Showing 6001 words to 9000 words out of 86237 words
ta dirzar wankin yan matan gidan harda na su kanenta ita dai burinta idan sun tashi su bata konce, ta kuma kallon mahaifinta dake kokarin shi dole sai ya yi mata wayo, wai wani harda
cewa wai ya siyar masu kadara, shi? Kudin aurwnsu bai taba wata a hannunsa ba komin yawansu zai kashe su ne ya dawo talakansa marar mutunci, yan yatsunta biyu ta hade ta yi tap tap da su suka bada dan sauti kafin ta ce" ka kirga kudi, ina so ka bawa Anna
kudi har million shida a cikin kudin da ka karba na auren mu domin na sani cinikinmu kake tamkar abin siyarwa baka amsan kasa da goma, ka bamu shida mu je birni tare da Anna mu siyo kaya mu dawo idan baka yi haka ba zan shiga duniya na saka ka a matsala ka
i da wanda ya kawo kudin aurena, ka san ni horonka ce
Yana tsaye bami bude har ta fice a gidan, kallonsa ya dawo wajen Anna, da sauri ya karaso ya ce" kina jinta kika yi tamkar baki gani bayan kin san tana jin nauyin zuciyarki? Ko ke kika kitsa mata a
taru a cuce ni? Har million shida? Ai kudin sun kusa karewa idan na baku haka!
Bata bashi amsa ba ta ci gaba da dakanta , nan ya juya wajen Agaishat ya ga shi take kallo
Ke dan ubanki daina kallona da wasu tula tulan idannuwanki masu kama da na mayu
, shegiya da aka kwaso cikin ki a waje aka yayaba min, dan bakin jini ko almajiri na yiwa tayi guduwa yake, zan zo in kwakwale miki idannuwan nan in baki a hannayen ki ki je ki kaiwa tsohon dan iskan nan da kike zuwa kina wuni wajen shi wama ya san ko me y
ake maki a bukar nan
Da sauri Annan ta juyo wajen shi, ta kai dubanta wajen Agaishat da ta sada kanta jikinta na bari, tausayin yarinyar ya kara dirar mata, nan ta kara gane shi ya sa idan ta fice take cika dare dan kar ta hadu da mutumin dake mahaifint
a aman ya zamo makiyinta , ta rasa da wata kalma zata kirayi mutumin dake miji a gareta, ta san ya yi karatu, sai dai son kudinsa ya fi imaninsa yawa
A hankali ta ce" ki je kawai zan idasa maki aikin
Da sauri ta ajiye wankin ta warware mayafinta na b
akin turkudi butubutu da shi ta yane jikinta gaba daya ta fice har tana hardewa tana waiwayen gidan nasa
Bakin wata bishiyar mangwaro ta zauna ta fashe da wani matsanancin kuka mai karfin gaske
Ku mu je a labarin Bak'a ce na saji
da
๐ซ๐ซ๐ซ
*BAK'A CE*
๐ซ๐ซ๐ซ
Na *SAJIDA*
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*
____________________________________
*
๐
KAINUWA WRITERS
โ
๐ผ
ASSOCIATION*
๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind
of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
6
โฃ
Kuka take tana murza goshinta a kan cinyarta dake lulube da turkudi, hawayen nan ya jika tur
kudin ya yayakune sannan ya gogun mata a fuska ya kara rinar da fuskar ya kasance wani waje ya fi wani wajen duhu sosai fuskar du ta yi jirwayi da ita
Sai da ta ci kukanta har kanta ya fara ciwo kafin take yin shiru, mangwaron nan ta kuma kallo gannin d
u ya yi jajajir ya nuna ya saka ta mike ta gyara zaninta da kyau ta kama kokarin hawa ,
Da kyar ta hau bakibakin ta kamo wa.inda ke kusa ta tsintsinka ta diro ta zauna nan tana gogewa da hannunta sai kuma ta sha abinta, yau bama zata iya zuwa wajen tsoho
ba ta san yana da ruwa goronsa kuwa ta kai masa gobe sai ta yi safiya ta je wajen shi
Wardugu, yanzu yanzu?
Kansa ya dafe ya ce" Ayya ko kin fasa tafiyar ne?
