsa ya kai fuskarta ya shiga share mata hawayen da suka fara zaryo mata a fuskarta suna masu yiwa juna murmushi.....

Alhinayett ce ta fara fitowa, inda

hankalinta ke kan Agaishat dake biye da ita suna hira harda dariya domin Agaishat ce ke fadin" ashe itama zata ga ranar da za.a ce ta yi saurayi wai harda aure? Ashe yan birni ba haka suke ba? A kauye bata taba tunanin ko mahaukacin kauye zai kulata ba,

Dif ta yi da maganar inda idannuwanta suka sauka kan Mu.azam da wata kyakyawar mata fara kar , jikinsu tamkar zai hade, sannan sai shafa fuskarta yake kamar mai rarashinta,,

Sanye Agaishat take da atampa an yi mata dinkin riga da sket, dinkin zamani ne

ya mugun karbar jikinta ga dauri da Ayya da kanta ta caka mata mai shegen kyau,

Fuskarta ba wata kwaliya sai dan jan baki mai ruwan atampar sai annurin amarci domin amarya ko ta daji ce tana fita daban,

Sosai take fitar da kamshi mai nutsar da zuciya, a

nnuri na fita a fuskarta, idan ta yi murmushi kuwa kaima zaka tsinci kanka da yi ne dan irin murmushinsu ke saka murmushi,

Idannuwanta dara dara da su sun sha kwali, dogon hancinta ya sauka kusa da dan madaidaicin bakinta mai lebe masu santsi da kyali dom

in kida yaushe tana amfani da rob san gyaran bushewar lebe da saka su laushi da kyali,

A hankali ya dora hannayensa duka biyu saman motar ya dora kansa ya tsura mata ido,

Wani abin ya fargar da shi inda ya yi saurin watsakewa ya juya da sauri ya nufi w

ajen garden,

Sai a lokacin Mu.azam ya ankara da su Agaishat, shi din ma gabansa ne ya fadi, inda har ya ji kafarsa na dan rawa, aman ya dake ya kama hannun Khadija suka suka nufi wajen su Agaishat........



👏🏻

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of re

aders}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

4





7





Yana karasawa ya dan fara kame kame yana dan susar kai, da kyar ya iya sakin murmushi yana duban Agaishat ya

ce" wife, ga Khadija, khadija ga matata.

Kanta ta juyo daga duban su Agaishat ta sauke kwayar idannuwanta cikin nasa, wanda ya ki bari su hada idon ya kawar da nasa wajen Agasihat wace itama su kawai take kallo inda ta ji wani irin faduwar gaba,

Khad

ija ta yi iya yinta ta karasa kusa da Agaishat da Alhinayett ta mika masu hannu tana sakin murmushin yake ta ce" asalamu alaikum,

Hannu Alhinayett ta fara bata tana mai amsa salamarta suka gaisa, hakama Agaishat wace Khadija ta ji hannunta wani irin lau

shi (toh ba dole ba, tunda ta zo Ayya ke tsaye kan du wata gaba ta jikinta , jiki kuwa na samun gyara nan da nan yake hadewa ya yi cas), ta yi mamakin irin kaushin hannunta duda ta tarar da ita a gidan su Wardugu,

Daga nan dugunzuma suka yi cikin falon A

yya inda Agaishat ta haye dan kanta ke sara mata, ita ta kasa gane wacece kuma tare da mijin da aka aura mata jiya? Sai a lokacin ta mike zaune daga saman bed dinta ta nufi wajen window ta daga labule dan gannin ina ya je? Ina ya tafi ne? Ta ganshi harma s

un yi ido hudu inda ta yi masa murmushi shi kuwa ya hade fuska, daga nan bata san ina ya nufa ba, aman motarsa na nan wajen hakan na nufin yana gidan.

Tunda ya je ya ja ya tsaya waje guda yana duban yanda lambun yake da irin sanyayan sanyin dake tashi a

ciki ya afka tunani, tambaya daya ya yiwa kansa wace ta saka kansa sarawa, idannuwansa ya lumshe ya dubi hannunsa a ransa ya shiga yiwa kansa fada kamar haka" ba kanka farau ba, da yawa sun rasa sun ci gaba da rayuwa, dole ya girgizaka domin kaima mutun n

e mai rai da lafia mai zuciya mai motsi, aman kuna yarda da wannan jarabawa zai kara daukaka darajarka a wajen ubangijinka, kai ba kowa bane face dan adam da Allah subahanahu wata ala kan jarabta a rayuwar yau da kulun, dan ka shiga hali na jarabawar rayuw

a ka aminta shine cika namiji,

Murmushi mai ciwo ya yi a fili ya ce" Wardugu, ? Kana bata time dinka bayan wannan baya cikin tsarin rayuwarka! ........