Da sauri ta mike ta nufi dakinta tana dafe kanta, yaron nan akoy kagauta
, bashi da hakuri yanzu in ba rigima ba a kai tsayen nan ya zo yace su yi tafiyar da a yanda ake bata labari garin can cikin jeji ne? Aman ba komai irin yanda take mafarkin mutumin nan abin ya tsaye mata a rai, tana tune sun yi da shi idan yaro ya samu la
fiya sai ta bashi salama da abinda ya sawaka sai dai ta zo tana yiwa Wardugu magani da magungunnan aka tashe su daga garin aka maido su Capital tun daga shi bata kara ganninsa ba domin ta neme shi sosai, sai kwanan nan take jin lanarin yanzu tsufa ya kama
shi sosai baya yawo yana garinsa na haihuwa harma an fada mata sunnan garin , tana son sauke nauyi domin kuwa tun daga kan maganin wajensa Allah ya aminta wardugu bai kuma Huka ba sai tana gannin haki ne ta je ta sauke ba wanda ya san gawar fari
Nade ta
fito da lifaya mai ruwan ja da kyalkyalin zaiba, lifayar sai baza kanshi take , Ayya ta kwana biyu a duniya aman karshe ce, akoy iya ado da sannin hakin turare, idan ka ganta sai ta birge ka gata da saka zinare tamkar ba da kudi take siya ba, danta ya ba
ta damar murza mulkin da ta ga dama
Tafiyar manya ba.a kwasan tufafi, mai aikinta baturiya ce ta fito da wata yar valise (yar akwati) yar karama wace a ciki ta saka du wani abin bukatarta ta nufi kofa dan kaiwa cikin mota
Gaba ya yi yana amsa waya da
aminiyarsa, kawarsa, wace du duniya itace babar kawarsa sai wa.inda ba za.a rasa ba, itace
basa fada, ta iya tafiyar da lamarinsa ta iya zama da shi , sannan du irin yanda ya ki jinnin jajayen buzaye ita wannan baya iya kyamatarta , ba.a shaifar mutun ama
n shi zai bigi kirji da halayen *ALHINAYETT*
Kana nufin yanzu yanzu? Bama zan yi maku bankwana ba?
Wardugu ya ce" Alhinayettt bafa wani jimawa zamu yi ba, ke dai ki yi mana adu.a
Yana fadin haka daidai yana zama cikin motar Hilux tamkar wani daki t
ana fa fadin waje,
Sai fa ya gama wayar ya dubo AYYA da ta tsura masa ido
Kallonta yake da alamar mamakin kallon domin irin kallon nan ne na tsare mutun idan ya yi karya
Bakinta ta dan turo ta ce" kuma ka ce ba budurwarka bace, mutunci ne bakwa w
ata soyaya da ita,
Murmushi ya yi do.in daman ya saka a ransa wannan ne, ya dan sasauto ya riko hannunta ya ce" Anna, aa, Alhinayett aminiyata ce, wace bani da amini ko aminiyar da ta kai ta
Yatsina fuska ta yi ta ce" karyar banza wai aminci mace d
a namiji ? Ai ba shi sai idan soyaya ake
Kawar da kansa ya yi ya ce" kin ce a lokacin da ya baki magungunnan da aka dura min ma tsofo ne, kuma har yanzu kina da tabacin yana raye? Ni din ma fa na jima a duniya
Murmushi ta saki ta mika hannayenta ma
su saye da zobunnan zinariya ta dankwashe masa kansa dan ta san yana so ta yi zuciya ne ita kuwa ba zata yi ba, halayensa tana gannin sai dai ta fada masa domin tun bai san kansa take tafe da shi ba
Sun Dauki hanyar airport dan zuwa garin Agadez daga n
an kuma ya nemi abinda zai kai su garin da suka nufa
Mali yaro ne ke wasa a wajen auren kawar Walyn ,
Tunda ta shigo wajen wasan yake kofata da kiran General wande, Walyn kin fice yaro (Matar general),
Tunda ta nemi wajen da tana iya gannin kowa kow
a na iya ganninta ta hakimce ta dauki kafa daya ta dora saman daya, ta karkace kadan ya kasance dankareriyar sarkarta ta zinari ta fito sosai, ta dora hannunta guda saman cinyarta awarwarayenta ma suka fito radau da su, takan dan saki dan murmushi hakoran
makarta su bayanna, ta dan juya ta kuma juyar da kanta tana karewa mata da yan matan wajen kallo tana auna su daya bayan daya,
Kari ake masa na hauka aman hankalinsa du ya karkata kanta, ya sani ne udan ta zuge bakin wannan jakar nata mai shegen
kyau sai
ya yi kwasa, jakar a yashe take kusa da kafarta tamkar ba komai na anfani ciki bayan kuwa a cikinta kudane da dankara dankaran wayoyinta na kece raini
A haka har aka fito daga salar isha.i bata mike ta je ta yi sallar ba suna zaune sun zagaye mawakin da
yakan silalewa ya bar yaransa da basu san ciwon kansu suma ba ya je ya gabatar da sallah ya dawo ya dora daga inda ya tsaya
Wannan dawowar da ya yi bai zame ko.ina ba sai gabanta domin ya lura yau yan mulkin ne, yan na isan ne, tana son nuna bambanci t
sakaninta da sautan matan wajen,
Yana zuwa ya shiga kodata, yana waketa, yana wake jarumtar mijinta
Kanta ya fashe , ya yi gingirigin
Ai kuwa ta dauki jakar nan ta yage bakinta ta shiga zuba masa masu aku wato jika goma goma tana dangalar masa tana y
i irin bata san ciwonsu ba sai da ta karar da jimki biyu wajen ya cika da ihu wata kawarta guda na daukanta vidio dan ta tura mata
A wannan rana an jima ana wasa wanda Walyn bata bar wajen wasan nan ba sai da aka gama sai da ta ga karyar ko wace yar karya
kafin take mikewa ta dauki jakarta kawayenta masu mata fada suka biyo bayanta har sai da ta shige dankareriyar bakar motarta bayan ta wankesu suma da kudi ta tayar ta halba bakin titi a lokacin har karfe goma sha daya ta buga na dare
Garin niamey capit
al ta niger du wanda ya taba shigota ya san gari ne dake baje ta ko.ina da polisai
Basa wasa kame suke tun karfin su, in dai ka kuskura ka taka doka toh fa zasu damke ka ne ba sasauci
Tukinta take cikin nutsuwa,
Danja ce ta tsayar da ita bakin inda po
lisai shida ke tsaye suna duba takardun mota na mashin, da kuma takardar shedan kai wanene
Hankalinta konce take jira danja ta saki domin ta san sun san number motar general ko sun kurbi giyar bera ba zasu tunkareta ba koda kuwa ta taka dokar domin ta ts
ira tunda ta hau motar *DOKA* gabadaya
Kwonkwonkwon karar kwonkwasa motarta,
Da mamaki ta dubi wajen
Wani saurayin police ne fuskarsa daure tamau ba alamun wasa a tatare da shi
Da yannayin rashin mutunci ta sauke gilashin motar ta sauke masa idan
nuwanta masu nuni da baka da wayo
Shima fuska a daure ya ce" madame vous etes en รฉtat d'arrestation, veillez sortir calmement nous nous occuperont de la voiture (Madame mun kama ki ki fito cikin nutsuwa zamu kula da motar)
Da mamaki take yi masa ka
llon sakarai, baki bude ta nuno shi da yatsarta ta ce" kai aman kai sabo ne ko? Waye kai? Ka san ko wacece ni?
Sadowa ya yi sosai ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" eh mun san ko ke wacece, umarnin mijinki ne in dai kika kai karfe bakwai a gari du wa
nda ya hadu da ke ya kai ki cel ki kwana da safe karfe goma a sake ki daidai gari ya cika kuma a rubuta a jarida!
Dum dum dum take jin maganar tamkar saukar aradu, quoi? (What), ita? A cel? Prison! Ita Walyn? Wardugu wardugu ta fada tun karfinta tana du
kan sitiyarin motar ta .........
Ohk
๐ซ๐ซ๐ซ
*BAK'A CE*
๐ซ๐ซ๐ซ
Na *SAJIDA*
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*
____________________________________
*
๐
KAINUWA WRITERS
โ
๐ผ
ASSOCIATION*
๐ค๐ป
```{United w
e stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
7
โฃ
Ita Wardugu xai yiwa wannan wula
kancin? Ta kwana a cikin kaso, batai sata batai komai ba? Dan kawai ta cika dare?
Wayarta ta warta a cikin jakarta ta shiga laluben numbersa wace ta sam zata same shi
Ta yi kira ya fi a kirga daidai lokacin polisawan sun zagayeta tamkar dai ta yi wa
ni gagarumin laifi
Hanjaki kwonce ya daga domin lokacin yana hakimce kan gadon hotel din da ya sauka ita Ayya tana can gidan sarkin Agadez matarsa uwar gidan ce kawarta ta kusa sosai, shi kuwa ya ki sauka a nan ya je hotel , bayan ya gama harkar kasuwan
cinsa ne kiran Walyn ya shigo wayarsa, domin Wardugu na sana.a.o.i ya san dadin nema , yakan ce ba dole ya nema ba shi mai Ayya da Walyn
Murya irin ta yan duniya ya ce" adibinira (wato matata ) (readers kar ku manta a wannan nvel yare hudu ne, buzanci,
tubanci, french da kuma hausa )
Murya ta sasauta tana tura hannunta cikin kannanuwan kitson da ta sha domin dai tubawa basa wasa da kitso ta ce" Haba mijina ya haka wannan tsatsauran hukuncin?