Zai ci gaba da yiwa kansa magana yar wayar da baima yi tunanin ya dauko ba ta dauki tsuwa a hankali

tana kidan nan na sojoji tamkar ana harba bindiga,

Shiru ya yi da maganar ya tamke fuska bai dauki wayar ba , bai kuma ci gaba da magangannun da yake ba,

Ya kai sau biyar ana kiran wayar dan haka ya saka hannunsa ya cirota ya duba sunnan,

WALYN,

Dagawa ya yi ya kara a kunnensa yana sauraro,

Asalamu alaikum General, docter Sagir Sulaiman ne, an kawo matarka emergency minti sha biyar da suka shige ne, yanzu da muka dan daidaita lamarin ne ta bamu wayar dan mu yi kiranka,

A dake ya ce" wani asi

biti?

Likitan ya ce" dan clinique dan gawo ne domin a inda ta samu hatsarin nan ne mafi kusanci da ita.

Katse kiran ya yi bai bashi amsa ba ya saka hannunsa cikin gashin kansa ya yamutsa ,

Juyawa ya yi da tafiyarsa mai kama da yana sauri aman a gad

arance ya nufi cikin gidansu wajen Ayya,

Tunda ya nufo wajen ta tsura masa ido, kallonsa take tana murmushin da bata san na meye ba,

Dan yatsanta ta nuna inda yake zuwa ta ce" ban taba gannin mutun mai rihima irin dan Ayya ba, ya san kan rigima, ko da

n Allah ya bashi dama ne? Wannan mutumen idan kokowa ta hadaka da shi ba zan so ganninka a karshe ba,

Dan bakinta ta murguda ta ce" ke Agaishat kin manta karfi daga zuciya ne?

Juyawa ta yi wajen madubi tana kallon kanta, a fili ta ce" nima mai karfi ce

!

Yana shiga falon ya tarar da su Mu.azam da Ayya da Khadija dake zaune zuru Ayya fuskarta a dan hade ba kamar kowani lokaci ba,

Tana ganninsa ta bala masa harara ta kauda kanta,

Murmushi ya yi a fili ya zauna yana duban Alhinayett dake son karant

ar yanayinsa, ya maida dubansa wajen Mu.azam,

Murmushi ya sakar masa sannan da ido ya yi masa maganar da shi kawai ya gane,

Mikewa ya yi ya bi bayan Ayya da ta mike ta yi sama dan ya san tana son ganinsa ne aman ba zata fada ba a gaban mutane

Yana s

higa ta mike da zafi zafi tamkar zata wanke shi da mari ta ja tunga gabansa ta ce" kai! , kai! Ka fita a idona na rufe! Kai Wardugu na fika danyen kai, yanzu dan raini ka zo na baka damar zuwa daurowa yarinya aure ka dawo dan bahagumen tunani ba zaka zo ka

fada min ya aka yi ba? Sannan yau ya shigo min da zankadediyar budurwa ya fada min aminiyarsa ce? Ohk tare kuke amintar kai da shi da yan matan ko? Ba zai yiwu ba, ba zan bashi y'ata a wannan halin ya je min da ita wata uwa duniyar ba, ba zan lamunci ya d

auki y'ar amana ya tafi nesa da ita ba, wannan yarinyar tamkar marainiya take nesa da iyayenta, nice uwarta nice ubanta, kuma ina son abina, Wardugu ba zan lamunci shashancin nan ba!

A hankali ya ja hannunta har bakin gado ya zaunar da ita, idannuwansa

sun kade sun masa ja, ya kamo hannun nata ya ce" *Ayya, a cikin gidan duniya, lungu lungu, ba inda kafata ba zata shigaba dan gannin halin da take ciki, ba zan lamunci ko kuda ya yi mata ilah ba!*

Da mamaki take dubansa, yannayin yanda ya yi maganar ha

r wata jijiya a gaban goshinsa take motsawa irin magana ne yake da zuciyarsa da gangar jikinsa,

Mikewa ya yi ya yi taku biyu zuwa uku ya dawo yana mai yamutsa gashin kansa ya zauna ya ce" Mu.azam bashi da lafia, wannan aminiyarsa ce mafi kusanci da shi,

ta zo min da maganar tana so a yi masa aiki wanda idan Allah ya taimake mu aka dace zai tashi, Ayya na roke ki, ki saki ranki, ki yiwa dukan lamarinnan kyakyawan gani, ki bashi matarsa su tafi,