Murmushi ya yi jin yanda ta sasauto, kennan dai sai yan
zu ta nufi gida ko? Muryarsa yanda take ya ce" hukuncin ya yi tsauri ne? Ko bai kai daidai da laifinki ba?
Idannuwanta ta lunshe tana jinsa har cikin ranta ta ce" matarka guda a prison? Ko laifi na yi ina tunanin na fi karfin nan sai dai ka hukunta ni a
gida a dakin mu a saman gadon barcin mu ka rungumeni ka matseni ka haukatani da lamuranka , na san ina cika dare kuma baka so aman mutun ai ajizi ne, ka yi mini uzuri Wardugu
Murmushi mai sauti ya sakar mata, ya ce" bara dai mu gwada wannan idan ya so
na dawo daga tafiar da baki tsaya kin ji ina zan je me zan je yi ba zamu yi magana
Fashe masa ta yi da kukan kisa , ta ci gaba da lalaba shi dan ya yarda ya yi masu magana su sakar mata hanya ta karasa gida dare na yi
Lumfashi ya sauke ya ce" ki bani
daya daga cikin su
Cike da murna ta mikawa wanda ya fi kusa da ita tana zabga masa harara
Yana kara wayar ya kame yana sara masa tamkar yana gabansa
Murya a kausashe ya ce" wasu sutura ne a jikin matata?
Murya a ladafce ya ce" aa oga, mu mun i
sa mu kali matarka? Bamu kala ba bamu san irin suturar jikinta ba
A ransa ya ayana han, kafin yake cewa" idan ta ki ta fito ku zauna da ita a nan har safiya ta yi , har karfe goma sha biyu na rana kowa ya kasance ya ganta, sannan ku gayaci jarida ku
bad
a cikaken labarin abinda ya faru, kar ku taba jikinta aman bata wahala, ka rike wayarta a hannunka sai goben ka bata! Sannan kar ku nuna mata wasa idan ta so kawo maku tsayaya ku tsoratata da bindiga
Da " a vos ordres ya amsa kafin yake katse layin ya s
aka a aljihun rigarsa
Wa ya ga zafi biyu
๐คฃ
Karfe uku ne fa na dare aman ji kake gam gam gam ana dukan yar kofar gidan nasa
Da sauri *Tibillal* wato mahaifiyar su Agaishat mata a wajen *ALGABIT* mahaifin su Gaishat ta zabura ta kai dubanta waj
en *AGAISHAT* dake zaune tsuru tun bugawar farko ta fara tana kallon kofar shigowar su
Mayafinta ta ja da kyau ta fito ta nufi dakin mijin nata
Tana zuwa ta tarar da shi a kwonce tamkar mai baci bayan ya farka ya yi tsuru daga kwoncen yana tsoron mik
ewa ma
Girgiza kafafuwansa ta fara ta ce" Algabit, Algabitt, ka tashi ana ta buga gidan nan
Hannunsa ya saka ya bige nata ya ce" naki na tashin, bayan a gari an san na amshi kudin auren yaranna , in na bude wani mugu ne fa? Koma waye ya yi hakurin sa
fe mana aman a wannan tsofon daren? Ba zan bude ba!
Gannin ya tashi sai balbaleta yake da fadan da hujojinsa na karya ta mike ta nufi kofar wanda ya saka ya hantsilo ya rarumi wukarsa ya ja tunga yana fadin" kar ki bude mana, koma waye a daren nan ba ba
kon alkhairi bane!
Janye sakatar ta yi ta bude kofar,
Fado mata ta yi a jiki tana kuka, jikinta du sai rawa yake, ga sanyin garin aman wata yar ficiciyar riga ce a jikinta, mutumin da ya kawota a rakumi ne ya ce" na ga gidan zan dawo da safe a bani
salamata!
Da tashin hankali Anna ta janyota cikin gidan tana ta kokarin kara dagota tana duba fuskarta dake da balshe ko.ina a tsannanin tashin hankali ta ce" *FATIMATA* fatimata , fatimata
Gaba daya mutanen gidan suka fito jin muryar Anna cikin ta
shin hankali
Da sauri Algabitt ya karaso ya janyota ya ce" Ke Fatimata, meye haka? Daga ina kike? Ya haka a tsiyace jiki a lalace? Ina mijin naki yake????
Dago kumburanrun idannuwanta ta yi ta sauke su kansa, da haushi haushi ta budi baki tun karfint
a ta ce"'""" Aba, sai na kashe shi, kuma ko zaka kashe ni sai na hana ka kara bada kannuna a irin