Galala take dubansa har ya karasa maganar ya mike ya nufi

fita,

Kuma juyowa ya yi ya ce" Walyn ce ta ba lafia, zan je clinik

Damuwarta ta nuna da yi masa adu.a, taso ma binsa aman ya nuna ta yi zamanta dan yayi imanin in dai Walyn na cikin hayacinta sai ta batawa mahaifiyarsa duda tana boyewa shi ai ba maka

ho bane,

Yana fitowa ya tsurawa kofar Agaishat ido, wani abin na tunzura shi ya je wani na hana shi,

A hankali ya taka ya je kofar dakin ya tsaya,

Hannunsa ya dora saman abin budewar ya lumshe ido,

Da sauri ya saki ya juya sai dai me Alhinayett ce

tsaye, bai san lokacin da ta hayo ba, bai san ko tun fitowarsa take wajen ba, idannuwansa sun rufe,

Hade fuska ya yi tam irin karma ta ga fuska ta kawo masa raini,

Rabata ya yi ya fice ya sauka kasa inda ta bi shi da wani irin kallo,

Hannayenta biyu

ta dora saman kanta, ta shiga girgiza kai da yaren buzanci ta ce" na shiga uku Nauyin baki ya saka aminina tafka barna, Wardugu me ka aikata haka?

Tura kofar Agaishat ta yi ta shiga da salama,

Agaishat dake kwonce saman bed ta mirgino tana amsawa da

murmushi shinfide a fuskarta tana duban Alhinayett,

A nitse Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat inda ta mike zaune tana duban yannayinta,

Hannayenta Alhinayett ta kamo tana dubanta cikin yaren buzanci ta ce" Tarhanine (masoyiya), ina son mu yi ma

gana da ke.

Agaishat ta bata hankalinta sosai ,

Alhinayett ta ce" ban taba aure ba, aman a islamiya an fada mana irin girma da darajar aure da kuma girman ikon miji a kan mata,

Sunna ce ta ma.aiki, daga lokacin da aka daura aurenki maganar mijinku t

a fi iko kanki fiye da ta iyayenki, kin ga kuwa banban nauyi ne da bawa zai kasa rintsawa idan ya tuna,

A yanzu ba maganar kina sonsa ko bakya sonsa, ba maganar ke wata ce ko wani ya tsaya maki, in dai mace na tsoron haduwarta da ubangiji to ya zama dole

ta gane itace karama mijinta ne baba, ta yi masa biyaya.

Agaishat, ki yiwa Mu.azam biyaya, kin samu tarbiya domin zaman da nayi da ke na dan lokaci jifa jifa ban ga rawar kai , tsayaya a tare da ke ba, zan so mijin aurenki ya yabe ki, ki ci gaba da girmam

a Ayya domin uwace a gare ki, ki nuna mata hankalinki ya kwonta da auren ko natama zai kwonta, kar ki tsananta bincike Agaishat, ke dai ki yi ta rokon Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi,

Tunda ta fara Agaishat kallonta take, ita sai yanzuma tsoro ya

shigeta, aure, aure, bautar Allah, sunnar ma.aiki, da tana tunanin ta yi nisa da iyayenta a hankali hankalinta ya kwonta da su Ayay harma ta samu gurbi mai girma ta basu a zuciyarta, aman yanzu gashi an mata aure? Kuma bama a kasar zasu zauna da mijin ba

domin Mu.azam na shirye shiryen su daga da Agaishat ne?

Hannayen Alhinayett ta damke tana dubanta ta ce" *ina jin tsoro, bana son barin su*,

A hankali ta dora kanta saman cinyar Alhinayett inda ita kuwa take dan bubuga bayanta alamar rarashi

Yana z

uwa kai tsaye office din likitan ya je, wanda ya tataba za.a mika takardun matarsa can ne dan hatsari ne

Gaisawa suka yi inda likitan ya nuna masa wajen zama,

Labarin lokaci da yannayin da aka kawota ya bashi, inda ya ce" tanada shigar yaron ciki ne

kuma ta karya da cokacola mai karfi bata ci komai bayan hakan ba,

Shi ya hadasa mata ciwon ciki mai tsanani ko nace mara hakan ya saka gudan jinin ya shiga barazanar zubewa, tana cikin wannan halin ta samu hatsarin domin ciwon ya girmami nutsuwarta,

A

hankali ya dago da idannuwansa ya sauke kan doctern, idannuwansa ya lumshe yana jin wani irin dadi na ratsa shi, ciki, a daidai lokacin da ya rasa wani abin ya samu wani,

Murya a kausashe ya ce" *Cikina, ba abinda ya samu cikina?*

To fa

😔

😔😔

, na zama raguwa, tun safe nake tsakurar rubutun nan

😔😔😔😔😔😢😢😢😢😢😢😢

🐫🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫🐫

Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login